Showing 174001 words to 177000 words out of 249515 words

Chapter 59 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1568

wancan gidan..." ta fadi haka tana nuna gidan, Matar tace "Ayya, Allah sarki, bismillah sannu da zuwa baiwar Allah, ai ko naji yan anguwa sun ce an tare a gidan ni dai ban ga kowa ba, ashe kuwa da gaske ne" Mayraah dai ta bi ta har cikin gidan ta zauna kan kujera a karamin parlon ta kara gaisheta, matar ta amsa da fara'a tace "Sannu da zuwa anguwanmu, ya sunanki?" Mayraah bata san sanda tace "Ilham, sunana Ilham.... ni daliba ce ina karatu ne cikin garin Abuja, shine aka samar min daki a nan in zauna" Matar tace "Allah sarki, toh Allah ya baki sa'a Ilham, ai ko zaki ji dadin zama cikinmu wallahi duk bamu da matsala, ni ana ce min Maman Hanan, yanzu zan zaga dake duk sauran gidajen a san juna" daga haka ta mike tace "Bari in dauko maki ruwa ki sha sai mu tafi" Mayraah dai sai kallon yarinyar dake kwance da bazata wuce shekara 8 ba tana numfashi ta baki take, har matar ta dawo Mayraah ta kalleta tace "Bata da lafiya ne yarinyar can?" Matar ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi Hanan ba lafiya yau kusan sati daya ko makaranta bata zuwa, tun dazu ma nake ta goge mata jiki da ruwan sanyi don naji zafin yau na daban ne da sauran ranaku, gashi zazzabin baya sauka wallahi" Da mamaki Mayraah tace "Kuma ba a kai ta asibiti ba har yanzu Aunty?" Maman Hanan tace "Baban magunguna ya siyo mata a chemist ake ta bata, wanda ya fara siyowa har sun kare ya sake siyo wasu" Mayraah couldn't stop looking at the woman with surprise, a ranta tana mamakin me yasa wasu iyayen ke irin wannan sakacin ace yaro bai da lafiya critically amma sai a wani je chemist a siyo masa magani, mikewa tayi ta tafi kusa da Hanan din ta durkusa tana kallonta don ko rufe baki bata iya yi kamar warce mura yayi ma mummunan kamu, and she is breathing noisily, Mayraah ta bude bakinta tana duba ciki, lokaci daya ta mike tana kallon Maman Hanan tace "Ya kamata a tafi da ita asibiti yanzu Aunty" Da damuwa Maman Hanan tace "Ko?" Mayraah tace "Gaskiya, a nemo adaidaita sahu a tafi asibitin kar a bata lokaci" Wani irin numfashi Hanan din ta fara yi, Maman Hanan ta maza ta dauketa tana jijjigata tace "Haka fa take yi tun dazu sai numfashin yayi kamar zai dauke wllh sai ya dawo, bari in kira baban nasu" Mayraah tace "Mu je kawai asibitin idan mun je can sai ki kirasa" A tare suka fita gidan, Maman Hanan duk ta gigice ko kulle gidan bata yi ba suka nufi titi, Mayraah dai bata karbi yarinyar a hannunta ba, a haka suka samu adaidaita sahu, wani Asibiti nesa da Sulejan Maman Hanan ta sa mai adaidaita sahun ya kai su, duk tunanin Mayraah zata ga babban asibiti saboda taga wajen da ɗan tafiya daga suleja, kawai taga clinic, though ba laifi kamar clinic din sananne ne don taga patients da yawa amma bata tunanin the clinic is well equipped suna isa entrance din clinic din basu fara karo da kowa ba sai Dr Khalil yana kokarin fitowa rike da makullin Motarsa, kallon mamaki yake ma Mayraah kamar yanda ita ma take kallonsa da mamaki, Maman Hanan ta saki ihu don taga kamar numfashin er yayi sama bai sake dawowa ba, Dr Khalil ya saka makullin motarsa a aljihu da sauri ya amshi Hanan din a hannunta ganin condition din da ta shiga ya juya ya koma cikin asibitin sauran nurses suka nufosa, Mayraah ta bi bayansa da sauri har ta isa dai dai wajensa tayi kasa da murya tace "I think it's Diphtheria, symptoms din ne..." Da sauri ya juya ya kalleta, ya kalli yarinyar hannunsa, amma saboda babu lokacin batawa kawai ya shiga da ita emergency dake reception wani likita da ya fito office ya bi bayansa da sauri, Mayraah ta koma gefe ta tsaya Maman Hanan kuwa sai kururuwa take a reception din nurses na bata hakuri, Dr Khalil na shiga emergency din kawai abinda Mayraah ta fada yasa hankalinsa bai kwanta ba ya saka safar hannu, da few protections sannan ya fara gwaje gwaje, nan ya tabbatar da abinda Mayraah ta fada haka ne, Likitan da ya shigo wanda shine me asibitin shi