Showing 96001 words to 99000 words out of 249515 words
ba tayi shiru tana sauraronsa, yace "How are you feeling now?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin ci abinci?" Tace "Na ci" yace "Ohk, good night" shiru tayi kamar bazata ta ce masa komai ba, sae kuma a hankali tace "Zaka zo school gobe?" Yace "Yau da kika sa na zo, kin zo?" Ta marairaice tace "Ae don bni da lafiya ne, amma gobe in sha Allah zan je" Yace "Allah ya kai mu, take care of ur self" a hankali tace "Sure" Daga haka ya katse wayar ta dinga kallon screen din. Washegari kafin bakwai da rabi Mayraah ta shirya ta fice daga gidan without anybody noticing her ban da Musa mai gadi, don bata ma ga alamar masu gidan sun tashi ba, ko shayin bata tsaya ta sha ba yau, ta isa har inda zata samu adaidaita sahun da zai kai ta makaranta, takwas dot ta shiga department dinsu, ita da Hamidah da wata Coursemate dinsu Amina suna zaune class don karfe takwas din suke da lectures, amma gashi har takwas da rabi lecturer din bai shigo ba, Hamidah na kallon Mayraah tace "Wai Badiyyah bata nan ne, na ga ta daina zuwa school long ago, ga exam is fast approaching" Mayraah tace "Ni ma ban sani ba kam, kilan tana Bichi, but nasan zata dawo tayi exams ai" Shigowan lecturer din ya sa duk aka nutsu a class din, Mayraah ta bude jakarta ta fiddo littafinta da pen, paying attention to their lecturer... Karfe goma da rabi suka fito daga lecture hall din, ta fiddo wayarta a jaka ta ga miss calls har shidda, uku na Maheer, biyu na Usman sai na Dr Musharraf guda daya, ta dinga kallon calls din, kawai tayi dialing na Dr Musharraf, yana fara ring ya daga ta gaishesa a hankali, ya amsa yace "Are you done with the lectures?" Ta zaro ido tace "How did u know i am in school?" Yace "Kawai na ji kamshin turarenki gaba daya department din" Bata san sanda tayi dariya ba ba tare da ta shirya ba, Hamidah dai na zaune kan gossip chair tana kallonta, ko Mayraah bata gaya mata ba tasan tana cikin damuwa cause it's obvious a fuskarta, Musharraf yayi shiru yana sauraron dariyan nata, can a hankali yace "Ina jiran ki a office now" tace "Sir zan ɗan yi karatu ne fa yanzu" Yace "Yauwa dama ina son in tambayeki, kin canza project supervisor ne ban sani ba?" Zaro ido tayi don ita ta ma mance da batun wani project, a hankali tace "Aa ban canza ba" Yace "Ok na zata kin canza, don naga mate dinki are almost done with theirs ke kuma har yanzu kina chapter 1" Da sauri tace "Aa wllh Chapter 3 ne" Yayi murmushi yace "Uhm i see" Ta marairaice tace "Amma sir ban zo da system dina ba" Yace "In kin gama karatun ina jiranki" Daga haka ya katse wayar. A hankali Mayraah tayi knocking din kofar office dinsa wajen karfe sha daya, sae da yayi mata izinin shigowa sannan ta bude kofar ta shiga, tun da ta shigo yake kallonta, ita kuwa kallo daya tayi masa ta karasa har inda yake ta sunkuyar da kai ta gaishesa da ladabi, ya mike offering her his seat yace "Ga wannan.... Naga kamar na gabanki basu maki ba" Murmushi tayi ta zauna kujeran dake gabanta a hankali tace "Ina kwana sir" Ya koma ya zauna underneath his breath yace "Lafiya lau.... how was ur night?" Ta kallesa tace "Good" Yace "Hope u slept well?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Ai baka kira ba" Shiru yayi yana kallonta babu ko kiftawa, bai taɓa tunanin bond dinsu zai dawo haka da Mayraah ba, don kafin faruwan issues din nan har tunani yake if she will ever change ko da sun yi aure sai gashi yanzu she talks to him openly, she expresses her feelings unlike before da yake rasa gane kanta komai kunya, komai shiru shiru, Mayraah dai sai kallonsa take jin yayi shiru, ya sakar mata murmushinsa me kyau yace "To an hana in ganki jiya, and i was sad about that" Ta sunkuyar da kanta tace "Ai saboda bani da lafiya ne shi yasa yaya yaki ya bari in fita, kawai... An ban magani na sha shine nayi bacci har yamma" Yace "Am glad u are okay now, no pains" Tace "There is, but ba kamar jiya ba" Yace "To kin sha maganin?" Tace "Ban yi breakfast ba" Da mamaki yace "Why?