Showing 69001 words to 72000 words out of 249515 words
ba akan wnn abun da yayi, to yanzu kuma kaga irin dukan da yayi mata, haka kawai ya ja min magana wajen Hajja" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ni dai yanzu duk ki bar zancen nan ki kwantar da hankalinki Ammi, ki samu kiyi breakfast ki sha drugs dinki ki kwanta, in sha Allah anjima za mu yi magana idan na je gidan" A hankali Ammi tace "Naji Mama Ladi na cewa zata je wajen naku yau, to bana son inyi magana ita ma ta juya min zance ne yasa ban ce mata komai ba, amma ai bai kamata daga tarewar yarinya a fara mata sintiri ba" Maheer yace "Ai ba komai don ta zo Ammi, ita da ba garin take ba, it's okay" Maheer ya juya jin an bude kofar dakin nasa, Yace "Za mu yi magana Ammi sai anjima" Ammi tace "To ka gaida Haseenar" Yace "In sha Allah" Sai kuma yayi maza yace "Mayraah fa?" Haseenah tayi still bakin kofar dakin bayan ta shigo tana kallonsa, Daga daya bangaren Ammi tace "Yanzu ta fita" Maheer yace "Hope she is much better yanzu ko?" Ammi tace "We will talk later Maheer let me get some rest" Maheer yace "To sai anjima" Daga haka ta katse wayar, juyawa yayi yana kallon Haseenah da ta wani hade rai tana ci gaba da kallonsa yace "Kin tashi baccin?" Bata tankasa ba ta juya ta fice daga dakin ya bi ta da kallo, sai kuma ya mike ya bi bayanta. Aunty Mariya ta kalli agogo dake nuna karfe takwas da yan mintuna na safe sannan ta kalli Mama Ladi tace "Mama Ladi ai yayi wuri yanzu mana, ki bari ko zuwa karfe sha daya ne, da kyar in sun tashi bacci ma yanzu" Mama Ladi dake saka dankunnenta irin na yan hamsin da ake siyarwa a kasuwa ta juya tana kallon Aunty Mariya tace "Mariya ba fa gidanki nace zan je ba balle ki gindaya min sharadi da ka'ida, gidan Mashir nace a kai ni, to ke meye naki a ciki banda rakiya da nace ki min in kina ra'ayi? In kuma baki ra'ayi ki sha zamanki, Mu a garinmu fa duk inda karfe bakwai da rabi na safe yayi to kaje inda zaka ka dawo har ka huta...." Juyawa Aunty Mariya ta yi ta nufi kofa Mama Ladi ta bi ta da harara ta ci gaba da saka dankunnenta, Tana gamawa ta tafi dakin Usman sai da ta kwankwasa yayi sau goma sannan ya bude kofar yana kallonta daga sama har kasa, buda baki tayi tace "Kai kuma ya da bacci bayan nace maka za mu fita yau, ko ka manta ne" Yace "Za mu fita mu je ina?" Cikin daga murya tace "Yau naga jaraba, ban gaya maka zaka kai ni gidan Mashir ba?" Yace "Da sassafen nan zaki je gidan nasa?" A fusace Mama Ladi tace "Mu fa a garinmu war haka har mutum yaje yayi sabgar gabansa ya dawo gida" Usman yace "To bari in shirya, koma daki ki jirani" Mama Ladi tace "To ya dai fi, ina nan ina jiranka" Daga haka ta juya ta bar wajen, ya kulle dakinsa ya ci gaba da kwanciyarsa, haka Mama Ladi ta tafi parlon Ammi tana ta raba ido tana jiransa... Wajen karfe sha daya Usman ya shigo parlon Ammi da sallama, Mama Ladi na kallonsa rai bace tace "Amma Usman ko don yanda na takarkare na dinga kare ka wajen Hajja jiya bai ci ka walakanta ni haka ba yau, tunda nake ban taɓa zuwa anguwa karfe sha daya ba..." Usman yayi murmushi yace "Yanzu dai tashi in kai ki" Mama Ladi tace "Haba don Allah, wallahi ba don kai ne ba da na fasa wannan gantalalliyar tafiyar in huta ma raina, wannan ai walakanci ne kuma ni ba a walakanta ni in dauka gaskiya, har fa gyangyadi sai da nayi na tashi" Ita dai Ammi bata ce masu komai ba, Usman bai yarda ya kalli inda Ammi take ba tun asuba da ya shigo ya gaisheta ta amsa masa kamar bazata amsa ba, Aunty Mariya ta shigo parlon Mayraah na biye da ita a baya rike da abinci, Mama Ladi ta mike tace "To kaga Mariyar da nace zata rakani, idan ita ma ta canza shawara ne sai in ji yanzu muyi tafiyarmu kawai" Aunty Mariya tace "Tafiyar ne?" Mama Ladi tace "Atoh, sai yanzu ya ga dama, dama uwar tace da kyar ya kai ni da yake tasan halin abunta, tana cikin fadin haka sai ga shi ya shigo tunda ɗan halaq ne" Aunty Mariya tace "To bari in dauko mayafi" dakin Ammi ta tafi dauko mayafinta, Mayraah ta karasa gaban Ammi ta ajiye mata abincin hannunta a hankali tace "Ammi ga abincin" juyawa tayi ta kalli Usman tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" Aunty Mariya na fitowa Mama Ladi ta dau katuwar jakarta wanda tace zata debo kayan gara ta rataye a kafada tace "Toh sai Allah ya mana dawowa kuma" Usman ya kalli Mayraah yace "Ke baza ki je ba?" Mama Ladi ta juyo tace "Atoh nace ta shirya mu je ta ki, ka santa da taurin kai tun tana yarinya, har Mariya sai da tayi mata magana kememe yarinyar nan taki, to me za mu yi mata?" Usman na kallonta yace "Dauko hijab dinki mu tafi" yana fadin haka ya nufi kofa ya fita, Mayraah ta juya ta kalli Ammi, Ammi tace "Tashi ku je" Mikewa tayi ta tafi dakinta, a parking space ta tarar da su suna jiranta, Aunty Mariya ta bude ma Mama Ladi bayan mota ta shige ciki sannan ita ma ta shiga, Mayraah ta karaso ta bude front seat ta shiga, sai da suka bar gidan Mama Ladi ta tuntsire da dariya har da kyakyatawa, Aunty Mariya ta saki baki tana kallonta, Usman kam ta madubi ya dinga kallonta, Tayi dariyar me isarta tace "Wai Usman me ya hadaka da Badiyya ne kayi mata wannan dukan mutuwan haka?" Kara tuntsirewa tayi da dariya har da kwanciya, Aunty Mariya bata san sanda ta fara dariyan ba ita ma don dariyar Mama Ladi ne ke bata dariya, Usman yace "Wacece kuma Badiyya?" Mama Ladi ta tsagaita dariyarta ta dago tana kallonsa, yace "Ai ban san ta ba" Mama Ladi ta kara tuntsirewa da dariya tace "Wallahi naji dadin abinda kayi mata, kawai inda raina ya baci da har take gane mutanen dake kanta, kyau ace bata gane kowa, ai jiya ka sha tsinuwa wajen Hajja" Usman na ci gaba da driving dinsa yace "Ina ruwana da tsinuwarta tunda ba ita ta haifeni ba" Mama Ladi tace "Atoh dai, nima shi na gani, ta dai kwasheta sun tafi ko yaya suka isa gida oho" Aunty Mariya tace "Amma me ta maka kayi mata wannan dukan Usman?" Usman yace "Ni wai wa yace ni na doketa? A ina muka hadu na doketa?" Mama Ladi ta kara fashewa da dariya tace "Nima dai haka nace, wa ya sani ko aljanin dare ne ya lallabce ta ake ta laka maka wai kai ne" Har suka isa gidan Maheer Usman bai sake cewa komai a motar ba, yayi parking a waje yana kallonsu ta