Showing 162001 words to 165000 words out of 249515 words
hannun Ammi ta amsa a rikice tana jujjuyawa tace "Ko sakin ki Mamudan yayi??" Ammi dai ta kasa cewa komai sai kuka take uncontrollably, Hajja ma ta fashe da kuka gashi ita ba iya karatu tayi ba balle ta karanta takardan taga na menene, cikin tashin hankali tace "Ki bude baki kiyi min magana don Allah, sakin ki Mamudan yayi wai??" Ganin Maheer ya shigo Parlon Hajja ta nufesa da sauri jiki na rawa tana nuna masa takardan tace "Maheer takardan meye wannan din?" Maheer yayi shiru yana kallonta da farko, can yace "Mayraah ce ta rubuta" Hajja tace "Mayraah kuma? Na meye to?" Maheer yace "Ta tafi" Hajja ta zaro ido tana kallonsa tace "Ta tafi? Ta tafi ina?" Maheer bai bata amsa ba ya juya ya fita daga parlon ya koma balcony ya tsaya, Hajja ta dawo da sauri tace "Ina wai Mayraahn ta tafi Ammi?" Cikin kuka Ammi tace "Allah ya gani ko 'ya yan cikina ban gwada masu son da nake ma Mayraah ba, ban taɓa mata kallon ba ni na haifeta ba tunda Allah ya bani ita, kallon jinina nake mata, soyayyar uwa da ɗan ta nayi mata....." Ta kasa ci gaba saboda kukan da ya ci karfin ta, Hajja ta zauna kan kujera ta rasa abun cewa, can ita ma ta fashe da kukan ta daga hannu sama tace "Allah mun gode maka, wannan wani irin fitina ne ke ta billo mana ni Sadeeyah daga wannan sai wannan? Wa ta sani a duniyar da har zata ce ta tafi? Ta tafi ina? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya tsine ma wannan mata ta Maheer duk ita ta jagwalgwala al-amarin nan, muna zaman mu lafiya ya auro annoba ta tarwatsa mana farin cikin mu, yanzu ita kanta Badiyyar bamu san inda ta tafi ba bamu san wani hali take ciki ba, ga Mayraah ma wai ta tafi, ta wa ta sani da zata ce ta tafi?" A ranan Abba ya maida Hajiya Amina sabon gidansa da ya gama ginawa har yayi furnishing not long ago a Miller road, he wanted to take Ammi by surprise, don ko su Maheer basu san da gidan ba balle ita, kawai rana daya yayi niyyar ce masu su shirya za su fita kawai sai ya kai su gidan daga nan kuma sai tarewa ba lallai ma su koma tsohon gidan ba, don shi ma a yanzu yana son barin anguwan da ya taso ya koma area with full security ya zauna, tsohon gidan nasa kuma ya saka cousin dinsa da matansa uku don kar gidan ya kasance babu kowa, Chalet kuma dama wani makocinsu dake biyan kudin haya da kyar don yawanci shi ke biya masa kudin hayan ma duk shekara, to shi yayi niyyar ba ma chalet din da matarsa da yaransa su zauna, to a yanzu kam ya ji zaman gidan ya fita ransa, tafiyar Mayraah ba karamin daga masa hankali yayi ba da distablizing dinsa, he wish zata canza tunani ta dawo gida don bata da wani gata a duk inda ma zata je yanzu, ya kuma san he tried his best, yayi bakin kokarinsa na ganin she wasn't traumatized or felt dejected with all what was happening, yayi iya kokarinsa all through the Saga but all his effort prove abortive, yasan da Ammi bata mata abinda tayi mata ba koma me zai ci gaba da faruwa bazata bar gida ba, baya jin zai iya yafe ma Ammi da ahalinta gaba dayansu, ba don yaranta ba babu abinda zai hanasa tura mata text kar ta dawo masa gida don har cikin ransa yaji baya ma son ganinta, amma bazai yi hakan ba ko don albarkacin su Maheer, don haka gwara kawai ya bar mata gidan kawai, daga ita har yaran nata. Karfe bakwai da rabi bayan gari yayi duhu Maheer ya kai Hajja gidanta, Throughout hours din da suka yi gidan Maheer kuka kawai Ammi take regretting so many things, kana ganinta kasan ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, she never expect things to go this way, ba kowa ya ja mata duk wannan abun ba sai Hajja da take kokarin ganin ta rabu lafiya da, pressure din Hajja duk shi ya ja mata wannan abu, she was only trying to please her mother in so many ways kar su samu matsala, Hajja kam ba bakin magana amma ta tsine ma Haseenah ya fi a kirga, ta rantse ta kuma rantse Maheer bazai ci gaba da zama da annoba, Abincin da ya fita ya siyo