Showing 117001 words to 120000 words out of 249515 words
fita, makullin kofar ya cire bayan ya fita ya kulle kofar ta waje, Mama Ladi ta rushe da kuka ta ajiye bread din hannunta tace "Toh nace masa mu tafi karayen dake yace zaki yi jarabawa, to shi jarabawan baza a iya kai maki karayen kiyi ba?" Ita dai Mayraah kallonta kawai take babu ko kiftawa amma bata ma san me take cewa ba, Mama Ladi tace "Toh ma jarabawan banza ba sai da kwanciyar hankali ake jarabawa ba, su ajiye maki duk randa kika dawo a baki kiyi mana, bari kawai in gama karyawa ya bamu kudin mota mu yi wucewar mu, ranan laraba da juma'a kadai Malamin ke shigowa karaye yafi zama a Maradi" Maheer na zaune parlon Abba tare da Usman ta dalilin kiransu da Abban yayi, they've never seen their father this angry kamar ba shi ba, he was really vibrating and raising his voice kamar zai ari baki, rai bace ya ci gaba yana cewa "In ma ta zauna gidan nan da Mayraah ko ta tattara ta tafi duk inda zata tafi i don't care, bata isa tace Mayraah bazata zauna a gidana ba, i am not tolerating that nonsense again, all this while na kauda kai nayi hakuri na bi su a yanda suke so, ba wai don ban san abinda nake bane, yanzu kuma babu wanda ya isa ya canza min tsarin gidana, Mayraah will keep on staying as comfortable as she was before in this house, babu wani wanda ya isa ya canza haka, duk wanda bazai zauna ba ya bar gidan" Daga Maheer har Usman were quiet, bude kofar parlon aka yi Ammi ta shigo, duk tana jin abinda Abba ke cewa tun daga part dinta cause he was raising his voice so high, tayi wani murmushi tana kallonsa da kyau tace "Ai ba sai ka zaunar da su kana ci min mutunci a gabansu akan Mayraah ba Mahmud, ga ku ga ta ai kai da 'ya yan ka sai ku zauna da ita ni kuma zan bar maku gidan" Abba yace "Ai ban hanaki tafiya ba, so ki tafi duk inda zaki, sai yanzu na kara fahimtar ke da iyayenki ba kwa son gaskiya, i repeat in dai kan Mayraah ce ki tafi duk inda zaki, she remains in this house tunda gidana ne nan din ba gidan uban kowa ba" Juyawa Ammi tayi ta fice daga parlon, Maheer ya ji kansa ya sara, Usman was also short of words, Abba na kallon Maheer strictly yace "Duk kayan Mayraah da ka kai gidanka ka kwaso ka dawo mata da shi gidan nan" Maheer yayi kasa da murya a hankali yace "Abba ku yi hakuri abun duk bai kai haka ba, yanzu Mayraah tana bukatar nutsuwa sosai, her final exams is in just 2 weeks time, i think it will be better ta zauna hostel don tayi concentrating...." Shiru yayi don gaba daya ya ma rasa yanda zai yi composing word din yanda zai yi making sense a kunnen Abba, bazai so ace Ammi ta bar gidan akan Mayraah ba, the issue is just taking another dimension, Abba yace "A gidan nan nace zata zauna ba hostel ba, all this years ai ba a hostel take karatun ba...." Usman ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Abba yace "Abba wannan final exams ne, she needs all the concentration, with what is happening now bazata samu nutsuwa ba, plss ka bari ta zauna hostel har after the exams, it's just for 3 week" Usman ya fadi haka ne shi ma saboda exactly tunanin da Maheer yayi shi ma yayi, it won't make sense Ammi ta tafi saboda Mayraah, Strictly Abba yace "Nace baxata zauna a hostel ba a gidan nan zata xauna tayi exams dinta" Duk suka yi shiru suna kallonsa, ya juya yayi wucewarsa daki, mikewa Usman yayi ya fita daga parlon, Maheer ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, gaba daya ya rasa tunanin me zai yi. A hankali Maheer ya bude kofar dakin Mayraah ya shiga, tsaye ya ganta bakin kofar dakin, Mama Ladi ta mike tace "Kai ya zaka kulle mu a daki kamar barayi kayi tafiyarka, sannan anya baxa ka duba ƙwaƙwalwar yarinyar nan ba tunda dae naji ance kai likita ne, tun daxu fa nake mata magana yanda kasan da bebiye nake, ni wallahi ta ban tsoro kawai dakewa nayi" Maheer ya tafi dakinsa da Mayraah, after letting her sit, ya duka gabanta a hankali yace "Kina ji na Mimi" kallonsa kawai take, yace "Do you have any frnd or Coursemate dake hostel?