Showing 132001 words to 135000 words out of 249515 words

Chapter 45 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1532

Yace "Ohk nawa ne kudin" ta sunkuyar da kai tace "Dubu hamsin" Yace "To zan tura maki" Da sauri ta kallesa ta wani washe baki tace "Nagode sosai yayana, Allah ya kara maka budi" Yace "Ameen" Juyawa tayi cike da farin ciki ta koma dakinta, Haseenah ta dinga kallon Maheer da yaki kallonta ya kulle kofarsa, kofar ta nufa a fusace ta bude ta shiga ta tsaya tana kallonsa tana huci tace "Maheer tun yaushe nake ce maka ina bukatar kudi kaki bani shine yanzu zaka dau har dubu hamsin ka ba ma wancan gantalalliyar da sae dae ta siya kwaya da kudin? dama da ni da ita wanene haƙƙinsa ke rataye wuyanka? wanene yafi cancanta ka ba ma kudi tsakanina da ita?" Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Ita ma haƙƙin nata ya kusa dawowa wuyata gaba daya kamar yanda naki haƙƙin ke wuyata, daga sannan zaki ga ita ma ta cancanci a bata kudin" kallonsa Haseenah ta dinga yi babu ko kiftawa as if trying to understand what he meant by saying so, can dai tana stammering tayi karfin halin cewa "Ban fahimci abinda kake nufi ba Maheer" A takaice yace "Zaki fahimta nan ba da dadewa ba, dama bana son ki fahimta da wuri sae lokacin yayi" Yana fadin haka ya mike ya fita daga dakin ya bar ta tsaye tana bin sa da kallo kamar idanuwanta za su fito tsabar kidimewa. Daren ranan nan Haseenah bata yi baccin kirki ba, da tayi zata farka a firgice saboda mafarkin Badiyyah, daga karshe ma parlor ta dawo ta zauna, ita ba sallah ba balle salati, da asuba tana jin Maheer ya fito daga dakinsa, tsaye yayi corridor yaki karasawa parlon ganin wutan parlon a kunne, can dai ya ɗan leka ya hango Haseenah zaune tayi tagumi, tun da aka kawota gidan bai taɓa ganin ta tashi da asuba ba, ko ya tasheta tayi sallan asuba bata tashi, yawanci sai gari ya waye tar take sallan asuban ta, yana ganinta a parlon ya nufi dakin Badiyyah ya fara knocking kofar dakin, Haseenah ta daga kai da sauri jin yana kwankwasa kofar dakin Badiyyah, mikewa tayi tana lekan corridor din taga ya bude kofar dakin yana kallon ciki yace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" Haseenah ta koma kan kujera ta zauna da sauri, ita kanta bata san wani kalan abu take ji a ranta ba tun daren jiya, har wani heartburn ke damunta tsabar tashin hankali, Maheer ya fito Parlon yayi mata kallo daya ya wuce masallaci, ta mike ta hau zaga parlon tana jin zuciyarta na mata tukuki, maganganun da ya gaya mata jiya a dakinsa ne kawai ke yawo mata a ka, daga karshe ta shige dakinta tana wani murmushi. Karfe goma saura Badiyyah ta fito daga dakinta, baccinta tayi har da minshari daren jiya tun bayan da Malam Dauda ya bata assurance babu wanda ya isa ya koreta a makarantar, sanye take cikin riga da skirt sai ɗan figigin mayafinta da handbag alamar fita zata yi, Haseenah na zaune dining area abun duniya ya taru ya mata yawa tayi nisa cikin sake saken da take a zuciyarta na nema ma kanta mafita, bata san ma sanda ta fito parlor daga cikin dakinta ba har ta zauna kan dinning chair tsabar tunani, ɗaga kai tayi jin kamshin turare ya baɗe parlon, suka