masu ma duk basu ci ba saboda babu kwanciyar hankalin ci, Maheer na maida Hajja gida ganin Ammi zata sauko daga motar Hajja ta kalleta tace "Ina kuma zaki kike kokarin saukowa?" Cike da karfin hali Ammi tace "Me zan koma gidan in yi Hajja? Babu amfanin komawata kawai" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Hajja tace "Ni kuma me zaki shigo min nan kiyi, ni fa ina ji a jikina babu inda Mayraah ta tafi in ma zaki kwantar da hankalinki, ki kwantar da hankalinki ki dukufa da addu'a ba ji ba gani wallahi zata dawo, babu abinda kukan nan zai kara ki da shi sai ma ki ja ma kanki wata cutar dama ke ba lafiyayya ba yanzu, kwanaki ma ba haka ta dinga yi ba da aka fasa auren kuma daga baya sai ta dawo, duk bacin rai ne da rashin madafa ba wai wani abu bane yasa tace ta tafi, tunda ita kanta tasan bata da inda za ta, bata da kowa da ya wuce mu, ai yarinya ce me hankali Mayraah, ina da tabbacin kilan gidan kawayenta ta tafi ta samu nutsuwa na ɗan lokaci, amma in sha Allahu zata dawo komin dare, ke kin taɓa ganin inda ɗa ya guji iyayensa komin laifin da suka masa? To ki sa ma ranki salama ki koma dakinki ki samu kuyi shawaran yanda za a fara cigiyarta a gun yan makarantarsu ke da mai gidan ki, wannan kawar tata da kika kira daxu ai ba ita kadai bace kawarta, kilan wajen wata daban taje, kar ki biye abinda Mamuda ya maki ki samesa a san na yi tun dare bai tsala ba, in sha Allahu Mayraah tana nan gun kawayenta, nima yanzu ina shiga zan buga lamban yan bichi in ji ko Badiyyah ta je can ko hankali zai kwanta, amma Mayraah kam nutsuwarta da sanin ya kamata ma bazai sa ta tafi wani waje ba, tana nan kusa da mu in sha Allah" Hajja na kai wa nan ta bude gidanta dake bude har sannan ta shiga ciki a hankali tana cewa "Wai ni yau da mutuncina da girmana aka kai Caji opis" Sai kuma ta fashe da kuka ta kulle gidan. Maheer ya bar anguwan bayan sun ajiye Hajja, tun dazu ko magana bai yarda ya hadasa da Ammi ba balle ya bata hakurin kukan da take, to me ma zai ce mata.
Wajen karfe tara Mayraah ta farka daga baccin da take, it was still raining but not heavily, zuwa sannan zazzabi ne sosai jikinta, ta daure ta sauka daga kan gadon ta lallaba ta bude jakarta ta ciro wani hijab ta saka sannan ta dau Atm card dinta, tana tafiya a hankali ta bude kofar dakin ta cire makullin sannan ta fita ta kulle kofar ta sauko kasa, reception din hotel din ta nufa cike da karfin hali tana kallon receptionist din tace "Plss where can i locate...." Kasa ci gaba tayi ta dafe kanta, receptionist din ta zagayo inda take da sauri ta riketa ganin tayi baya zata fadi tace "Are you okay Madam?" colleague din receptionist din shi ma ya taho da sauri suna mata sannu, Mayraah dai gyada masu kai kawai, receptionist din ta karasa da ita inda kujera yake ta xaunar da ita kan kujera tana kallonta, sauran ma'aikatan wajen ma duk suka taho suka tsaya kan su, Receptionist din tace "Amma baki da lafiya ko?" Mayraah ta kasa bata amsa sbda sarkewa da breathing dinta ya soma yi, nan duk suka rikice aka fara mata fifita duk da sanyin gari, wata worker din wajen na cewa ko dai a tafi da ita asibiti don babu wani tanadi incase of such emergency a hotel din, Wani mutumi ne ya shigo Reception from upstairs zai fita waje, ya tsaya ganin yanda ma'aikatan hotel din suka taru waje daya sai fifita suke ma Mayraah, ya karasa inda suke yace "Hope all is well?" Wani ma'aikaci yace "Bata da lafiya ne muna jiran za a dauko makullin mota a tafi da ita asibiti" Yace "Subhanallah, why not mu tafi asibitin since i am with my car key, i am going out now" Yana fadin haka ya tsaya gaban Mayraah yana kallonta yace "Sannu, are you Asthmatic?" Mayraah bata ma san yana yi ba don zuwa sannan double take ganinsu gaba daya, da sauri ya kalli receptionist din yace "Ku fito da ita kawai, mu tafi asibitin" Yana fadin haka ya fita in a haste don tada motarsa dake parking space, receptionist din suka tafi da Mayraah motar tasa, ya bude