Showing 198001 words to 201000 words out of 249515 words
da yawa" Da mugun mamaki tace "To asibitin sa ne nan din with his principality?" Murmushi Dr Khalil yayi yace "Ba nashi bane, amma he is the second in command, he is a braniac Mayraah yasan aiki sosai, i think his dad is also a Dr in the US yanzu haka, and he is an only son, dole sai kinyi hakuri da shi, ni ina maki sha'awar son ace kin zama staff a nan saboda zaki ga advantage din hakan nan gaba" Daukar jakarta tayi tace "Tun da ka dawo ni zan tafi" Yace "No, i spoke to him now, zai yi interviewing dinki, he is less busy a office yanzu" Sosai gabanta ya fadi tace "But i am not ready Dr" yace "Dole ayi inputing data dinki yau Mayraah, don gobe me asibitin nan will be around saboda next workshop da za mu je, kin ga idan bai baki employment din ba u are not a staff, sannan babu vacancy, and they will be none anytime soon" Mayraah da taji hankalinta ya tashi tace "To amma wani irin interview zai min, i don't have knowledge of how it is..." Dr Khalil ya katse ta yace "Just compose ur self, u are not dull Mayraah, i know u can do it" Bude drawer yayi ya ciro farin takarda ya mika mata yace "Apology letter, in kinje kin gaishesa sai ki basa hakuri da baki respectfully sannan ki mika masa wannan" Sake baki Mayraah tayi tana kallon takardan, can tace "Apology letter for what? Are we in secondary school?" Dr Khalil ya daure fuska yana kallonta, da tasan stress din da yayi going through yau duk a kanta da bazata ci gaba da stressing dinsa ba ita ma, first yaje shawo kan matarsa duk a kanta, secondly ko gamawa da matar tasa bai yi ba sai ga kiran MD babu abinda ya mance bai gaya masa a waya ba, yana shigowa asibitin yanzu yaje ya samu MD after almost 30 minutes of persuasion ya shawo kansa har ya yarda yayi mata interview din yau and she is here trying to complicate issues the more, Mayraah ta amshi takardan, on a serious note Dr Khalil yace "Mayraah ko zaginki yayi kice kin gode, kuma kar ki kuskura ki fito office din duk ma me zai ce maki" Ta ɗan yi murmushi kawai ta juya ta fita, ya zauna ya sauke ajiyar zuciya a yanda ya lura ma ta fi MD din girman kai amma bata sani ba, Mayraah na tafiya sama ta tsaya kofar office din MD din tana kallon sunan dake manne jikin kofar daga sama.
[7/25, 7:04 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah tayi knocking din office din a hankali ta koma gefe ta tsaya, jin ba a amsa ba bayan some seconds ta sake knocking, Sai da tayi knocking sau uku sannan taji ya bada izinin shigowa, ta bude kofar a hankali suna hada ido tun kan ta saka kafarta cikin office din yayi saurin cewa "I am occupied Madam, leave and come back tomorrow 8am prompt" yana fadin haka ya ci gaba da sipping juice dake hannunsa yana operating laptop, kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa, a karo na farko tun barin ta gida Musharraf ya fado mata a rai, don last day da ta je kai masa project work dinta a office dinsa da yanda yace ta tafi ta dawo 5:30pm prompt ne ya shiga rotating a kanta, ganin bata bar bakin kofar ba ya daga kai ya sake kallonta ya hade rai yace "Are you daft?" Wani tsinannen kallo ta jefa masa, wanda hakan yasa ya ajiye juice din hannunsa ba tare da yasan yayi hakan ba cause he was taken aback by her reaction, tuni ta kulle kofar office din ta bar wajen fuskarta daure, har ta sauka second floor ta kasa kauda tunanin Musharraf da ya mamaye ranta wanda hakan yasa kuzarinta ya ragu, office din Dr Khalil tayi knocking ta shiga bayan yayi mata izini, da mamaki yake kallonta ya mike tsaye yace "What happened again?" Ta kirkiri murmushi tace "No, na samesa yana cin abinci ne, shine yace in bari gobe karfe takwas na safe idan Allah ya kai mu" Dr Khalil yace "Are you sure Mayraah?" Ta gyada masa kai tace "Da gaske fa, yace gobe da safe in sha Allah" Dr Khalil ya koma ya zauna yace "Ohk" Daukar handbag