hada ido da Badiyyah, sai da taji wani mugun faduwan gaba, Badiyyah ta nufeta tace "Ina breakfast din Haseenah?" Wani bacin rai da takaici ya zo ma Haseenah har wuya ta dinga jin zuciyarta na wani tafarfasa tayi mata banza ta ki cewa komai, Badiyyah ta bude coolers da ta gani kan dinning taga babu komai ciki, ta wuce kitchen nan ma taga ko ruwan zafi Haseenah bata dafa a gidan ba, Badiyyah ta fito a fusace tana kallonta tace "Amma dai gaskiya baki kyautawa Haseenah, wannan ai mugunta ce da baƙin hali, yanzu haka kike son in fita ban karya ba kenan? mutum na gidanki amma ki dinga barin sa da yunwa saboda ke muguwa ce" still Haseenah ta mata banza sae girgiza kafa take, juyawa Badiyyah tayi a mugun fusace ta nufi corridor zuwa dakin Maheer kamar zata tashi sama, ta kwankwasa kofar tana jiransa ya bude, yana bude kofar tace "Yaya wai kana ganin yau ma Haseenah bata yi ma mutane breakfast a gidan nan ba ko? Haka jiya ta sa na tafi exam hall ban ci komai ba nayi exam din ina jin yunwa da jiri na gama na fito, yanzu kuma zan je gidan Hajja na je zan dau breakfast naga ko kunna gas din matar nan bata yi ba" Duk Haseenah na jin abinda Badiyyah ke cewa saboda cikin daga murya take maganar, Maheer ya fito daga dakin ya dawo parlor Badiyyah na biye da shi a baya, kallon Haseenah dake zaune dining yayi yace "Ke me yasa baki girka breakfast din ba?" Haseenah ta masa wani matsiyacin kallo tace "Ko kai yau baka isa in maka breakfast a gidan nan ba balle wata katuwa can" Badiyyah ta nufeta tana huci tace "Shi yayan nawa kike gaya ma magana haka saboda baki da tarbiya??" Haseenah dai taki ce mata komai don tana buda baki bata san kalan tereran da Badiyyah zata mata ba a wajen shi yasa tayi mata shiru tun daxu, Maheer na kallon Badiyyah yace "Ki shiga dakina ki dauko min makullin mota in ajiye ki gidan Hajjan, idan kin je can sai kiyi breakfast din" Badiyyah ta galla ma Haseenah wani harara ta bar parlon, Haseenah ji tayi kamar numfashinta zai dauke don takaici, wai Badiyyah taje dakinsa?? to ko Mayraah da ta zauna gidan nan bata taɓa tsayawa bakin kofar dakinsa ba balle ta shiga dakinsa, wasu hawaye ne suka cika idonta ba tare da ta sani ba, a haka Badiyyah ta dauko makullin motarsa ya amsa tayi ma Haseenah gwalo ta bi bayansa suka fice daga parlon, Haseenah ta fashe da matsanancin kuka ta zamo kasa ta zauna tace "Na shiga uku na lalace ta ina zan fara ni Haseenah" Maheer na ajiye Badiyyah kofar gidan Hajja ta sauka tana kallonsa tana washe baki tace "Baza ka shigo ku gaisa da Hajja da Ammi ba Yaya" Ya dake yace "Sauri nake" Daga haka ya ja motarsa ya bar wajen ta dinga daga masa hannu kafin ta shiga gidan cike da farin ciki, sai da ta tsaya jikin kofar parlon ta kasa kunne, Hajja dake zaune parlorn rike da cup din kunu tana kallon Ammi dake linke kayanta cikin akwati tace "Hakuri kawai za ki yi, ko don yaron nan Maheer, dubi yanda ya daga hankalinsa kullum sai ya zo gidan nan yaro ɗan albarka me gudun zuciyar uwarsa, ga kuma Umar da ke hanya gobe, kin ga bai kamata ya dawo ace baki gidan ba tunda shi bai san abinda ke faruwa ba har yanzu, gwara kuma da ba a gaya masa ba kar aje karatunsa ya