Showing 81001 words to 84000 words out of 249515 words

Chapter 28 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1559

tsofaffin kayan yaransu an kawo ma jaririyan, har kudi aka hada da bai taka kara ya karya ba aka bamu, da shi muka fara siya mata madara, ni dai duk hankalina bai nutsu da rikon yarinyar ba kawai ina jin kunya Hajja ne, a ranan na fita naje kasuwa inda nake dako a biyani kafin in harhada yan kudadena in siya kaya marasu tsada in shiga Cameroon in siyar sai inyi wata daya ban gama hada kudin siyan kayan ba wani lkcn duk abinda na samu ma dole da shi za a ci abinci, that same day da muka tsinci Mayraah ina kasuwa from no where sai ga wani bawan Allah ya bani dubu goma daga kai masa kaya mota, imagine 10 thousand 22 years ago, ai kaga ba karamin kudi bane, nayi ta farin ciki na koma gida duk da ko minti talatin banyi da fitowa ba, a washegari sai ga wata dubu uku daga wata Hajiya ita ma na dau mata kaya zuwa mota, let me make this brief, tun daga sannan ba ayi ranan da zan fita ba a min kyauta ba, me yawa, ɗan kadan a haka dai kullum, nan na dinga saran kaya ina shiga Cameroon a kwana biyu uku kaya suke karewa tas ga riba wanda a baya sai inyi sati uku a Cameroon kaya basu kare ba, tun daga samun Mayraah hanyoyin arziki suka dinga bude mana ta ko ina, ta yanda bamu taɓa tunani ba a rayuwarmu, in less than few months ni kaina na tsorata da abinda na tara, nayi ta jin tsoro, haka ma Amminku wanda nasan da bata san halina ba tunani zata yi sata na fara, amma abu sai kara ci gaba yake, harkoki na ta bunkasa kan kace me kafin wata 12 muka tattaro muka dawo kano, kaga kuwa samun Mayraah alkhairi ne a garemu, kuma ko da muka dawo Kano barka kawai ake shigowa yi ma Ammi tunda shekaranmu daya a can muka samu Mayraah, tana wata sha biyu kuma muka dawo Kano, don haka babu wanda ya kawo cewar ba er mu bace Mayraah, ku kanku where very happy bayan dawowarmu don an sanar maku Amminku ta haihu tun bamu dawo ba.... Usman ya ɗaga kai yana kallon Abba jin yayi shiru, Abba ya nisa yace "Ko da wasa mu ma bamu taba zaton akwai randa za mu yi ma 'ya yan da muka haifa tayin auren Mayraah ba don duk daya muka dauke ku gaba daya babu banbanci, amma muna namu Allah kuma na nasa...." A hankali Usman yace "Yanzun ma hakan baxai faru ba Abba, we will continue being the brothers we are to her, for better for worst we will protect her and will always be there for her, babu wanda zai taɓa ta ya kwana lafiya, ko da yau ta samu wani da zai aureta kallon banza idan ya hadasa da ita balle har ya kai ga goranta mata asali zai gane she has a Barrister as a brother and 2 other elder Brothers, not even outsider ko na cikin gida ne yace zai takura Mayraah i in particular can go to any extent na kwatar mata 'yancin ta, i will take that personally i am assuring you Abba, don haka har abada babu aure tsakaninmu da Mayraah, she remains our blood sis" Yana kai wa nan ya mike yace "I want to excuse my self sir" Abba ya gyada masa kai, ya juya ya fice daga parlon Abba ya bi sa da kallo. Maheer ne tsaye dakin Ammi kansa a kasa duk da bacin ran dake tare da shi bai nuna a fuska ba but deep down him he is boiling and yana ta controlling kansa baya son yayi wani magana da zai kara hurting din Amminsa hankalinta ya kara tashi, gwara ya bar ta ma taji da wanda take ciki yanzu, Ammi dai sai goge hawayen da ya ki tsaya mata take maganar ma ta kasa ci gaba da yi, not long ago ta dawo daga gidan Hajja don ko minti sha biyar bata yi da shigowa gidan ba, after a 5 minutes silence tsakaninsu Maheer ya dago kansa yana kallon Ammi yace "Shikenan... Na kuma fahimce ki Ammi, for the meantime Mayraah zata koma gidana...." Ammi ta daga kai tana kallonsa, yace "Eh zata dawo gidana, a nan kuma zata zauna, Hajja don't have any say in this, ba kuma wai don Hajja zata hanata zaman nan gidan Abba bane yasa zata koma gidana don zamanta a gidan