Showing 219001 words to 222000 words out of 249515 words

Chapter 74 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1562

"Tashi mu je ki ga dakin ki" Mikewa Mayraah tayi ta bi bayanta suka tafi sama, Hajiya Amina ta bude mata dakin tace "This is ur room" Mayraah ta dinga kallon dakin ganin tsadaddun furnitures din ciki kamar dakin amarya, sauke kanta tayi kasa ta karasa cikin dakin. Bayan isha Mayraah na daki tana kokarin dialing number Dr Khalil saboda miss calls dinsa da ta gani Hajiya Amina ta shigo, hakan yasa ta fasa kiran, zaunawa gefen gadon Hajiya Amina tayi tana kallonta tace "Abincin ya isheki?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na koshi" Hajiya Amina tace "To maa sha Allah, ya kika baro su Amminku?" Mayraah tace "Lafiya lau, tana gaisheki" Hajiya Amina tace "Ina amsawa, chatting kike ne" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Aa" Hajiya Amina tayi murmushi tace "To yanzu waye surkin namu ne?" Mayraah ta ɗan kalleta sai kuma ta sunkuyar da kai, Hajiya Amina na murmushi tace "Feel free to talk to me dear, i am also ur mother" Mayraah ta ɗan kirkiri murmushi da kyar tace "Aa ba kowa" Hajiya Amina tace "Are you sure?" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina tayi shiru tana kallonta, can a hankali tace "Ni kuma kin san wa nake maki sha'awa Mayraah?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ba tare da ta shirya yin hakan ba, Hajiya Amina tayi kasa da murya tace "Yayanki" Mayraah dai ta dinga kallonta tana imagining wani yayan take nufi har ranta bata kawo su Maheer ba fa tunda ita dai tasan ba aure tsakaninsu a mentality dinta, Hajiya Amina tace "Kin ga ya san halinki, ya san wacece ke, kema kuma kin san halinsa kilan har littafi sai ki iya rubutawa akan halayyarsa, you 2 will make a perfect couple Mayraah, beside he is a calm and gentleman" Mayraah ta sunkuyar da kai feeling uncomfortable with the conversation, har cikin ranta bata san wani yayan take nufi ba fa ita, Hajiya Amina tace "Kin dai ga abinda ya faru akan aurenki kwanaki, so hakan kadai shine rufin asirinmu gaba daya" Hajiya Amina ta kalli wayar hannunta dake ring ta mike tace "Bari in amsa waya" Daga haka ta nufi kofar Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita.
[8/1, 10:45 PM] Khaleesat Haiydar💖: Wajen karfe goma Mayraah na kwance sai juye juye take, har a lokacin maganganun Hajiya Amina sun kasa fita daga ranta, tayi kokarin gano wani yayan nata take nufi amma taki bari zuciyarta ya kai tunanin ta kan brothers dinta she just believe ba su bane and she is sure of that, wayarta ne ya fara vibrate, ta jawo a hankali tana kallon me kiran, Dr Khalil ta gani da kamar bazata daga ba sai kuma tayi picking ta kai kunne, gaisawa suka yi yace "Ina kika shiga yau baki picking call?" A hankali tace "Bana jin dadi ne" Yace "Subhanallah, what's wrong with you?" Tace "Kawai kamar zazzabi ne" Yace "Allah ya sauke" Tace "Ameen thank you" Yace "Dama za mu shigo kano gobe, kinga if it's okay we can come over mu duba ki kafin mu koma Abuja" Mayraah tayi shiru, can tace "Kai da wa?" Yace "Dr Balogun da Hamid, mun shigo wani program ne" Mayraah tace "Toh shikenan Allah ya kai mu" Yace "Ameen, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen Nagode sosai" Yace "Kinsan Ceo din ma ta koma tun last week but nan da few days zata shigo saboda workshop da za ayi" Mayraah tace "Ohk, Allah ya kai mu" Yace "Ameen, till tomorrow, in mun shigo kafin zan kira ki in sha Allah" Tace "To a gaida min twins" Yace "Za su ji" Daga haka ya katse wayar, mikewa zaune tayi tana tunanin yanda zata samu gobe ta koma gida wajen Ammi in ma Dr Khalil za su zo gwara suje can din su sameta a gidansu, don ita dai tasan nan ba gidansu bane, wayarta ta sake daukowa tayi dialing number Maheer, yana fara ringing ya daga a hankali tace "Yaya" Yace "Mimi" tace "Good evening" Yace "So u still have my digit" Tayi murmushi kamar yana ganinta, yace "To ya aka yi?" Tace "Yaya plss i want to come back home tomorrow" Yace "Da gobe da jibi duk daya