samu matsala, amma wannan yaron naki Usman kam ki binkita ko canja maki shi akayi a asibiti gaskiya" Ita dae Ammi bata ce komai ba hada kayan nata kawai take, Hajja tace "Duk ɗan kwarai baxai banzatar da uwarsa yanda Usman yayi ba...." Ammi ta katseta tace "Yana fa kirana a waya ke ce dai baki sani ba Hajja" a fusace Hajja tace "Kiran banza kiran hofi, shi Maheer kiranki yake ba zuwa yake ba da yake yana son gamawa da duniya lafiya, kawai kin haifi jaraba kawai, azzalumin yaro, wllhi yana nan sae yayi mamakin matsayin da Badiyyah zata kai a rayuwar nan, kuma sae yayi da ya sanin duk abinda yayi mata, da na dauki duk jikokina daya a zuciyata amma yanzu kam kowa da matsayinsa wallahi, ko da wasa kada Usman ya nuna yasan Badiyyah wataran" Ita dae Ammi bata sake cewa Hajja komai ba, Badiyyah ta bude kofar parlon ta zube kasa ta rushe da kuka sosai ta kwanta, tsabar gigicewa sae da Hajja ta kusa zubar da kunun hannunta ta mike da sauri ta nufeta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, lafiya Badiyya, me ya faru" Ammi ma ta nufeta hankali a tashe, Cikin kuka Badiyyah tace "Hajja jiya za mu yi jarabawa a aji na manta na shiga da wani takarda a hannuna shine Mayraah ta kira wata malama a ajin tace mata gani can na shigo da satan amsa, kuma wallahi ba satan amsa bane wani takarda ne daban, yanzu an koreni a makarantar gaba daya Hajja" Hajja ta juya ta kalli Ammi da ta nemi waje ta zauna tana kallon Badiyyah da mamaki jin abinda take cewa, ita dai Badiyyah rusa kuka kawai take duk ta cika parlon da kururuwarta tana cewa ita fa an koreta a makaranta saboda Mayraah, Hajja tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ita Mayraahn ta maki wannan sharrin? kuma ke baki da bakin da zaki ce masu ba satan amsa bane a hannunki Badiyyah? Yau ga matsiyaciyar yarinya, sai yanzu na kara tabbatar da karin maganar nan na Hausa da suke cewa tsintattciyar mage bata mage, In da can suna mata kallon er uwarki a makarantar ke baza ki buda baki kice masu babu abinda kika hada da ita ba yanzu ba ma ta gidanku? Iyye Badiyyah?" Cikin kuka Badiyyah tace "Babu wanda ya saurareni wallahi Hajja, kawai korata suka yi" Ammi da duk jikinta yayi sanyi ta mike ta shiga daki tayi dialing number Maheer har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma no response, ta fi minti biyu tsaye parlon kafin ta dawo parlor, taga Hajja zaune ta cika famm kiris ya rage ta fashe, Ammi ta kwantar da murya tace "In sha Allahu ma ba a koreki ba Badiyyah, na kira Maheer ina jin ba ya kusa da waya da sai in ji yanda za ayi ko zuwa makarantar za ayi a samu malaman in ya kama ko nawa ne a basu su yi hakuri, kuma ke ma ai tun jiya kuna fitowa daga exams din ya kamata ki zo ki sanar da abinda ke faruwa" Badiyyah na shessheka tace "Gidan ya Maheer kawai na tafi shi kuma bai dawo ba sai da daddare sannan nayi bacci, shine yanzu da safe na zo nan" Ammi ta zauna tace "In sha Allahu za a san yanda za ayi, za a samu malaman" Duk da Ammi har cikin ranta take jin she have nothing to do with Mayraah anymore, ta dalilin Mayraah ta ga abubuwa marasu dadi da bata taɓa expecting a rayuwarta ba, ta dalilin Mayraah yau rabonta