Showing 84001 words to 87000 words out of 249515 words
duk da bansan me ya faru ba" Mayraah ta fashe da kuka ta kasa ce masa komai, cikin sanyin murya yace "Ki min alkawarin kuna gama final exams za mu tafi a daura mana aure Mayraah, ki min alkawarin baza ki canza ra'ayinki ba idan lokacin ya zo" Tana share idonta tace "Bazan canza ra'ayina ba sai in kai zaka canza naka, sai in kai ne zaka fasa aurena Sir" Yayi wani murmushi yace "The last thing i will do on earth is to deny u Mayraah, in kika ga ban aureki ba to bana numfashi ne, i am making you this promise" Wayarsa ne ya fara ring, duk suka juya suna kallon wayar, Maheer ne ke kira still, Musharraf ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallonta, ita dai sunkuyar da kanta tayi, Musharraf ya dauko wayar, da sauri ta rike hannunsa cikin rawan murya tace "Me zaka ce masa?" Calmly yace "I know what to tell him" Daga haka ya mike ya nufi kofa ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, bayan some minutes Musharraf ya dawo dakin yana kallonta, Sunkuyar da kanta tayi, a hankali yace "Tashi mu je Baby" Ƙin tashi tayi kuma bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita ya mika mata hannu, kauda kai tayi hawaye cike idonta ta sauko daga kan gadon tana kallonsa tace "What did u tell him?" Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "You know I won't tell him u are in my house, so no need to worry" A takaice tace "I won't be worried even if u should tell him that" Daga haka ta dau yoghurt din da ya ajiye mata ta sha kadan sannan ta nufi kofa da sauran, ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya sauke ajiyar zuciya, wayarta da ya ajiye a dakin ya daukar mata da magungunanta sannan ya dau makullin Motarsa ya fita, parlor ya sameta a tsaye, ya karaso inda take tsaye, ta kallesa tace "How comfortable are you in a dusty house?" Ya langwabar da kai yace "I was sick" Bata sake cewa komai ba, ya mika mata wayarta ta amsa sannan suka fita parlon, tana tsaye jikin motarsa bayan ya kunna to warm it up, ya zagayo inda take yana facing dinta yayi kasa da murya yace "I still want to remind u of how insecure i am with ur brothers Mayraah" Tana kallonsa a hankali tace "Insecure in what aspect?" Yace "Yanzu akwai aure tsakaninku" Da mamaki Mayraah tace "So u think ni zan iya auren daya daga cikin wa enda na taso nake ma kallon yayyina na jini? Mu yi aure da su as husband and wife or what? I don't understand" Tunanin hakan sai da yasa Mayraah ta fara jin wani sanyi na shigarta ta yaya ma hakan zai yiwu? How? tana girgiza kai tace "That's an abomination to me and them also" Matsawa tayi da sauri tana zaro ido ganin he is trying to lean on her, yayi hanzarin rikota onto him, tace "Meye haka?" Yayi kasa da murya yace "Not even a goodbye kiss Baby?" Kasa ce masa komai tayi, kawai wanda yayi mata ranan a gidansa ya fado mata, she wanted resisting this but he left her with no space for that..... Har suka bar unguwan Mayraah bata ce komai ba a motar, banda kamshin turarensa babu abinda ya cika mata hanci, kuma daga jikinta kamshin ke tashi, Bayan tafiyar kusan minti ashirin Mayraah ta gansu a area din makarantar su ya nemi waje yayi parking, still ita dai bata ce komai ba, ya jinginar da kansa da kujeran motar ya lumshe ido, bayan few minutes wayarsa ya fara ring, dauka yayi, yayi picking ganin Maheer ne ke kira, ita dai Mayraah idonta na kan titi, Musharraf yace "Yea sai ka wuce traffic light, i parked in front" Yana fadin haka ya Katse wayar ya juya yana kallon Mayraah da taki cewa komai har sannan, ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Are you still angry Baby?" Ita dai bata ce masa komai ba, ɗan murmushi yyi caressing her hand a hankali yace "I am sorry Baby, u know i love you" Mayraah ce ta fara ganin motar Maheer, Musharraf na sighting dinsa ya dau wayarsa ya kirasa yace yayi parking kawai, juyawa yayi yana kallonta yace "I told him kina school, and i met u here...." Ta dauke idonta zuwa daya side din, yace "Za ki