Showing 216001 words to 219000 words out of 249515 words

Chapter 73 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1515

ba kiranta zaka yi ba tukun" Yace "Na kirata ai" Bin bayansa tayi har suka iso kofar shiga cikin gidan, Mayraah was shock ganin Hajiya Amina ta bude masu kofa, da fara'a take masu sannu da zuwa, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta, da tasan nan Ya Usman zai kawota da babu abinda zai sa ta biyo sa, haka nan dai ta zauna kan kujera ta gaisheta, Hajiya Amina ta amsa da murmushi tana tambayarta Ammi Mayraah bata dago kanta ba tace "Tana nan lafiya" Hajiya Amina ta kalli Usman tace "Kwana biyu shiru baka billo ba Barrister" Sai kuma da sauri tace "Au na tuna Yallabai yace min kaje kaduna, to ya aikin?" Yace "Alhamdulillah" mikewa yayi yace "Zan shiga masallaci inyi sallah" Tace "Toh shkkn" Daga haka ya fita parlor zai tafi masallacin dake jikin gidan daga gefe wanda Abba ya gina, Hajiya Amina na kallon Mayraah tace "Mu je Abban naki na sama a parlor ki gaishesa" Mayraah ta mike har a sannan fuskarta babu wani walwala ta bi bayanta zuwa upstairs, Abba yayi farin cikin kawo Mayraah da Usman yayi, dama yana ta son ce ma Ammi a kawota gidan ko yini ne tayi amma ya bar ma zuciyarsa don bai san yanda Ammi zata dau batun ba, liyafar abincin da Hajiya Amina ta ajiye masa ya zuba masu tare da Mayraah, Hajiya Amina tace "Je ki ga ko yayan naki ya dawo masallaci ya zo ya ci abinci" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga dakin ta sauka downstairs, Zaunawa tayi kan kujera ganin Usman bai shigo ba, bayan some minutes sai ga shi ya shigo parlon, ta tashi tana kallonsa tace "Yaya wai kaje sama inji Abba, pls yaya kana gama cin abincin ka maida ni gida plsss don Allah" Sosai ta marairaice masa don har ga Allah gida kawai take son ta ganta, Yace "Nan din ba gida bane?" Ta wani hade rai tace "Ni dai pls mu tafi gida" Sama ya wuce ta bi bayansa har zuwa parlon Abba, kusan duk bayan kwana biyu sai Usman ya zo gidan sai in baya gari, Maheer ne dai tun ranan da Abba ya kirasa ya zo bai sake bin hanyar gidan ba har yau, Da kyar Mayraah ke cin abincin da Abba ya zuba masu, Hajiya Amina na zaune parlon tana kallon TV, har daga karshe Mayraah ta mike tace ta koshi, Hajiya Amina tace "To mu je kiyi sallan isha" Babu yanda Mayraah ta iya haka ta mike ta bi bayanta suka fita parlon zuwa part dinta, bayan tafiyarsu with few minutes Usman ya ajiye spoon din hannunsa, Abba yace "Are you satisfied" Usman bai yarda ya kallesa ba, kansa na kasa yace "Sure... dama Abba akwai maganar da nake son zan yi maka" Abba na kallonsa yace "Ohk, i am all ears barrister" Ganin yayi shiru kamar me tunanin ta inda zai fara maganar Abba yace "Ina jin ka Usman, tell me what is it" Usman ya daga kai a hankali ya kalli Abba.....
