Showing 21001 words to 24000 words out of 249515 words
so, Hajja bata jin maganar kowa sai ita ko don tana kulla mata shinkafa a leda ta kai mata ne oho, amma banda haka ko ita da bazata amince da wannan abu da aka maki ba, me aka yi akayi Mera kuma Allah na tuba? Ana nufin Mera ta fi ki matsayi wajen Ammi ko Hajja kenan? To ko dai cutar mantuwa ce ta kama su, kina er kanwarta uwa daya uba daya a maki haka akan Mera?" Badiyya dake ta kallon Mama Ladi tace "Ko dai baki gane wacce Mayraahn nake nufi ba?" Mama Ladi tace "Ni ko na gane warce kike nufi, ko ba er wajen Ammi ba? Ko ba wannan tsigalalliyar fara doguwa da hanci zarere kamar biro" Badiyya ta hade rai tace "Ita mana... Ita ce ta kwace saurayina za a masu aure yanzu haka saura wata daya" Murmushi Mama Ladi tayi ta rike haɓa tace "Ikon Allah, dama ance in da ranka zaka ga abubuwa iri iri, to gashi ko na ga wannan"
07087865788✍🏻
WhatsApp only.
[5/31, 4:45 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖
By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻
6......
Babu wanda ya kai Ammi shiga tashin hankalin disappearance din Badiyyah, Maheer dama ko a jikinsa ya shirya ya fita aiki wajen karfe tara, Mayraah ma shi ya sa ta tafi lectures, don ita ma hankalinta ya tashi ganin yanda Ammi ta damu sosai, gashi Ammi ta kasa gaya ma Abba abinda ke faruwa har dai ya fita wajen karfe goma, dama kafin ya fita ta nemi izinin zuwa wajen Hajja, yana fita kuwa ta bi bayansa zuwa gidan Mahaifiyarta... Hajja dai ta bi ta da kallo har ta nemi waje ta zauna sannan tace "Ke baki da aiki sae daga ma kanki hankali akan abinda bai kai ya kawo ba matar nan, waye bai san halin Badiyyah ba, yarinyar da nima ta sha min haka in tashi da sassafe in ga babu ita a gida, nace maki ki kwantar da hankalinki kin ki" Da damuwa Ammi tace "To Hajja naga na kira Bichi sunce bata je ba, ga shi har yanzu wayarta a kashe kinga kuwa dole in damu ai" Hajja tace "Yanzu haka tana wajen kawayen nan nata da basa gaya mata gaskiya, sai can yamma nasan zata tafi Bichin, haka nan take sai dai in mantawa kika yi, don haka ki kwantar da hankalinki kawai, in dai Badiyya ce zata aikata abinda yafi haka ma" Har kusan la'asar Ammi bata bar gidan Hajja ba, lokaci lokaci kuma take kiran layin Badiyya still sai ta ji a kashe, a takaice dai ranan ta kira Badiyya ya fi sau Hamsin, Hajja tace "Kin ga ki tashi ki koma gida yamma ya gabato" Ammi "Me zan girka maki kafin in tafi?" Hajja tace "Ga dai sauran girkin da kika yi da rana ai ya isheni har ma zan ba almajiri a ciki" Hajja bata rufe baki ba wayarta ya fara ring, ta dauka tana nuna ma Ammi screen din tace "Waye?" Lokaci daya Ammi ta sauke wani ajiyar zuciya ganin Badiyya ce ke kiran Hajja, Ammi tace "Ita ce" Hajja tace "Ahaf, taga daman kunna wayar kenan, Allah dai ya shirya mana ita kawai"' Hajja ta daga kiran tare da saka handsfree tayi sallama, daga daya bangaren Badiyya tace "Ina yini Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau Badiyya, ina kika je duk kika bi kika daga ma mutane hankali haka?" Badiyya tace "Kawai na tafi Bichi, kuma zan yi sati zuwa kwana goma a nan kafin in dawo" Hajja ta buda baki tace "Makarantar fa Badiyya? Ba naji ance a matakin karshe ku ke ba? Wa zai maki jarabawan?" Badiyya tace "Kwana goma fa kawai zanyi in dawo ai" Hajja tace "To me yasa kika tafi babu ko sallama duk kowa ya bi ya damu, ko Ammin taki fa baki sanar ma tafiyarki ba duk ta daga hankali" Badiyya tace "Kawai ni Hajja bazan iya zaman gidan ba ana nuna min wariyar launin fata saboda iyayena sun mutu, Shi Maheer yayi ta min fada yana min tsawa kamar wani ubana kuma ko fuska baya sake min alamar dai bai ji dadin zuwana gidan su ba, ita kuma Mayraah saboda ni taki zaman dakinta ta kwashe duk wani abun amfaninta ta fita, kwata kwata ma ta daina kwana dakin kuma ko magana bata min tun da naje wllh, kawai dai alamar babu wanda yayi farin ciki da dawowata gidan, shi sa kawai na taho Bichi idan nayi kwana goma a nan na huta zan dawo