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, yace "Say something Mimi" Ta gyada masa kai, mikewa yayi yace "Abba zae maki magana, tell him hostel kike so ki zauna for ur final exams" Daga haka ya tafi Parlon Abba tare da ita.... A tare Maheer da Usman ke kokarin su yi convincing Abba to let Mayraah be in hostel har bayan exams dinta, Abba ya nuna sam bai amince ta je wani hostel ba, ita dae Mayraah na zaune parlon duk tana jin su, Abba yace "Kuma kada wanda ya sake kawo min maganar hostel" Sae a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon Abba cikin sanyin murya tace "Abba dama a can nake so in zauna inyi exams din, many of my Coursemates are also coming back to hostel till the final exams, i will concentrate more" A ranan da yamma Maheer ya maida Mayraah hostel nan kusa da makarantarsu bayan yaga Abba ya fita daga gidan don Abba na iya cewa sae ana gobe exams, shi kuma tun da Ammi ta fita gidan da safe hankalinsa yayi mugun tashi kwata kwata bai so abun ya kai haka ba, tare Mayraah zata zauna da kanwar wata colleague dinsa wajen aiki, ita yarinyar tana level 200..... ya sauko mata da duk kayanta da zata bukata tana kai wa cikin dakin sabuwar roommate din nata tana ajiyewa, all this while Maheer na tsaye jikin mota yana bin ta da kallo, kawai tausayinta yake ji har cikin ransa, he wish he can't take away all this sad moment for her, handbag dinta ta dauka lastly a motarsa, a hankali yace "Mimi" bata yarda ta kallesa ba, nan da nan yayi noticing hawayen dake makale idonta, dawo da ita yyi jikin motar yace "Mimi i trust baxa ki ce zaki je ko ina ba shi yasa na kawo ki nan, i trust you Mimi, i know 24/7 karatun exams dinki za ki yi a nan because ur 5 years over everything for now, pls Mimi do not betray my trust, kar ki bari zuciyarki yayi leading dinki zuwa yin abinda bai kamata ba, Ammi and Abba are still ur parent, we are ur brothers, in sha Allah all this will come to pass very soon, ki cire komai a zuciyarki kiyi concentrating kan exams dinki to make Abba and Ammi proud, kinga da kyar muka shawo kan Abba ya yarda ki dawo hostel idan wani abu ya sameki a nan mu Abba zae yi blaming, mu kuma muna son ki maida hankali ne yasa muka ce ki dawo nan, duk sanda kike son wani abu just give me a call.... Usman is on his way now with ur foodstuffs" ko rufe baki bai yi ba sae ga motar Usman, bayan yayi parking Maheer ya nufi motar tasa, ita dae tana tsaye tana kallonsu, babu abinda Usman bai siya mata ba na abinci barin wanda yasan ta fi so irin su junk food da drink, suna tsaye duk ta shiga da su cikin hostel din, Usman na kallonta bayan ta dawo yace "Meye babu a kayan?" Ta girgiza kai tace "Ba komai" yace "Ohk, if u need anything ki kirani" Ta gyada masa kai tace "Nagode" motarsa ya koma ya bar su tsaye da Maheer ya wuce, Maheer bai bar wajen ba sai kusan karfe shidda. Gidan Hajja ya nufa, bayan yayi parking a kofar gida sae da yayi sallan magrib a masallacin dake layin sannan ya shiga cikin gidan, ya kai minti daya tsaye bakin kofar Parlon don bai ma san me zai tarar ba idan ya shiga, can dai daga karshe ya bude kofar ya shiga da sallama, Hajja na zaune parlon ga Badiyyah kwance a gefenta tana mata fiffita tana jero mata sannu, Haseenah ma na zaune parlon tana zuba madara a cup zata hada shayi, kallon Ammi dake zaune kan darduma ta idar da sallah yayi, tana ganinsa kuwa ta tamke fuska, ya zauna kan kujera yana kallon Hajja a hankali yace "Ina yini Hajja?" A takaice Hajja tace "Lafiya lau" yace "Ya mai jikin?" Hajja tayi banza da shi, Haseenah ta kallesa tace "Ina yini" Yace "Lafiya" Ya sake kallon Ammi cikin sanyin murya yace "Ina yini Ammi?" Mikewa tayi ta shige dakin Hajja ta kulle kofa, Hajja dae ta kyabe baki ta ci gaba da yi ma Badiyyah