shigo school gobe?" Juyawa tayi ta kallesa, ta marairaice tace "Are you coming?" Yace "Sure" Tace "Ohk" ganin Maheer yayi parking Musharraf ya sauka daga motarsa, Maheer ya karaso ya basa hannu suka gaisa, ita dai Mayraah taki sauka daga cikin motar, Musharraf ya zaga ya bude mata motar yana kallonta, Tayi kokarin ganin hawayen dake taruwa idonta bai zubo ba ta sauko daga motar, Yoghurt din da ta bude ya dauka da ledan magungunanta ya mika mata, ta amsa ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Thank you" Musharraf ya kalli Maheer dake kallonsu, yayi feigning smile yace "I will be on my way Dr" Maheer yace "Thank you so much Dr Musharraf" Musharraf na kallon Mayraah yace "Take care of ur self" Daga haka ya zaga ya bude front seat ya shiga ya bar wajen, Maheer ya amshi ledan hannunta da drink yana kallonta yace "Mu je" bata yarda ta kallesa ba ta nufi motarsa tana share hawayen dake sakko mata, back seat ta bude ta shiga, ya shiga motar suka bar wajen, har suka yi nisa Maheer ya rasa me zai ce mata, ita dai sai goge hawayenta take da hijab din jikinta..... Mamaki ne ya cika Mayraah ganin inda ya kawota, bayan yayi parking a compound din gidan ya sakko ya bude mata side dinta yana kallonta, tayi karfin halin cewa "But me yasa zaka kawo ni nan yaya?" Yace "Nobody is at home" Shiru tayi ta kasa cewa komai, She knows he isn't saying the truth, lkci daya maganganun Hajja na dazu da safe ya fara dawo mata, to dama ta yaya Ammi zata zabeta akan Mahaifiyarta, shikenan Hajja ta rabata da Amminta kenan, shkkn bazata sake zama gidan da ta taso take tunanin gidan iyayen da suka haifeta ne ba, ta kalli Maheer dake kallonta shi ma ya kasa cewa komai don yasan ma tunanin da take, lkci daya duk jikinsa yayi sanyi, cikin rawan murya tana girgiza masa kai tace "Yaya bazan iya zama da Aunty Haseenah ba, kai ma kasan bata so na, ko in nemi favor wajen Hamidah in zauna gidansu har in gama exams?" Maheer ya kamo hannunta ya sakko da ita daga motar yace "Haseenah bata isa ta zama obstacle na zamanki a gidana ba Mimi, it's my house not her's, kuma dolenta ta zauna dake in dai tana son zama da ni" Mayraah ta fashe da kuka don yanzu kuma ganin abubuwan take kamar a mafarki, ta yaya ma za ace Ammi da Abba ba su ne suka haifeta ba, anya ba mafarki ma take ba tukun, why will they even say Ammi and Abba are not her parents, or are they pranking her?? Maheer ya kasa ci gaba da jure kukan nata ya rungumeta yana jin kukan nata har ciki ransa yace "Plss stop this Mimi...." Sai da tayi kukanta me isanta sannan ya dago kanta yana kallonta, he is just short of words, ya ma rasa wani kalma zai yi amfani da shi wajen rarrashinta, can dai yayi karfin halin cewa "Kiyi hakuri Mimi, we all never bargained for this...." Kai Kawai ta gyada masa, ya share mata idonta sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan, ko parlor bai tsaya da ita ba ya tafi da ita dakin da yayi mata furnishing duk a yau, hatta kayanta ya kwaso mata daga can gidan with the help of Usman, Mayraah ta karasa cikin dakin ta zauna gefen gado tana goge idonta, duk ta ma gaji da kukan she's exhausted with crying, durkusawa yayi gabanta yace "Me zan siyo maki ki ci Mimi?" Tayi shiru tana kallonsa ko kiftawa babu, yace "Anything?" Ta gyada masa kai kawai, mikewa yayi yace "Toh kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah, i will be right back" Bata san sanda tace "Are you leaving me all alone with her?" Maheer ya girgiza kai yace "Ae bata nan, kuma ko tana nan babu abinda zai faru" Daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita.... Tun safe sai yanzu hankalin Maheer ya kwanta, don ko da suka fara waya da Musharraf ya sanar masa suna tare da Mayraah bai samu rest of mind ba har sai da ya ganta, yana driving zuwa inda zai samo mata abinci kiran Usman ya shigo wayarsa.... Mayraah ta gaji da zama ta mike a hankali tana kallon akwatunan kayanta dake dakin, bathroom ta shiga taga duk wani abu da zata bukata yana cikin bandakin, tayi wanka tayi