Showing 30001 words to 33000 words out of 249515 words

Chapter 11 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1504

tukunna a ina ma za su hadu da Musharraf ya amshi abincin, ko tambayarsa ma fa bata yi ba ta fito daga gida, sannan bata ma san maganin da zata siyo masa ba tunda bai gaya mata ba, Tana kokarin dialing numbersa sai ga kiransa ya shigo wayarta ta daga ta kai kunne, yace "Where are you?" Tace "Yanzu na fito eatry, wani Drugs zan siya maka?" Nan ya gaya mata drugs da zata siyo tace "Toh, amma ta yaya za a kai maka abincin da maganin? Dispatch rider?" Musharraf yayi shiru jin abinda tace, jin shirun yayi yawa tace "Hello?" Yace "Dispatch ridern zaki ba abincin da zan ci?" Ta ɗan hade rai tace "To ya za mu yi, do u have the strength to drive ka fito ka amsa?" A takaice yace "I don't have" Tace "To ai ni ban san inda kake ba, and beside i can't say...." Ya katse ta yace "I will send u d address of my location" ta buda ido da mamaki tace "Sae na je har can kake nufi?" Shiru yayi, cike da damuwa tace "Am i suppose to come to ur location?" A hankali yace "Toh shikenan ki samu dispatch rider din ki basa magungunan kadai ya kawo min" tace "Abincin fa?" Yace "Bazan ci ba, it is not proper for a dispatcher to deliver my food" Tayi shirun few seconds, a ranta kuwa tunani take, how is it wrong for a dispatcher to deliver someone's food? a hankali tace "Let me get the drugs, sai ka turo min address din location din naka, ina isowa unguwan sai ka fito ka amsa" Yace "Alright tnx" Katse wayar tayi, ta nemi nearest pharmacy ta siya masa magungunan da ya gaya mata, tun kan ta fito pharmacy din address dinsa ya shigo wayarta, bayan ta fito ta samu adaidaita sahu ta gaya masa inda zata sannan ta shiga, nan kuma gabanta ya dinga faduwa, what if ta hadu da any of her family members or relatives? tunanin hakan yasa gabanta ya tsananta faduwa and she became so uncomfortable, sae kusan biyar da minti talatin da biyar suka isa layin, mai adaidaitan yace "Nan ne unguwar Hajiya" Mayraah dake ta bin unguwan that is so quiet da kallo tace "Pls kayi hakuri yanzu zan mika sakon nan sai ka maida ni, ban ga alamar zan samu adaidaita sahu a nan ba" Yace "To, amma kiyi sauri kinga yayyafi ake" tace "To Nagode" Da sauri ta shiga dialing number Musharraf, yana fara ring ya daga, tace "I am at the street, ka fito ka amsa pls, mai adaidaita sahu yana jirana kar mu bata masa lokaci kaga an fara yayyafi" Musharraf yace "Ki basa kudinsa, zan ajiye ki gida" Ta wani zaro ido tace "I don't understand? Kai da baka da lafiya, pls i am going back together with the Tricycle" Yace "I will try and take you back Mayraah, bana son ruwan nan ya taba ki" Ta sauka daga cikin adaidaita sahun don she is not comfortable making call in front of the owner, A bit worried tace "Don girman Allah ka fito ka amshi abincin nan da magani in koma gida, wllh ce ma Ammi nayi zanje gidansu Hamida, da kyar fa ta bar ni, don Allah ni dai tsoro nake ji kar ayi finding out inda na je kayi hakuri ka zo ka amshi abincin in wuce gidanmu" Musharraf yace "Mayraah..." Kamar zata yi kuka tace "Ina ji" Yace "Ki sallami mai tricycle din nan nace, ba ni nace zan ajiye ki gida ba?" Tace "Am sorry I can't, kayi hakuri ka fito ka amshi abincinka in koma gida" Yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, ta koma gun mai adaidaita sahun tana basa hakuri, tana ta tsaye jikin tricycle din duk da yayyafi da ake ba me yawa ba, sae ga Musharraf ya fito daga gate din dake opposite dinta, ita bata ma san nan ne gidan ba kawai sun tsaya ne ita da ɗan sahun, tun da ya fito take kallonsa, bata taɓa sanin he is this vast and broad ba sai yau, ko don bata yarda ta kallesa a school ne saboda kunya, bashi da haske a inda take, ma'ana tafi sa haske sosai amma kuma shi ba baƙi bane, duk hancinta kuwa ya fi ta, and he have got a very beautiful eyes with thick eyebrows that one can ever imagine, lips dinsa look so cute on his face, duk a cikin few