[8/1, 7:00 PM] Khaleesat Haiydar💖: Shiru Abba yayi yana ta kallon Usman, can ya ɗan yi murmushi yace "Did you say this to anybody? I mean did u discuss it to anyone?" Usman ya girgiza masa kai without looking at him, Abba ya sauke ajiyar zuciya, bayan few seconds yace "Not even her?" Usman yace "Eh" Abba na gyada kai yace "Gaskiya nayi farin ciki da wannan batun Usman, i am so happy about it, and this is what i wished for few months back, but...." Usman ya daga kai ya kalli Abba, calmly Abba yace "I want u to let ur intentions be known to her before anything...." Usman ya girgiza kai da sauri yace "Abba kawai ba sae nayi hakan ba, kawai dai..." Sai kuma yayi shiru, Abba yace "You have to Usman, kwanaki i wasn't willing to give her an alternative cause tunanina hakan kadae ne mafita gare mu da ita baki daya, and i understand you too then da kayi declining... But yanzu i don't think i will do anything without her consent, say ur mind to her, go on a courtship with her...." Kallon Abba kawai yake baya ko kifta ido, Abba jinjina masa kai giving him assurance yace "Ko nan da sati daya ne in dai da consent dinta you gat my back son" Usman bai iya yace komai ba ya sauke kansa, Abba dai sae kallonsa yake, bude kofar parlon aka yi Mayraah ta shigo da sallama, Abba ne kawai ke kallonta, Usman kam bai daga kai ba, har ta karaso ta zauna gefensa tana kallonsa tace "Yaya na gama mu tafi gida" Abba yace "Nan din ba gida bane?" Ta kallesa ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Abba ae ban ce ma Ammi zamu kwana ba shi yasa" Abba ya gyada kai yace "Toh in kin ce mata sai ki zo kiyi weekend a nan din" Mayraah dai bata ce komai ba ta mike tana kallon Usman tace "Yaya Ammi fa tace kar dare yayi sosai" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta yace "To ba yanzu zan tafi ba" Ta marairaice tana kallonsa, mikewa Abba yayi yace "Naga ko karfe tara bai karasa ba ai Mimi, so there is still time, bari inje inyi sallah" Fita yayi daga parlon, Mayraah ta zauna kusa da shi kamar zata yi kuka tace "Yaya pls kaga dai Ammi bata san za mu zo nan ba ko, kuma ce min kayi wajen Maleeha fa za mu je, ni dai ka tashi mu tafi gida don Allah" jin yayi shiru ta ɓata fuska tace "Ka ji mana yaya" Sai a sannan ya juya ya kalleta yace "Nan din daji ne?" Ta turo baki ta koma ta jingina jikin kujera tana kallonsa fuskarta a daure, har bayan minti sha biyar bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba a parlon, lkci lkci take turo baki duk yana lura da ita, can ya mike tsaye, tana ganin haka ita ma ta tashi, ya kalleta yace "Ke a nan fa za ki kwana" Ko rufe baki bai yi ba tace "Wallahi bazan kwana ba" Tana fadin haka ta nufi kofa yace "Kar ki fita" Dawowa tayi tana kallonsa kiris ya rage ta fashe da kuka, ya koma ya zauna kan kujera, a hankali yace "Now tell me, me yasa baza ki kwana nan ba?" Ta zauna kasa daga gefensa tace "Kawai wajen Ammi zan tafi" Jin bai ce komai ba ta daga kai suka hada ido, tace "Pls mu tafi yaya" Hajiya Amina ce ta shigo parlon tana kallon sauran abincin da ba a taɓa ba tace "Ka ci abincin kuwa barrister?" Yace "Eh na ci, za mu tafi ne" Hajiya Amina tace "Ina ce ai a nan Mayraah zata kwana" Usman yace "Bata zo da shirin kwana ba" Hajiya Amina tace "Toh shikenan, ko weekend ne sai ta zo" Mayraah ta sauke wani ajiyar zuciyar relieve sanda taga sun bar gidan. Sai da suka yi nisa sosai ta kallesa tace "Yaya baza mu siya ma Ammi Apples da watermelon ba?" Yace "Ok za ki siya mata?" Tayi er dariya tace "I am not together with my Atm?" Ya ɗan kalleta yace "Nawa za a ara maki?" Ta langwabar da kai tace "Like 10k" Yace "Ohk" gun da ake siyar da fruits yayi parking ta juya ta kallesa tana jiran ya bata kudin taje ta siyo, bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo, bayan wasu mintuna ya dawo ya ajiye mata ledan kan kafarta yace "15k, sai ki biya yaushe?" Dariya tayi tace "Muna isa gida" Yace "Alright" Suna isa gida bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta jira shi ma ya sauka, bayan ya rufe motar ya jingina jiki folding his arms yace "Mun iso gida" Bata san sanda ta fashe da dariya ba tace "Yaya ko ciki fa bamu shiga ba" Yace "Toh" Daga haka ya nufi cikin gidan, ta bi bayansa tana murmushi, suna shiga parlor Maheer kadai ne zaune yana danna wayarsa, sau daya Usman ya kallesa ya wuce sama, Mayraah na ganin Maheer ta nufi kujeran da yake ta zauna kasa ta ajiye ledan hannunta tana kallonsa tace "Ina yini yaya" Yace "Ina ku ka je?" Ta buda ido tace "Yaya ce min fa yayi wajen budurwarsa zai je shine ya kai ni Miller road, ashe wajen Abba zai je" Maheer ya maida dubansa kan waya yace "Ohk" Tace "Yaya ka ara min 15k cash pls" ya kalleta yace "Me za ki yi da 15k?" Tana murmushi tace "Just borrow me pls" Yace "Sai ki maida yaushe" Dariya ne ya taho mata tace "Gobe da safe" Yace "Ohk, mu je in baki" yana fadin haka ya mike, tashi tayi ita ma ganin ya nufi kofar fita tace "Aa yaya zan jira a nan ka kawo min pls" Ya juya yana kallonta yace "Why?