alwala sannan ta fito daga bandakin, akwati daya ta bude ta ciro wani kayan da zata sa da hijab, sannan tayi sallan Isha.... Maheer na dawowa gida bayan yayi parking a parking lot wayarsa ya fara ringing, yana dubawa yaga Haseenah ce ke kiransa tun dazu take kiransa yaki dagawa, yayi ta kallon wayar daga karshe ya daga ya kai kunne, tun ranan da ya kai ta gida sai yau ya daga kiranta duk da kusan kullum sai ta kirasa yafi sau goma amma baya dagawa, daga daya bangaren Haseenah ta fashe da kuka cikin tashin hankali tace "Maheer yanzu zuwa gidanmu kayi ka tona min asiri akan abinda ni nasan ban taɓa aikatawa ba a rayuwata ta duniya? Maheer me kaje kace ma iyayena da suke ta kirana haka tun safe?" Maheer dake sauraronta yace "Haseenah dama da na ajiye ki kofar gidanku nace ki tafi wani waje daban ne?" Cikin kuka tace "Ta yaya kake tunanin zan iya shiga gida Maheer? Me zance masu idan na shiga? Did u even know who my mum is??" Maheer yace "Ina kika tafi?" Ta marairaice tace "I was confuse kawai na tafi gidan kawata, idan na shiga gida ban san me zan ce masu ba" Maheer yace "Bani address din gidan kawar taki in zo yanzu" Ta zaro ido gabanta na faduwa sosai, da sauri ta kauda zancen tana shesshekan kuka tace "Maheer ka gaya min me kaje kace ma iyayena ko hankalina zai kwanta? Wllh na kasa sukuni tun dazu, gashi na ki daga kiransu, what did u say to them?" Yace "Ohk, zuwa nayi nace masu ina neman alfarman su sanar maki kanwata Mayraah zata dawo gidana da zama saboda final exams dinta.... Na maki magana kin nuna ke baki amince ba, don haka shi yasa na zo har gida na sanar masu su da suka isa da ke, domin akan haka za mu iya samun issues a zaman aurenmu da ke wanda bai kamata ba, don kuwa yanxu haka bakya gidana" Shiru Haseenah tayi tana sauraronsa da mugun mamaki trying to understand what he is trying to say, can dai tace "Ban gane Mayraah zata dawo gidanka ba Maheer? Wace Mayraah din? Da can daga gidanka Mayraah ke zuwa makaranta?" Yace "Look Haseenah, i am not forcing you to stay under same roof with Mayraah, kawai dai nasan ke zan iya canza ki at anytime amma ita bazan iya canzata ba tunda jinina ce ita, kuma in har kina so na da gaske dole ki so jinina, don haka ni ba da gadara nake ce maki Mayraah zata dawo gidana ba, Aa alfarma nake nema a wajenki kanwata ta dawo gidana for sometimes don zata fara final exams dinta, in kuma kina ganin baza ki iya ba to bana jin zan iya ci gaba da rayuwa da warce bata son jinina, it's now left for u to decide, though it's request not command...." Haseenah da taji zuciyarta na tafarfasa amma tunda dai neman hanyan komawa dakinta take asirinta a rufe, ta dake tace "Atohh tunda ba kaina zata zauna ba ina ruwana da ita Maheer, ba fa kaina zata zauna ba" Yace "Glad u reason dat..." Ita dai tayi shiru tunani iri iri na yawo a ranta, Maheer yace "Kina ina in zo in dauke ki yanzu?" Tace "Gaskiya ban shirya ba, sai dai gobe" Yace "Allah ya kai mu"
MAYRAAH Is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
[6/24, 6:01 PM] Khaleesat Haiydar💖: Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga our very own Barrister Inna (Aunty Fatima) Allah Ubangiji ya iya maki, ya raya maki zuri'a, ya kawo cinikin turaren wuta kaca kaca ki bude plaza a Gombe kina daddaga shoulders🥰
Lush and Scrumptious (The Mardiyya without letter R) da kawarta ICE, kuma na gaisheku da fatan alkhairi Allah ya kawo maku mazaje na gari, Sis Aisha Abba (Ummu Janan) i greet you and Baby Janan, Allah ya raya maki ita yayi mata albarka🥰
My lovely fans, i love u all as always, Allah ya iya maku💖