dinta tayi tana kallonsa tace "Na gaji, ina son in tafi" Yace "Toh ki gaida su Ummi, inna dai na gidan Baffan su Mimi, cousin din Zainab zata yi aure next week" Tayi murmushi tace "Allah sarki, pls idan twins sun tashi kace masu sai mun sake haduwa i will miss them" Yace "To zan gaya masu" juyawa tayi ta fita daga office din ta sauka downstairs, sallama tayi da Nurse Hafsat sannan ta fita haraban asibitin, zaunawa tayi karkashin wani bishiya ta ciro wayarta a jaka, a hankali ta fara dialing number Musharraf da ake samunsa not his private line dake kulle, tafi minti uku tana kallon numbers din ta runtse ido kawai ta goge ta maida wayar cikin jakarta ta mike walking slowly ta fita daga asibitin, tana taran adaidaita sahu ta gaya masa inda zai kai ta sannan ta shiga, after many minutes ride yayi parking inda tace ya tsaya sannan tace "Don Allah ka jira ni zan amshi sako ne sai ka kai ni wani wajen daban" Yace "Toh" Karasawa tayi ta shiga shagon Aminu, gaisawa suka yi da fara'a yace "Ya makarantar Hajiya" Tace "Alhamdulillah ya kasuwa?" Yace "Lafiya lau wallahi, kin ga na kwana biyu ma ban shiga Sulejan ba ni" Tace "Allah sarki, don Allah SIM card nake son zan kara siya" Yace "Toh wani network kenan?" Tace "Ko wanne, sai ka hada min da katin dubu daya" Dauko mata yayi ta ciro dubu biyar a jakanta ta basa tace "Ka saka katin waya da sauran canjin" Godiya ya mata sosai bayan ya amsa, tayi murmushi ta yi masa sallama ta koma cikin adaidaita sahun dake jiranta. Mayraah na sauka kofar gidan Ummi bayan ta ba mai adaidaita sahun kudinsa ta shiga gidan, Ahmad na zaune compound making a phone call, kawai ta ɗan masa murmushi not wanting to distract him ya bi ta da ido har ta shiga gidan, karime kadai ce a gidan bayan sun gaisa karime tace "Ai ko awa daya yan gidan basu yi da fita ba in gaya maki, kinsan aminiyar Hajiya ke aurar da er ta, to can Hajiya ta tafi da Mimi, gobe asabar ne daurin aure ranan lahadi kuma ayi taron biki, ina jin ranan lahadin za su dawo, Hassan da Hussaini kuma sun je gidan baffansu tare da Inna tun jiya, Baffan zai aurar da er sa satin nan da za mu shiga" Mayraah dake zaune parlon tana danna wayarta tace "Allah sarki" Karime tace "Ai gobe baki da aiki ko?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ta ɗan yi murmushi, Karime tace "Sai mu je gidan bikin kawai tare, Hajiya ta ce in je gobe, ina jin bata san za ki dawo ba tunda mun san can Suleja kike weekend dinki" Mayraah tace "Zan je aiki goben in sha Allah" ta fada haka ne ba don tana da intention din zuwa asibitin gobe ba sai don kawai bata son bin karime gidan bikin, Karime tace "Allah sarki, to bari in zubo maki abinci" Daga haka ta mike ta shiga kitchen Mayraah ta bi ta da kallo, Karime zata yi shekara kusan arba'in da biyu, kuma ta fi shekara bakwai tare da Ummi sai dai taje ganin yaranta da iyayenta a kauyensu ta dawo don ta zama kamar wata er uwar Ummi, Karime na kawo mata abincin ta ajiye Mayraah tace "Nagode sosai" Karime tace "Kin ga da daddare ba sai mun yi girki ba, tun da akwai burodi kawai soya kwai za mu yi mu sha shayi don shi yallabai dama shayi yake sha da daddare" Mayraah dai ta ɗan yi murmushi ta dau plate din abincin ta fara ci, sama sama take biye karime da ta cikata da hira a parlon don duk ta kagu ta wuce daki ta saka sabon sim card da ta siyo, kiran la'asar ya sa Mayraah ta mike ta tafi kai plate din kitchen ta wanke sannan ta dawo ta tarar har Karime ta shiga daki ita ma zata yi sallah, Mayraah ta dau jakanta ta wuce nata dakin da take sauka a gidan, alwala tayi, bayan ta idar da sallah ta dau sabon sim din ta saka a wayarta, ganin ya hau ta loda katin, dialing din number Musharraf tayi da sabon Sim card din, tana ji ya fara ring sai da gabanta ya fadi, ta daura goshinta saman knees dinta har sannan zuciyarta na bugawa tana jiran ya daga, sai da ya kusa katsewa taji ya daga, shiru tayi shi ma yayi shiru bai ce komai ba, after few seconds taji ya katse wayar, murmushi tayi don tasan dama bazai ce komai ba in dai bai san number ba haka yake, sake dialing number tayi duk da a ranta tasan ba lallai ya sake dagawa ba ai kam har ya gama ringing bai daga ba, kawai ta kashe sim card din cikin wayar ta ajiye wayar ta kwanta. Mama Ladi ce zaune gefen Hajja dake jingine da bango tana zaune kan shimfidar da aka mata a parlonta wajen karfe biyar na yamma, Mama Ladi na washe baki tace "Alhamdulillah jiki ai ya fara kyau, gashi har kin kusa shanye shayin, tun jiya fargabana ta ina zan fara jinyarki idan shanyewar barin jiki ya sameki, wallahi hankalina yayi matukar tashi bazan boye ma kowa ba" Ammi dai na zaune parlon tana kallonsu, Aunty Mariya kuma na kitchen tana dama ma Hajja kunu, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Ke fa nace maki ki tashi ki tafi gida kar Mamuda ya ga rashin hankalinmu ya sake tabbatar da mu kananun mutane ne, tun shekaranjiya fa kike nan ko mutuwa aka yi ya ci ace kin koma dakinki barin ma ga Hajja har ta fara tashi zaune ga kuma shayi tana sha, nima zuwa anjima in sha Allahu zan taho sai Mariya ta zauna tayi jinyar Hajjan da me laulayin can, don gaskiya bazan iya jure ƙarnin aman da Badiyyah take kirba mana ba, in tayi aman ƙarnin har nan malam, to a kan me, ɗa ba ɗan sunna ba ta dinga cutar mu da ƙarni, bazan iya ba wallahi" A karo na farko Hajja ta bude baki a hankali tana girgiza kai tace "A fitar min da ita daga gidana dama jira nake in gama shan shayin inyi magana, a tafi da ita duk inda za aje da ita, in ko ba haka ba in bi Mariya mu tafi kaduna ta sauke ni gidan yahanasu" Tana magana ne hawaye na sauka idonta, Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "A fita da ita a kai ta ina Hajja? Ko dai baki gane wa nake nufi ba, Badiyyah fa nake magana, Badiyya guda fa taki" Hajja na gyada kai wani bakin ciki na kara tokare mata makogwaro tace "Ita Ladi, bazata kwanar min a gida yau ba ta tafi duk inda za ta, ni ma kaduna zan tafi gun yahanasu" Ammi tayi kasa da murya tace "To ina za ta Hajja? Da dai kin yi...." Dakatar da ita Hajja tayi cikin rawan murya tace "Wallahi tallahi bazan kwana da Badiyyah gidan nan ba yau kun ji har na rantse, dama ina ta addu'ar in samu karfin yin magana tun jiya Allah bai bani iko ba sai yanzu, to Allah ya isa tsakanina da ita, Allah ya isa, Allah ya isa wannan abun gorin da ta ja min har karshen rayuwata, duk soyayyar da na nuna mata saboda tausayin maraicinta duk jan ta jiki da nayi don kawar mata da maraici a rayuwarta sakayyar da Badiyyah zata min kenan, da haka zata saka min? ta cuce ni, ta ja min abun kunya, ta ja min abun magana, ta ja min abin gorin da har in koma ga mahaliccina...." Kasa ci gaba tayi saboda tarin da ta fara kamar zata shide tana gwalo ido, Mama Ladi tayi saurin mikewa tana kallon Ammi tace "Kin ga tun da tace a fitar mata da ita daga gidan nan bazata kwanar mata ba to gaskiya ki shiga ki temaka mata ta hada kayanta a akwati a dora ta motar Bichi ta tafi wajen dangin ubanta, haka kawai bakin cikinta bazai kashe min yayata ba in shiga uku, maza a fita da ita ba ruwana, ko kuma ni in je in hado mata tsummokaran nata da kaina" Hajja na kuka tana tari tace "Ku fita da ita ko ni in tafi, ku fitar min da ita nace" Mama Ladi ta nufi dakin Badiyyah da gudu tana cewa "Daga wannan tarin fa wani ake zare ran, wallahi ba ruwana Badiyyah ta zo ta tafi kar in rasa yayata" kwance Mama Ladi ta tarar da Badiyyah shame shame a kasa kamar mara galihu, ko bin ta kanta bata yi ba tana toshe hanci ta bude inda kayanta suke ta dinga kwaso su tana zubawa cikin akwatin da ta bude, Badiyyah sai bin ta take da ido tana sauke numfashi a hankali, tun shekaranjiya babu me bi ta kanta a gidan sai Ammi dake ajiye mata kunu a bakin kofar dakinta tayi tafiyarta, ji take kamar mutuwa kawai zata yi, komai ya dena