madubi, Mama Ladi tace "Motar bazata iya shiga gidan bane?" Usman yace "Ai juyawa zan yi" Aunty Mariya tace "Ka juya kuma? Aa jiranmu zaka yi, duka duka minti nawa za mu yi" Mama Ladi tace "Ban gane minti ba Mariya, wai nufinki muna shiga mu fito kamar barayi?" Da mamaki Aunty Mariya ke kallonta, Mama Ladi tace "Ni dai ba ruwana, bude min mota in sauka...." Aunty Mariya ta bude motar ta fara sauka sannan Mama Ladi ta sauko, Bude motar Mayraah tayi ita ma ta sauka, Aunty Mariya tace "Kai baza ka shiga ba Usman?" Yace "Aa" Mama Ladi tace "Haba ya kake haka ne komai naka babu tsari, gidan yayan naka ne baza ka shiga ba ka sa masa albarka yayi aure, ko hassada kake da shi" Tuni Aunty Mariya ta nufi gate Mayraah ta bi bayanta, sau daya Aunty Mariya tayi knocking kofar shiga entrance din parlon gidan aka bude.. Maheer ya koma gefe da murmushi fuskarsa ganinsu yace "Sannu da zuwa Aunty" Aunty Mariya ta shiga parlon Mayraah na biye da ita tace "Sannu ango, ya gidan?" Sai da suka zauna parlon ya karaso ya zauna shi ma ya gaida Aunty Mariya da ladabi, ta amsa tace "Ya gidan" Yace "Alhamdulillah" Kallon Mayraah yayi suna hada ido tace "Ina kwana" Ya mata murmushi yace "Lafiya lau Mimi, ya su Ammi?" Tace "Alhmdlh" Maheer ya kalli Aunty Mariya yace "To ina Mama Ladin?" Ko rufe baki bai yi ba sai ga ta da Usman sun shigo parlon tana cewa "To kaga ai shi ma sai yaji dadi ka shigo" Maheer ya mike yana mata sannu da zuwa, Tace "Ina amaryar?" Yace "Bari in mata magana tana daki" Usman yace "Good morning" Maheer na kallonsa yace "Morning" Juyawa yayi ya bar parlon, Aunty Mariya ta kalli Usman da yaki zama ya tsaya bayan kujera tace "Kai kuma ya haka kamar Soja? In zama zama, in kuma fita fita" Ɗan murmushi yayi ya karaso cikin parlon ya zauna, Ba a dau lokaci ba Maheer ya dawo parlon yace "Tana fitowa yanzu" kitchen ya tafi ya kawo masu ruwa da drinks ya ajiye, for almost 15 minutes Haseenah bata fito ba, Mama Ladi sai hira take da Maheer tana basa labarin yanda aka samu wanda ya lakada ma Badiyya duka kuma har yanzu ba a san ko waye ba, shi dai Usman danna wayarsa kawai yake, Aunty Mariya dai sai zuba ido take taga fitowar Haseenah shiru har bayan minti ashirin, Can Mama Ladi ta ankara tace "To wai ita amaryar er wani sarki ce ita da zata shanya mu a nan kamar yan iska?" Maheer yace "Erm ina jin wanka take" Daga haka ya mike, Aunty Mariya ta tabe baki, dakin ya sake komawa ya sameta kwance tana danna wayarta, da mamaki yace "Haseenah wai baki ji abinda nace maki bane?" Haseenah ta ajiye wayarta ta wani hade rai tace "Haba don Allah daga kawo mutum ko 24hrs bai yi ba za a fara masa sintiri haka Maheer? Wani dan gidanmu ka ga ya zo gidan nan? Ai ko ba komai an san ina tare da gajiya sai a bar ni in huta ko na sati biyu ne tukun kafin a fara min zarya, amma ya daga tarewa kawai a fara zuwa min gida da safe haka" Kallonta kawai Maheer yake ko kiftawa babu, ya ma rasa abinda zai ce mata, bayan few seconds ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da harara, tun da ya fito Aunty Mariya ke kallonsa, bai yarda ya