Showing 177001 words to 180000 words out of 249515 words

Chapter 60 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1553

dinga yi ita da Ladi wai suke ce min shegiyar marainiya annamimiya, har da ce min na rasa mashinshini shekarata arba'in" Hajja dake zaune tana kallonta tayi kasa da murya tace "Har ita Ammin?" Cikin kuka Badiyyah tace "Ba ita ta fara ba ma ta koreni daga Parlon, ni wallahi kar wanda ya sake shiga harkata babu hadina da su tunda basa so na, idan ba haka ba zan zagi mutum ba ruwana" Hajja dai ta kasa cewa komai amma gaba daya ranta yayi mugun baci, can tace "Ki rabu da su kowa yayi na gari don kansa, amma na Ammi ya fi bani mamaki, ban yi mamakin na Ladi ba tunda ita dama mahaukaciya ce er iska" Badiyyah ta kalleta da sauri tace "Ita ce ma tace in tashi in fita in bata waje fa nace maki, wallahi Ammi ce ta fara" Hajja tace "Kawai tace ki tashi ki fita??" Badiyyah ta fashe da sabon kuka tace "Eh mana" Hajja ta dau wayarta a hankali tace "Kira min Ammin" Badiyyah ta amshi wayar ta yi dialing number Ammi yana fara ring ta mika ma Hajja, Ammi na share parlonta, Mama Ladi kuma na zaune ta daura kafa daya kan daya tana cewa "Kema sai ki ji kin kara jin kwari a jikinki ba wai ki sakar min komai kamar baiwa ba kina zaune gefe daya kan darduma kamar me takaba, ko mutuwa Mera tayi a yanzu ai ya ci ace mun fara saka ma ranmu salama mun fara hakura" Sai da Ammi ta daga kai ta kalli Mama Ladi da ta ci gaba da kallon tv ko a jikinta maganar da tayi, Ammi dai ta ci gaba da sharan ba wai don tana jin dadin jikinta ba kawai Mama Ladi ce ta tilasta sai tayi shara karfi da yaji, wayar Ammi ne ya fara ring, ta mike ta dau wayar Mama Ladi na kallonta tace "Waye?" Ammi tayi shiru at first, sai kuma a hankali tace "Hajja ce" Mama Ladi ta mike da sauri ta fizge wayar tace "Ina ake dagawa?" Ammi dai ta kasa cewa komai, a fusace Mama Ladi tace "Don Allah ki daga min kar ya katse" Ammi tayi picking call din, Mama Ladi tace "Salama alekum, yaya ina wuni" Daga daya bangaren Hajja tace "Ina Ammin?" Mama Ladi tace "Sallah take shine na daga, ya aka yi ne?" Hajja tace "Ban sani ba, halan wajenki Badiyyan taje da zaki ci mata mutunci Ladi?" Mama Ladi tace "Wacece kuma Badiyyah? Ayyo wai Badiyyah jikar ki? Wato don ba a bar ki kin kwana cikin barayi ba shine har bakinki zai kara furta sunan Badiyyah gatsal Hajja?" A fusace Hajja tace "Kar ki gaya min maganar banza Ladi, ke wace irin munafukar mace ce me hada fitina ne? Ki ba Ammi wayar ba dake zan yi magana ba" Mama Ladi tace "Wallahi bazan bata ba, in bata wayar ki kara daga mata hankali tunda in ta mutu ni nayi asara ba ke ba, ki bar mata taji da ɓacewar er ta mana Hajja, duk ke da Badiyyah fa ku ka dinga juya matar nan har ta kora er ta kwaya daya ta shiga duniya saboda son zuciya irin taku, gashi kun ja mata kishiya me diri har Mamuda ya dauke kishiyar sun koma dankareren sabon gidansa da ya gina ya bar ita Ammin a walakance a nan cikin yaku bayi Mashir ke gaya min jiya da daddare, wa ya ja mata banda ke da jikarki da tsinanniyar surkarta, Wallahi ban taɓa ganin uwar da bata son kwanciyar hankalin 'ya yanta ba irin ki Hajja, ko ni da ɓan taɓa