da gidan mijinta wata daya currr kuma har a lokacin ko bin ta kanta Abba bai yi ba, yanzun ma ba don Hajja da ta tilasta ta koma gida saboda Umar dake hanya ba ko shekara nawa za suyi ita da Abba a haka sai dai su yi, wai duk ta dalilin er da ba karamin jahadi tayi ba na rainonta tun tana tsumma, er da da farko kin amincewa yayi ta rike ta, shine yau saboda ita yayi mata wannan rashin mutuncin da girmanta da shekarunta, bata taɓa da ta sanin abinda ta aikata na alkhairi irin wannan ba, tayi da ta sanin don ko jin sunan Mayraah ma bata son yi, duk da wannan abubuwan amma deep down tasan Mayraah bazata yi abinda Badiyyah tace ba, dama can Badiyyah na da history din satan amsa a koreta a school, idan kuma ba satan amsa ba to point din ta will be very low har sai an koreta a makarantar, Hajja tace "Mu muka ga karshen taimako, dama ance ba kowa taimako ya ke amsa ba, mu kam bai amshe mu ba wallahi"
[7/8, 5:15 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer na zaune parlon Hajja wajen karfe biyu da rabi na rana bayan kiran da Ammi tayi masa, duk tunaninsa gida zai maida ta kamar yanda dai suka tsara a jiya da ya zo gidan, don ba karamin kai ruwa rana akayi ba kafin Ammi ta yarda zata koma gida, at first she was reluctant don tace ita da komawa gidan Abba sai dai wani ikon Allah kuma, kusan kullum idan Maheer yaje gidan hakuri kawai yake bata ta janye vow din nan da tayi ta koma gida, yawanci ma abinda ke kai sa gidan Hajja kenan kawai ya ba Ammi hakuri har cikin ransa he is not happy da zaman gidan Hajja da take, gashi ba isassun dakuna, don ma Badiyyah na gidansa banda haka dole sai dai tayi sharing daki da bandaki da ita don yasan Ammi bazata dinga kwana dakin Hajja ba, to a jiya sai da Hajja ta saka baki har da nuna bacin ranta, wanda a baya idan yana ma Ammi magiyan ta koma gida sai dai Hajja ta kyabe baki ta kauda kai, wani lokacin kuma tace shi Mamudan ai bai biyota ba har yau balle ta kwashi kafa ta koma masa gida kamar bata da gata, to jiya dai kam Hajja ta saka baki kan Ammi tayi hakuri kawai ta koma don 'ya yanta amma ba don Mamuda ba, wanda hakan na nuni da ita ma abun ya fara isarta tunda Abba yaki waiwayansu balle ya biyo su har sannan, da yake Ammi na jin maganar Hajja kuma bata son duk abinda zai sosa ranta wannan yasa kawai ta yadda zata koma amma ba don ranta ya so ba sai don babu yanda ta iya, Shiru Maheer yayi yana kallon Hajja har ta kai aya rai a bace, Maheer ya ma rasa abinda zai ce tsabar mamaki, kullum sake mamakin mugayen halin Badiyyah yake, dama tun da ta kyallara ido ta ga ya shigo gidan ta saka kai ta fice daga gidan tunda tasan abinda ta hada, after few seconds Maheer ya girgiza kai very careful with his words kar ya tunzura Hajja ko ya bata ma Ammi rai yace "Hajja karya Badiyyah take gaskiya, jiya da na koma gida idonta biyu bata yi bacci ba don a parlor na sameta zaune har na tambayeta ya jarabawa tace min Alhamdulillah, amma ku nan tace maku ai tayi bacci kafin in koma gida, yanzu kawai abinda zai faru kamar yanda Ammi tace aje a samu Malaman sai mu je tare da ke ko Ammin ai suna wajen sanda abun ya faru sai su mana bayanin duk yanda aka yi a