Showing 126001 words to 129000 words out of 249515 words
an dasa ta, tsabar yanda abun ya bugi Haseenah a haka Maheer da Badiyyah suka fito suka sameta tsaye har lkcn kamar statue, Maheer ya wuceta without looking at her, Badiyyah ta kulle dakinta da makulli ta saka makullin cikin jakarta sannan ta yafa ɗan iskan gyalenta ta bi bayan Maheer tana kallon Haseenah tace "Kawata sai mun dawo" Haseenah ta bi ta da kallo har taga sun fita daga parlor, dakinta ta shige da sauri ta xauna gefen gado ta jawo wayarta ta fashe da matsanancin kuka tayi dialing number cousin sister dinta Ramlah, Ramlah na dagawa Haseenah ta kara rushewa da kuka sosai tace "Ramlah wallahi na gaji, na gaji, ji nake kamar xuciyata zai fashe Ramlah, sai yanzu na gane gwara min Mayraah sau dubu a gidan nan tun da ita bazata min wannan abinda Badiyyah take yi a gidana ba kuma shi ma bai wani kula Mayraan a gabana, Ramlah kin ga abinda nake gani a gidana kuwa?" Daga daya bangaren Ramlah tace "Dalla ba wani gwara, ke dai nace ki kwantar da hankalinki ba dai mu mun san abinda muka shirya ba?" Cikin kuka Haseenah tace "Tsoro nake kada tsinanniyar kakan nan tasa tace ya auri Badiyyah tun da an ga suna shiri yanzu, kar ita ma Badiyyar ta zo ta fara sonsa tunda ba hankali isasshe gareta ba, wallahi ina ji a jikina at anytime komai zai iya faruwa idan ban kawo karshen wannan abun ba cikin gaggawa, gashi har yau Maheer yaki kulani" Ramlah tace "Kin ga ni bana gida yanzu haka Haseenah, tun da dai nace ki kwantar da hankalinki ki kwantar da hankalinki kawai, auren nan sai kace bamu yi ba mun fito, Mun fa san kan ko wani tsiya, wallahi Badiyyah da kafarta zata bar maki gida yanda ita wannan mara asalin ma ta bar gidanki" Haseenah na shessheka tace "Amma fa na gaya maki yanda kakar nan tasu ke ji da Badiyyar nan, don ita ce ma ke control dinta wallahi, ni dai wallahi gwara min Mayraah a gidan nan da Badiyyah, Ramlah da na sani da ban hada Badiyyah da malamina ba, kullum da fargaban haka nake kwana nake tashi" Ramlah tace "Kinga ni don Allah zan kiraki in na koma gida" Daga haka ta katse wayarta, Haseenah ta dinga kuka a ranta tana tunanin menene yasa ita dai komai nata bai tafiya dai dai a rayuwar nan, daga wannan sai wannan, ga Maheer ya juya mata baya aure ko wata daya bai cika ba amma sai reto auren nata yake. Throughout daren yau Mayraah bata yi wani bacci ba kasancewar washegari za su fara exams, she is trying by all means taga tayi covering din course din da suke da shi da safe, ita kanta tasan she is not fully prepared for the exam, to amma ta rasa ta yanda zata yi karatun ya shiga kanta, it seems her brain is just weak, a haka dai ta shiga makaranta karfe bakwai da rabi for the exam, rabonta da makarantar tun last week monday, Mayraah ta nuna ma wani lecturer dinsu dake tsaye bakin hall din da za su yi exams ID card dinta sannan ta shiga ciki, seat din da ya nuna mata ta nufa, tana zaunawa sai ga Badiyyah ma ta shigo ta zauna kujeran dake gefen na Mayraah don nan aka nuna mata ta zauna, sai dai akwai ɗan tazara tsakaninsu, a haka aka fara raba masu answer sheet, kamar ance Mayraah ta daga kai taga Musharraf tsaye at the far end of the hall yana danna wayarsa, ta dauke kanta da sauri bata sake kallon side din ba, a haka har suka fara exams din, Mayraah ta dinga kallon questions din that look strange in her eyes, tunani ta fara yi ko dai ba handout din ta karanta ba, though the questions look familiar but she is just confuse, just few minutes da fara jarabawan Mayraah ta sunkuyar da kanta trying to calm herself down, ta lura Badiyyah na ta mutsu mutsu cikin Hijab, Mayraah ta kalli side dinta, sai da gabanta ya fadi ganin wayarta take lullubewa da hijab bayan ta ciro shi daga bra dinta, duk da how strict the invigilators where haka Badiyyah ta dinga satan amsa da wayarta cikin dubara tana yi tana keeping serious face, Mayraah gabanta ya dinga faduwa don in dai lecturer ya kamata to kora ne direct bbu wani corner corner, after like 30 minutes Dr Musharraf ya karaso gaban Badiyyah yana kallonta, tayi saurin cusa wayar tsakanin cinyoyinta, can ya ɗan kalli colleagues dinsa ko kadan bai son attention dinsu ya dawo wajen, hakan yasa ya ɗan fara zagaye zagaye a wajen, sai kuma ya tsaya dab da ita, yayi kasa da murya yace "Bring the phone Badiyyah" Badiyyah jikinta ya fara rawa, ta ciro wayar gabanta na mugun faduwa, kawai ya kai hannu ya karba without letting anyone notice them ya saka a aljihu ya bar wajen, Badiyyah ta sauke ajiyar zuciya, Mayraah ta bi Musharraf da kallo.....