haihuwa ba bazan yi wannan abinda kike yi ba Hajja, kuma in baki yi hankali da yarinyar nan Badiyyah ba wallahi zata sa a rataye ki muyi ta koke koke muna nema maki rahama wajen Allah" Hajja da ranta yayi mugun baci tace "Ladi ni kike gaya ma wa ennan maganganun? Ni Ladi?" Mama Ladi tace "Toh me na ce? Ni dai Allah ya gani ba rashin kunya na maki ba gaskiya nake gaya maki, haka kawai in ki gaya maki Allah ya kama ni, aa ba ruwana wallahi" Hajja tace "Ba komai, Nagode Ladi, ni dai kike ci ma mutunci haka ko? Ita Ammin ta sa ki gaggaya min wannan maganganun ko?" Mama Ladi tace "Wacece Ammi? Ammi da yanzu haka gata can Mashir ya sa mata ruwan drif, ni dai ba ruwana sai anjima ba rashin kunya na maki ba gaskiya ce dama ance daci gareta" Daga haka ta karasa gun Ammi da sauri tana mata alamar ta katse, Ammi ta katse wayar tana kallon Mama Ladi babu ko kiftawa don kalmar da tayi wai Mamuda ya dauke kishiya sun koma dankareren sabon gidansa ne kawai ke ta yawo kan Ammi, can a hankali Ammi tace "Sabon gida ya koma da matar?" Mama Ladi dake share zufar goshinta tace "Wa?" Ammi ta kasa cewa komai, Can Mama Ladi ta tuna maganganunta a waya, da sauri tace "Haba duk shirgata nake ko zata dawo hankalinta fa, ba nan Mamudan ya kwana jiya ba? Kawai na gaya mata haka ne don in gigitata ta shiga taitayinta ta kyaleki kiyi zaman aurenki lafiya, amma wannan Amarya ai ina jin tana gidansu yanzu haka tun da gashi daga zuwanta komai ya kara tabarbarewa, ai shi Mamudan ba wawa bane" Ammi dai bata sake cewa komai ba, Mama Ladi ta dau tsintsiyar ta ci gaba da sharan tace "Dama baki yi niyyar yi ba, tafi ki zauna kawai ni da kika mayar boyi boyi saboda daga kauye nake sai in ta yi ai tunda za a ban in ci in koshi" Ammi ta koma ta zauna amma zuciyarta ya kasa kwanciya da maganar sabon gidan da Mama Ladi tayi. Mayraah na zaune parlon Maman Hanan da yamma don ranan aka yi sadakan uku, zuwa sannan ma duk mutane sun watse sai yan uwanta, Sosai mutuwar yarinyar ya girgiza uwar gashi tun ita bata sake haihuwa ba shekarar yarinyar takwas, Mayraah ta kalli wayarta da yayi vibrate taga number Dr Khalil da ta kira dazu da safe ne da bai daga ba sai yanzu ya biyota, tayi silencing wayar tana kallon Maman Hanan tace "Aunty bari in shiga gida, sai gobe idan na shigo in sha Allah, sai ki basu takardan da na rubuta maki maganin a siyo maki ki sha zaki samu bacci in sha Allah" a hankali Maman Hanan tace "To Nagode Ilham, baki debi abincin ba kuma" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Na koshi wallahi, nima wanda na dafa ban cinye ba" Maman Hanan tace "Toh shikenan sai kin shigo goben" Mikewa Mayraah tayi suka yi sallama da mutanen parlon sannan ta fita ta koma gida, bayan ta kulle gate din ta shiga daki ta yi dialing number Dr Khalil, sai da ya kusa katsewa ya daga tayi sallama ya amsa sannan ta gaishesa, yace "Wa ke magana?" Tace "Ilham ce" Yace "Oh, Ilham sorry u called tun dazu, ina busy ne wllh" Tace "Ba damuwa, ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, gobe ki shigo asibitin da safe kawai" A hankali tace "Toh" Yace "Yeah, in kin shigo sai ki kirani" Tace "To Allah ya kai mu Nagode" Sallama suka