ajin, ae su baza su yi karya ba" Hajja ta katse sa tace "Ka ji ka da wata magana, zuwa za ayi a titsiye su kake nufi kenan, mutanan da za aje a lallaba su yi hakuri su bar ta ta koma ta ci gaba da jarabawanta kake so a je a kure, ai zuwa kawai za ayi a lallaba su ba wai a titsiye su ba, cuta ne an riga an cuceta kawai sae kuma neman mafita" Maheer ya gyada kai don bai son jan zancen yace "Toh shikenan, zan je makarantar ranan litinin in sha Allah" Hajja ta hade rai tace "Me ya hana baza ka je yau ba sae Litinin?" Yace "Yau asabar babu makaranta ai, sai Litinin din" Hajja tace "To Allah ya kai mu, amma ina lafiya za a kori yarinya da tayi shekara biyar tana wahala a makaranta ga uban kashe kudi" Maheer ya kalli Ammi yace "Za mu tafi ne yanzu Ammi?" A takaice Ammi tace "Ban shirya ba" Shiru yayi, sai kuma ya mike yace "Toh zuwa Anjima zan dawo" Ammi tace "Kar ka ba kanka wahala ban yi niyyar zuwa ko ina yau ba" Hajja tace "Aa ke kuma, anjima da la'asar kawai ya dawo ya kai ki gida tunda haka aka tsara idan ya so ranan litinin din sai yaje can gidan ya dauke ki ku je makarantar tare a ba Malaman hakuri, idan ma wani abu za a basu ko kaɗara na ne sai in siyar a basu" Maheer dai yayi masu sallama ya juya ya fita daga Parlon, shi dai ba kawai ya ji su ba ya kuma lallaba ya bar parlon ba tare da yayi masu musu ba, sun zata primary school ne da za aje a ba Malaman hakuri, motarsa ya shige ya bar anguwan, ban da yana da plan dinsa na barin Badiyyah a gidansa da yau ya koreta wallahi but there is still time. Da sallama Maheer ya shiga parlon Abba ta dalilin kiransa da yayi shi ma, don ko gida bai karasa ba daga gidan Hajja sae ga kiran Abba, hakan kawai yasa ya nufi gida maimakon gidansa da yayi niyyar komawa, tun shigowarsa gidan mood dinsa ya canza gaba daya don har bai son zuwa gidan saboda rashin Ammi da Mayraah, the house is soo empty without them, ya zauna ƙasan carpet ya gaida Abba dake duba wasu takardu, Abba ya amsa sannan yace "Yauwa kace Mayraah sun gama jarabawan ae ko?" Yace "Eh sun gama" Abba yace "Good, kaje ka dawo da ita da kayanta gaba daya yau" Maheer yayi shiru yana kallonsa shi ya so ace sai Ammi ta dawo kafin Mayraah ta dawo gidan, Abba yace "Ko kuna da wani plan da ku ka kulla kai da uwarka ne kake kallona haka?" Maheer ya sunkuyar da kansa bai ce masa komai ba, Calmly Abba yace "Wai ma tsaya tukunna in tambayeka, ana nufin ni a gidana bani da wani say sai abinda uwarka da danginta suka shirya? Yau ko ba Mayraah ba idan nayi niyyar kawo yara goma gidan nan akwai wanda ya isa yayi questioning dina akan haka? To a yau ba sai gobe ba nace ka dauko Mayraah ka dawo da ita gida tun da sun gama jarabawan" Maheer ya gyada kai cikin sanyin murya yace "Dama zan dawo da ita kamar yanda kace Abba, kawai nayi tunanin sai zuwa next week tun da basu gama project ba har yanzu" Abba yace "To yau nace ka dawo da ita ba next week ba, zata karasa project din a nan, wai ku kuna ma da imani kai da mahaifiyarka da danginta kuwa? That gal is an orphan, ta taso bata san kowa ba sai mu, all of a sudden this unforeseen circumstance came

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login