Showing 168001 words to 171000 words out of 249515 words
zata an gano inda take ne shine Abba yace ya zo anguwan ya dauketa, ashe kawai bacin rai zai zo ya ji, Dai dai nan Hajiya Amina ta sauko downstairs Maheer ya dinga kallonta babu ko kiftawa, ta karaso parlon tace "Sannu da zuwa Maheer" Ya sunkuyar da kansa yace "Ina wuni" Tace "Lafiya lau" Sai kuma ta kalli Abba tace "Alhaji ya ake ciki, kun sake waya da yan sandan ne?" Abba yace "Sun ce inyi expecting call dinsu ko zuwa nan da magrib, so ina jira in sha Allah" A hankali Hajiya Amina tace "Toh Allah ya sa a dace" Daga haka ta juya ta koma sama, Maheer felt so bad at what he saw, wato dauko matar nan Abba yayi suka dawo nan suka bar Ammi ita daya a can gidan, lokaci daya duk jikinsa yayi sanyi damuwan suka taru suka cunkushe masa a zuciya, ga na Mayraah, ga Haseenah da Abba ke cewa lallai sai ya zauna da ita, ga kuma halin da Amminsa ke ciki, ga Abba na neman kaurace mata, cikin sanyin jiki ya mike yana kallon Abba, Abba yace "Mu je ka duba gidan, i finished it few months back ban dai gaya maku bane kawai" Maheer ya dake yace "Sai na sake dawowa Abba, babu kowa a asibitin, zan koma ne" Abba yace "Ohk, nima ina jiran kiran yan sandan ne idan sun kirani naji yanda ake ciki na dan samu nutsuwa to zan zo asibitin da Hajiya Amina ko zuwa bayan isha ne in sha Allah" Maheer ya ki ce masa komai ya nufi kofa zai fita, can kuma dai ya juyo yayi gathering courage yace "Abba ina ɗan son za mu yi magana in babu damuwa" Abba ya mike yace "Okay" Can babban compound din gidan suka fita, Maheer na kallon Abba yayi kasa da murya cikin ladabi yace "Amma kayi hakuri in maganata zata ɓata maka rai Abba, Abba i don't think Ammi deserves this from you...." Abba ya dakatar da shi yace "Ni nayi deserving abinda ta min? Ni nayi deserving walakanci da rashin mutuncin da ta min wanda gashi yanzu a sanadin selfishness dinta ban san whereabout din Mayraah ba? Maheer let me be frank with you, for now I can't withstand the sight of ur mother billahi, albarkacinku kawai ta ci ban ce mata kar ta sake dawo min gidana ba, tayi failing dina ta yanda bana tunani, assuming the issue is just between us bazan wani damuwa ba, amma ta jefa rayuwar yarinya karama a halaka, ko da ace yanzu Mayraah na gun shi saurayin nata da muke zargi mahaifiyarku bata cuceta ba? Don't forget ta dalilinta Mayraah ta samu guts din zuwa gidan saurayi for days now, duk ita ce silar duk abinda ya samu Mayraah in ma rayuwarta ya lalace to alhaki akan Ammin ku, da ace ita bata juya mata baya ba komin pressure din kakanku da ahalinta Mayraah bazata yi tunanin barin gida, tare da kai muka karanta wasikar da ta bari ai ko? So kar ka kuma ce min Ammi bata yi deserving abinda na mata ba, sabon gidan nan da kake gani ban taɓa tunanin ba ita ce zata fara shiga ciki ba don ita nake gina ma, so do not blame me for my actions, And mind you ni ba jahili bane Maheer nasan abinda nake...." Maheer dai kansa na kasa bai sake cewa komai ba amma zuciyarsa fal yake da tausayin mahaifiyarsa, he felt so really bad, Abba yace "So duk abinda ake ciki a station din i will call and let you know" Daga haka Abba ya juya ya koma cikin gidan, Maheer ya bude motarsa duk jikinsa a sanyaye mai gadi ya bude masa gate ya fita daga gidan. Karfe shidda da rabi Musharraf ya fito station Maminsa na biye da shi a baya, after few seconds Usman ya fito ya nufi motarsa, sai ga Abba ma ya fito bai ko kallesu ba ya nufi tasa motar shi ma, Mami ta bi Abba da kallo har sannan maganganunsa na mata zafi a rai, Maheer ne ya fito ya nufi tasa motar shi ma without looking at them, Mami na kallon Musharraf on a serious note tace "Look at me Musharraf" Musharraf dake saka agogonsa ya juya ya kalleta tace "Babu kai babu yarinyar nan har abada, ni ban san ai guardian din nata marasu mutunci bane marasu daraja...." Musharraf ya katse ta yace "To ba su Kawu Mansur da Aunty Halima bane suka fara masu rashin mutunci ba Mami" Tsawa Mami tayi masa tace "Ina magana kana magana? to wallahi idan kana son kaga bacin rai na