seconds Mayraah ta kare masa kallon nan kafin tayi saurin dauke idonta, nan kuma taji gabanta na faduwa sosai, har ya karaso inda suke, da kyar tayi karfin halin cewa "Good evening sir, ga abincin da magani, i don't know if you will...." Kasa ci gaba tayi da mamaki ganin kudi yan dubu dubu da bata san nawa bane ya mika ma mai adaidaita sahun yace masa zai iya tafiya, Mai adaidaita sahu bai ko kalleta ba ya fara kokarin reverse da machine dinsa, Mayraah ta kasa cewa komai cause she became so confused and lost of words lokaci daya, da kyar ta kallesa tace "What is the meaning of this?" Yace "Ke baki da aiki sai yin musu da ni ko? ban taɓa ce maki abu kinyi direct ba sai kinyi musu, is that how u will be treating me after the marriage?" Kamar zata yi kuka tace "I told u i lied to my Mother about where i am going to, me yasa baza kayi considering dina ba sir, i did this because i was so worried about you" Shiru yayi yana kallonta, Lokaci daya hawaye ya cika idonta ita ma tana kallonsa, babu abinda ke kara karyar masa da zuciya sae hawayenta duk da Nikab din fuskarta he can see the tears in her eyes, yayi kasa da murya yace "I promise u in just 10 mins time zan maida ki gida Mayraah, i appreciate ur care and concern toward me, the rain is going to make u wet, mu shiga ciki in shirya sai in kai ki gida, kiyi hakuri" Tana goge hawayen idonta tace "I will wait outside, zan jira ka a nan" Yace "Bana son ki kara min musu, since ni nace zan kai ki gida, just do as i say" Yana fadin haka ya juya ya nufi gate din gidan da ya fito, hawaye ya dinga sauka idonta tana bin sa da kallo, nan da nan ta jika Nikab dinta, don ma babu kowa a Unguwan, bayan few seconds ta bi sa zuwa cikin gidan tana shiga gate din gidan ta zauna ɗan dakalin dake kofar dakin da aka yi ma Mai gadi, ya kulle gate din, ita dai sai kallonsa take gabanta na wani irin faduwa, dukawa yayi gabanta yana kallonta a hankali yace "Mayraah kinsan saboda ke na shiga wannan halin da nake ciki yanzu? Throughout yesterday night i couldn't sleep, ban taba shiga damuwa irin damuwar da na shiga daga jiya zuwa yau ba Mayraah, i am so disturbed" Kasa ci gaba yayi, yayi shiru yana kallonta, Maganganunsa suka dinga mata yawo a kai, ya shiga damuwa saboda ita kuma? As how? To me tayi masa? Dage Nikab din fuskarta tayi tana kallonsa for some seconds, can ta marairaice tace "Did i offend you in anyway? Ka gaya min don Allah ko wani laifin nayi maka, me yasa zaka shiga damuwa saboda ni?" Sunkuyar da kansa yayi bai ce mata komai ba, nan taji hankalinta ya kara tashi, cike da damuwa tace "Don girman Allah kayi hakuri ka gaya min sir, wllhi ban san me nayi ba, how did i offend you?" Nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta, Yayi gathering courage, da kyar yace "Baki min komai ba Mayraah, baki taɓa min komai ba, asali ma u are the most nicest, Pious, gentle lady i have ever come across all my life, samun mace irinki sai an tona, i am always proud u accepted me after all the up and downs, ina alfahari da ranan da na fara haduwa da ke, amma ina son ki min wani alkawari Mayraah" Ta zuba masa ido tana kallonsa and he could see the confusion in her eyes, ya kamo hannunta yace "Ki min alkawarin duk runtsi, duk tsanani, no matter d situation no matter what is going to happen baza ki taɓa rabuwa da ni ba!" Mayraah ta kasa cewa komai, ganin yanda ya kafeta da ido tayi karfin halin cewa "Amma ban taɓa cewa zan rabu da kai ba, me yasa kake fadin haka?" Yace "Baza ki gane ba Mayraah, nasan baki taɓa cewa baki sona ba, but ban san ko zaki iya canza ra'ayinki at anytime from now, may be because of pressure or whatever, amma ina son ki sani as far as ni Abdallah ban ce zan rabu da ke ba kuma ban guje ki ba baki da hujjan bari na no matter what, i mean no matter anything Mayraah" Ta sauke idonta tace "I have no intention of leaving you, bani da wannan niyyar, ban taɓa irin wannan tunanin ba, ta yaya zan ce zan barka bayan aurenmu saura yan