fifita don ba wuta a gidan, Haseenah ta mika ma Hajja shayin da ta hada cikin ladabi tace "Bari in je inyi sallah Hajja" Hajja tace "Toh Allah maki albarka er nan" Haseenah ta ɗan yi murmushi tace "Ameen Hajja" Daga haka ta mike ta shiga dakin Badiyyah ta kulle kofa, Maheer yayi kasa da murya yace "Don Allah Hajja ku yi hakuri da abubuwan nan da suka faru, wannan duk sharrin shaidan ne ba wani abu ba" a fusace Hajja tace "Ae shaidaniyar na nan tare da ku, babu wani shaidan sae ita, daga abun arziki sae ya juye ya zama na tsiya? Kai tun da kake ka taɓa ganin ubanka da uwarka sun samu sabani har ya daga mata murya? To kaga kuwa ae shaidaniya ce yarinyar nan, a kanta kai har kasan ka saki matar ka ta sunna wanda duka duka yau sati nawa da auren, dubi er uwarka ta jini halin da take ciki duk a kanta, to wallahi da mun san haka gari zae waye in na bari Ammi ta riketa shegiya nake, da mutum na sanin gaibu wllh da babu abinda zae sa mu fara shigo da ita zuri'ar mu...." Maheer felt so bad akan accusation din da Hajja ke ma Mayraah, don nan da nan yaji zuciyarsa na tafarfasa, amma dae ya dake yace "Abinda zae faru ya riga ya faru Hajja, kuma Mimi bata ma gidan yanzu haka, tunda Abba ya ga ran Ammi ya ɓaci ya sa aka kai ta gidan kawu Lawali, so Ammi zata iya komawa gida yanzu don Allah ki bata hakuri Hajja" Hajja tace "Ba ruwana wallahi, ae rufe ido yayi ya ci mata mutunci a gaban surkarta duk akan yarinyar da muka tsinta da kyakkyawar manufa, da kuma yake zakalkalewa kan Mayraan ance maku yyi niyyar riketa ne da farko?? Har da ku a kwayewa uwar ku baya a kan wannan yarinyar?" Maheer yace "Hajja wannan duk ya wuce, ki ba Ammi hakuri ta koma gida don Allah" Hajja tace "Ni nayi mata laifi da zan bata hakuri?" Shiru yayi bai ce komai ba, can ya mike ya tafi dakin da Ammi ta shiga yaji ta sa makulli, dawowa parlon yayi duk jikinsa yayi sanyi, ya zauna yana kallon Hajja, Hajja tace "Babu abinda zaka gaya mata yanzu da zata saurareka, kawai ka dau matarka ku tafi gida sai da safe" a hankali Maheer yace "Amma don Allah ki kara bata hakuri, gobe in sha Allah zan zo da safe" Hajja tace "Dauki matarka nace ku tafi sai da safe, ka bar mu muji da abinda ya tsaya mana a rai" Tana fadin haka ta mike ta je kira masa Haseenah da ta shige daki, suna fitowa parlorn Maheer ya tashi ya isa inda Badiyya take kwance yana kallonta yace "Ya jikin naki?" Pretending tayi kamar tana bacci, ya kalli Hajja yace "Ko za mu tafi gidana tare da ita saboda in dubata har ta samu sauki?" Haseenah ta juya ta kallesa da sauri, Hajja tace "Taje tayi me a gidanka Maheer? Ba zuwa gidan naka da tayi bane yasa aka kusa illata min ita? Aa babu inda zata je nasan ko hada baki ku ka yi da ɗan iskan kanin naka ku karasa kasheta??" Yayi kasa da murya yace "Ki bar wannan zancen don Allah Hajja, wannan ai saboda lafiyarta yasa nace mu je da ita ba wani abu ba" Badiyyah dake sauraronsu, ta mike zaune tana wani mitsike ido tace "Zan je" Hajja tace "Zaki iya taka kafafuwan ne da kike cewa za ki je?" Tace "Zan daure" Ita duk saboda yin waya da Malamin da Haseenah ta bata numbersa yasa take so ta bar gidan, don tasan definitely Ammi a dakinta zata kwanta bazata ce zata kwanta dakin Hajja ba, shkkn yanzu kuma bata da privacy tunda Ammi na gidan ba damar waya, ga shi daki biyu kadai ne a gidan, sannan tun jiya da daddare yace ta kirasa kafin abun nan ya faru har yau kuma bata kira ba babu privacy duk da yanda take fama da kanta, don duk jikinta ciwo yake mata ba na wasa ba, ga kafafuwanta don dai likitoci sun ce ba karaya bane amma ita sai take jin kamar sun karye ne kawai, hannunta daya ma mugun ciwo yake mata aka ce targade ne shine aka gyara mata a asibitin ko amfani bata iya yi da hannun har sannan, tana kallon Hajja da kyar tace "Hajja ki sa min kayana kala uku a jaka" Hajja tace "Ba fa inda za ki je nace su je su karasa ki, ke wai baki