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Ohk akwai abincin da Mami ta zuba min yana mota, kinsan every day in dai ina gida sai ta min breakfast kafin in fito, ni kuma bana ci, wani lokacin in ba cleaners or security...." Makullin motarsa ya dauko ya mika mata yace "Get the food, I don't even know what she prepared" Mayraah dai kallonsa kawai take, yace "Ko in je in dauko maki" tayi murmushi tace "Sir ni bazan iya cin abinci a school ba" Yace "Aa cewa za ki yi, sir ni bazan iya cin abincin gidanku ba" Mayraah ta zaro ido tace "Wallahi sir ba haka bane" zai yi magana aka yi knocking din office door din, Mayraah zata tashi yace "Is there anything wrong?" Ta girgiza masa kai, yace "To koma ki zauna" Komawa tayi ta zauna ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta, yayi ma me knocking din izinin shigowa office din, daga bakin kofa ta tsaya bayan ta shigo a hankali tace "Good morning sir" Mayraah ta daga kai jin muryar warce ta ji sai dai bata juya ba balle ta kalleta, Dr Musharraf yace "Morning Badiyyah, how are you?" Tana makale jikin kofar tace "I am fine sir" Yace "You can come in" Ta karaso cikin office din tana tafiya kamar me tsoron taka kasa, ta tsaya ɗan nesa da table dinsa tana jujjuya textbook din hannunta tace "Sir dama plss tambaya nake son zanyi akwai abinda ban gane ba... I don't know if u will have the time...." Dr Musharraf yace "Ohk, is it pertaining to my course?" Ta gyada kai da sauri, ɗan murmushi yayi ganin kamar she looks nervous yace "Why are you tensed Badiyyah? You have all right to ask ur lecturer duk abinda baki gane ba, kawo textbook din in ga" Ta karasa har kan table din ta mika masa textbook din da ladabi, tuni fitinannen kamshinta ya baza office din, sai a sannan suka hada ido da Mayraah, Mayraah ta dauke idonta ta ci gaba da danna wayarta, Musharraf ya nuna ma Badiyyah kujeran dake kallon na Mayraah yace "You can sit" a hankali ta zauna edge din kujeran tana wasa da hannunta, sanye take da wani atamfa da dinkin yayi matukar yi mata kyau ya amshi jikinta, ga mayafinta da ta daura saman kai, hannunta kuwa ya sha lalle baƙi da ja da ya kara haska farar fatarta, light make up ne a fuskarta that made her look naturally beautiful, Duk a few seconds Mayraah tayi mata wnn kallon ta side eye, Dr Musharraf ya gama duba abinda Badiyyah tace bata gane ba sannan ya mike ya zagayo ta inda take zaune ya ajiye textbook din a side dinta yace "Now listen, so that u won't get confuse, ba wani abu me wahala bane" Badiyyah da taji kamshin turarensa ya cikata don dab da ita ya duka taji kamar ta sume a inda take a zaune, ko sanin abinda yake cewa ma bata yi ba, nan ya fara kokarin mata explaining din abinda tace bata gane ba, ita dai kallonsa take ko kiftawa babu, bata san haka gayen nan ya hadu ba sai yau da take kallonsa dab dab da ita, his nose, his eyes, his white teeth, his thick eyebrows, cute lips, the way he speaks fluently, and the best of all his cool scent me makalewa a hancin mutum, Subhanallah.... ji tayi kamar ta jawo sa ta rungumesa gam gam, bayaninsa kawai yake amma babu abinda Badiyyah take ji a abinda yake cewa, Mayraah ta mike rike da jakarta, Musharraf ya juya ya kalleta, makullin motarsa ya dauka ya bata yace "Gashi ki dauko stuff din" without looking at him tace "Aa zan yi picking call ne, i will be back" Daga haka ta juya ta nufi kofa ta fice daga office din, Musharraf ya jawo kujeran da ta zauna ya zauna a kai, yana facing din Badiyyah da ta riga ta gama narkewa a wajen, yace "Hope you get where i am heading?" Ta gyada masa kai da sauri, nan ya ci gaba da mata bayanin da bata ganewa ita kuma ta dinga kallonsa babu ko kiftawa.... Mayraah na sauka downstairs kiran Usman ya sake shigowa wayarta, dagawa tayi, a hankali tace "Ina kwana yaya" Yace "Baki ga calls dina bane?" Turo baki tayi tace "Yanzu muka fito lectures ai" yace "Me yasa kika ce in kawo maki jakarki kin san da sassafe za ki fita?" Tace "Ka kawo ne?" Yace "Fito