gidanki, sauran kayana dake can gidan dama ki aika a kwaso min a ajiye nan gidanki" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "To shikenan sai kin dawo, ina gaida mutan gidan gaba daya" Badiyya tace "Za su ji" Daga haka ta katse wayar, Mama Ladi dake dama fura tace "To kin ga haka ae ya fi kar tashin hankali yasa er uwata ta shiga wani hali in shiga uku" Badiyya dae bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayarta ta koma ta jingina da gadon karfe tana kallon Mama ladi, Mama ladi tace "Wai ya naga duk kin dawo wani iri" Badiyya dai bata ce komai ba, amma fa kana ganinta kasan she looks confuse.... Ammi kam tayi jigum tana kallon Hajja bayan ta ajiye wayar hannunta, ta ma kasa cewa komai maganganun Badiyya kawai ke mata yawo a kai, Hajja ta kyabe baki tace "Ki tashi kawai ki tafi gida, Allah ya sauwake, amma Mayraah bata kyauta abinda tayi mata ba, da bata yi mata haka ba, Su dama 'ya yan nan naki maza ni nasan ba son Badiyyah suke ba tun asali, dubi abinda Usman yayi mata ranan kamar wata mara galihu, kawai an maidata baren karfi da yaji, haka ae babu dadi, in su basu hada komai da ita ke kam ai dolenki ce..." Lokaci daya hawaye ya kawo idon Ammi jikinta yayi sanyi, Hajja tace "Ni ba kuka za ki min ba, ki tashi ki tafi sae anjima, amma ki gargadi Mayraah abinda tayi sam bata kyauta ba..." A hankali Ammi ta girgiza kai tana hawaye tace "Ni ban isa in canza maki tunaninki akan abubuwan nan dake faruwa a kwanakin nan ba Hajja, nasan akwai abubuwa da yawa a ranki da baza ki iya fadi ba, sannan nasan duk abinda zance maki bazai sauya tunaninki na cewar ina fifita Mayraah akan Badiyya ba, kuma ina ta kokarin gudun hakan amma abun ya ci tura, dai dai da second daya ban taɓa fifita Mayraah akan Badiyya ba Allah shine shaida...." Hajja ta dakatar da ita da sauri tace "Ke kin fi kowa sanin ba haka nake ba, Allah ya sauwake kuma in zama haka, ni babu komai ƙasan raina sai Alkhairi, ai ɗa na kowa ne bawa sai me shi, Allah dai ya rufa mana asiri duniya da lahira, in ma akwai wani zargi da kike yi a ranki da har yake damunki yau da kullum to ki gogesa, ba komai ke hanaki sukuni da aikin koke koke ba illa abinda kika dasa a ranki yake nukurkusan ki, ni ai ba yarinya bace, don haka ki tashi ki tafi gida kawai, yara kuma gaba dayansu Allah yayi masu albarka, duk daya suke a wajena babu banbanci har ga Allah" Har Ammi ta bar gidan Hajja jikinta a sanyaye yake, why is all this happening all of a sudden, duk kwanan nan bata samun nutsuwa ta rasa dalili, ta saƙa wancan ta warware duk ita kadai a ranta, tun dai da aka kawo kudin auren Mayraah, Ko da ta koma gida maimakon tayi scolding Mayraah kan abinda Badiyyah tace a kanta bata yi hakan ba, sai ma kara jan abarta da tayi a jiki tana kuma jin ta har cikin ranta.... Throughout satin tare Mayraah suka dinga zuwa kasuwa da very close frnds din Ammi guda biyu, kaya na gani na fada suka dinga siya mata na lefe masu tsada da quality, within period din kuma Dr Musharraf ya tura mata sauran 3M din, Ammi tayi ta mata fada me yasa zata bari ya kara turo kudi, wannan ai rashin godiyar Allah ne da kai kai inda Allah bai kai mutum ba, kafin sunday suka gama hada komai na lefe, Abaya da akwatuna ne sai jewelries kawai ba a siya ba.... Ranan litinin da yamma Musharraf ya tura driver dinsu ya je daukan kayan don a zuba su cikin akwati, bayan magrib Mayraah ta sauko downstairs sanye da hijab har kasa, Ammi ce zaune parlon da Usman, Mayraah ta karasa kusa da Ammi ta durkusa kasa tace "Ammi yana jirana a waje" Ammi na kallonta tace "To amma kar ki dade" Mayraah tace "Toh Ammi" Ta kalli Usman dake kallonta sannan ta mike, Usman yace "Me yasa shi bazai zo ido na ganin ido ba" Ita dai Mayraah bata ce komai ba, Ammi ta kallesa tace "Ai bai ma fiye zuwa da daddare ba" Mayraah ta juya ta nufi kofa kamar munafuka, Usman yace "Saura ayi isha kina waje" juyawa tayi ta kallesa, Ammi ta hararesa tace "Yi tafiyarki ki rabu da shi, wani ya hanasa dinga zuwa zancen shi ma..." Mayraah ta ɗan yi murmushi ta fita daga parlon. slowly take tafiya har ta isa kofar gidan, ta jingina da motarsa tana jiran ya sauko, sauke glass yayi lkci daya turarensa ya gauraya wajen, yana kallonta yace "I am not staying long, ki shigo mu yi magana...." Ba musu ta bude motar ta shiga sannan ta kulle ta jinginar da kanta da kujeran motar cikin sanyin murya tace "Good evening sir" Yana kallonta yace "Me yasa baki je school ba yau?