masu back seat, ma'aikaciyar hotel din daya ce ta shiga motar tare da Mayraah za su tafi asibitin bayan ta amshi Atm din Mayraah dake hannunta kar ta yar, makullin dakin kuma ta ba colleagues dinta su mayar cikin hotel din, tuni ya ja motar suka bar haraban hotel din bayan an bude masu gate. Mutumin na driving din ya kira wani abokinsa yana dagawa yace "Hello Dr kana hospital ne?" Sai kuma yace "Ohk, to dama emergency ne, wata baiwar Allah ce bata da lafiya muna hanyan asibitin yanzu" Daga haka ya katse wayar. A hankali Mayraah ta bude idonta after an hour a asibitin, ido hudu tayi da receptionist din dake zaune ward din ana jiran tashin Mayraah don ta kira yan uwanta kafin ma'aikaciyar ta koma hotel bakin aikinta as instructed by the hotel manager, matar ta sakar ma Mayraah murmushi ta mike tace "Sannu fa" Mayraah ta mike zaune da kyar tana bin ward din da kallo, it's so big and clean, daga gani kasan ba karamin asibiti bane ko daga gadon da take kwance zaka gane hakan, Receptionist din tace "Bari in masu magana ince kin tashi...." Daga haka ta fita daga babban ward din, Mayraah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Cctv camera dake ward din, maida dubanta tayi kan drip da aka makala mata a hannu, dai dai nan aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, wani mutumi ne ya shigo tare da wani dake biye da shi a baya with white lab coat da stethoscope a wuyansa, ita dai duk kallonsu take har suka iso bakin gadon da take, mutumin da ya fara shigowa dakin ya ɗan duka ya dafa gadon yana kallonta yace "Baiwar Allah ya jikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Likitan ya karaso ya kara gudun drip din kafin shi ma ya kalleta yace "Hope you are feeling much better now?" Tace "Sure" Yace "To Maa sha Allah" Receptionist din tace "Manager yace ta kira yan uwanta sai ni in koma bakin aikina" Sosai gaban Mayraah ya fadi, likitan yace "Eh gaskiya ne, ai kun ma yi kokari for such hospitality" Sai kuma ya kalli Mayraah yace "Ki kira yan gidanku yanzu ki sanar masu kina asibiti" Da sauri tace "Ai wayar na dakin hotel din" Mutumin da ya kawota hospital ya ciro wayarsa ya mika mata yace "Za ki iya amfani da nawa" Sosai gabanta ya fadi, ta amshi wayar tana tunanin yanda zata yi, nan da nan dubara ya fado mata tayi dialing din layinta dake kashe ta sa handsfree, duk suka dinga kallonta jin switch off, a hankali tace "Number Abbanmu ne, bari in kira yayana" Daga haka ta sake dialing other line dinta nan ma aka ce switch off, Mayraah ta kalli receptionist din tace "Za ki iya tafiya, Nagode sosai, nasan zuwa anjima zan samesu a waya" Receptionist din tace "Toh Allah ya kara lafiya, ga Atm card dinki" Mayraah har ta mance da Atm card din, ta amsa tana juyawa tace "Nagode" Receptionist din tayi mata Allah ya kara lafiya, zata fita mutumin da ya kawo su yace "Ko za ki jira mu koma tare in 30mins time" Tace "Ayya, kar ka damu zan samu Cab idan na fita, kaga instruction din manager dinmu kenan, yace tana farkawa in dawo bakin aiki" Yace "To ba laifi" Daga haka ta fita daga ward din. Mayraah na gyara Hijab din jikinta a hankali tace "Naji sauki fa, kawai za a iya sallamata in biya bill din" Dr Khalil ya kalli abokinsa Ahmad kamar yanda Ahmad din ma ya kallesa, can Dr Khalil yace "Ae ba a gama baki proper medications ba, kuma kinga ko rabi drip din hannunki bai kusa ba" Mayraah tace "Ni fa i am okay, kawai jinina ne yayi kasa, but i am better now" Ahmad yace "Ohk then, ka sallameta Dr, sae kawai a rubuta mata drugs" Dr Khalil yayi kasa da murya yace "To ae kasan ka'idar hospital din nan...." Ahmad yace "To tace zata canza hospital, It's not ur fault" Dr Khalil yace "Ohk then"