mata dadi a rayuwar, Mama Ladi na gama cusa kayan cikin akwati tana kallonta tace "Tashi ki fita a samar maki adaidaita sahu ki tafi can gun dangin ubanki su yi jinya, mu ba yan iska bane duk ta sunna aka same mu, don haka baza mu yi jinyan cikin shege ba Allah ya tambayemu" Badiyyah ta mike zaune da kyar tashin hankali karara a kan jemammen fuskarta tace "Mama Ladi wallahi basa so na, ko a baya ba jin dadin zaman can garin nake ba don Allah ki rufa min asiri Mama Ladi" Mama Ladi bata sake sauraronta ba ta fito parlor da akwatinta, Ammi na tsaye tana kallon Hajja dake kuka hade da tari ta dage a fitar mata da Badiyyah daga gidan, Mama Ladi tace "To ni dai bani da karfin dagota Ammi ki je ki fito da ita ga akwatin nata na fito da shi, ko shatar adaidaita sahu ne sai a dauko mu biyasa ya kai ta har Bichi" Sai ga Badiyyah ta shigo parlon da rarrafe ta fashe da kuka tace "Don girman Allah Hajja ki ce ma Mama Ladi a bar ni nan bazan iya zaman Bichi ba basa sona ke ma kin sani" Wani rikicewa Hajja tayi ganin Badiyyah ta dinga tari da karfi tana nuna alamar a fitar mata da ita, Dole haka Ammi ta fita da Badiyyah compound don Hajja ta dena ganinta, Mama Ladi ta dauki akwatin Badiyyah ta bi su da shi, Badiyyah ta rike kafar Ammi tana kuka sosai tace "Don Allah Ammi kema kinsan bani da inda zan je, basa sona a Bichi, don Allah ku yi min rai Ammi" Ammi dai na tsaye ta kasa cewa komai, Mama Ladi na ajiye masu akwatin ta koma gun er uwarta Hajja tace "An fitar da ita yanzu za a daura ta a mota ya kai ta Bichin don Allah ki kwantar da hankalinki yaya" Hajja dake ta sauke numfashi da kyar Aunty Mariya na durkushe gabanta ta rike hannayenta biyu, cikin sarkewar murya tace "Mariya ki kai ni wajen yahanasu kawai" Aunty Mariya ta kwantar da murya tace "Hajja yamma yayi mu kama hanyar kaduna yanzu, ki yi hakuri gobe da sassafe sai mu tafi in Allah ya yarda" Mama Ladi ta zauna gefenta tace "Tafiyar yamma babu dadi yaya, gobe da asuba har ni sai mu je Kadunan in hankalinki zai kwanta da haka, idan ya so idan nayi kwana biyu sai in bar ki tare da yahanasun ni in dawo" Kai kawai Hajja ke gyada masu tana sauke numfashi, Ammi dai an bar ta tsaye da Badiyyah da akwatinta a tsakar gida ta rasa yanda zata yi, Aunty Mariya ta kira da wayarta dake hannunta, ba a dau lokaci ba Aunty Mariya ta fito tsakar gidan, ko kallon Badiyyah dake kwance ƙasan compound din tana rusa kuka bata yi ba ta karasa gun Ammi da ta koma gefe tana jiranta, Ammi na kallon Aunty Mariya cike da damuwa tace "Yanzu ya za mu yi Mariya?" Aunty Mariya tace "Ya za mu yi me Ammi?" Ammi tace "To ina za a kai yarinyar nan yanzu?" A takaice Aunty Mariya tace "Aa, ba dangin ubanta na Bichi ba, ko kin manta ne Ammi" nan da nan hawaye ya cika idon Ammi tace "Kar ki manta Mariya yau ace Rukayya na da rai...." Kasa ci gaba tayi saboda kukan da ya taho mata, Aunty Mariya dai tayi shiru nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, cikin rawan murya Ammi tace "Hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, ko mun ki ko mun so Badiyyah ta mu ce, er uwar mu ta jini ce ta haifeta gashi bata doron kasa yau ga halin da er ta ke ciki, kuma Allah ya gani mun yi bakin kokarinmu kan Badiyyah, i tried my best Mariya, my children tried their best also, ke za a ce ba a garin kike ba, Amma Allah yasan kokarin da nayi kan Badiyyah" kasa ci gaba Ammi tayi, Aunty Mariya ta goge hawayen idonta tace "Yanzu ya za mu yi yaya?" Ammi na hawaye tace "Wallahi ban sani ba, kin ga tace bata son ganinta ni kuma yanzu ba ɗa bane a gidana, i don't have that power anymore, ban san ko Mahmud zai amince Badiyyah ta koma can ba" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni kuma kin san family house nake, bazan dau Badiyyah da ciki in fara kai ta gidana ba ya zame min abun gori gun facalolina da dangin mijina" Ammi na gyada kai tace "Haka ne, kawai yanzu daukarta