yi ya katse wayar, haka kawai taji gabanta na faduwa, ta zauna gefen katifa tana tunanin yanda zata fara aiki a babban asibitin nan cikin manyan health workers da suka yi shekara da shekaru a aikin, za ma ta iya kuwa? Anya ma zata iya tuna abubuwa yanzu don gani take kamar kanta baya ja, haka nan ta kwana cikin zulumi da tunani iri iri a ranta, gari na wayewa bayan ta shirya cikin doguwar riga ta saka hijab dinta har kasa da tayi iron, shayi kawai ta iya sha don duk a tsorace take, bayan ta gama ta dau nose mask dinta ta saka sannan ta dauki handbag dinta ta fita ta kulle gidan, sai da ta fara lekawa gidan Maman Hanan ta gaisheta ta tambayeta ko ta samu bacci, Maman Hanan tace "Ai kam na samu bacci sosai Ilham, Nagode fita za ki yi ne?" Mayraah tace "Eh zan tafi makaranta" Maman Hanan tace "Toh Allah ya tsare sai kin dawo" Daga haka Mayraah ta fita ta kama hanyar cikin garin Abuja, tana isa asibitin wajen karfe goma saura bugun zuciyarta ya tsananta ita kanta ta rasa me yasa ta zama so tensed haka, sau biyu ta kira Dr Khalil bai daga ba, ta zauna reception bayan ta gaida wasu nurses da ta gani, wata nurse na tambayarta ko tana da appointment da Dr ne, Mayraah ta girgiza kai zata yi magana sai ga Dr Khalil ya shigo Reception din, yana ganin Mayraah yace "Meet me at my office" Daga haka ya wuce sama ta mike ta bi bayansa zuwa office din nasa, bayan ta shigo ta gaishesa ya amsa yace "Zauna mana" Zaunawa tayi kan kujera tana kallonsa, wani leda ya dauko ya ajiye mata kan table yace "Ur Scrubs and shoes, Allah ya sa su maki" Mayraah ta dau ledan, Dr Khalil yace "Ya kamar kina tsoron ledan" Ɗan murmushi tayi tace "Aa" Yace "Zaki fara aikin yau ai?" Mayraah ta rasa abinda zata ce, ya nuna mata wani kofa a office dinsa yace "Ki shiga nan ki gwada scrubs din ko za su maki da shoes din" Ta gyada masa kai sannan ta mike tana rike da ledan ta nufi kofar da ya nuna mata ta bude ta shiga, bayan few minutes ta fito sanye da hijab dinta tana kallonsa tace "Sun yi" Yace "To me yasa baki bari a jikin ki ba kika cire, u are resuming work today" Mayraah dai kawai tayi murmushi ta koma ta zauna tana kallon sa, kwankwasa office din aka yi yayi izinin shigowa wata nurse ce ta shigo warce bazata haura 30 years ba ta gaishesa da ladabi, yace "Morning Hafsat, ga sabon staff dinmu zan damka maki ita yanzu, ki dinga guiding dinta pls, for now she is not working amma komai za ki yi you make sure tana kusa da ke tana gani" Nurse Hafsat ta karaso tana murmushi tace "To ba damuwa sir, in sha Allah i will do so" Yace "Transferring dinta aka yi zuwa nan ko da wani ya tambayeki...." Hafsat tace "In sha Allah sir" Dr Khalil ya kalli Mayraah yace "Nurse Ilham, follow your colleague zata nuna maki inda zaki saka scrub din ki" a hankali Mayraah tace "To Nagode" Daga haka ta mike tana rike da ledan ta bi bayan Nurse Hafsat suka fita, suna sauka reception din few nurses dake wajen suka bi su da kallo, Nurse Hafsat ta kai Mayraah changing room tace "You are welcome to be part of Us in this great hospital Nurse Ilham" Mayraah tana murmushi tace "Thank you" Mayraah na gama saka scrub din ta fito daga bandaki Hafsat tace "Waow kin