Musharraf kar ka fita sabgar er mutanen nan" Da damuwa Musharraf yace "To Mami ina ma take yanxu? Ba ma sai an san inda take ba before all this, we should even pray she is safe" a fusace Mami tace "Oho that's not my problem, ni dai na gaya maka in ba fushina kake so ba babu kai babu ita har abada kuwa, in kuma bakina kake so to bismillah" Kallon Mami kawai Musharraf yake helplessly don bai taɓa ganin Maminsa so angry at him ba haka, truly Abba da Usman sun yi maganganun da ko ma wa aka gaya ma sai ransa ya baci, but shi duk wannan ba damuwarsa bane, matsalarsa kawai inda Mayraah take, Dai dai nan Yayan late father dinsa wato Hon Alhaji Kabir Saminu ya fito daga station din, escort dinsa dake haraban Police station din suka nufosa da sauri, Yana kallon Musharraf strictly yace "Kai..." Musharraf ya juya ya kallesa sannan ya sunkuyar da kai, strictly Alhaji Kabir yace "Babu kai babu er kananun mutanen can daga this very moment, ban da ma kai wawa ne mahaukaci meye zaka ci gaba da bibiyar yarinyar da bata da asali? Are you stupid? Kai mutuncinka ne yanzu police station da suka kawo ka? Wallahi ban da mahaifiyarka da ta hana da babu abinda zai hanani Shari'a da su, mutanen banza kawai mutanen hofi makaryata, su har suna da wani sauran mutunci bayan lamarinsu babu komai facce karya, da mutuncin ka kan wata yarinya can mara asali an kawo ka nan ana tuhumarka sai kace wani Kidnapper ko ɗan fashi, da ban tako tun daga kaduna na zo nan yau ba kana zaton ba cikin barayi zaka kwana a cell ba yau? To wallahi kashedi na farko da na karshe kenan nake maka babu kai babu er su ko da kai ne HOD din department din ba Lecturer din ta ba, nonsense" Shi dai Musharraf kansa na kasa ko sanin abinda kawun nasa ke cewa bai yi ba, don tunanin ta yanda zai fara neman Mayraah kawai yake a ransa, Alhaji Kabir ya kalli Mami yace "Tare kike da motar ki Hajiya" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Ehh da motata nake" Alhaji Kabir yace "Shikenan.... ni zan koma kaduna yanzu" Mami tace "Baza ka bari gobe ba Alhaji" Yace "Ina da appointment da yawa goben, so we will be heading to airport now" Mami tace "Toh shikenan, Allah ya tsare, a gaida su Hajiya da yaran" Yace "In sha Allah" Ko kallon Musharraf bai yi ba ya nufi inda motar sa yake with his escort, sai ga DPO ya fito yace "Honorable tafiyar kenan?" Alhaji Kabir yace "Ehh wallahi zan koma kd yau ne" Har mota suka tafi tare da Dpo din, wanda abokinsa ne for long, Mami ta nufi motar ta without looking at Musharraf, bin bayanta yayi yana tafiya a hankali, ya bude back seat ya shiga, ita dai bata ce masa komai ba, suna kama hanya Mami tace "In dai ban isa da kai ba Musharraf wallahi ka ci gaba da kula yarinyar nan, ni kuma zan nuna maka ba kai kadai na haifa ba" Shi dai bai ce mata komai ba ya jinginar da kansa da kujera abinda ya damesa daban, wato yanda zai fara neman whereabout din Mayraah. Kamar yanda Alhaji Kabir ya kasance abokin Dpo, haka Abba ma Dpo din childhood frnd dinsa ne, kawai aka sulhunta su a wajen don an duba call history din Musharraf don ganin when last ma suka yi communicating da Mayraah aka ga babu communication kwata kwata tsakaninsu for long banda just of recent da ya dinga kiran wayarta baya samu, kamfanin layin da Mayraah ke amfani shi sun yi confirming babu wayar da ya shiga tsakaninsu for more than a month now, sannan asibiti da Musharraf ya kai ta ma an bincika an gano ba shi kadai ya kai ba tare da Dr Asma'u warce ita ma lecturer dinta ce suka je asibitin, har Dr Asma'u sai da aka kira a issue din to confirm. Bayan Mayraah ta idar da sallan Magrib a dakin hotel din da take ta bude jakarta ta ciro wayarta tana jujjuyawa, ciro sim dinta duk biyun tayi, ta mike ta zubar da su a karamin dust bin dake dakin sannan ta saka hijab dinta ta dau Atm card dinta ta fito daga dakinta ta sauka kasan reception, bayan sun gaisa da ma'aikatan hotel din dake zaune reception din ta fita, tsaye tayi bakin titi tana jiran adaidaita sahu, har ta samu tace "Don Allah Malam nearest supermarket nake son ka kai ni" