Showing 150001 words to 153000 words out of 249515 words
kan a maida ta gida sai Hajiya Amina ta kwana da Mayraah ba amma taki, Hajiya Amina na kallon Abba tace "To kawai ka tafi bar Alhaji" Da sauri Mama Ladi tace "Aa, bi shi ku tafi, ni kadai raina na isa in dubata, abinda duk 'ya yan mijina da jikoki haka na dinga wahala da su in aka kwantar da su a asibiti gashi gantalallun ko bin ta kaina basa yi yanzu, ai in da sabo ni dai na saba da jinyan jama'a a asibiti, kawai ku tafi kuyi baccinku ni ina nan" Babu yanda suka iya haka nan suka tafi gida leaving Musharraf behind duk da Abba yace masa ya tafi gida shi ma it's already late, Mama Ladi na kallon Musharraf bayan tafiyarsu Abba tace "To kai kuma bawan Allah ai mun gode kuma haka, ka kama hanya kayi tafiyarka Allah ya saka da Alkhairi, ko da wani abun da kake so a baka ne da ka kasa ka tsare ka ki tafiya?" Musharraf dake kallonta yayi mata sallama ya juya ya fita daga ward din, tace "Haba, kai ba saninka aka yi ba ba komai ba, daga kawo yarinya asibiti kawai sai ka makale cikin mu kaki tafiya, in ma wani abu kake so a baka ai da tun wuri kayi ma Mamudan magana ko er dubu biyar ce ya sallameka da shi" reception Musharraf ya koma ya zauna don bai jin zai iya tafiya gida, tun da Musharraf ya fita daga dakin Mama Ladi ta dau bargon da Hajiya Amina ta kawo ma Mayraah sabo fil da shi a leda ta fiddo shi ta warware ta shimfida kasa ta kwanta, ko minti biyu bata yi da kwanciya ba ta cika dakin da minsharinta. Wajen karfe sha biyu da rabi Mayraah ta farka, sosai kanta yayi mata nauyi ta kasa bude idonta gaba daya, ta mike zaune da kyar tana bin dakin da kallo, amma ta kasa sunkuyawa ta ga wanda ke minshari a kasa tsabar ciwon kai, a hankali aka bude kofar dakin Musharraf ya tsaya bakin kofar yana kallon Mama Ladi dake ta baccinta kamar a dakinta take, ya karaso cikin ward din bayan ya kulle kofar a hankali, ya nufi gadon yana kallon Mayraah da damuwa yace "Baby kin tashi? How are you feeling now?" Ta kasa cewa komai, bude flask yayi ya fara hada mata shayi me kauri sannan ya mika mata yace "Zaki iya rikewa?" Ta amshi shayin ya zauna plastic chair dake kusa da wajen yana kallonta, a hankali ta dinga shan shayin, ta sha me ɗan yawa ta mayar masa da sauran ya ajiye, ya dau magungunan da Dr din ya bari a dakin da za a bata idan ta farka, ya budesu ya bata ta amsa ta sha da bottle water, ganin tana disconnecting drip din daga hannunta yace "Me yasa kike cirewa?" Cike da karfin hali tace "Zan yi sallah" Yace "Ohk" Tashi yayi ya cire mata da kansa, sannan ya kamo hannunta ta sauka daga kan gadon a hankali, duk wannan abun Mama Ladi na ta buga minsharinta kamar kato na bacci, Mayraah na idar da sallah Musharraf ya maida mata ruwan, yana kallonta yayi kasa da murya yace "I am sorry Mayraah, i am sorry for everything" Ita dai bata ce masa komai ba, a hankali yace "You know i love u so much" Komawa tayi ta kwanta ta kulle idonta, bai kuma ce mata komai ba sai kallonta yake, har yaga alamar ta koma bacci. Musharraf bai bar dakin ba sai da aka kira sallan Asuba, kuma har sannan Mama Ladi bata farka ba, ya kamo hannun Mayraah dake bacci yayi pecking dinsa sannan ya fita daga ward din ya kulle kofar. Washegari da safe karfe bakwai Mama Ladi na zaune kan Bargon da ta kwana ta hada shayinta cikin Cup, Mayraah dai na kwance idonta rufe duk da ba bacci take ba, Bude kofar ward din aka yi Hajiya Amina ta shigo da sallama da basket din breakfast, Mama Ladi ta amsa sallaman, Hajiya Amina ta gaisheta da ladabi, Mama Ladi tace "Lafiya lau" Hajiya Amina tace "Ya kwanan takura" Mama Ladi tace "Wani kwana er nan? Ni ina naga ta bacci an bar min amanar yarinya, ke dai kawai ayi sha'ani, ita kam dai ta sha baccinta" Hajiya Amina tace "Allah sarki, dama gida zaki tafi yanzu ki samu kiyi wanka ki karya sai ki kwanta kiyi baccin ki huta" Mama Ladi tace "Aa ni ba sai na wani je gida ba, abinda in da sabo na saba, sae in iya kai wa wani daren a haka ma" Hajiya Amina tace "Toh bari in zuba maki abincin kawai ki karya" Mama Ladi tace "Yauwa to, dama yunwa nake ji" Karfe takwas Musharraf ya shigo ward din har yaje gida yayi wanka ya dawo, Mama Ladi na kallonsa tace "Yau naga bala'i sake dawowa kayi ɗan nan? Ba nace ka tafi mun gode ba" Hajiya Amina tace "Mama naji fa Alhaji yace malamin makarantarsu ne, shi ne ma ya kawota asibitin" Mama Ladi tace "Ayyoo to kai ba sai kayi bayani ba, wallahi na zata irin gayun nan ne masu zaman banza, naga sai sintiri yake kamar yana son a biyasa abinda yayi, ashe malami ne sannu kaji yaro" Musharraf dai murmushi kawai yake ya karaso, tana kallonsa tace "Ai tun da ka tafi ka bar mu wajen karfe sha biyun nan har yanzu a haka nake, hana rantsuwa dai na ɗan gyangyada" Musharraf ya dinga kallonta babu ko kiftawa.