ne Mimi, just be patient, or is there any problem?" Ta girgiza kai tace "I am not comfortable" shiru yayi, sae kuma yace "Kiyi hakuri ki bari har jibin sae ki dawo gida kar Abba yayi fushi" Bata sake cewa komai ba, yace "Are you there?" Cikin sanyin murya tace "Na ji" yace "Good gal" Tace "Zan kwanta" Yace "Ohk sleep tight, kin ci abinci?" Ta gyada masa kai yace "To sai da safe" katse wayar tayi ta ajiye ta rufe ido. Washegari da yamma Mayraah na kitchen tana girkin da Hajiya Amina ta sa tayi masu, tuwo ne da vegetable soup tace tayi, Mayraah har ta mance rabon da tayi girki, bata fito kitchen din ba sae kusan karfe biyar bayan ta gama komai, zaune taga Usman parlor, ta ɗan buda ido tace "Lah yaya yaushe ka zo?" Ya kalleta sannan ya ci gaba da danna wayarsa yace "Now" tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Tace "Ya Ammi fa?" Yace "She's fine" tace "In kawo maka tuwon na gama" Yace "Na ci abinci a gida" tace "Ohk" karasowa cikin parlon tayi tana kallonsa ta zauna gefensa tayi murmushi tace "You look cute" ya daga kai ya kalleta yace "Really" ta gyada masa kai still looking at him, yace "Ke ma" ta zaro ido tace "Nima me?" Yace "Abinda kika ce min" ta kyalkyale da dariya tace "Ae ka fi ni kyau, shi yasa Maleeha take ji da kai" shi dai kallonta kawai yake, sai kuma ya kamo hannunta calmly yace "Ke kuma kin fi Maleehar kyau ai" Mayraah tayi shiru jin abinda yace, lkci daya ya saketa ya ciro wayarsa zai fara dannawa, tayi kasa da murya tace "Yaya don Allah in zaka tafi zan iya bin ka?" Yace "Abba yace sai gobe" Hajiya Amina ce ta sakko downstairs ganin Usman tace "Yaushe ka shigo barrister?" Yace "Yanzu" mikewa Mayraah tayi Hajiya Amina tace "Har kin gama girkin kenan?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na gama" Hajiya Amina tace "To Sannu da aiki" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta wuce sama Usman ya bi ta da ido, Hajiya Amina ta karaso ta zauna tana kallonsa tace "Ya gidan?" Yace "Alhamdulillah" Mayraah na shiga daki ta dau wayarta taga kiran Dr Khalil har uku an hour ago, zaro ido tayi don ta mance yace mata za su zo yau, kiransa ta fara yi, yana fara ring ya daga yace "Bacci kike ne?" Tace "Aa ina ƙasa ne, ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya jiki?" Tace "Alhmdlh naji sauki" yace "Ba don an ɗaga flight dinmu ba ae kilan da yanxu muna Abuja, sae 8pm Flight din, so now.... ina ne anguwan naku?" Ta ɗan yi shiru sae kuma tace "I will call you back in few minutes time" yace "Ohk then" katse wayar tayi ta sauka downstairs, gun Usman ta nufa don Hajiya Amina ta shiga kitchen, ta zauna kasa daga gefensa tana kallonsa tace "Yaya wannan Dr din nan ne za su zo su nan wai sun shigo kano wani program, can they?" Usman yace "It's okay... Mun yi waya da shi ae daxu na tambayesa ko zai karaso yace min babu time saboda flight dinsu 3pm ne" Mayraah tace "Eh yace min an ɗaga flight din sai dare, i just saw his call" Usman yace "Ohk send him the address" Tace "Ai ban sani ba to, gashi kayi masa sending...." Tana fadin haka ta mika masa wayarta, Amsan wayar yayi ya rubuta address din gidan ya bata tayi sending ma Dr Khalil, sai ga kiransa ya shigo wayarta ta daga yace "Ohk expect us in 30mins time" Tace "To Allah ya kai mu" katse wayar tayi ta ajiye tana kallon Usman dake kallonta yace "Kije ki gaya mata za ki yi baƙi" Mayraah tayi shiru, sai ga Hajiya Amina ta shigo parlon da abinci ta debo masa, ya kalleta yace "Na fa ci abinci a gida" Tace "Ko kadan ne ka ci" Mayraah dai ta mike zata wuce sama don taje tayi wanka Hajiya Amina tace "Kema naga ba ki wani son cin abinci, dawo sai ku ci tare" Mayraah ta kalli Usman da ya kalleta shi ma, Hajiya Amina ta ajiye masu tuwo da vegetable soup tace "Taho ku ci Hajiya" Mayraah tayi murmushin karfin hali kawai ta koma ta zauna, Hajiya Amina tayi wucewar ta sama, tuwon Mayraah ta fara ci ba tare da ta jira sa ba, bayan few minutes ya sakko kasa shi ma ya dau spoon ya fara cin tuwon, tana kallonsa tace "Is it sweet?" Yace "Wa yayi?" Ta langwabar