[7/16, 1:35 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan rubuce rubuce Dr Khalil yayi discharging Mayraah, daga gefe kuma ya rubuta mata drugs a wani takarda ya mika mata yace "Ki siya wannan a pharmacy, Allah ya kara lafiya" Ta amshi takardan cikin sanyin murya tace "Thank you, nawa bill dina?" Ya nuna Ahmad dake zaune yace "Yayi clearing din bill din" Ta juya ta kalli Ahmad din kafin tace komai ya mike yace "Idan hotel din za ki koma nima can zan tafi yanzu, in kuma da inda zaki sai inyi dropping dinki it's already late now" Mayraah tace "Toh Nagode" Fita suka yi daga ward din likitan na biye da su, Mayraah ta dinga bin asibitin da kallo ganin na masu hannu da shuni ne don har da jajayen fata ta gani a asibitin, a haka har suka fito haraban hospital din, ruwan ya tsaya gaba daya amma ko ina yayi mugun sanyi, ta takure cikin hijab dinta har suka isa inda yayi parking motar sa, ta bude front seat ta shiga bayan shi ma ya shiga motar, sae da suka fita hospital din ta dinga jin wani yunwa ba na wasa ba, dai dai wani eatry tace "I want to get something here pls if u won't mind" yace "Ohk" parking yayi, ta bude motar ta sauka ta kulle masa sannan ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta dawo motar rike da leda ta bude ta shiga, sae a sannan ta tuna kanta kadae ta siya ma abinci fa, bayan ya fara tafiya ta ɗan kallesa tace "in siya maka ne?" yace "No, na ci abinci, thank you" Bata sake cewa komai ba, tana ganin pharmacy har zata ce ya tsaya ta siya maganin da aka mata prescribing sae kuma ta fasa da zumar zata siya gobe idan ta bar hotel din, suna isa bayan yayi parking ta sauka tayi masa godiya ta shiga hotel din ta bar sa a baya kamar ba tare suke ba, tsaye take a reception tana jiran makullin dakinta shi ma ya shigo, ana bata aka basa nasa ta bari ya fara tafiya sama, sannan ita ma ta wuce sama, nan taga ashe dakinsa na kallon nata ne ma, ita dae bata kallesa ba ta bude dakin nata ta shiga ta kulle kofar da makulli. Tun da suka dawo asibitin Mayraah ke kwance bata yi bacci ba, don tana shigowa daki kamar tare ta shigo da cramps, wanda a hospital ko alamarsa bata sake ji ba tun da ta farka har suka bar asibitin, tun tana daurewa ta sauko kasa ta sake koma kan gado, ta mike tsaye ta zauna har dai ta kasa ci gaba da jurewa, nan da nan ta fara fita hayyacinta, wajen karfe daya da rabi ta bude kofar dakinta ta fito ko sanin ta fito ma bata yi ba saboda ciwon yayi mata yawa, ta durkusa bakin kofar dakin da taga ya shiga ta kwankwasa da kyar, sae da ta kwankwasa sau uku sannan taji yana tambayar waye, cikin rawan murya tace "Ni ce" bude kofar yayi ganinta Durkushe ya koma baya da sauri yana kallonta, ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "Don Allah ka taimaka ka kai ni asibiti" Kallon mamaki yake mata, ta hade hannunta tana kuka sosai tace "Don Allah kayi sauri, wallahi baxan iya ba kuma" Komawa daki yayi ya dauko makullin motar tasa ya fito, sai a sannan ta mike ta jingina da bango har sannan tana kuka, ya kulle dakinsa ya tafi nata ya bude, tana kallonsa ya shiga sai gashi ya fito da hijab dinta ya mika mata, amsa tayi ta sa da sauri, ya kulle nata dakin ma da makulli, a daddafe ta bi sa suka sauka downstairs ya mika ma yan reception din makullansu sannan suka fita tana biye da shi a baya zuwa parking space. Har suka isa asibitin Mayraah kuka take don ita kadai tasan abinda take ji, shi dai tun da ya mata sannu sau hudu ya ja bakinsa yayi shiru.... Dr Khalil ya fito ward din da Mayraah take yana kallon Ahmad dake zaune corridor din wards din ya jingina da bango idonsa a kulle yace "Hey wai bacci kake a nan" Ahmad ya bude ido yace "Really, karfe nawa yanzu?" Dr Khalil yace "Biyu ya wuce, Flight din naka na karfe nawa ne?" Ahmad yace "Karfe biyar" Dr Khalil yace "Nan dae da 3 hours" Ahmad yace "In sha Allah" Dr Khalil yace "Tayi bacci yanzu, i think zaka iya komawa hotel din kar kaje kayi missing Flight dinka, ita kuma zuwa safe za mu yi expecting yan uwanta, daga nan sai ayi discharging dinta don it's just cramps, But still idan baza ka takura ba mu je office dina ka kwanta zuwa 3:30 sai ka tafi hotel din daga can ka wuce airport" Ahmad ya mike yace "Ohk I will prefer that"