ga yanda ya maki kyau kuwa kamar sai da aka auna ki kafin a dinka" Mayraah dai ta kirkiri murmushi, Nurse Hafsat tace "You look smart on this scrub" Mayraah was a bit comfortable cikin uniform din saboda me Hijab ne duk da karamin hijab ne, unlike yanda taga wasu nurses babu hijab sai scrub cap amma tana tunanin ba musulmai bane don Hafsat ma nata uniform din da karamin Hijab a kai, Hafsat tace "Wani makarantar kika yi?" A hankali Mayraah ta gaya mata school din da ta gama, Hafsat ta wara ido tace "Da gaske? Wani department?" Mayraah ta gaya mata, Hafsat tace "Lahhh, nima shi nayi ai, mun gama kusan 8 years kenan" Mayraah da bata son zancen tayi saurin cewa "Ayya, ina zan bar jakana yanzu?" Wata nurse ce ta shigo wajen ta kalli Hafsat sannan ta kalli Mayraah, can ta maida dubanta kan Hafsat tace "There is an emergency" Daga haka ta juya ta fita, Hafsat ta amshi jakan Mayraah da sauri ta bude wani safe ta saka ciki da ledan second scrub da takalmin Mayraah sannan ta kulle safe din ta ja Mayraah suka fita daga room din da sauri.
[7/19, 12:06 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na zaune wani ward da babu kowa ciki ta daura kanta kan gadon idonta a lumshe, ga cup din Caffeine drink da bata shanye ba kan table dake kusa da ita, Dr Khalil ne ya shigo ward din tare da wani Dr Hamid, duk suka nufota Dr Hamid na kallonta yace "Why didn't u lie down?" Mayraah ta daga kai da sauri tana kallonsu don bata ji shigowarsu ba alamar bacci ya fara daukarta, Dr Khalil ya kalli cup din coffeen yaga rabi kawai ta sha yace "Me yasa baki shanye ba?" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Ya isheni" Wata nurse ce ta shigo ward din rike da blood pressure gauge, Dr Hamid yace "Check the Bp again" Nurse din ta kama hannun Mayraah ta hau duba Blood pressure dinta, bayan ɗan lokaci da dago tana nuna masu tace "It's almost normal sir" Dr Khalil na kallon Mayraah yace "Ki kwanta ki yi relaxing zuwa anjima kadan" Mikewa tayi ta cire takalman kafanta a hankali sannan ta hau kan gadon ta kwanta, Dr Hamid ya juya suka fita tare da Dr Khalil, Dr Hamid na kallon Dr Khalil yace "When was she employed here? I have never noticed her, naga kuma babu vacancy, in ma akwai 'ya yan masu ƙasar suke ba ma ae" Dr Khalil ya ɗan shafa kai yace "Ai ina jin transfer aka mata..." Dr Hamid na gyada kai yace "But she is really good gaskiya, irin nurses da nake son aiki da kenan, tana da nutsuwa da composure wajen aiki she did all the sutures perfectly without waiting for directive, ba ko wace nurse ce zata iya ba, Intradermal suture fa, even Dr Balogun commended her" Dr Khalil na gyada kai yace "Nima na gani, i was also surprised, stress din aikin ne yayi weighing dinta down, dama kuma bata da lafiya tace min" Dr Hamid yace "She needs to work on her diet, and decrease her carbs intake, hypotension ai ba abu bane me kyau" Dr Khalil yace "Gaskiya kam" Mayraah na bacci wajen karfe shidda saura Dr Khalil ya shigo ward din da take, ya taɓa gadon da take kai ta bude ido a hankali, yace "How are you feeling now?" Ta mike zaune tace "I feel better" yace "Pls avoid eating lot of carb food Ilham, bai kamata jininki na