da kai tace "Ni mana" Yace "Bari in gama tukun sae inji ko yayi" Dariya tayi ta ci gaba da cin tuwon ta, bata wani ci da yawa ba ta tashi ta bar masa ta wuce sama, sai da ta fara zuwa dakin Hajiya Amina ta sanar mata da zuwansu Dr Khalil sannan ta koma dakinta tayi wanka ta shirya, jikin windown dakin ta tsaya tana viewing din unguwan that's beautiful, sai abun yake mata kamar ta taɓa zuwa anguwan nan, ko ma dai ba shi ba ita dai tasan ta zo area kamar haka, Lkci daya Musharraf ya fado mata, ta zaro ido gabanta na faduwa, kamar unguwan da ta taɓa zuwa ta samesa fa, tana cikin wannan tunanin wayarta dake kan gado yayi vibrate ta juya ta dauko wayar ta daga ganin Dr Khalil ne, yayi mata sallama yace "To, ga mu a house number din" A hankali tace "Ohk" Katse wayar tayi ta dau veil dinta ta fita, bata tadda Usman a parlor ba, hakan ya bata mamaki, sai ta koma sama ta gaya ma Hajiya Amina baƙin sun iso, Hajiya Amina tace "Ba sai kin fita ba bari zan kira mai gadi ya bude masu gate din kawai" Mayraah tace "To, yaya ya tafi ne?" Hajiya Amina tace "Eh dama Daura zai tafi, kuma ya wuce" Mayraah tayi shiru, sai kuma tace "Bai ce min zai tafi ba" Hajiya Amina tace "Ai na zata kun yi sallama" Mayraah bata sake cewa komai ba Hajiya Amina ta kira mai gadi tace ya bude ma baƙi gate, Mayraah ta juya ta fita daga dakin. Bayan some mintues ta sauka Downstairs don bude masu kofa, tana buɗe kofar taga Dr Khalil, murmushi tayi masa tace "Sannu da zuwa Baban twins" har cikin parlon tayi masa iso bayan sun gaisa ta kawo masa ruwa da lemo, yace "Ya jikin?" Tace "Naji sauki, kace har da su Dr Hamid" yace "Ohh su mota za su bi zuwa kd sannan su dau train, sun wuce tun dazu, nima hakan na so yi but it's not possible" Mayraah tace "Allah sarki" Hajiya Amina ta shigo parlon suka gaisa da khalil da fara'a sannan ta koma sama, Dr Khalil yace "Ita ce Ammin?" Murmushi kawai Mayraah tayi, yace "I spoke to ur brother, the Barrister, about ur work.... he said he will get back to me idan yayi magana da Abbanku, that was today in the morning so ban san ya za su yi ba, ina dae jiran kiransa" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, yace "So duk yanda Abbanku yace haka za ayi, i hope za su bar ki kiyi aikin, in future za ki ji dadin hakan, no matter how wealthy ur parents are yana da kyau ace kai ma kana da source of naka income din" Mayraah tayi murmushin karfin hali bayan ta tuna she is just an abandoned orphan warce ko gadon wa enda take ma kallon iyayenta bata da shi, tunanin hakan ba karamin distablizing dinta yayi ba a lokacin, Dr Khalil yace "I think zan zo in tafi airport kar in yi missing flight...." A hankali tace "Baka sha ruwan ba ai" yace "I am okay, i just ate" tace "Toh shikenan" ya mike yace "Kiyi ma Ammi sallama pls" tace "In sha Allah" rakasa tayi bakin kofar parlon, yace "Baza ki rakani har waje ba kenan" tayi murmushi tace "Zan raka ka" A tare suka nufi gate din gidan suka fita har kofar gida, ya kalli Mayraah yace "Mu je ku gaisa da wani Dr, kin dai san sa...." tace "Ohk" karasawa gun motar tayi Dr Khalil ya bude kujera me zaman banza, turus Mayraah tayi tana kallon wanda ke zaune, shi ma tunda ya kalleta sau daya ya dauke idonsa yana ci gaba da kallon abinda yake yi a waya ya wani keeping serious face, ta kalli Dr Khalil da yayi mata alama da she should greet him, hakan yasa a takaice tace "Good day" ko jira ya amsa bata yi ba ta bar wajen, bata san shi ma bayi da niyyar amsawa ba, tana kallon Dr khalil tace "To Dr Allah ya tsare, a gaida min twins" Dr Khalil ya girgiza kai yana kara jinjina halinta, ta sakar masa murmushi tayi wucewarta cikin gida, Ta madubi MD ya bi ta da kallo har ta shige gidan, sae kuma ya kalli Dr Khalil yace "Wannan fitsararriyar yarinyar kake dagewa in shiga cikin gidan in duba ko? Does she even look like someone that is sick at all? Wallahi idan na maka Allah ya isa ɓata min lokaci da kayi sai Allah ya kama ka, what nonsense, yanzu meye amfanin nan din da ka kawo mu?" Dr Khalil ya kasa rike dariyarsa don daga