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.
[7/6, 4:52 PM] Khaleesat Haiydar💖: *I dedicate the whole of this page to MAYRAAH Conversation groups💖, ina yin ku irin 💯 din nan, Allah Ubangiji ya iya maku, ya biya maku duk bukatunku na alkhairi ya raya zuri'a* _Team Musharraf ina kara bamu hakuri, mu kwantar da hankalinmu komai zai daidaita, Team Maheer kuma su ci kansu babu mai ba yaji, Team Usumanu kuma kamar yanda muka kasa gane zuciyarsa su ma har yau bamu san zuciyarsu ba gaskiya, su dinga buda baki ko za mu gane inda suka dosa_🙄
Mayraah ta sunkuyar da kanta saboda hawayen da taji ya kawo idonta, bata taɓa shiga exams hall taji kanta so empty like today ba, ɗaga kai tayi after some minutes ta goge tears dinta, suka hada ido da Dr Musharraf dake kallonta, dauke kanta tayi daga direction din, Badiyyah dai sai kallon Mayraah take tana murmushi kasa kasa ganin sunanta da reg number kawai ta rubuta a booklet, yawanci idan suna exams in dai Dr Musharraf na invigilating zama yake yi colleagues dinsa su yi invigilating din, ko nan da can bai son zuwa, yau kam ya amshi attendance sheet going round to give each and every student to sign, har ya iso roll din da Mayraah take zaune, yana isa gabanta taki yarda ta dago kanta, ya ajiye mata sheet din attendance din kan booklet dinta, ya amshi pen dinta dake hannunta ya ajiye mata nasa, kallon pen din nasa ta dinga yi ba tare da ta yarda ta daga kai ta kallesa ba, can dai ta dau pen din nasa tayi signing attendance din, ya dau attendance sheet din ya bar wajen, lkci daya duk kamshin turarensa ya cika mata hanci, ta wani hade rai ta ajiye pen din nasa kawai kan booklet, dai dai nan wani lecturer dinsu ya karaso inda take ya tsaya yace "Are you not comfortable here?" Ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Yes sir" Yace "Ok let me change ur sit" Mikewa tayi ta dau booklet dinta da pen din Dr Musharraf ta bi bayan lecturer din ya kai ta har gaban hall ya nuna mata kujera da table dake kusa da podium ta karasa ta zauna, tana zaunawa ta bude booklet din sai ta samu kanta kuma da fara rubutu, 50 minutes da fara rubutunta ta gama abinda zata iya a questions din, zuwa Lokacin students sun gama sun fara fita class din, sai a sannan ta lura Badiyyah ma ta fita, ta hada ido da Musharraf that is sitting opposite to her, yana amsan booklets din wa enda suka gama, ta rufe booklet dinta ta mike ta tafi zata yi submitting, tana ajiyewa gabansa ya dauka ya bude, ita dai kanta na kasa tana jiran ya bata attendance tayi signout don yana hannnunsa attendance sheet din, after few seconds ya ajiye mata yana kallonta, pen dinsa dake hannunta ta ajiye zata dau nata da ta ga ya ajiye kan table yayi saurin daukewa, daukan nasa din tayi, tayi signing ta fice daga hall din, Hamidah na ganin Mayraah ta fito ta nufeta tana kallonta tace "How was the paper Mayraah?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Alhmdlh" Hamidah tace "Toh Allah ya bamu sa'a" Mayraah tace "Ameen" Hostel Mayraah ta wuce bata kara ko minti daya a department din ba. Mayraah na kwance ita kadai a daki da yamma tana ta tunane tunane, zuwa yanzu tunani har ya zame mata jiki, tayi wannan tayi wancan, wani tayi murmushi, wani kuma taji hawaye ya cika idonta, wayarta ne ya fara vibrate, ta jawo wayar a hankali tana kallon screen din ta ga Maheer ke kiranta, da kamar bazata daga ba don dazu ya kirata bayan ta dawo hostel, can dai ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yace "How r u Mimi?" Tace "Alhamdulillah, ina yini" Yace "Bacci kike ko karatu?" Tace "Just lying down...." Yace "Ohk, na bada sako a kawo maki ki fita kofar gida ki amsa" Shiru tayi sai taji da ma tace masa tana school, yace "Hello" a hankali tace "Toh" Daga haka ta mike ta