ma ya koma baya closing his nose with nose mask ya buda ido sosai yace "Diphtheria, wannan sai dai a tafi da ita Abuja Dr.... Babu facilities a nan" Dr Khalil bai cire protective gown din jikinsa ba ya dau yarinyar ya fita daga emergency din, kawai ya nufi motarsa Maman Hanan ta bi sa a guje tana cewa "Ina za a kai ta Dr?" Ya kalli Mayraah dake tsaye ta kasa cewa komai yace "Ki taho da ita asibiti can Abuja" Daga haka ya shiga motar da likitan suka zuwa cikin Abuja, Mayraah har gajiya tayi da lallashin Maman Hanan a hanya har suka karasa Abuja, bata mance sunan asibitin ba wanda is so popular duk da asibitin masu kudi ne, suka hau adaidaita sahu ya kai su har asibitin, Sun fi minti ashirin zaune a katon reception din hospital din, bakaken fata da fararen fata sai kai koma suke a reception din, everywhere is just so organized kamar a kasar waje, suna kuma da lokacin zuwa duba mara lafiya ba anyhow ake shigowa ba, Mayraah ta kalli Maman Hanan for the countless time tace "Maman Hanan kiyi hakuri da kukan nan addu'a kawai za kiyi mata, in sha Allah zata samu lafiya kin ga nan babban asibiti ne" tausayinta kawai Mayraah take don ta san ko da an kwantar da Hanan to ko ita baza a bari ta zauna da ita ba sbda infection din is contagious, don su inda ake kwantar da masu cutar ma daban ne ba kowa ke shiga ba sae ma'aikatan asibitin, After another 20 minutes wata nurse sanye da cute uniform dinta ta nufosu tana kallon Mayraah da turanci tace likita na bukatarta a office, Mayraah ta mike tana kallon nurse din ita ma da turanci ta tambayeta ina office din, Nurse din tace "First floor, office number 1, Dr Khalil" Mayraah tace "Ohk" Maman Hanan ta mike da sauri cikin rawan murya tace "Tare za mu je?" Mayraah tace "Aa ki jira yanzun nan zan fito ai" Daga haka ta wuce sama ta isa har office number din da nurse din tace mata tayi knocking, sai da aka mata izini ta shiga, the office was large and organized, ko ina fes fes ga Ac a kunne, yana zaune kan office chair dinsa ya canza kaya alamar har yayi freshen up, ta karasa har front din table din ta zauna tana kallonsa tace "Dr ya jikinta?" Ya kalleta yace "Ina mance sunanki, pls remind me" A takaice Mayraah tace "Ilham" Yace "Ilham, how did u know it's Diphtheria?" Ta ɗan buda ido thinking of what to say sai kuma da sauri tace "Na taɓa koyon aiki a wani karamin asibiti" Yace "Really, kina da experience kenan in haka ne" Ta ɗan yi murmushin karfin hali bata ce komai ba, yace "Kin samu hostel din?" A hankali tace "Aa ina wajen aunt dina a suleja" Yace "What about ur parent" Tayi shiru tana kallon sa, kawai ta samu kanta da cewa "They are late" Ya ɗan sauke kansa sai kuma yace "Allah ya ji kansu" Tace "Ameen" Yace "But idan baki samu hostel ba ai akwai off campus da zaki samu cikin gari, isn't suleja too far for you? Yayi nisa fa zuwa school din" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi shiru da ya tuna ba fa kowa ake haifa da silver spoon ba barin ita da tace iyayenta sun mutu, probably bazata iya affording off campus ba, can yace "Wani course aka baki admission yanzu?" Mayraah ta rasa ma me zata ce masa, can dai "Microbiology" Ya gyada kai yace "That's good, i guess ur Aunty isn't financially stable ko?" Nan ma kawai tayi murmushi, ya sauke ɗan ajiyar zuciya yace "Mu kinga nan ba a daukan health workers sai da Qualified medical certification, infact ba mu da vacancy ma yanzu haka, we are dealing with just qualified medical staffs don wasu daga likitocin mu ma turawa ne da indians, so i will see if it will be possible in san yanda zan yi inyi attaching dinki ko during weekend ne as an auxiliary Nurse don ki samu ki dinga fending for ur self kar ki sakar ma mutane burden dinki su gaji da wuri" Mayraah kallonsa kawai take da mamaki and she couldn't believe her ears, aiki a babban asibitin nan?? can tace "Zan ji dadi idan ka min haka" Yace "But fa dole sai ta bayan gida zan yi maki wannan abun don we have strict orders a asibitin nan...." Mayraah tayi shiru tana kallonsa, Calmly yace "Kar