Mayraahn har MD din ba karamin dariya suka basa ba, Dr Khalil ya zagaya ya shiga driver seat, MD yace "Allah bazan yafe maka ba, haka kawai kayi forcing dina mun zo nan yarinya ta fito ta min rashin kunya? Do you have any grudges against me Khalil?" Dr Khalil na danne dariyarsa yace "Oga boss i never forced u, kai da kace zaka Yola meye na biyo mu kano program din da kafi karfin attending, da ba sae ka tafi yolan ba kawai, sai dai in sharri zaka min sir, kuma fa ta ce maka good day" a fusace MD yace "Da na buge mata baki zata san good day, ni sa'anta ne da zata ce min good day, do i look like her mate ko an gaya mata ina harka da yara, wannan fa bata wuce 16 years ba idan aka duba real date of birth dinta" Dr Khalil ya tada motar suka bar layin, MD ya gyara zama yace "Nonsense, saboda suna common Miller road shine take tunanin kowa sa'anta ne?" Dr Khalil yace "Yanzu dai ba Ghetto ka ganta ba balle ka samu abun fade" MD yace "Muna komawa Abuja zan yi erazing data din da ka bani, she should come for interview....." Dr Khalil dai murmushi kawai yake yana driving dinsa, can dai yace "Kai fa Dr ko manyan likitoci ba harkansu kake shiga ba, sabgar gabanka kawai kake baka da lokacin su balle wannan yarinyar da kace shekaranta 16, naga ita dai ta samu time dinka sosai"
[8/2, 7:27 PM] Khaleesat Haiydar💖: Ranan Lahadi karfe sha daya Mayraah ta gama shiryawa ta rufe karamin jakarta, sannan ta dau wayarta ta kira Maheer, yana fara ring ya daga, yace "Mimi" Tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau, how was ur night" Tace "Alhmdlh, dama ce maka zan yi na shirya" Yace "But ai sai da yamma Mimi" Ta ɓata fuska tace "Don Allah yaya ka zo ka tafi da ni gida, yau fa Abba yace, it doesn't matter ko da safe ne ko da yamma" Yace "Toh kin ga ina wajen aiki yanzu, after work sai in biyo in dauke ki, be patient please" Ji tayi kamar ta fashe da kuka, yace "Are you there?" da kyar tace "Na ji" Daga haka ta katse wayarta tana turo baki, bude kofar aka yi ta juya, Hajiya Amina ta shigo tace "Mu je ki rakani gidan makotanmu in masu gaisuwa, they lost their daughter 4 days ago" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta ciro Hijab dinta ta saka sannan ta bi Hajiya Amina suka fita, gidan dake kusa da na Abba suka shiga, Bayan Hajiya Amina tayi masu gaisuwa ta gabatar masu da kanta a matsayin neighbor dinsu don tun zuwanta anguwan ba gidan wanda ta shiga, godiya suka mata sosai, Ita dai Mayraah na zaune, bayan ɗan lokaci Hajiya Amina tace "Toh bari mu koma, Allah ya gafarta mata, ya bada hakurin rashi" Suka mata godiya sosai sannan ta fita parlon da Mayraah, suna fita gate din gidan Mayraah ta dinga kallon motar dake tafiya duk da ya wuce gidan da suka fito, Hajiya Amina tace "Kinsan wanda ke cikin motar ne irin wannan kallo haka" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa" Daga haka ta bi ta suka shiga cikin gida, tana komawa dakinta ta dau wayarta, dialing number dinsa tayi da ainahin sim da take using yanzu, har ya katse bai daga ba, ta sake kira sai ya daga, shiru tayi, yana jin haka yace "Mayraah" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Good morning Sir" Yace "Me yasa kika daina kunna line din da kika kirani da shi kwanaki, pls me yasa kike min haka Mayraah, is it because i care? Is it because i love you" Nan da nan jikin Mayraah yayi sanyi jin yanda yake maganar, a hankali yace "Mayraah" Cike da karfin hali tace "Ina ji... naga ka fito gida yanzu, ina za ka?" Musharraf ya kalli inda yayi parking a anguwan, everywhere was so silent balle ace ta ji hayaniyar mota or so, yace "Did u just guess?" Tayi murmushi tace "I saw you.... But in my dream" cikin sanyin murya yace "Mayraah my life isn't the same again ever since you left me, ban san haka so yake ba i wouldn't have started wllh, ni ban gujeki ba duk situation din da ya faru ke kika gujeni, da na sani da na ci gaba da zamana ban fara relationship ba, i had no luck in relationship kuma tsakanina da Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login