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita, still looking at her yace "Why?" Ta sauke ajiyar zuciya tace "I am not going there because of ur wife" Yace "Do not call her my wife again Mimi, Haseenah is not my wife" Ita dai bata ce komai ba, yace "Mu je" a hankali ta fara tafiya tana biye da shi a baya, sai da suka iso chalet din tace "Amma bazan shiga ba, i will wait outside Yaya" Tana fadin haka ta tsaya dai dai stairs din chalet din, shi ma bai yi forcing dinta ta shiga ba, yana bude kofa Haseenah dake zaune kan kujera tana waya ta katse wayar tana goge hawayen idonta tana kallonsa, ko kallonta bai yi ba ya bar kofar a bude ya wuce daki, kamshin turaren da ta dinga ji na shigowa parlon ya sa ta mike ta taho bakin kofa don jikinta ya bata da mutum a wajen, tana ganin Mayraah bata bari sun hada ido ba ta koma inda take ta zauna, ba a dau lokaci ba Maheer ya fito da cash din a hannu, ya mika ma Mayraah ta amsa tace "Thank you Yaya" Shi dai bai ce mata komai ba yana kallonta, ta juya ta sauka daga chalet din ta koma main building din gidan da sauri, ledan fruits din ta dauko sai da ta fara zuwa dakin Usman tayi knocking ya bude kofar ganinta ya koma ciki ya zauna, ta bi bayansa tana murmushi tace "Ga kudin" Amsa yayi ya ajiye gefensa, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Washegari Mayraah na idar da sallan asuba bayan ta gama azkar ta shiga dakin da Badiyyah take, zaune ta sameta kasa, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ya jikin?" Badiyyah ta gyada mata kai, Mayraah tace "In kawo maki kunun ko shayi" Badiyyah tace "Ko wanne" Mikewa Mayraah tayi ta fita, Bangaren Ammi ta fara tafiya don ta gaisheta, tana shiga ta tadda Mama Ladi na minshari kan darduman da tayi sallah, dakin Ammi ta karasa tayi sallama, Ammi ta amsa mata, ta shiga dakin... Maheer na zaune gefen Ammi, ita kuma tana zaune kan darduma, Mayraah ta duka kusa da Ammi ta gaisheta, Ammi tace "Kin tashi lafiya" Mayraah tace "Alhmdlh" Kallon Maheer dake kallonta tayi tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau" Mikewa tayi tace "Zan dawo Ammi" Daga haka ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, sai kuma ta kalli Maheer a hankali tace "We will continue later Maheer" Bai bari sun hada ido ba yace "Ohk" daga haka ya mike ya fita daga dakin. The next day friday Mayraah na dakin Badiyyah da yamma Mama Ladi ta shigo, Mama Ladi tayi tagumi daga tsayen da take tace "Naga abinda ya isheni ni Ladiyo, Wato ke dai Mera baza ki ji shawaran da nake baki ba ko? Baki da aiki sai makale ma wannan mata kamar almajira, nace ki fita hanyarta kiyi ta kanki kin ki, me yasa kike cusa kanki a abinda bai shafeki bane? yarinyar da kowa yasan ba sonki take ba tun asali, yarinyar da saboda ita kiri kiri aka fasa aurenki da ɗan matsiyatan can, ko ke baki lura alhakinki ke bin ta ba? Ko wani me ciki za ki ganta fes fes gwanin sha'awa amma Badiyyah kamar sabuwar almajirar kana rod dake garin kaduna, ke ko don kar kije ki shaƙi wata cutar baza ki kama kanki daga zuwa inda Badiyyah take ba? To ni dai ba ruwana Mamuda na kiranki, yana can parlon Ammi yace ki je" Daga haka Mama Ladi ta fice daga dakin tana toshe hanci, Mayraah ta kalli Badiyyah da hawaye ya cika idonta, kasa ce mata komai tayi amma har cikin ranta bata son abinda Mama Ladi ke yi ma Badiyyah a gidan, abun yayi yawa, mikewa tayi ta fita daga dakin ta tafi bangaren Ammi, Abba na zaune parlorn Ammi, Ammi kuma na ta harkan gabanta, Mayraah ta zauna ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Anjima Usman zai kai ki can gidan Hajiya Amina kiyi weekend, mai aikinta bata nan" Sai a sannan Ammi ta juya ta kalli Abba, Mayraah dai ta kasa cewa komai tana kallon Abba, Abba