Showing 201001 words to 204000 words out of 249515 words
zan yi mu tafi gida sai in ga yanda za mu yi da Mamuda" Aunty Mariya tayi kasa da murya tace "In har ya nuna bai amince ba ko jayayya kar kiyi da shi Ammi, ki nemi izini kawai ki kai ta Bichi gobe, nima goben za mu tafi da Hajja kadunan tunda tace baxata zauna nan ba, ga Mama Ladi tace za ta bi mu" Ammi tace "Toh shikenan" Aunty Mariya ce ta fita ta samo masu adaidaita sahu, aka saka akwatin Badiyyah a ciki, Ammi ta daure fuska tana kallon Badiyyah dake kwance a kasa tace "Tashi ki fita" Da rarrafe Badiyyah ta karasa gate din ta lallaba ta shiga adaidaita sahun, Aunty Mariya tayi ma Ammi sallama tana tsaye har adaidaita sahun ya juya ya bar layin sannan ta koma cikin gida. Ammi na isa gida dab da magrib ta sauka ta ba me adaidaita sahun kudinsa sannan ta sauko da akwatin Badiyyah ba tare da ta bi ta kanta ba ta shiga cikin gidan, Badiyyah ta sauko da kyar tana biye da ita a baya tana maida numfashi, Ammi taga motar Abba a garage alamar yana nan, Haseenah ce ta fito daga Chalet sanye da Hijab bayan ta leko compound jin an bude gate taga Ammi ce, ta sauka kasa ta karasa gun Ammi tace "Ammi sannu da zuwa" Ko kallonta Ammi bata yi ba tace "Sannu" Zata amshi akwatin hannun Ammi, Ammi ta ki sake mata tace ta bar shi kawai, tun shekaranjiya Haseenah ke gidan bayan an sallameta daga asibiti kamar yanda Abba ya umarce Maheer ya kawo ta gidan don tana ma gidan Badiyyah tayi wannan tonan sililin a parlon Hajja, kamar ance Haseenah ta juya taga Badiyyah ta shigo compound wujiga wujiga duk ta rame tayi baki, nan da nan Haseenah ta hade rai ta kauda kai, Badiyyah dake fama da kanta ko bin ta kan Haseenah bata yi ba ta shige cikin gidan da sauri don kwanciya kawai take son yi ga amai da ke taso mata, Haseenah ta ɗan yi jim, sai kuma ta bi bayansu zuwa main building din gidan ita ma, a parlor ta tadda Badiyyah ta kwanta, Ammi kuma ta haura sama, Lokaci daya ta ga Badiyyah ta mike da gudu ta shige bandakin dake parlor tana kakarin amai, bude baki Haseenah tayi da mamaki bayan ta bi ta da kallo, a hankali tace "Amai kuma??" Can dai ta juya da sauri ta fita daga parlon ta koma Chalet din da take. Ammi tayi shiru tana kallon Abba a sanyaye don maganganu kawai yake cikin fada inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, har ya kai aya, can ta sauke kanta kasa cike da karfin hali tace "Shikenan Yallabai kayi hakuri... kayi hakuri, goben sai in kai ta Bichi idan Allah ya kai mu" A takaice Abba yace "Da dai ya fi don bazata zauna a gidana ba i stand my words" Daga haka ya mike ya shige Bedroom dinsa Ammi ta bi sa da kallo wasu hawaye na sauka idonta, duk ya canza kamar ba shi ba, Abba da ko ɗaga mata murya baya yi idan yana mata magana a baya, abu ko bai masa ba idan tace haka take so to haka nan zai yi don baya son bacin ranta kwata kwata amma yanzu duk babu wannan, duk hakan na neman zama tarihi daga yan watannin nan da suka shude, he is now a changed person, tunanin hakan ya kara breaking heart dinta sosai, ta mike ta fita daga parlonsa ta koma bangarenta ta ci kukanta ta gode Allah.....