dau hijab dinta ta saka ta fita waje, tsaye tayi bakin gate din hostel din ganin Abba, bata san sanda ta nufesa ba da farin cikin ganinsa ta gaishesa, ganin yanda ta rame Abba yace "Kina cin abinci kuwa Mayraah?" Maheer dai na tsaye jikin mota shi ma yana kallonta, he is not happy with the way take ramewa kullum, tun shekaranjiya rabonsa da ita sai dai ya kirata a waya, yana bata enough space kamar yanda tace don tayi karatu, Mayraah na murmushi a hankali tace "Ina ci fa Abba" Abba bai gamsu da hakan ba ya kalli Maheer yace "I don't think she is comfortable here Maheer, ta dawo gida kawai" da sauri Mayraah tace "Abba exams ne fa, but ina cin abinci wallahi, karatun da nake yi ne shi yasa" Abba yace "Papers nawa ku ka yi yanzu?" Tace "On monday muka yi daya, muna da wani gobe Thursday in sha Allah" Abba yace "Sai kuma yaushe bayan na gobe?" Mayraah tace "Sai kuma Monday" Abba ya kalli Maheer yace "Idan tayi paper din gobe ta dawo gida for the weekend, bring her back home" Lokaci daya Mayraah taji gabanta ya fadi ita gaba daya bata ma son tuna gidan, da sauri tace "Amma Abba za mu yi practical a laboratory for Monday's paper, friday and Saturday duk za mu shiga school, ka tambayi yaya ya sani ai" Abba yace "Duka courses din nawa ne gaba daya?" Tace "Guda 6 with project" Abba yace "Toh za ku gama da wuri kenan" Mayraah dai ta yi murmushi kawai ta gyada masa kai, duk da dai intervals na 2 days ne for every course, Siyayya sosai Abba yayi mata Maheer ya fito mata da su daga mota ta shiga da su cikin hostel, minti sha biyar kawai Abba yayi suka wuce tare da Maheer, ita kuma ta koma cikin hostel, zaunawa tayi tana kallon handout din da ta ajiye gefen gado, tun jiya ta kasa bude handout tun da taga course din Musharraf za su yi, ba shi ba har course din nasa taji ta tsana har cikin ranta, wanda a da it's among her best... Sai can da daddare bayan tayi isha ta jawo handout din ta ɗan yi scrolling daga karshe kawai ta ajiye tayi kwanciyarta don ranta kara baci yake just scrolling through the handout... Washegari tana zaune hall din exam din nasu da booklet dinta da aka masu sharing suna jiran question paper, kamar ran Monday yau ma Badiyyah a gefenta ta zauna, ita dai ko kallon side dinta bata yi ba, wani lecturer dinsu ne yayi sharing masu question paper din don Musharraf din ma bai shigo ba, ta dinga kallon takardan questions din, tuni Badiyyah aka fara rubutu babu ɓata lokaci ana murmushi irin anyi karatun nan, Mayraah na daga kai after some minutes taga Musharraf zaune hall din, tayi saurin dauke kai ko da mistake bata sake kallon side din da yake ba, bata wani stressing kanta ba a exam din, she just wrote what she can cause bata ma yi karatun ba ai, an hour into the exams ta mike ta tafi inda zata yi submitting booklet dinta, kallonta kawai Musharraf yake ta cikin glasses din idonsa, zata yi signing attendance dake gabansa ya janye, ya amshi booklet din nata ya bude, ita dai taki yarda ta kallesa ta wani hade rai tana tsaye, rufewa yayi ya ajiye mata right in front of her yace "Go back" ta dau booklet dinta ta juya ta koma ta zauna fuskarta a daure, yawanci invigilators din close colleagues din Musharraf ne shi yasa nobody was against his action a lkcn, Mayraah ta rufe booklet din ta hade kanta da table ba tare da ta kara ko fullstop a abinda ta rubuta ba, kusan ita ce karshen fita hall din bayan duk Coursemate dinta har Badiyyah sun fita, ta tafi tayi submitting gun wani lecturer tayi signing out ta fice without looking at Musharraf da ya bi ta da kallo ta cikin glass, ba wanda zai ce ita yake kallo. Sauran exams din haka Mayraah tayi su ba yanda ta saba exams dinta ba, hakan ke kara daga mata hankali, ita yanzu she is not even after any first class kawai ta samu