nan ma Hajja bata da say cause this is our father's house, ban san irin zaman da za ku fara yi da Mayraah ba idan ta ci gaba da zama a gidan nan shi yasa zan maida ta gidana, don haka gobe zan je gidansu Haseenah in daukota, duk sanda Hajja ta gane kuskuren abinda take kokarin yi fine, zan so ki rabu da ita lafiya, don haka ki ci gaba da yi mata biyayya...." Aunty Mariya ce ta shigo dakin da akwatinta, tana kallon Ammi cikin sanyin murya tace "Toh Ammi, ni zan tafi sai mun yi waya" Kai kawai Ammi ta gyada mata tana share hawayen da ya ki tsaya mata har sannan, Aunty Mariya ta kalli Maheer tace "Zan tafi Maheer" Sauke idonsa yayi yace "Bari in kai ki park Aunty" Fita tayi daga dakin ya juya ya bi bayanta, bayan ya kullo kofar Aunty Mariya na kallonsa cike da damuwa tace "Ku yi hakuri Maheer, kuyi hakuri da duk abubuwan nan dake faruwa, Allah zai daidaita al-amarin nan in sha Allah, sannan nasan Mayraah bazata yi nisa ba, duk inda ta tafi zata dawo a yau da izinin Allah, tunda Hajja tace in tafi gwara in tafi kawai" Shi dai Maheer bai ce mata komai ba, ta fara tafiya ya bi bayanta.
A hankali Mayraah ta bude idonta, ta dinga bin dakin da take da kallo, kwance take saman gado an rufeta da lallausan farin duvet, ta mike zaune da sauri trying to recall where she is, and who brought her here, idonta ya sauka kan alluran dake kan bedside drawer da drugs, cikin few seconds komai ya fara dawo mata, ta cire duvet din jikinta zata sauka daga kan gadon taji kamar an soka mata mashi a kirjinta, dafe kirjin tayi da sauri feeling so much pain, dai dai nan aka bude kofar dakin, ta daga kai ta kallesa, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta, can dai ya karasa yana tafiya a hankali ya isa har inda take ya zauna cikin sanyin murya yace "How are you feeling now?" Tun safe sai a yanzu taji kukan da ta kasa yi ya taho mata ta kasa controlling kanta, kamo hannunta yayi yace "Noo pls kar kiyi stressing kanki Mayraah, u need rest" Ta warce hannunta daga nasa cikin kuka tace "Saboda kasan wacece ni shi yasa kake avoiding dina yanzu kake kashe wayarka don baka son...." Dakatar da ita Musharraf yayi yana girgiza kai yace "That is the last thing i will do on earth Mayraah, and mind u tun kafin ke kanki ki san ko wacece ke na riga ki sani, kuma hakan bai sa naji kin canza a zuciyata ba, i switched off my phone for my mental health..." Tace "You are avoiding me because of ur mental health?" Yayi shiru yana kallonta kamar yanda ita ma ke kallonsa, daga fuskarsa kadai zaka gane ya rame, he doesn't even look normal, can ya juya yana kallon side daban yayi kasa da murya yace "Na ba Dr Maheer space ne ya gama maki duk injections dinki da aka yi prescribing, sannan ya kula dake kamar yanda likitan ya umarta, so i had to back off for my sanity" Kallonsa kawai Mayraah take, ya mike tsaye yana facing dinta, hawaye ne kawai ke sauka idonta tace "But that isn't enough to let u ignore me all this while, when u know i will need u the most during this hard time" A hankali Musharraf yace "Kinsan yanzu da aure tsakaninku da Maheer and Usman?" Kallonsa Mayraah take babu ko kiftawa, ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa, ba a dau lokaci ba ya dawo dakin da plate din abinci da ruwa, ya ajiye mata kan bedside drawer yana kallonta yace "Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, zaunawa yayi kusa da ita yayi kasa da murya yace "I am sorry Mayraah.... u know i love you soo much, ina sonki fiye da yanda kike zato, amma the thought of Maheer made me sick for all the 3 days da kika ji wayata a kashe, i became insecure zuciyata na ta raya min abubuwa da yawa, kilan saboda abubuwan nan da suka faru Abba can just decide to get u married to Maheer or Usman, the thought of that nearly took my life this 3 days, Mayraah I can't imagine loosing u, i don't know what will become of me idan na rasa ki, kiyi hakuri ki yarda da ni mu je a daura mana aure, i promise to give u all the love in this life, i will protect you till my last breathe, u will neva regret trusting me" Mayraah na share hawayen dake sauka idonta a hankali tace "I have to because i have no option, a yanzu ina ga bani da kowa kuma bani da inda zan je, i am all alone in this life" Musharraf ya girgiza kai ya kamo hannunta yace "You are not alone Mayraah" Tana kallonsa cikin rawan murya tace "I don't know what is happening but i overheard my grandma telling Ammi to choose between i and her, she said....