kwanaki? Me kayi min?" Ya ɗan yi murmushin karfin hali, yayi kasa da murya yace "I know u won't get it right Mayraah, amma ina son kiyi min alkawarin ko kafin bikinmu, ko bayan bikinmu duk wani abu da zance maki zaki amince da shi babu musu" Ta dinga kallonsa tace "Kamar me kenan sir?" Yace "Abun da ya shafi rayuwata da ke, kiyi alkawarin zaki yarda da duk abinda na tsara" Ta sauke ajiyar zuciya tace "Nayi alkawari, i will be obedient in sha Allah, in dai bai saɓa ma mahaliccina ba" Ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta, A hankali yace "Sannan kiyi alkawarin duk runtsi duk tsanani, muna tare da juna daga this very moment har forever" Ta ɗan yi murmushi tace "In sha Allah" Yace "I love you Mayraah, and nothing can ever change my love toward you" Ta rufe fuskarta kan gwiwanta a hankali tace "Same with me" Yace "Ba ma sai na kai ki kin gaida Mamina ba again, after the wedding zata san ki" Mayraah ta dago tana kallonsa amma bata ce komai ba, yace "Give me just 10 mins yanzu zan fito sai in maida ke gida, nasan baza ki yarda ki shiga parlor ba, i know u have trust issues, kawai ki jirani a parking lot don kar ki jike da yawa" Yana fadin haka ya mike ya nufi cikin gidan ta bi sa da kallo, tasan har ranta tana son Musharraf, amma sai taji kamar yau an kara mata sonsa ne, bata daina kallonsa ba har ya shiga cikin gidan, ta kasa tashi daga inda take zaune duk da ruwan is just drizzling kadan kadan, kamar yanda ya fada bayan minti goma sai gashi ya fito rike da makullin mota, mikewa tayi da damuwa ta nufesa tace "Sir baka ci abincin ba" Yace "Sai na dawo bana son magariba yayi baki koma gida ba, tayi shiru tana kallonsa, ya bude mata motarsa dake parking space yana kallonta, karasowa tayi ta shiga cikin motar ya kulle mata, sai da ya fara bude gate sannan ya dawo ya shiga motar yayi driving dinsa out of the compound, ita dai sai bin sa da kallo take, har ya dawo motar bayan ya kulle gate din suka bar unguwan. Mayraah bata yarda Musharraf ya kai ta har kofar gidansu ba, shi ma kuma bai yi insisting ba, ta bude motar zata sauka kenan ta zaro ido, ta juya da sauri tana kallonsa tace "Nace ma Ammi zan amso handout wajen Hamida, i can't go in without Handout...." Bata rufe baki ba ya juya ya dauko wani material a back seat ya mika mata, sosai hankalinta ya kwanta, ta amsa tace "Thank you" Yana kallonta a hankali yace "Welcome" Bude motar tayi ta sauka tace "Sai da safe sir, Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen" Sae da taga yayi reverse sannan ta fara tafiya zuwa kofar gidansu, sosai gabanta ya fadi ganin Usman zaune bakin gate din gidan, ta ma san ya ga saukanta daga motar Musharraf ganin yanda yake kallonta from head to toes, Tana isa gate din yace "Wa ya ajiye ki a mota?" Ta juya ta kalli bayanta taga tuni motar Musharraf ya bar layin, kin ce masa komai yayi, ya mike jin ana kiran magrib yace "Zaki gaya min motar waye bari a idar da sllh" Daga haka ya wuce cikin gida, ta wani tura masa baki ta bi bayansa zuwa cikin gidan, tana biye da shi tace "Yaya gidansu Hamida fa nace, to da ya kirani yaji ina can ne shine dama yana kusa da anguwan sai kawai ya maido ni gida" Usman ya juya yana kallonta, komawa baya tayi da sauri, yace "Yaushe kika koyi karya Mayraah?" Tayi narai narai da ido tace "Yaya i am not lying" Yace "Ohk bari a idar da sallah zan kira Hamidar" Ko damuwa bata yi ba saboda tasan bai da number Hamida, ya tsaya bakin tap dake compound din zai yi alwala ita kuma ta wuce cikin gida, Sai da ta fara zuwa dakin Ammi don sanar mata ta dawo, Aunty Mariya tace "Ai kam kinyi sauri" Ammi tace "Mahir din ne ya dawo da ke?" Mayraah tace "Aa ban ma ce ya zo ya daukeni ba" Ammi tace "Toh ki je kiyi sallah" Juyawa tayi ta fita daga dakin, Aunty Mariya tace "Wai ya batun gyaran jiki, tun fa ana saura wata biyu ake farawa Ammi" Ammi tace "Ni ba sanin yanda ake yi nayi ba, tunda dai Allah ya kawo ki ai sai duk ayi abinda ya kamata" Aunty Mariya tace "Toh naji tana zancen test, kamata yayi ace daga yau ma ta daina fita" Ammi tace "Matakin karshe fa suke yanzu, nan da sati shidda ma nake jin za su fara final exams" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya bada sa'a, tare suke da Badiyya ko?" Ammi tace "Eh" Aunty Mariya tace "Kinga ai har yanzu bata zo ta gaisheni ba" Ammi tace "Zata zo"