Mayraah na kwance dakinta bayan isha Karime ta shigo da sallama tace "Hajiya Ilham ga can kwan na soya maki a kitchen sai ki yanki bredin da zai isheki ki debi ruwan shayi a flask ki bar ma yallabai sauran, ni zan shiga gidan makociyarmu in duba jikin er ta ta kone a kafa, to duk yau ban shiga ba" Mayraah ta gyada mata kai tace "In zan ci zan je in dauka" Karime tace "Toh sai na dawo" Mayraah ta bi ta da kallo sae kuma tace "Amma ba dadewa za ki yi ba ko?" Karime ta juyo tace "Toh akwai dae wani pim din hausa da ake yi duk ranan juma'a, wani lokacin in Ummi ta shiga ta kwanta da wuri na kan je gidan in kalla, kinsan duk an rufe tashoshin gidan nan saboda yan biyun nan maxa da yarinyar nan Mimi da basu son maida hankali su yi karatu sai kallo, to yallabai duk ya rufe tasoshin ba a kallon finafinai a gidan nan, ke baki ga tun da kika zo sae dai ki ga an kamo tashan labarai ba" Mayraah tace "Yanzu dai kallo za ki je yi kenan" Karime ta kyalkyale da dariya tace "Baxan boye maki ba shi zan je inyi gaskiya, karfe goma ake gama pim din, ana gamawa zan dawo in sha Allah" Mayraah tace "Toh... Shikenan, sai kin dawo" Karime tace "Toh kar dai ki bar kwan ya sandare" Daga haka ta fita daga dakin.
[7/26, 7:51 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah ta sauko daga kan gadon da take kwance bayan tafiyar karime da kusan minti sha biyar, wayarta ta dauko ta bude second sim din da ta kashe tun dazu, ta zauna gefen gado tana ta kallon wayar as if contemplating to call him again or not to, after many minutes of thinking ta ajiye wayar a hankali ta mike ta shiga bandaki, wanka tayi ta fito, tana cikin dauko daya daga dogayen rigunan bacci da ta siya a Suleja cikin jakarta taji wayar ta na vibrate, ta dauko kayan baccin ta mike tana gyara daurin towel din jikinta ta karasa kusa da wayar tana duba me kiranta, sai da gabanta ya fadi ganin number Musharraf, ta zauna gefen gadon a hankali ta dau wayar tana kallo, har ya katse bata daga ba, ya sake kira nan ma bata daga ba har ya gama ringing, sake kira yayi this time around sai ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren ta ji yace "Pls who is this?" Ai bata san sanda ta zamo kasa ta zauna ba, she just realized she missed him so very much, ta kasa cewa komai zuciyar ta na bugawa, daga daya bangaren yace "I know u can hear me, pls say something...." Mayraah ta jinginar da kanta da gado a hankali tace "Good evening" Musharraf ya mike tsaye daga zaunen da yake yace "Mayraah" Shiru tayi bata ce komai ba, ya marairaice mata yace "Plss tell me kina ina Mayraah?" A hankali tace "Ina lafiya" Trying all best to be calm yace "I know, yes i know, amma plss ki gaya min inda kike trust me, tell me pls Mayraah, just trust me pls" Lkci daya ya birkice mata, Ta langwabar da kai tace "You don't worry about that" Yace "Nooo pls, Mayraah kin san halin da kika tafi kika bar ni ciki kuwa, not only me, ur brothers, ur parent, haba Mayraah, pls i am begging u ki gaya min inda kike, Baby don't u trust me?" Mayraah ta lumshe ido ta bude tace "I am somewhere far away, kar ka damu tunda ka ga na kira ka i am fine, and i just wanted to say hi...." A hankali yace "Mayraah" bude kofar dakin taji anyi ta juya da sauri taga Ahmad, kallonsa ta dinga yi don duk tunaninta idan ya ga yanayin da take zai fita sai taga ba haka ba, instead he is even walking in, dauke kanta tayi zuciyarta na bugawa tace "I will call you back" Bata jira cewar Musharraf ba ta katse wayar wondering dalilin da zai sa ya shigo mata daki duk da yanayin da ya ganta, she just tied a towel, gefen gadon ta ji alamar ya zauna, lkci daya ta juya ta kallesa tace "I am sorry, i want to dress up" Ya ɗan yi shiru yana kallonta, sai kuma ya buda mata hannu alamar what is there? Kasa motsawa tayi daga inda take zaune with shock amma taki nuna hakan a fuskarta, ko hijab dinta ta kasa yunkurin daukowa don dole sai ta tashi zata yi hakan, banda faduwa babu abinda gabanta yake gaba daya ta rasa wani tunanin zata yi a lokacin, silencing kiran da Musharraf yake ta yi mata tayi ta ajiye wayar a gefenta, kawai gani tayi ya dawo gabanta ya durkusa yana