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, Musharraf ya jawota kusa da shi yace "It's okay Mayraah, baki ji ta bane da kyau, u misheard her, yanzu ki ci abinci ki sha magani, it's almost magrib" Yana fadin haka ya dauko abincin ya fara bata a baki, cokali daya ta ci ta girgiza masa kai da kyar tace "Bazan iya ci ba, my chest is aching" Yace "Bari in kawo maki shayi" Tashi yayi ya fita daga dakin, ta koma ta jingina da gadon all this while sai yanzu ta ɗan ji ta samu relieve, bayan some minutes ya dawo dakin da cup din shayi ya mika mata yace "I diluted it, babu zafi" Amsa tayi ta fara sha, ya dauko mata magungunan yana bude mata, tana gama shan shayin ta amshi maganin ta sha, yace "Zan je masallaci in dawo, kiyi alwala kema kiyi sallah" Ta gyada masa kai ya mike ya fita daga dakin.... Ko da Musharraf ya dawo Mayraah har tayi sallah, ya ajiye mata yoghurt da ya shigo mata da shi ya zauna yana kallonta yace "Are you feeling pain any where?" Ta girgiza masa kai, a hankali tace "But what will be the outcome of my final exams?" Yayi shiru yana kallonta, can a hankali yace "Shouldn't we get married first before thinking of that Mayraah...." Mayraah ta zuba masa manyan idanuwanta, bude side drawer yayi ya ciro wayarsa ya kunna yace "Let me make a call, if possible in ga ko za mu iya zuwa Abuja gobe..." Ita dai kallonsa kawai take, yana kunna wayan bayan ya gama booting kira ya shigo wayar, ya daga kai ya kalleta ganin me kiransa, hade rai tayi ganin Dr Maheer a gaban screen din......


MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788
[6/23, 8:19 PM] Khaleesat Haiydar💖: Har kiran Maheer ya katse Musharraf bai daga ba, can ya jefar da wayar kan gado ya hade rai yace "I see no reason why he should call me because u are missing, what does that mean?" ita dai bata ce komai ba, ta koma tayi lamo kan gadon tana kallonsa, Sake ringing wayar ya fara yi, Musharraf ya kalli screen din yaga Mami ce ke kiransa this time around, ya sauke ajiyar zuciya, sai da kiran ya kusa katsewa sannan ya dau wayan yayi picking ya sa handsfree ya ajiye gefen gadon yayi shiru, Daga daya bangaren Mami tace "Musharraf" A hankali yace "Good evening Mami" cike da damuwa Mami tace "Me yasa ka kashe wayar ka yau kwana uku kenan?" Shiru yayi bai ce komai ba, Mami tace "I am talking to you Musharraf" Musharraf yace "Ina hutawa ne" Mami tace "Kai kenan baza ka amshi kaddaran da Allah ya dora maka hannu bibbiyu ba kana matsayin ka na musulmi? baka tunanin nima kana saka ni cikin damuwa da sleepless night? Why will u just switch off u phones, Kasan adadin kiran da nake ma wayarka a rana kuwa?" Yayi kasa da murya yace "Am good Mami u need not to worry about me, i will take care of my self, nace maki kawai hutawa nake" Mami tace "Yanzu kana ina?