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*
[7/13, 6:11 PM] Khaleesat Haiydar💖: Karfe goma saura Abba ya zo asibitin duba Mayraah, tana zaune kan gado da fruits a gabanta an sa mata wani drip din don wancan ya kare, Ta daga kai tana kallon Abba dake tambayarta ya jikinta tace "Da sauki Abba" Yace "Are you sure?" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya kara afuwa daughter" Mama Ladi tace "Yo jiya ina ma ta samu sararin shan kankana da su lemo, jiki ai yayi sauki Mamuda" Abba yace "Gaskiya ne, yanzu zaki tashi in maida ke gida kema kiyi wanka ki huta kiyi bacci Mama, ita kuma Hajiya Amina ta zauna nan da ita zuwa anjima...." Mama Ladi ta katse sa tace "Aa ai ba cewa nayi na gaji da jinyan ba Mamuda, ita Aminar ta koma kawai ko girki ne sai tayi ta kawo mana" Abba yace "Aa da dai mun tafi gida kin huta Mama" Mama Ladi tace "Na fa ce kar ku damu da wai ban yi bacci ba, na saba da irin wannan jinya a asibiti, idan Aminan ta kawo abincin anjima muka ci sai a maida ni gida inyi wanka, in ba a sallameta ba har zuwa dare sai a dawo dani nan wajenta" Abba yace "Toh shkkn" Hajiya Amina na kallon Mayraah tace "Allah ya kara lafiya dear, anjima zan dawo in sha Allah" Kai kawai Mayraah ta gyada mata, Hajiya Amina tayi ma Mama Ladi sallama sannan suka fita da Abba, Mama Ladi ta jawo sauran ƙwan da ke cikin warmer da Mayraah ta ki ci ta fara ci. Mayraah na kwance wajen karfe sha biyu da rabi ta kalli Mama Ladi dake shan lemon ɓawo tace "Mama, yaya ya zo ina bacci ne?" Mama Ladi tace "Waye kuma yaya? Mashir ko Usman?" Mayraah ta gyada mata kai, Mama Ladi tace "Yanzu lemon nan da nake sha nazarin da nake kenan a raina wallahi, ai baza su ce basu ji baki da lafiya ba kina asibiti tun da tun a jiyan da ake ta neman inda kika tafi har Mashir sai da Mamuda ya kira aji ko kin je gidansa Mashir yace a'a baki je ba, ai idan ya damu da sai ya zo gidan a daren da yaji ba a ganki ba amma wallahi bamu ga ko keyarsa ba, tun da garin Allah ya waye nake zuba ido in ga shi ko Usman sun zo duba ki shiru har yanzu ana neman karfe sha biyu, babu shi, babu Usuman din balle uwa uba kafurar nan don ni dai na fara tunanin anya Ammi musulunci take kuwa, kai kamar fa bata cikinmu yanzu gaskiya, ke ki ga fa sai wani bare can da kawai taimakonki yayi ya kawo ki asibiti ke ta sintirin shigowa duba mu kamar wasu marasu galihun dangi, jiya ma sai da na kore yaron wajen karfe sha biyun dare sannan ya tafi, kina ganin yau da sassafe kuma sai gashi, ga yaron kyakkyawa da shi kamar bafillatani ne ina ji, to daga shi sai Mamuda da sabuwar amaryarsa kadai ke zuwa mana, ma'aikatan asibitin ba sai suyi tunanin bamu da dangi bane" Ko rufe baki Mama Ladi bata yi ba aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, Musharraf ne ya shigo da sallama with basket of food, Mama Ladi ta gyara zama ta ajiye bawon lemon hannunta tana ɗan murmushi tace "Sannu da zuwa" Ya ajiye abincin ya gaisheta, ta amsa da fara'a tace "To wai ya ma sunanka ne?" Yace "Sunana Musharraf" Mama Ladi ta gwalo ido tace "Musharri? Sharri fa kace?" Mayraah ta kauda kai ta ɗan yi murmushi, Musharraf ya sunkuyar da kansa yace "Abdallah ake kirana" Mama Ladi tace "Ayyo, har hankalina ya tashi, to sannu da zuwa Audullahi, naji dadin yanda ka nuna ka damu da jikata daga taimako, Allah ya maka albarka" Ya ɗan yi murmushi yace "Ameen" Mama Ladi tace "Dama ina ta jiran wanda zai zo nima in ɗan samu in fita in ɗan motsa kafafuwana, tun jiya mutum na waje daya kamar gunki kada jini ya daskare min" Daga haka ta mike tana yafa gyalanta ta nufi kofa, Musharraf ya nufi Mayraah bayan ta fita yana kallonta yace "How are you feeling now dear?