ki damu, i will try my best zaki fara aiki a nan in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya sa, but i am sorry about that admission da nace na samu da naje makarantar ba haka bane" Yace "I don't get you" Ta sunkuyar da kai tace "An ban admission din da dadewa ne, sai yanzu muka tara kudin makarantar ban san ashe ba a haka ba, da naje makarantar shine suka ce anyi cancelling admission din long ago" Yace "Subhanallah" Daga haka bai sake cewa komai ba, ita dai kallonsa kawai take, yayi kasa da murya yace "Kar ki damu Ilham, zaki fara aiki a nan, and the salary is good sai kiyi ta saving ki sake sabon jamb ki nemi wani admission din" Ta ɗan yi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen" Da sauri tace "Plss ya jikin yarinyar??" A hankali yace "She is late already, before we could do anything" Mayraah da gabanta ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Yace "Ya ku ke da matar?" Nan da nan hawaye ya kawo idon Mayraah tace "Neigbor dinmu ce a Suleja" Yace "Sai hakuri, yarinyar ta rasu" Ta masa wani kallo tace "Shine tun dazu baka gaya min ba??" Mikewa tayi tana share idonta ta nufi kofa yace "Wait Ilham" Ta juya ta kallesa yace "Ce mata za kiyi nace ta bada number baban yarinyar ita kuma ku tafi gida a kawo ma yarinyar abinci, so i will communicate with the father, bama son ta hada mana commotion a nan" Cikin sanyin murya Mayraah tace "Sai dai nurses din su gaya mata ni bazan iya ba" Ya dau waya yace "I will tell dem now" Kiran nurses din yayi downstairs, Mayraah kuma ta fita a sanyaye.
[7/18, 8:04 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na tsaye gefe wata Nurse tayi ma Maman Hanan bayanin da Dr Khalil yayi mata a waya na cewar ta bada number mai gidanta sannan ta koma gida ta dauko ma Hanan kayan sa wa, ko minti daya Maman Hanan bata kara asibitin ba bayan ta bada number mijinta bata bi ta kan Mayraah ba ta fita da sauri zata koma gida, Mayraah dai ta bi ta da kallo ciki da tausayinta, tana tafiya a hankali ta nufi kofar fita reception din ita ma, Dr Khalil ya sauko downstairs kenan ganin Mayraah zata fita ya bi bayanta har suka fito haraban asibitin yace "Na kira mijin nata suna hanya yanzu haka..." Mayraah ta gyada kai tace "Toh, Allah ya ji kanta, Allah ya basu hakurin rashi" Yace "Ameen, haka yawanci wasu mutanen suke sai yaro ya jigata ake kawo sa asibiti..." Mayraah tace "Na fa shiga gidan ne nayi insisting mu tafi asibiti amma bata da intention din kai ta asibiti don tace mijin ya siya mata magani a chemist" Dr Khalil yayi murmushi yace "Yanzu ina kika nufa?" Tace "Zan koma gida" Yace "Ohk, bari in baki transport naga ko jaka babu a hannunki" Sai a sannan Mayraah ta lura ashe empty handed ta fito, ta kalli Dr Khalil, sai kuma ta fara fidgeting fingers dinta tace "Wallahi ban ma yi noticing haka na taho ba, i was so disturb with the little girls condition" Yace "Sure haka ne, ai kema kin yi kokari" Ya sa hannu aljihu ya ciro 5k yace "Wannan ai zai kai ki gida" Ta ɗan risina ta amsa tace "Nagode sosai" Yace "U are welcome, yanzu idan na samar maki space a nan din how will i communicate with you?" Tayi shiru don ita ko haddace new number dinta bata yi ba, can ta kallesa tace "Ka bani complimentary card dinka sai in kira da number ta, new number ne, bani da shi a kai" Yace "Ohk, zan ba Nurse su kawo maki yanzu, take care of ur self" Tace "I will, thank you" Daga haka ya juya ya koma cikin asibitin ta bi sa da kallo, bayan some minutes sai ga wata nurse ta fito, ta nufo inda Mayraah ke tsaye ta mika mata complimentary card din Dr Khalil, Mayraah ta amsa tayi mata godiya sannan ta juya ta fara tafiya, after minutes walk saboda girman compound din ta iso babban gate din fita haraban asibitin securities din wajen suka bude mata gate din ta fita. Mayraah na komawa suleja taga maza cike kofar gidansu Maman Hanan ana jiran gawarta, mata kuwa sai shiga gate din gidan suke, jikin Mayraah yayi sanyi sosai ta bude nata gate din ta shiga don baza ta iya shiga gidan taga koke koken da ake ba.