Washegari lahadi throughout Mayraah na daki tana karatu for tomorrow's test don bata son lecturers dinta su sake saka ta gaba, har bayan la'asar tana daki studying her handout, Aunty Mariya ta shigo dakinta tace "Mayraah ki sakko Hajja ta zo tana son ganinki" Mayraah ta mike ta dau Hijab dinta ta saka, ta bi bayan Aunty Mariya, Hajja na zaune parlor an shimfida mata wani carpet din ana ta fiddo mata lefen Mayraah tana ta saka albarka cike da farin ciki, ta ma rasa yanda zata yi don murna, Mayraah ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Hajja sannu da zuwa" Hajja ta rungumeta tace "Lallai kin yi goshi Mayraah, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi, Allah ya nuna mana na yan baya haka, Allah sa mijinki ne shi har aljanna" Sai a sannan Mayraah ta lura da Badiyya dake zaune kan kujera ta daura kafa daya kan daya kamar yar tasha, tana ta bin kayan da kallo fuskar nan nata babu yabo babu fallasa, wani daci take ji a makogwaronta tsabar hassada, Mayraah tace "Ina wuni Aunty Badiyya" Badiyya bata ko kalli inda take ba tayi pretending kamar bata ji ta ba, Hajja tace "Ke Badiyya, Amarya tana gaisheki" Sai a sannan Badiyya ta ɗan kalli Mayraah tace "Ohk, lafiya" Mai gadi ne yayi sallama dai dai bakin kofar parlon, duk aka daga kai ana kallonsa don baya shigowa parlon yau sai ga shi, wani akwati ne da aka yi yayinsa tun tale tale a lkcn su inna na yan mata ne a hannunsa, kana ganinsa kasan shi ma he is not comfortable shigowarsa parlon, Yana kame kame yace "Cewa tayi sai na shigo mata da shi, bakuwa ce aka yi" Muryar Mama Ladi suka ji tana cewa "To ko dai ba boyi boyin gidan bane? Ya zan baka kayana ka shigar min da shi gida ka dinga nokewa, kasan daga inda nake ne, ku haka ku ke yi a garin nan?" Sosai gaban Ammi ya fadi ta juya ta kalli Aunty Mariya da ita ma tayi shock, Hajja tace "lale lale, muryar wa nake ji kamar ta Ladi" Ladi tace "Ni ce mana yaya, tun asuba na biyo hanya ashe rubabbiyar mota na shiga abu ba arziki in gaya maki, tafiya daya biyu mota ta lalace, tafiya daya biyu ta fara wani ƙara tana hayaki, ni dai nayi ma dreban Allah ya isa, yanda motar take a rube haka shima wani rubabben tsoho ne in gaya maki, mu dai mun yi barka da muka shigo kano lafiya" Badiyya ta mike da sauri ta tafi ta rungume Mama Ladi cike da murna tana cewa "Sannu da zuwa Mama" Mama Ladi tace "Yauwa sannu Badiyya, ina Mashir din da na zo bikinsa?" Hajja na nuna Mayraah tace "Ai har da na Mayraah, amarya ne da ango ai a gidan" Mama Ladi tace "Wacece kuma Mayraah?" Mayraah na murmushi tace "Sannu da zuwa Mama" Tuni Ammi dake ta kirkiran Murmushi ta mike tace "Kin sha hanya Mama Ladi, sannu da zuwa..." Amsan Handbag dinta tayi tana kallon Aunty Mariya tace "Mariya maza yi mata shimfida a dakin can, ki kunna mata ruwa a bandaki..." Mama Ladi tace "Aa ni dakin saman bene za a kai ni in zauna" Ammi tace "To bismillah Mama Ladi" Sama ta nufa Mama Ladi na kallon Hajja tace "Bari in watsa ruwa in dawo mu gaisa yaya" Daga haka ta bi bayan Ammi, amma ta kasa hawa benen saboda ciwon kafa, Aunty Mariya tace "Kinga kasa zai fi maki fa Mama Ladi" Mama Ladi tace "Babu ruwanki" a haka ta daure ta fara hawa benen tana yi tana hutawa, sai da hawa benen ya dauketa kusan minti sha biyar.....



07087865788
WhatsApp only.....
[6/3, 3:16 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖




_By khaleesat Haiydar_✍🏻





9.....


Aunty Mariya na kallon Hajja tayi kasa kasa da murya tace "Don girman Allah Hajja in zaki koma gida kice mata ta bi ki ku tafi, kin dai san halin Mama Ladi" Hajja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login