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ba inda kike jin ciwo?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "Mami ta bada abinci a kawo maki, zata zo dubaki nace mata ba sai ta zo ba" Mayraah ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Nagode" Hannu zai kai goshinta ta kauce da sauri, yayi kasa da murya yace "I just want to feel ur temperature" A takaice tace "Don't worry, i felt it my self minutes ago" Bai sake cewa komai ba ya zauna kan kujera, yace "Ammi bata nan ne? Naga ban kanta ba har yanzu" Mayraah ta gyada masa kai kawai, sai kuma ta kwanta ta juya masa baya don bata son zancen, a hankali Musharraf yace "Thursday za ku yi Internal Defense, but u need not to worry about that, external din ma kar ki damu i will sort it out, kina bukatan hutu sosai yanzu" Murya can kasa Mayraah tace "Thank you" shi dai kallonta kawai yake don har a lokacin bata juyo ba, ko minti biyar ba ayi da fitan Mama Ladi ba sai ga ta ta dawo tace "Toh Alhamdulillah na zaga har na dawo" Musharraf yace "To sannu da dawowa Mama" Mama Ladi tace "To amma na fa ji ana ta kiran sallah a masallaci" Mikewa yayi yace "Eh yanzu zan tafi" Tace "To maza ka tafi" yana fita Mama Ladi ta hau bude abincin da ya kawo, buda baki tayi tace "Kai kai kai, wannan abinci haka kamar a gidan sarauta" sai kuma tayi murmushi ta kalli Mayraah tace "Za ki ci ne?" Mayraah tace "Na koshi" Mama Ladi bata sake bin ta kanta ba ta dau plate ta fara zuba abincin ta tula nama ta koma ta zauna tana ci. Throughout ranan daga Mama Ladi, Hajiya Amina sai Musharraf idan ya shigo ne kadai ke tare da Mayraah a asibitin, wajen karfe uku na yamma 3 of her lecturers tare da Dr Asmau suka zo dubata a asibitin da ledan fruits, Mama Ladi sai sa masu albarka take bayan Mayraah ta sanar mata malaman makarantansu ne har suka tafi, Sai a sannan Mayraah ta koma ta kwanta da tunani iri iri cike fal ranta, she felt so relieved da ta tuna bata da wani issue na project da defense a yanzu kuma, she will just assume ta gama kawai. karfe uku da rabi Hajiya Amina ta koma gida don yin girkin dare ta kawo masu, sai bayan da suka fita Mama Ladi ta rike kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah wadaran Ammi, Allah wadaran kafirin zuciya irin nata, wato har 'ya yan ma ta hanasu zuwa kenan, magana na ta ci na ba daman inyi gaban wannan baiwar Allah dake ta hidima da mu a asibitin nan taje kawai ta raina mu, Kaiii a gaskiya Mamuda bai yi dacen uwar gida ba bazan ci amana in ki fada ba gaskiya" Ita dai Mayraah na kwance bata ce komai ba banda ɗan murmushi da tayi, Mama Ladi ta ciro wayarta da aka nannade da rubber band ta mika ma Mayraah tace "Kira min Mashir din" Mayraah ta kalleta, a hankali tace "Me za ki ce masa Mama, kawai ki..." Katseta Mama Ladi tayi a fusace tace "Ina ruwanki? Ke dai ba kawai cewa nayi ki kira min shi ba ki miko min" Mayraah ta amshi wayar tayi dialing number Maheer ta mika ma Mama Ladi da ta danna handsfree, sai da ya kusa katsewa ya daga, Mama Ladi bata amsa sallamansa ba tace "Mashir wai baka da labarin an kwantar da kanwarka tun shekaranjiya yau kwananta uku kenan a asibiti?" Maheer ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Ai bana gari" Mama Ladi tace "Baka gari? To shi Usuman shi ma baya gari da wannan farin yaron da ya dawo jiya?" Maheer yace "Gaskiya ban sani ba" Mama