ko da pass ne ta tafi don ita kanta tasan bata abun arziki a exams din nan, komin dadewan da zata yi tana karatu sai ta ji bata iya rikesa a kai kamar da, nan da nan karatun yake bin iska, a haka har suka yi 5 exams, ya rage masu just last paper dinsu da za suyi on Friday, saboda wahalan course din sannan tasan bata da wani score me yawa a test yasa ta dage tayi karatu ba na wasa ba, ana gobe za su rubuta last paper din nasu tana kwance tana replying message din da Maheer yayi mata ta WhatsApp, bayan ta gama replying dinsa wani message ya shigo mata, ta bude message din ganin bata da number a contact dinta, Pdf taga an turo mata guda biyu with her name, ta bude taga complete project dinta ne from chapter 1 to end, daya pdf din kuma taga project Defense slide ne, tana fita daga cikin slide din taga message kamar haka "Print out 3 copies, 1 for ur Supervisor, 2 for ur project co-odinator, to be submitted to ur external supervisor.... submit ur Supervisor's copy on Monday 5:30pm prompt" Mayraah ta fita daga cikin message din ba tare da tayi reply ba ta ajiye wayar, time din da aka sa ne ya tsaya mata, ta sake dauko wayar ta bude message din tana sake kallon time din wai 5:30pm, tabe baki tayi ta jawo handout dinta ta ci gaba da karatun ta. Washegari da safe karfe goma Mayraah na zaune hall bayan an raba masu booklet suna jiran question paper dinsu, kowa ka gani a class din kasan a tsorace yake da last paper din nan, ga malamin ba shi da kirki, don Malamin da ya kirata office yana mata masifa ne kwanaki, a haka har aka masu sharing question paper, Badiyyah na zaune seat din da take zama tun fara exams din, yau ma Hijab ne har kasa a jikinta, Mayraah ta lura duk ranan da take so tayi expo ne take sako Hijab, ranan da bazata yi ba to mayafi take sakawa, 40 minutes da fara exams din Mayraah taga Badiyyah na ta mutsu mutsu cikin Hijab, ita dai rubutunta kawai take kafin ta mance abinda ke kanta tunda bata iya rike hadda for long yanzu.... Lokaci daya duk yan ajin suka juya jin wata lecturer dinsu da ta nufi Badiyyah da sauri tana bata instruction din ta tashi tsaye cikin tsawa, tuni sauran lecturers din maza dake Hall din suma suka nufo Badiyyah, Badiyyah dake ta zazzare ido tayi kasa da hannunta ta cukuikuye wani takarda ta jefar kusa da Mayraah, Mayraah ta zaro ido tana kallonta a tsorace, tuni lecturers din suka zagaye seat dun Badiyyah, a tsakiyan Booklet dinta suka ciro papers cike da rubutu an linkesu neatly, Badiyyah ta fashe da kuka a tsorace tana nuna Mayraah cikin rawan murya tace "Wallahi ba ni kadai bace har da ita, we were passing answers to each other wllh tllh" Lecturers din suka kalli Mayraah da ta zaro ido, wani ya karasa kusa da ita ya durkusa ya dau takardan da ya gani yana instructing din Mayraah ta tashi tsaye, nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah ta ma rasa abinda zata ce tsabar rikicewa, lecturer din ya warware takardan da Badiyyah ta jefa mata yana dubawa, tuni wani lecturer har ya yage envelope din mal-practice form jikinsa na rawa ya ciro biyu ya ajiye daya kan table din Mayraah, dayan kuma kan table din Badiyyah, wani student dake zaune bayan Mayraah ya daga hannu alamar zai yi magana yace "Wallahi sir jefo ma Mayraah takardan kawai tayi da taga an kamata, amma they are not together sir" Sai a sannan Mayraah ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "Sir u can check d paper and my answer booklet if they correlate, wallahi i am not together with her" Wata security lady da ta ta karaso cikin Hall din ne tace "Malam naga fa duk abinda ya faru, ita wancan matar me satan amsan ce ta jefo ma yarinyar nan takardan nan da ta ga an kamata, i saw everything from outside.... Tun dazu nake noticing tana mutsu mutsu but