yace "Sai ki dau kayan da za ki tafi da su" Ammi na kallon Abba cikin karfin hali tace "Mamuda kawai fitowa za kayi kace min kana son ta koma gidan matarka, ba sai ka yi wani corner corner ba, just go straight to the point" Mayraah ta sunkuyar da kanta lokaci daya har hawaye ya kawo idonta, Abba na kallon Mayraah yace "Tashi ki tafi kiyi abinda nace maki" Mayraah ta mike ta juya ta nufi kowa hawayen dake makale idonta ya zubo fuskarta ta fita daga parlon, sai a sannan Ammi ta fashe da kuka ta nufi dakinta, Abba ya bi ta da kallo, sai kuma ya tashi ya bi bayanta, kuka sosai ya sameta tana yi, ya zauna gefen gado yace "Kin ga, babu ta yanda za ayi kice zan raba ki da Mayraah, Mayraah is staying there for just 2 days ta dawo nan..." Cikin kuka Ammi ta katse sa tace "To ban amince ba Mamuda, kuma bazan taɓa amincewa ba, babu inda Mayraah za ta je ai ba wani ɗan iskan ya rainan min ita har zuwa yau ba, ba wani ya sha min wahalanta ba, ba wani ya...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai zuciyarta na mata zafi tace "Mamuda kar ka sa inji ina dana sanin aurenka, abinda ban taɓa yi ba sai yanzu da aurenmu ya doshi shekaru arba'in, wahalan da na ci a gidanka da irin sadaukarwa ta da abinda zaka biya ni kenan? Is this what i deserve Mamuda? Is this how to pay me? Ko me zan maka na cancanci haka? Me yasa zaka yi saurin mance halacci na gareka? After all my sacrifice yanzu wata from no where zata zo ta fi ni ƙima da mutunci a idonka, wata ce zata zo tayi reaping where she never sowed, ban taɓa zaton haka daga gareka ba Mamuda, kuma a duk zaman mu in dai na cuceka...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai ta mike ta bar masa dakin kawai, ya sake tashi ya bi ta parlor. Mayraah na dakinta bayan ta ci kukanta Abba ya kwankwasa kofar ya bude, mikewa tayi daga zaunen da take tana kallonsa, Abba yace "Dauko kayanki" Yana fadin haka ya bar bakin kofar, jikin Mayraah yayi sanyi sosai, fitowa tayi daga dakin ta tafi bangaren Ammi, a bedroom dinta ta sameta, Mayraah ta karasa kusa da ita ta zauna ta ma rasa abinda zata ce, Ammi tayi karfin halin cewa "Ki je kiyi yanda Abbanki yace Mayraah" Mayraah ta fashe da kuka tace "Ammi ni bana son in je gidan" Ammi tace "Ran sunday za ki dawo in sha Allah, in ma ba a dawo dake ba zan sa Maheer yaje ya dauko ki, be a good girl kije ki dau kayanki kala biyu" Kuka kawai Mayraah take, Ammi tace "Tashi ki je my dear" Mikewa tayi tana goge hawayen idonta ta tafi ta dau kayan nata kala biyu a karamin jakanta, tana dawowa bangaren Ammi ta tadda Abba a parlon, hakan ya sa ta juya ta fita ta sauka downstairs kawai, bayan kusan minti sha biyar Abba ya sauko yace "Je ki mata sallama ki zo mu tafi, i don't want go miss my flight" A hankali Mayraah ta mike ta wuce sama zuwa part din Ammi, a parlor ta sameta still a zaune, Mayraah ta zauna kasa tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ammi don Allah kiyi hakuri..." Sai kuma ta fashe da kuka, Ammi ta dafa kanta tace "Kar ki damu daughter, u are not to be blame, ba komai, ranan lahadi Maheer zai je ya dauko ki" Mayraah ta gyada mata kai hawaye na sauka idonta, Ammi tace "Tashi ki je, idan yayi dropping dinki airport zai wuce" Mayraah ta mike tana goge hawayenta ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo tana kokarin ganin hawayen da ya taru idonta bai zubo mata ba, Sai da Mayraah ta fara shiga dakin da Badiyyah take, ta duka gabanta tace "Zan je Miller road" Da sauri Badiyyah ta mike zaune ganin jakar hannunta cike da karfin hali tace "Yaushe za ki dawo?" Tana fadin haka hawaye ya cika idonta, Mayraah ta kwantar da murya tace "On Sunday in sha Allah, ba dadewa zan yi ba" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata hawaye na sauka idonta, Mayraah ta mike ta fita daga dakin duk jikinta yayi sanyi. Suna isa gidan a waje Abba yayi parking suka shiga ciki, Hajiya Amina tayi farin cikin ganin Mayraah sosai, ganin yanda ta makale bakin kofa tace karaso ciki mana, sai a sannan ta karasa ciki ta xauna, sallama kawai Abba yayi ma Hajiya Amina, tayi amsa addu'an Allah ya tsare ta rakasa har compound ita dai Mayraah na zaune kan kujera makale da jakarta, sabon drivern da Abba ya dauka a gidan shi yayi driving dinsa zuwa airport, Hajiya Amina ta dawo parlor tana kallon Mayraah tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login