department dinku ki amshi jakarki" Daga haka ya katse wayar, ta saka wayarta cikin jakan hannunta ta tafi inda zata samu Hamidah tace "Hamidah sai gobe in sha Allah" Hamidah tace "Lectures din anjima fa?" Mayraah tace "Kawai ki min attendance pls" Hamidah tace "Toh shikenan sai gobe" Daga haka Mayraah ta juya ta fita daga department din, ba ma kusa da department din nasu yayi parking ba, haka ta karasa har inda ya tsaya da kafa, ta bude motar tana kallonsa tace "Ina kwana" Ya dau jakarta ya mika mata, taki amsa, ta marairaice tace "Yaya don Allah ka ajiye ni gida" Daga sama har kasa yake kallonta yace "Kun gama lectures din ne?" Tace "Kawai na gaji, ina son in kwanta" bata jira me zai ce ba ta shiga motar ta kulle ta jinginar da kanta da kujera without looking at him, bayan few seconds ya tada motar suka bar school din, suna hawa main road ta ɗan juya ta kalli bayan motar jin aroma din abinci dake tashi, ledan wani babban eatry ta gani, can dai ta kallesa tace "I am even hungry" A takaice yace "Me too" Ta ɗan hade rai, sai kuma tace "Naga abinci a back seat fa" Ya jefa mata wani kallo yace "To naki ne?" Shiru tayi tana kallonsa, bata sake ce masa komai ba ta kauda kanta, wayarsa dake ajiye ya fara ring ya daga yace "I am on my way" after some minutes ride sai ga su a gate din wata makaranta wanda ke gaba da na su Mayraah, suna shiga school din bayan sunyi tafiya kadan ya juya yana kallonta yace "Will u wait for me under that tree?" Mayraah ta kallesa tace "No, i will follow u" Ya hade rai yace "Kika san inda zan je?" tace "To me yasa baka son in ganta ne Yaya?" Yace "Ki ga wa?" Ta langwabar da kai tace "Warce zaka kai ma abincin mana" Yace "You are not serious" Er dariya tayi tace "Dama yaya kana da budurwa ashe?" Ya tsuke fuska yace "Yaushe na fara wasa da ke" Ta rufe bakinta bata sake cewa komai ba, suna isa department din yayi parking, wayar da zai yi ma sai da ya sauka daga motar sannan yayi, ita dai Mayraah murmushi kawai take tana bin sa da kallo, baza ta manta ba few months back Ammi ta dage wai ai Usman bai da budurwa, saboda taga shi baya kawo mata waya su gaisa da budurwan yanda Maheer ke yi, shkkn Ammi ta saka a rai ai bashi da kowa, ita kuwa Mayraah ta dage ma Ammi kan cewar yana da ita kawai dai saboda shi introvert ne shi yasa ake ga kamar ba shi da, still dai Ammi bata yarda da Mayraah ba a lokacin, Mayraah wished daga nan wajen Ammi zata je ta kai mata news din nan, tunanin nan yasa lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta jinginar da kanta da kujeran motar tana tunanin wannan sabuwar rayuwar tata, knocking din da taji ana yi ta side dinta ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada, wata ta gani tsaye jikin motar tana mata murmushi, Mayraah ta bude motar tana kallonta, baza su wuce age mates ba da yarinyar, ita ma doguwa ce fara me kyau da ita, Mayraah ta sauko daga cikin motar tana mata murmushi kamar yanda yarinyar ma ke mata, yarinyar tace "Hi Mayraah, i am Maleeha, nice meeting you for the first time" Mayraah tace "Nice meeting you too Maleeha, ya lectures" Maleeha tace "Alhamdulillah, ya naki?" Mayraah tace "Same too" Maleeha tace "I have been longing in hadu dake sai yau Allah ya yi" Mayraah tace "Ai kam, i am happy to meet you" Maleeha tace "Barrister ya gaya min Nursing Science kike yi, ni kuma i am studying Biochem, final year student just as you" Mayraah tace "Maa sha Allah, Allah ya bamu sa'a gaba daya" Lokaci daya Mayraah taji tana son Maleeha har cikin ranta, Usman ya zagayo inda suke ya bude back seat ya ciro ledan da ya kawo ma Maleeha ya mika mata yace "Sai anjima" ta amshi ledan tana kallonsa, ya kalli Mayraah yace "Shiga mota mu tafi" Maleeha tace "Tunda i am done with lectures for today ka bar ta mana plss, so we can stay together, and know our selves better" Usman yace "Not today" Mayraah ta tuna fa yanzu dole gida zai ajiye ta daga ita sai Haseenah, bata san sanda tace "Ya Usman, i will stay... sai anjima zan tafi gida ba yanzu