Mayraah na zaune kan darduma tun bayan da ta idar da sallahn isha bata tashi wajen ba tayi nisa tunanin da take ta ji an bude kofar dakin, da sauri ta juya tana kallon kofar, Maheer ya shigo da sallama rike da plate da ledan takeaway din abinci a hannunsa, karasawa yayi kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan ya ciro takeaway din ciki sannan ya juye a plate, ya daga kai suka hada ido ya sakar mata murmushi yace "Ur favorite" Ta sauke idonta tace "Thank you" Yace "Kinyi wankan?" Ta gyada masa kai, ya mike yace "Ohk bari in saka maki kayanki a press kafin ki gama cin abincin" Yana fadin haka ya mike ya nufi akwatunanta guda uku dake dakin ya bude guda daya, ta maida dubanta kan abincin gabanta ta fara ci a hankali, Absentmindedly take cin abincin da ko taste dinsa bata ji a bakinta, bayan wani lokaci ta juya taga ya bude wani akwatin with her inners inside, da sauri ta ajiye spoon din hannunta tace "Aa, ka bar min wannan zan yi da kaina" Ya juya ya kalleta yace "Ohk" maida akwatin yayi ya bude wani, ta ci gaba da cin abincinta, har ya gama jera mata duk kayan a press ko quarter din shinkafar bata iya ta ci ba, ya dawo kusa da ita yace "You are not eating Mimi, ko baki son shinkafan ne yau?" A hankali ta matsar da plate din tace "Na koshi" Yace "Ko in kawo maki Milo?" Ta girgiza masa kai tace "I am full" ya dau ledan maganin da Dr Musharraf ya siya mata ya fiddo su yana duba su, ita dai kallonsa kawai take, after examining the drugs ya ballar mata su ya mika mata yace "Take" ta mika hannu ta amsa sannan ta sha da ruwan goran dake gefenta, yace "Tunda baza ki ci abincin ba ni bani in ci" Daukan plate din tayi ta mika masa ya amsa, ta mike ta shiga bandaki zata wanke bakinta, Maheer ya juya yana kallon gefensa, Hijab dinta ya tsura ma ido for few seconds, can ya dauka ya kai hanci yana perceiving din scent din Hijab din, dai dai nan ta fito tana cewa "Yaya babu toothpaste a ciki" Shiru tayi tana kallonsa, ya ajiye hijab din da sauru yace "Oh ok bari in dauko maki yanzu" Yana fadin haka ya ajiye plate din hannunsa ya mike ya fita daga dakin, Mayraah ta karasa bakin gadon ta dau Hijab din nata ta kai hanci ita ma, ajiyewa tayi ta sauke idonta kasa ta juya a hankali ta koma inda take tsaye, can kuma ta sake komawa gun Hijab din ta dauka ta shiga bandaki ta saka a bucket ta zazzaga detergent dake cikin bandakin ta bude pampo, yana dawowa dakin ya kwankwasa mata bathroom din, ta bude kofar ta amshi toothpaste din sannan ta kulle, juyawa yayi ya dau abincin da ta bari ya fita daga dakin, Mayraah ta gama wanke bakinta ta dauro alwala ta fito, kwanciya tayi gefen gadon ta lumshe ido after so many thought that ran through her mind bacci ya dauketa, Wajen karfe goma Maheer ya shigo dakin, ya karaso kan gadon yana kallonta yace "Kinyi alwala kafin ki kwanta Mimi?" Kai kawai ta gyada masa idonta a lumshe, yace "To gyara kwanciyarki" Ta koma middle of d bed ta kwanta, ya rufa mata duvet yace "Don't forget to pray" Ta gyada masa kai, ya rage AC, ya kashe wutan dakin gaba daya sannan ya fita ya kullo mata kofar. Washegari da asuba Maheer zai tafi masallaci ya shigo dakin don tada ta, bai yi mamakin ganin ta tashi ba don a gida karfe biyar take tashi dama, ya fita zuwa masallaci, Mayraah na idar da sallah ta koma ta kwanta, for the past 4 days sai jiya tayi bacci sosai da daddare yanzun ma kuma wani baccin take ji kilan har da maganin bacci a magungunan da Musharraf ya bata, karfe takwas da kusan rabi ta farka, da sauri ta mike bayan ta tuna ai zata school yau, ta shiga bandaki don yin wanka, kafin tara da rabi har ta gama shiryawa, ta zauna gefen gado tayi jim tana bin dakin da kallo, babu abinda babu ciki, and it look beautiful, can dai ganin lokaci na wucewa kuma karfe goma take da lectures ta mike ta nufi kofa ta bude a hankali, main parlor ta shigo, ta dinga bin parlon da kallo, sosai parlon ma ya hadu yayi kyau, cream with touch of gold ne yawancin abubuwan parlon, ta kalli hanyar kitchen sannan ta nufi can, tana bude kofar ta gansa tsaye yana peeling Irish, ya juya yana kallonta yace "Good morning Mimi" A hankali tace "Good morning Yaya" Yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin yi bacci sosai?" Ta gyada masa kai, yace "That's great" Karasawa tayi cikin kitchen din tace "Kawo in fere" Yace "Aa ke da baki da lafiya, kawai kije kiyi kwanciyarki i will serve u breakfast in bed...." Ɗan murmushi tayi wanda iyakarsa lips