kallesu ba ya zauna yace "Tana bandaki ne" Mayraah dai na kusa da Aunty Mariya a zaune, Mama Ladi tace "Ai ko ita ce warce ta fi kowa kiba saɓar saɓar a duniya ya ci ace ta gama wankan ta fito haka, awan mu daya fa yanzu a nan a zaune, wacece wannan ka aura haka Maheer? Ko har an fesa mata daga karaye nake ne take kokarin kawo min raini?? Shi fa karayen nan ba kauye bace don ma ku ji in fada maku" Usman ya mike ya nufi kofa ya bar parlon, Mama Ladi tace "Tada motar ga mu nan fitowa yanzun nan Usman...." Maheer yyi kasa da murya yace "Mama yanzu fa zata fito, ae nasan wankan take ne" Mama Ladi ta mika masa jakarta tace "Oho ko ma canza fata take, ni dai gashi kwaso min gara in san inda dare yayi min" Maheer ya amshi jakar yace "Mama kin san yanda mata suke dadewa a bandaki fa, yanzun nan zaki ga ta fito" Bai jira me zata ce ba ya tafi kitchen din, Haseenah ta mike zaune daga kwancen da take tana nazari, to ko ba komai ai zata so taga wa enda suka zo gidan, hijab dinta ta dauka ta saka sannan ta fito parlon, da Mayraah ta fara hada ido, wani irin faduwa gabanta yayi da farko ta kasa karasowa, Mayraah ta dauke idonta, Haseenah ta karasa parlon tana tafiya a hankali ta zauna empty chair ta gaishesu kamar me ciwon baki, Mama Ladi na kallonta da kyau tace "Mijin naki bai gaya maki mu su waye bane halan?" Ta dan girgiza kai ba tare da tace komai ba tana ɗan juya ido, Mama Ladi tace "Toh kanwar kakarsa ce ni uwa daya uba daya, ita kuma wancan da kike gani kanwar uwarsa ce uwa daya uba daya, ta gefenta kuma kanwarsa ce, sai dai kawai akwai aure a tsakaninsu ne a yanzu ba kamar yanda kika sani ba a baya, yanzu abubuwa sun canza, duk da dama mu mun san da auren tsakaninsu su ne dai basu sani ba, amma kanwarsa ce halaq malak" Sosai gaban Mayraah ya fadi, sai dai na Haseenah ya fi nata faduwa, Mama Ladi ta ci gaba tace "Shine dama nace a kawo ni in ga gidan ɗa na in sa albarka, ba wai zuwa nayi takanas saboda ke ba, tunda ai na ganki a can gidan" Tana kai wa nan ta mike tace "Mariya zaga da ni in ga gidan mu yi wucewar mu" Ko gama mikewa Aunty Mariya bata yi ba Mayraah ta mike, Mama Ladi tace "Yauwa mu je har ke kika gidan yayan naki..." kitchen suka ga Mayraah ta nufa, Mama Ladi tace "Au to, ganawa zata je tayi da yayan nata, mu je Mariya" Haseenah ta dinga bin Mayraah da kallo zuciyarta na bugawa, Aunty Mariya ta bude wani spare room tace "Wannan dakin baƙi ne ina jin" Mama Ladi tace "Waiii gashi da girma kuwa, kinga ai ko hutu aka yi Mera zata iya zuwa nan tayi hutun ta idan can gidan ya isheta" Mayraah na shiga kitchen din Maheer dake ta deban chin chin da cokali yana saka ma Mama Ladi a jakarta ya juya, he was surprise to see her, ita kanta sai ta daburce ta fara kame kame tace "Dama, dama yaya ina son ka ara min wayarka ne" Maheer yace "Did u misplaced urs?" Ta gyada masa kai, yace "To anjima zan kai maki wani gida, wanne kike so?" Shiru tayi tana wasa da handle din kofar kitchen din, yace "Ohk nama san wanda kike so" Ta ɗan kallesa tace "To wanne?" Yace "Idan na kai zaki gani" Ita dai bata sake cewa komai ba, yace "Zo ki debar mata snacks din ban san yanda ake yi ba" Karasawa ciki tayi, ta amshi jakar sannan ta fara debo kayan garan tana zubawa a ciki, yana tsaye gefe yana jiran ta gama zubawa aka bude kofar kitchen din, Haseenah na huci cikin daga murya tace "I am not going to tolerate this Maheer" Maheer kallonta kawai yake, Mayraah bata ko dago ba ta dinga zuba ma Mama Ladi alkakin da take, Haseenah ta karaso cikin kitchen din jikinta na wani tsuma tsabar bacin rai ta ci gaba da cewa "Bazan dauka ba wallahi, bazan yarda wata banza da baku hada komai da ita ba ta dinga shigo min gida...." Sai a sannan Maheer yace "Kin san wani abu Haseenah? Za ki iya yi min rashin kunyanki, ki gaya min duk abinda ranki yake so in dauka, amma kar ki kuskura ki sa Mimi a rashin hankalin ki don a nan ne ranki zai yi mugun baci wallahi, ki cire Mimi a bakin ki" Cikin daga murya Haseenah tace "Do ur worst Maheer, nace do ur worst, ba Mimi ba Momo, na sa ta a baki din yi abinda zaka yi in ga, kuma karya nayi ne? Ko da abinda ka hada da ita banda kasancewarta er uwarka musulma? To wa ma yasan ko kafura aka haifeta, A yanzu dai Maheer babu wanda bai san wacece ita ba duk da ni ka munafurceni baka gaya min abinda ke faruwa ba da fasa aurenta da aka yi saboda rashin asalinta, to har gida ake samu na a gaya min duk abinda ya faru, kowa yasan bata da asali, er tsintuwa ce kawai warce ma ba a san ta hanyar da aka sameta ba" Kallonta kawai Maheer yake babu ko kiftawa, Haseenah na tafe hannu tace "In sha Allahu kuma sai ta zama abun kyama a al'umma, don dama irinsu ai abun kyama ne tunda a walakance aka yasar da ita, kai kanka sai kaji gwara ka saka makiyin ka a ido da ka saka ta a ido, sannan tun ma kafin haka sai ta fara nuna maku cewar ita tsintattciyar mage ce...." Haseenah na kai wa nan ta fice daga kitchen din tana huci, Sai bayan kusan second ashirin Maheer ya iya juyawa ya kalli Mayraah, kulle jakar hannunta take kokarin yi, duk da idonta a kasa yake but he can see the tears filled in her eyes, lokaci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya ma rasa me zai ce mata, ta ajiye masa jakan hannunta a kan cabinet ta nufi kofa ta fita daga kitchen din, har sannan su Mama Ladi basu fito parlon ba, Haseenah da ta kasa zaune sai safa da marwa take a parlon zuciyarta na wani irin ƙuna ta bi Mayraah da ta nufi kofa da kallo, har ta fice daga parlon, wani murmushi Haseenah tayi ganin har da hawaye a idonta, nan da nan taji ta samu nutsuwa a ranta ta nemi kujera ta zauna ta sauke wani ajiyar zuciya, Mayraah na isa kofar gida ta tadda Usman a tsaye jikin motarsa ya rungume hannayensa yana jiran 12 dot yayi idan yaga basu fito ba yayi wucewarsa, tun da ta fito yake kallonta, ganin yanayinta yace "Me ya faru?" Ta karaso kusa da motar ta kasa ce masa komai, lokaci daya kawai ta fashe da kuka, da mamaki yace "Ke meye haka?" Kuka kawai take kamar ranta zai fita, kalle kallen wajen ya fara yi yaga babu kowa, yace "Talk to me, an maki wani abu ne?" Still taki ce masa komai sai kuka, ya jawota gefensa yana kallonta yace "Baza ki gaya min me ya