Mama Ladi na zaune parlon Ammi tana hada mata kwadon salad tana cewa "Ai tunda har yace maki ana bakin kokarin ganin an nemota kawai ki kwantar da hankalinki, ki cire komai a ranki Mamuda bazai maki karya ba tunda ba gantalalle bane shi, sannan yasan manya manyan mutane a kasar nan, ba gashi ana tafiya da Hajja gidan yan sanda ba sai gashi kawai waya yayi ko zuwa caji opis din bai yi ba aka sako Hajja, to tunda yace maki Mera ma ana ta bakin kokarin ganin an samota to muna nan dake zaki ga an samo ta an sakota w mota an dawo da ita gida" Ita dai Ammi kallon Mama Ladi kawai take, Mama Ladi ta gama hadin salad da take bayan ta cika kuli kuli sannan ta tura shi gaban Ammi tace "Kina fara ci zaki ji bakinki sakayau, daga nan kuma komai ma zaki iya ci don buda maki ciki zai yi" Ganin Ammi bata ce komai ba kuma bata dau salad din ba Mama Ladi ta hade rai tace "Ke ni fa na gaji da maki bauta kina maida ni er banza, kinsan inda naje na samo salaq din nan na kwadanta maki kuwa? anguwan naku duk na yaku bayi wani yakunennen salaq suke siyarwa duk ƙasa, sai da nayi tafiya me nisa na samo wannan wllh, duk kwantar maki da hankalin da Mamuda yayi bai ci ace kin hakura kin fawwala ma Allah komai ba, ita fa wannan shegiyar Meran ba yarinya bace duk mun sani, da gangangan ta mana haka kuma wallahi in muka ce baza mu yafe mata ba ta zaunu, don ta wahal da zuciyoyinmu ta cuce mu, ki saki ranki ki ci gaba da harkokin ki in taga kowa yayi banza da ita zata dawo gidan, amma yanzu tasan duk mun damu shi yasa taki dawowa take gana mana azaba" Ammi ta dau salad din ta fara ci a hankali, Mama Ladi tace "To ko ke fa, ga kaji can an kawo an cika a firiji ina jin Mamuda ne yasa aka kawo, anjima sai in farfesa mana muyi ta ci da bredi abunmu bakinmu alekum" Sallama aka yi kofar parlon duk suka juya, Badiyyah ce ta shigo cikin wasu matsattsun dinki ta rataye gyale a wuya hannunta rike da handbag ta karaso har inda suke ta zauna kan kujera tana kallon Ammi tace "Ammi ina yini" Ammi bata sake kallonta ba tana ci gaba da cin salad din hannunta a takaice tace "Lafiya lau" Badiyyah ta kalli Mama Ladi da ta saki baki tana kallonta, babu yabo babu fallasa tace "Ina yini" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Sannu jarabar duniya, wato har kin dawo daga yawon tamɓelen naki kenan kamar akuya, shegiyar marainiya annamimiya shedaniya me tarwatsa zumunci, to uwar me ya kawo ki gidan nan ko ance maki Hajjan tana nan ne, baki san hanyar kuturun gidanta bane kika yo mana nan?" Badiyyah ta wani hade rai tana hararanta tace "Ni gaskiya ki daina zagina Mama Ladi, me na maki? Ko meye ruwana da ke daga shigowata zaki fara zagina haka? Wallahi ki dena ina gaya maki" Bata rufe baki ba Ammi na nuna mata kofa tace "Tashi ki fita" Badiyyah ta kalli Ammi da sauri irin bata yi expecting haka ba, Mama Ladi kuwa ta rarumi spatula da ta gama hadin ƙwado ta jefa mata da karfi tace "Tashi ki fita shegiya guzumar banza kawai, shi sa gashi kin doshi arba'in har yau ba mashinshini saboda mugun hali" Badiyyah ta fashe da kuka ta mike ta fice daga parlon da sauri, Mama Ladi na huci tace "Wallahi ni na raina dangin Sanisa in har suka bari Badiyyah ta ci bulus, haka kawai ta fasa masu kan er su har ana hango ƙwaƙwalwa su kyaleta kuma, a ina aka taɓa haka kamar Sanisar bata da gata, ni Allah da na san gidan dangin Sanisar sai in tashi yanzu in je ince masu Badiyyah ta dawo amma in masu kashedi kar su sake cewa za su kama er uwata Badiyyar dai ta dawo su koma gidan za su ganta" Ammi dai bata ce komai ba sai cin salad din gabanta take Absentmindedly. Direct gida Badiyyah ta koma tana shiga parlon Hajja ta zauna kasa ta mimmike kafa ta fashe da matsanancin kuka tace "Dama sai da nace maki bazan je ba kika ce sai naje duba Ammi bata da lafiya, sai da nace maki wallahi bazan je ba kika takurani, daga dawowata kika dameni sai naje duba Ammi to wallahi duk zagina suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login