kallon idonta as if counting his words yace "I understand what u are going through Mayraah, Khalil briefed me earlier, it's sad and i get kin fito ne ki samu relieve by chilling away ur worries right? i love ur courage and braveness" Mayraah ta fara matsawa jikin gadon a hankali tana kallonsa babu ko kiftawa, a hankali tace "You are drunk" Buda ido yayi sosai yana gyada mata kai yace "Not much though, but how did u know? Ko kema kina sha ne?" Tayi murmushin da iyakarsa lips tace "Yeah" ya kara buda ido yace "Really?" Ta gyada masa kai tace "I won't mind some" Ya karyar da kai yace "Unfortunately I can't bring that home because of my Ummi, i drink only outside" Sosai gaban Mayraah ya fadi a tunaninta zai ce bari yaje ya dauko mata ne tasan na kwatanci, nan da nan hankalinta ya tashi, yayi kasa da murya holding on to her hand yace "Would u mind us spending the night somewhere...." Ta dake tace "Somewhere like??" Yace "Hotel, club, guess inn... And what have you" Tayi saurin gyada masa kai tace "Ohk, let me get dressed" Yayi kasa da murya yace "Thank you...." Bata yarda ta mike ba a gabansa, gaba daya idonsa na kirjinta, da sauri tace "Can u excuse me in shirya?" Yace "C'mon meye in kin shirya while am here" Daga ta zai yi ta wani fizge hannunta tace "Stop it" Ya mike yace "Ohk then" Jikin window ya koma ya tsaya ya rungume hannunsa yace "Ki shirya" Babu yanda ta iya haka ta mike tsaye, wani takaici ya tokare mata wuya, she was trying her best kar ta bari hawaye ya taran mata a ido, daukan kayanta tayi ta shiga bandaki ya bi ta da ido, sai a sannan hawaye ya fara sauka idonta ta jingina da bangon bandakin bayan few minutes ta saka kayan ta fito ta dau Hijab dinta ta saka, ta dau handbag dinta with her charger and phone, duk yana ta bin ta da kallo, without looking at him tace "I am done" har suka fita compound din gidan a motarsa Mayraah bata yarda sun hada ido ba, kamo hannunta yayi yana kallonta yace "or should we go for the hotel we met first?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ohk, but do u have an international passport?" Duk da tana da shi haka ta girgiza masa kai tace "Nop" Da mamaki yace "Why? Big gal kamar ki ace baki da International passport" Ta yi feigning murmushi bata dai ce komai ba, yayi kasa da murya yace "I will get you one if u don't mind, sai a maki visa ko na Uk ne don zaman kasar nan baya wani cire ma mutum damuwa a rai ga sa ido irin na malam bahaushe, u need to be far far away, i think next week zan koma i will try and see if we can make it together" Mayraah tace "Thank you" All through the ride shi yake ta surutunsa, ita kam tayi nisa tunanin da take suna isa hotel din kafin ya shiga ciki ta kallesa tace "Zan ɗan amso abu a mart din can na gaba, wait for me" Yace "Me za ki amso?" Tace "Chewing gum" Yace "Oh ok, bari in amso maki" Ta masa murmushi tace "Ai baka san irin wanda nake so ba" Yace "True" Bude motar tayi ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace "Not every girl that left home is a bitch, not every girl that left home is useless, don kaga na baro gida ba yana nufin ni er iska bace, kuma hakan ba yana nufin bani da tarbiya bane, i chose leaving home because of my mental health..." Tana kai wa nan tayi tafiyarta, sai a sannan wasu hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, ko waiwayawa bata yi ba har tayi nisa daga hotel din, tana isowa main road ta tare adaidaita sahu ta shiga ta gaya masa inda zai kai ta, har suka iso bata san sun iso ba don tayi nisa tunanin da take ga hawayen da ke ta saukan mata, sai da mai tricycle din yayi alerting dinta sannan ta sauka tana goge idonta ta basa kudinsa, tana shiga gate ta nemi kujera ta zauna, sai da tayi kukanta me isarta sannan ta ciro wayarta, missed calls din Musharraf ta gani ya fi goma, tayi dialing number Dr Khalil yana fara ringing ya daga, gaishesa tayi a hankali, ya amsa yace "Ya kike, ya gida?" Tace "Alhmdlh, are you at work?" Yace "Yeah ina night duty, Why do u ask?" Tace "Aa just want to be sure" Yace "Are you okay?" Wasu hawaye ne suka cika idonta kawai ta katse wayar, mikewa tayi taji ya sake kiranta