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma a hankali tace "I was having headache" Ya dinga kallonta, can yayi kasa da murya yace "Mayraah" Juyawa tayi ta kallesa suka hada ido, sosai gabanta ya fadi, shi ya fara sauke idonsa yace "Tell me... menene yake damunki? for almost a week u are moody, What's happening wifey?" Tana kallonsa da manyan idonta tace "Ba abinda yake damuna fa" Yace "Ur test scores were poor..." Mayraah ta dinga kallonsa tana nazarin wani test ma suka yi, sai kuma tace "Na Dr Garba?" Yace "Test nawa ku ka yi last week?" A hankali tace "Uku" Yace "You didn't perform well in all" Kasa cewa komai tayi, and at the same time she look disturb and sad, Ganin yanayin da ta shiga yace "Tell me, baki yi karatu bane?" Ta langwabar da kanta a hankali tace "Wallahi nayi" Yace "Kinga it's ur final semester Mayraah, u need to add in more effort... Idan akwai abinda yake damunki ki gaya min yanzu, feel free to tell me Baby" Cikin sanyin murya tace "Pls sir baza a iya barin bikin sai bayan na gama final exams ba?" Shiru yayi yana kallonta for almost 40 seconds, jin yayi shiru ta ɗan kallesa suka hada ido, kamo hannunta yayi ta janye da sauri tare da turo baki, yace "Me yasa kike son a bar bikin sai bayan final exams?" Tace "So i can concentrateq fully" Yace "No Mayraah, in 2 weeks time za ayi bikinmu in sha Allah, i know u are in ur final semester i will give u the whole time, I won't stress u, zan fi kowa son ganin kin fito da first class dinki, i promise bazan takura ki ba, naga kuma nema kike ki dawo 2.1, your performance is dropping terribly..." Mayraah dai bata dago kanta ba, yace "Idan ma kina son ki zauna gidanku bayan anyi bikin har zuwa sanda za ku gama exams din it's okay by me" Ta kallesa cikin sanyin murya tace "Toh ka bari in zauna gidan namu har in gama exams din" yace "Consider that done" Ta sauke kanta tace "Thank you so much" Ya sakar mata Murmushinsa me kyau underneath his breath yace "My pleasure" Tace "Yaushe za mu yi test dinka?" Yace "Gobe" ta dago da sauri tana kallonsa duk da ta san gobe ne amma tunaninta zae ɗaga masu, yace "I know u can do it Dear" Ta marairaice tace "Plss sir ka bar shi on Wednesday mana" yace "Ae bana zuwa Wednesday, beside i will be going to Abuja that day" tayi shiru tana kallonsa, ya shafa beard dinsa yace "Zan tura maki AOC, and u can forward to ur colleagues a group dinku na WhatsApp, kinga su ma sun ci albarkacinki kenan" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "To mun gode Sir" Yace "Sai bayan biki zaki daina ce min Sir din nan?" Ta ɗan saci kallonsa amma taki cewa komai, Ya lumshe ido ya bude, yace "Kinsan Friday za a kawo lefen ki?" Mayraah da sai da gabanta ya fadi tayi shiru bata basa amsa ba, yace "Yeah, on sunday sae in kaiki ki gaida Mamina with her sisters, they are all around" Mayraah dai ta kasa cewa komai, yace "We have just this week, daga next week bazan samu lokacin kai ki ba" Jin she is quiet yace "You are not saying anything Wife" Ta yi gathering courage tace "Allah ya kai mu lafiya" Ya kalli agogon wrist dinsa yace "It's almost time for isha, zan tafi yanzu"