Ladi tace "Toh ko da baka gari ai sai ka kira kace a baka Meran kaji jikinta, yarinyar da aka kawo asibiti bata numfashi sai da kyar yau ta fara numfashi amma duk cikin kai da yan uwanka babu wanda ya zo dubata?" a hankali Maheer yace "Aiki naje ne Mama" Mama Ladi tace "To ba laifi" Daga haka ta ba Mayraah wayarta tace "Kashe min" Mayraah ta amsa ta katse sannan ta mika mata. Karfe shidda saura likitan ya shigo daki zai sallami Mayraah, Mama Ladi tace "Kar fa mu koma gida jikin ya kara rikicewa dafta, ni dai ina ga gwara a bari a ga zuwa gobe tukun" Likitan na murmushi yace "Jinin nata ya dawo normal Baaba, kawai magunguna zata ci gaba da sha, da kuma wasu cimar da zata maida hankali gun ci yanzu, duk na gaya ma Abbanta" Mama Ladi tace "Toh shikenan, amma ai uban bai san za ayi sallama ba yau, ga abinci can anje gida za a kawo mana kuma" Likitan yace "Bamu jima da gama waya da shi ba, yace zai zo bayan magariba ya tafi da ku gida" Mama Ladi tace "Atoh shikenan ba damuwa, Allah maka albarka" Likitan yace "Ameen Baaba" Ya maida dubansa kan Mayraah yace "Allah ya kara afuwa yan mata" A hankali tace "Ameen Nagode" Juyawa yayi ya fita, Mama Ladi tace "To kuma idan muka tafi wannan malamin ya kara kawo abinci fa, kar fa asa yaje yayi asaran abinci da sun bari can bayan isha'i a sallame mu" Mayraah dai kallon Mama Ladi kawai take, don tayi nisa tunanin da take bata ma san me Mama Ladi take cewa ba, Bude kofar aka yi Musharraf ya shigo Mama ladi tace "Kaga ɗan halaq yanzu nake maganarka nace kar kuma ka zo ka tarar bama nan, don za a sallame mu inji likita" Musharraf yayi murmushi ya gaisheta yace "Ai ina asibitin dama ban tafi ba" Mama Ladi tace "Allah sarki" karasawa yayi ya ajiye ma Mayraah jakarta na makaranta yace "Kin ji sauki sosai ko?" Ta gyada masa kai, yayi kasa da murya yanda Mama Ladi baza taji maganar ba yace "Can i come home in dubaki?" Sai a sannan Mayraah ta daga kai suka hada ido, tayi saurin sauke idonta tace "Gobe in sha Allah" Yace "Toh Allah ya kai mu" Tace "Ameen" Musharraf yace "Dr din yace min Abba is on his way zai kai ku gida yanzu, so ni zan wuce, and i need one favor from u pls Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa, a hankali yace "Unblock me plss" Shiru tayi bata ce komai ba yace "Pls" Ta bude jakar ta ciro wayarta, yana kallonta tayi unblocking digit dinsa, a hankali yace "Saura Whatsapp" nan ma ta shiga tayi unblocking dinsa, ya sakar mata murmushi yace "Thanks" Daga haka ya juya yayi ma Mama Ladi sallama tace "Au har zaka tafi kai ma, toh mun gode Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen ya Allah Mama, Allah ya kara mata lafiya" Mama Ladi tace "Ameen, idan ya so ko gida ne zaka iya zuwa ka dubata kanka tsaye kaji?" Yace "In sha Allahu zan zo gobe" Mama Ladi na washe baki tace "To muna nan muna jiranka" Daga haka ya fita daga ward din, Mama Ladi ta dawo kusa da Mayraah tace "Ke ko dai sonki yake ne, wannan kulan da yake baki kamar ba banza ba wllhi" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa ba haka bane" Mama Ladi ta koma ta zauna tace "To ke me kika sani, mu da muka ga jiya muka ga yau, Allah dai ya kawo sa goben ni zan bincikesa don bana son nuku nuku" Mayraah dai bata ce mata komai ba, ana idar da magrib Abba ya iso ya daukesu duk suka wuce gida. Suna isa gida bayan Abba yayi parking Mayraah ta sauka daga cikin motar, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Jira za mu yi magana Mamuda" Abba yace "To Mama" Mama Ladi ta sauko daga motar tana