kasa haka ba, more veggies to ur diet" Ita dai tayi shiru, yace "Yanxu yamma bai yi ba kice za ki koma Suleja? And I don't think it will be possible kullum kina komawa can kina zuwa nan, the distance..." Mayraah tayi saurin katse sa tace "Ai mun yi magana da Aunt dina da mijinta tun da kace zaka samar min aiki sai suka ce ko hostel na student ne sai in samu a nan Abuja in zauna saboda da nisa daga can garin ace in dinga zuwa nan kullum, duk sanda bana da aiki sai in je sulejan" Shiru tayi don ita kanta sai taji kamar maganar bai mata ba a kunnenta, shi dai Khalil kallonta kawai yake as if observing something, har ta tsargu ko ya gano karya take ne, gabanta dai sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, after few seconds of silence yace "Shikenan, amma at the first place da nace zan samar maki aiki ai kamata yayi ita aunt din ko Uncle dinki wani ya biyoki nan don tabbatar da hakan tunda yanzu kowa yasan yanda duniyar ta dawo, amma naga duk basu yi hakan ba" Nan gaban Mayraah ya tsananta bugawa cikin few seconds tayi cracking brain dinta ta samo abinda zata fada tana kallonsa tace "Ranan da muka zo da matar nan da yarinyarta ta rasu ai tare muke da aunt din nawa, ita komawa gida tayi ta bar mu, to nace mata nan asibitin ne...." Dr Khalil na kallonta yace "Even at that Ilham, amma ya ku ke da ita aunt din taki na Suleja? I mean dangantakar ku?" Mayraah taji hankalinta ya fara tashi, amma ta dake tana kallonsa tace "Kawai ta taɓa auren dad dina ne kafin ya rasu" Dr Khalil yace "Ur stepmom kenan?" Ta gyada masa kai tana kokarin sauka daga kan gadon alamar tambayoyin sun isheta, Dr Khalil yace "How about ur mum?" Ta wani kallesa a takaice tace "But i told u my parents are late" Ita kanta tasan she sounds pissed off, Dr Khalil yace "Dangin mamanki da babanki fa?" Tace "Dr... suna bauchi, admission din nan ya kawo ni Abuja ban san anyi cancelling dinsa ba, if not ni bani da kowa a Abuja ai sai stepmom dita a suleja" Dr Khalil na nodding kansa yace "Ohk i get, to bari zan kai ki inda zaki yi passing night din yau don yanzu yamma yayi kice zaki koma Suleja, amma ki fara kiran stepmom din taki ki sanar masu tukun, sai ku samu wani alternative din inda zaki zauna a Abuja" a hankali Mayraah tace "To" a ranta kuwa tunanin ina zai samar mata ta kwana take, kawai ita dai taji har ranta ta yarda da Dr Khalil don yawancin abubuwa idan yana yi ma kallon Maheer kawai take masa, kusan personality dinsu da halinsu daya, tun daga caring, tausayi, sannan he is also very free like Maheer, uwa uba kuma ta lura he is also observant just like Maheer, dole sai ta tsaya at alert incase ya mata tambaya ta jefa masa amsa babu bata lokaci yanda bazai sa zargin komai a ransa ba, Da sauri ta kallesa don har a sannan kallonta yake as if dai yana nazari, tace "To in kwana a asibitin kawai mana" Yace "Aa ai asibiti ba wajen kwana bane idan ba dole ba, kuma u need much rest, yanzu ki tashi ki dauko stuffs dinki, let me get my car key don i will still have to come back akwai surgery da za mu yi bayan magrib...." Mayraah tace "Toh" Sai da ya fita ward din sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login