ba" Maleeha tayi murmushi tace "Anjima kawai zan sa drivern mu ya fara ajiyeta before dropping me home" Usman ya zaga ya shiga motarsa ya bar su nan a tsaye, ko minti goma bai yi da tafiya ba sai ga message dinsa ya shigo wayar Mayraah, ta bude message din tana karantawa kamar haka "Watch ur words" ta mayar da wayar cikin jakarta kawai, Mayraah bata yi regretting staying back tare da Maleeha ba cause she enjoyed both her company and her 2 frnds kuma dukkansu sa'aninta ne, bayan sun idar da sallahn asr a masallaci Mayraah ta ciro wayarta a jaka taga miss calls din Dr Musharraf har uku sai na Maheer biyu, wayar a total silence yake don haka bata jin kira sai dai ta ga miss calls kuma she like it that way, zata ajiye wayar sai ga kiran Maheer ya sake shigowa, tayi excusing kanta ta bar jakanta wajen Maleeha sannan ta fita outside of the mosque, a karkashin bishiya ta zauna bayan ta daga kiran, daga daya bangaren Maheer yace "Mimi me yasa baki responding to my calls?" Tace "Muna lectures dazu, yanzu kuma mun idar da sallah ne" Yace "Why did u leave home without waiting for me?" Tace "Saboda ban san sanda zaka tashi ba, kuma ina da lectures karfe takwas" Yace "Me yasa baza ki kira wayata ba, sannan kawai kin fita without taking breakfast" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Zan kawo maki abinci yanzu" Tace "Aa ni na ci abinci yaya" Yace "A ina kika ci abinci?" Tace "Ya Usman ya kawo min" Shiru Maheer yayi, can dai yace "Yaushe?" Tace "Da rana" Yace "When is ur lectures terminating?" Tace "Anjima" Yace "6 kenan?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Eh" Yace "Zan zo in dauke ki" Tace "Ya Usman will pick me" Yace "Ohk, is that so?" Tace "Haka ya ce min" Maheer yace "Ok" Daga haka ya katse wayarsa ta turo baki, Mikewa tayi ta koma cikin masallacin. karfe biyar saura Maleeha ta kira Usman to tell him za su yi dropping Mayraah ba sai ya zo ba, yace "No Maleeha, ina hanya zan zo in dauketa" Maleeha tace "Toh sai ka zo" Suna karkashin bishiya gaban department din nasu Usman ya iso, tuni driver din Maleeha ya zo makarantar amma tana jiran Usman ya fara daukan Mayraah kafin ita ma ta tafi, Maleeha ta raka Mayraah har bakin motar Usman, suka yi sallama, tana kallon Usman tace "I will be going home too, nagode sosai Barrister" Yace "Ohk, a gaida su Umma" Daga haka ya bar department din, bayan sun fita makarantar yana kallon Mayraah ya wani hade rai yace "Hope u didn't talk too much?" Ta kallesa ta wara ido tare da dafe kirjinta tace "Did i use to talk much yaya?" Yace "Look Malama stop being silly.... Maleeha is my frnd, she is just a frnd kar ki yi zaton budurwata ce or anything of such, kanwar abokina ce ita, so mun saba da ita ta dalilin Hafeez, but we are only frnds da ita" Mayraah bata san sanda tayi dariya ba tace "Ae dama na san she is ur frnd, and nima zata zama frnd dina daga yanzu, and beside i never asked for all this explanation" Kallonta kawai yake, ta kallesa suka hada ido ta fashe da dariya, daure fuska yayi nan da nan ta kama kanta, imagine wai yau ya Usman ne ke taking time trying to explain to her what she neva asked for, ita bata ma san ya iya dogon bayani ba sae yau, wani dariya ya kara zuwa mata ba tare da ta shirya ba, shi dae driving dinsa kawai yake. Mayraah na shiga compound bayan Usman ya ajiyeta taga Maheer bai dawo aiki ba, kawai ta karasa ta zauna kan wani kujera da ta gani a parking space don bata jin zata shiga gidan, tana ta zaune a wajen har kusan karfe shidda sai gashi ya dawo, yana parking ya sauko daga motar, ta mike tana kallonsa tace "Sannu da dawowa" Da mamaki yace "Bata bude maki kofar bane yau ma?" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa kawai iska nake sha a nan" Ya mika mata ledan hannunsa ta amsa, sannan ya nufi entrance din gidan tana biye da shi a baya, yana bude kofar parlon hayaki me kama da na turaren wuta da ya turnike ko ina na parlon ya ce masu salamu alaikum, Mayraah na ganin haka ta juya da sauri ta bar entrance din parlon,