bata daga ba ta shiga cikin asibitin, sau uku yana kiranta bata daga ba, tana shiga reception ta gaida nurses da ta gani ta haura sama zuwa office dinsa, wata nurse fa'iza ta mike da sauri ta tafi inda jakarta yake ta ciro wayarta ta fara kiran Zainab. Dr khalil na zaune still calling her line ta shiga office din ko knocking bata yi ba, yana ganinta ya mike yana kallonta, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kan kujera, ya zagayo yace "Mayraah are you okay?" Bata san sanda ta fashe da kuka ba, ya iso gabanta da mamaki yace "Lafiya? Talk to me, me yake faruwa?" Duk da tambayoyin nan da yake jefo mata hankalinsa kawai ya tafi kan kila Zainab taje ta sameta ne a gida don not long ago ya kira Ummi tace masa tana gidan biki, ganin taki basa amsa sai kuka take ya duka gabanta yace "Plss talk to me Mayraah, an maki wani abun ne?" Bude office din aka yi duk suka juya, MD ne ya shigo, Dr Khalil ya mike yana kallonsa, Mayraah ta kauda kanta da sauri, tunda ya kallesu sau daya bai sake kallonsu ba ya ajiye files din hannunsa yana kallon Khalil yace "See me off" Dr Khalil yace "Ohk" fita yayi office din Dr Khalil na kallon Mayraah yace "I will be back right away" Daga haka ya fita daga office din ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake sauka idonta. Dr Khalil na kallon MD bayan sun fita reception yace "Drivern ya iso ne?" MD yace "Ban kirasa ba, just drop me" Dr Khalil yace "Ni fa da na ga kayi dare na zata u will pass the night here MD" MD na mika masa makullin hannunsa yace "Ka taba ganin na kwana asibiti in ba dole ba?" Dr Khalil bai amshi makullin nasa ba yace "Sae dai mu je a motata ka bar naka a nan, tunda zan dawo asibitin" MD yace "Mu tafi a nawa sai ka dawo da shi, bazan iya jira sai kaje sama ka dauko key ba" Yana fadin haka ya bude front seat ya shiga, Dr Khalil ya zaga ya shiga driver seat, sai da suka bar asibitin Dr Khalil yayi dialing number Mayraah, tana dagawa yace "Nan da 30 minutes zan dawo in sha Allah, ki jirani" yana gama fadin haka ya katse wayar, MD dake kallonsa yace "Wato ita wannan mannerless teenager din budurwarka ce shi yasa ka dage sai ta samu aiki a asibitin nan ku jone salon ka daina maida hankali a aikin ka ko, sannan ita wannan er mitsitsiyar yarinyar har yaushe aka haifeta tayi degree? thank God ba aikin za a bata ba, kuma baza a taɓa bata ba as far as i remain the MD in here, sannan on a serious note bana son sake ganinta a asibitin nan, she is neither a staff nor a patient don haka ban ga dalilin da zata dinga shigowa ba, i will talk to the securities not to let her in from henceforth" Dr Khalil dai bai tankasa ba driving dinsa kawai yake. Bayan tafiyar Khalil da kusan minti arba'in Mayraah dai na zaune office dinsa ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da take taji an bude kofar office din ta juya duk tunaninta shi ne ya dawo, sosai gabanta ya fadi ganin Zainab ta shigo office din fuska a murtuke kamar an jefota, Mayraah ta sauke idonta daga kallonta, lokaci daya jikinta yayi sanyi, Zainab ta karaso har gabanta tana kallonta da kyau tace "Ke don kaza kazanki duk fadin garin Abuja baki ga maza yan iska mara mafada karuwai irinki ba sai mijina za ki makale ma? Baki ga matsiyata masu zaman kansu kaman ki ba sai mijina? To wai ma ke uban wa yace maki Khalil ɗan iska ne? ko kuma ance maki shi ma daga sama ya fado bashi da iyaye kamar ki? Don in har kina da iyaye ban jin zaki dinga irin wannan kazamin rayuwar da kike kamar sakakkiyar akuya a garin Abuja, baki can baki nan, baki gidan mutane, baki asibiti, baki hotel, baki Suleja da kika kama gida kike zaman kanki ko ance maki duk ban bincika ba? to bari ki ji wallahi wallahi ina ja maki kunne da babban baƙi ki fita harkar mijina, i am warning u ki fita harkar khalil, stay away from my husband kada inyi maki abinda baki taɓa zato ba a rayuwarki don wallahi ba mutunci ne da ni ba, ba ni da kirki wallahi, sannan in ba zina iyayenki suka yi suka haifeki ba to ki bar min gidan uwata ki kama gabanki ki je can ki ci gaba da rayuwar zaman kai da kike a suleja, mu gidanmu gidan tarbiya ne, sai ki wani dinga yawo da