da zuciya ne, ko da kudi idan aka ce ki koma gidan Maheer sai ki koma?" Badiyyah ta wani hade rai tace "To wai ke ina ruwanki Hajja, in zaki hada min kayan ki hada in kuma baza ki hada ba in tashi inyi da kaina" Haseenah dai na tsaye taki cewa komai, Hajja tace "Toh, Allah dai ya ga na fita hakkin ki, dama so nayi ki zauna nan in maki duk abinda ya kamata" Daga haka Hajja ta mike ta shiga dakin Badiyyah, ba a dau lokaci ba ta fito da jakar kayanta ya hada mata kala uku, Maheer ya amsa yana kallon Badiyyah yace "Zaki iya tashi ai" Da kyar ta mike tsaye tana dingisa kafafuwanta da suke mata azababben ciwo, ya kama hannunta suka nufi kofa yace "Sai da safe Hajja" Hajja dai taki cewa komai don har ranta bata so Badiyyah ta sake komawa gidan ba to amma ya zata mata tunda taki ji, can ciki Haseenah tayi ma Hajja sai da safe ta bi bayansu fuskarta babu walwala, back seat ya bude ma Badiyyah ta shiga da kyar da kyar tana washh washh yana mata sannu, ya ajiye jakar kayanta a booth, Haseenah ta bude gaba ta shiga ta zauna, shi ma ya shiga motar suka bar anguwan, sai da suka yi nisa yace "Me za ki ci Badiyyah?" Badiyyah da ta kwanta bayan motar kamar er yarinya ta marairaice tace "Ai bana iya cin abinci" Yace "Toh bari a siya maki kaza da yoghurt, kilan appetite dinki ya dawo" Haseenah ta juya ta ɗan kallesa, ya samu inda zai siya ma Badiyyah abinda yace, yayi parking sannan ya sauka daga motar, bayan wani lokaci sai gashi ya dawo da leda daya tal, ya bude back seat ya ajiye ma Badiyyah, nan da nan kamshin kazar ta gauraye mota, ya koma driver seat ya tada motar suka kama hanyar gida, suna isa gida a kofar gida yayi parking, duk tunanin Haseenah zai koma ne su ma ya siyo masu kazar, ya bude ma Badiyyah back seat ta lallaba ta sauko tana rike da ledan kazarta da yoghurt, ya ciro jakanta a booth, all this while ko kallo Haseenah dake ta bin su da ido bata ishesa ba, a haka dai suka shiga cikin gidan Haseenah na tafiya a hankali tana biye da su fuskarta a daure, ya bude ma Badiyyah wani spare room ba wanda Mayraah ta zauna ba, fuuu Haseenah ta shige dakinta ta zauna gefen gado ta cire hijab dinta don wani mugun zafi ta dinga ji, can dai ta kasa ci gaba da zama ta fito corridor ta gansa ya dauko plate da cup ya shiga dakin da Badiyyah take, da ido ta bi sa har ya fito daga dakin ya fice daga gidan gaba daya, mota ya shiga ya kama hanyar inda Mayraah take don tun dazu hankalinsa gaba daya na kanta, kaza ya siya mata da drink din da yasan tafi so me sanyi, yana isa ya tadda motar Usman a kofar gate din hostel din, Mayraah dake zaune kan wani dakali tare da Usman dake danna wayarsa ta bi motar Maheer da kallo, tun da Usman ya zo after magrib basu yi maganar da ya wuce na minti biyu ba ya fara danna waya, lkci lkci dai zai daga kai ya kalleta, ita dai kawai tana zaune gefensa tayi nisa tunanin da take har ta hango motar Maheer.
MAYRAAH is 500 Via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
[7/4, 7:37 PM] Khaleesat Haiydar💖: Usman ya mike bayan Maheer yayi parking, ya kalli Mayraah yace "Sae da safe" Daga haka ya nufi inda motarsa take, ita dae kawai ta bi sa da kallo, Maheer bai sauko ba har sae da yaga Usman ya tafi sannan ya bude motarsa ya fito, ya nufeta ya zauna inda Usman ya tashi yace "Hope kin ci abinci" ta kallesa ta gaishesa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, tana karba bayan taji abinda ke ciki tace "Yaya ya kawo min, but i will give my roommate this" Maheer yace "Ohk, me kika dafa?" Ta girgiza kai tace "Roommate dina ta ban shinkafa" yace "Kuma kin ci?" Duk da ko spoon biyu bata ci ba a shinkafar da Ummi ta zuba mata kawai sae ta gyada masa kai, ya mata murmushi yace "Good, gobe za ki shiga school ae?" Ta girgiza masa kai kawai, bai sake cewa komai ba, ita ma tayi shiru, Allah ya sani kawai daurewa take and she is trying to act she is okay, but deep down she