Washegari Mayraah na zaune class tare da sauran Coursemates dinta ko wanne da sheet of paper a gabansa da question paper, ita dai sai juya pen din hannunta take, she looks so confuse cause ta yi karatu jiya da daddare don sai da ta kai kusan karfe daya kafin ta kwanta, but ji tayi kamar bata bude handout din ba kwata kwata, ga wani ciwon kai da ya sa ta gaba, ta daga kai ta kalli Dr Musharraf dake tsaye hall din wearing a sparkling white shirt, baƙin glasses ne a idonsa so she can't tell where he is looking in particular, ta ɗan bi hall din da kallo, Zaune taga Badiyya tare da clique dinta ta dage sai kwafan na Amira take da gefen ido, tun last week rabonta da school sai yau, bayan kusan minti talatin Mayraah ta mike kawai ta linke takardanta, Hamida sai kallonta take da mamaki ganin fa bata ga tayi rubutu ba, ta dinga mata alamar ta tsaya kar taje tayi submitting amma tuni Mayraah ta nufi inda Dr Musharraf ke tsaye, tana kallonsa tace "Where can i submit sir?" Ya mika mata hannu ta basa takardan, zata juya ta bar wajen as if in a whisper yace "Wait" ta tsaya ba tare da ta kalli fuskarsa ba, bude takardan yayi yaga sunanta kawai ta rubuta sai course da code, ya dinga kallonta kafin ya mayar mata da takardan yace "Go back and sit my friend" Ta amshi takardan ta juya a hankali ta koma, Badiyya dake kallonsu ta wani tabe baki ta ci gaba da satan answers din Amira da gefen ido, kusan sai da duk yan class din suka yi submit suka fita har Badiyya da clique dinta, ajin ya rage few students sai Mayraah dake ta juya pen dinta, zuwa sannan dai ta samu ta tuna solution din second question din kuma ta rubuta, yana cewa 5 minutes more amsan number 1 ya dira kanta in full speed, within that 5 minutes ta amsa question din ta kusa cika fullscap, dama questions hudu ne, to ta samu ta amsa biyu, zuwa sannan su hudu ne kawai a ajin da basu gama ba, ta mike ta tafi ta basa takardan ta ya amsa yana kallonta, ta juya ta fita daga class din ya bi ta da kallo ta cikin glass... Gun Hamida ta nufa, Hamida ta mike ganinta tace "What happened, baki yi karatu bane Mayraah, ina ta daga maki script dina kiyi rubutu amma baki kalla ba" Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tace "Kema kinsan bazan iya ba, but na samu nayi answering guda biyu...." Hamida tace "To Allah ya bamu sa'a gaba daya" Wani Coursemate dinsu Nasir ne ya nufo su, yana kallon Mayraah yace "Dr Mu'azzam na kiranki Mayraah" Mayraah ta ɗan buda ido tace "Ni kuma?" Yace "Eh" Ta kalli Hamida da sauri tace "Me na masa?" Hamida tayi dariya tace "Ke dai kije ki ji, ba munyi test dinsa ba last week, kilan he is impressed with your performance" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi don kaf department din nan babu wanda bai san Dr Mu'azzam da masifarsa ba, kusan kowa shakkarsa yake, babu wanda yake son encounter ya hada su, nan dai ta sa Hamida ta rakata sama zuwa office dinsa, Suna isa bakin kofar Hamida ta kara gaba ta bar ta da sauri kafin ma ya ganta, Mayraah ta sauke ajiyar zuciya gabanta na faduwa tayi knocking kofar office din a hankali, sai da ta sake knocking aka amsa sannan aka mata izinin shiga, ta bude kofar ta shiga ciki ta rufe yana zaune office din tare da wani prof wanda shi ma lecturer dinsu ne, lkci daya gabanta ya tsananta faduwa don tsoron encounter ya hadata da lecturers din department din nan nasu take, ta risina ta gaishesu gaba daya, cikin fada Dr Mu'azzam yace "Ke what is wrong with u this semester with poor performances up and down, wani abu yana damun kanki ne?" Mayraah ta hadiye wani abu da ya tsaya mata da kyar ta girgiza kai tace "No sir" ita ihunsa kadae gigitata yake, Prof Habibu yana kallonta yace "Madam sai a final semester dinki zaki fara wasa? Are you okay? Or do you have any family issues u are handling?" Cikin fada Dr Mu'azzam yace "If not that she is one of our best student i won't waste my time looking for her, to ina ruwanmu idan student ya zama unserious, Prof kasan shi fa student yana da mentality din cewar yana shiga final semester ya ma gama karatun gaba daya, sai yayi ta abinda yaga dama, ke me yake faruwa dake haka? Ko Dr Musharraf ne ke damunki da baki iya maida hankali a karatunki yanzu?" Mayraah ta kasa cewa komai kanta a kasa, Prof ya kalli Dr Mu'azzam a bit surprise yace "Wani Musharraf din?" Dr Mu'azzam yace "Dr Musharraf dai da ka sani, ae fiancee dinsa ce, ba a kai maka IV office