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Abuja" Tace "To ka dawo gida Musharraf, hankalina baxai taɓa kwanciya ba idan ba gida ka dawo ba na ganka, it's not the end of life don an rabaka da warce kake so, dama can Allah ya riga da ya tsara baza ku yi aure a yanzu dai da ita ba, and there is always a reason for everything da kaga ya faru a rayuwar nan kuma Allah kadae yasan dai dai, so who are we to question him? sai kaga kilan Allah ya sake hadaku da ita nan gaba a inda bakwa zato, kuma in har matarka ce ko nan da shekara nawa ne babu abinda zae hana ka aurenta, be patient for now pls Musharraf, do not rush things, gaggawa na shaidan ne, ita ma if u have access na contacting dinta ka kwantar mata da hankali kada all the 5 years she spent in school ya tafi a banza tayi asaransa, nursing science is not a joke, she needs to graduate and get her cert, don a yanzu karatu na daya daga cikin gatanta a rayuwar nan, duk da foster parent dinta really tried for her ita ma ya kamata ace tana da abinda zata taimaki kanta da shi nan gaba without being too dependant on any one, idan tana da rabon ganawa da danginta a duk inda suke zata gana da su komin daren dadewa, everything is just a matter of time, don haka kuyi hakuri gaba daya, tun da har ka iya hakuri da rashin mahaifinka da kanwarka in a motor accident wannan ma Allah zai sa maka hakuri har yayi maku abinda yafi alkhairi daga kai har ita yarinyar, find a way to access her ku yi magana ta fahimta da ita, ka kara kwantar mata da hankali, do not be a coward son...." A hankali Musharraf yace "Thank you Mami" Mami tace "Plss gobe ka dawo gida ina son ganinka ka ji" Yace "In sha Allah" Tace "To maa sha Allah, ka ci abinci?" Yace "Na ci" Tace "Toh sai da safe, plss kar ka sake kashe wayarka son" Yace "I won't" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Musharraf ya juya yana kallon Mayraah da ta rufe fuskarta da pillow, gaba daya jikinsa yayi sanyi da maganganun Mami, ya koma inda take ya zauna kusa da ita cikin sanyin murya yace "Baby" Mikewa zaune tayi hawaye na sauka idonta tana kallonsa, nan da nan ta karyar masa da zuciya, he hate seeing her cry, cikin rawan murya tace "What Mami is saying is the truth, may be ba yanzu bane lokacin auren mu, kilan ba yanzu Allah ya rubuta za mu yi aure ba, dama tun kafin faruwan abubuwan nan ina ji a jikina kamar baza mu yi aure ba yanzu" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Kauda kai Musharraf yayi, bayan few seconds ya juyo ya kalleta.... Ta mike zaune tana share idonta tace "But i don't have anywhere to go to" Musharraf yace "Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "I will keep on telling you not to be an ingrate, Ammi da Abba where the best of parent to you, basu taɓa failing dinki as parent ba, they raised u well, gave u quality education, protect you in whatever way they can, sun baki tarbiyyar da wasu dake tare da iyayen nasu ma basu samu ba, they gave u both Motherly and fatherly love, babu abinda kika rasa a rayuwar nan, ko da kika ji ina cewa mu je mu yi aure a wani wajen i don't have intentions of separating u from dem forever, komin daren dadewa za mu dawo, a yanzu nasan baza su taɓa bani aurenki ba bayan abubuwan nan da suka faru ni kuma zuciyata bazata iya jure hakan ba, you overheard our conversation with Mami, it won't be fair in bari 5 years dinki a university ya tafi a haka nan ba, kiyi hakuri baby, after ur final exams za mu je mu yi aurenmu, baza kuma mu dawo ba sai after u give me 2 beautiful kids like you" Kallonsa kawai Mayraah take, ya kamo hannunta a hankali yace "Yes dear, idan na tafi dake yanzu baki karasa karatun nan ba ban maki adalci ba cause zaki bukacesa a gaba it will be ur weapon against all odd in future" Hawaye na sauka idonta tace "A ina zan zauna in gama exams din?" Yayi kasa da murya yace "Gidanku, wajen Amminki da Abba" Ta kauda kai tana girgiza kai tace "Saboda ni ai bazai yiwu Ammi ta bijire ma mahaifiyarta ba, ta ce mata ta zabi ko ni ko ita, kaga bazan so abinda zai sa Ammi taki yi ma Hajja biyayya ba" Musharraf yace "Haka za kiyi hakuri ki zauna har ki gama exams din Mayraah, that doesn't mean ance ki bar gidan, Abba ma bazai yarda da haka ba, nasan Ammi ma komin me mahaifiyarta zata ce bazata so ki bar gidan ba bayan sun san baki da inda za ki, trust me Hajja doesn't mean all what she said

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login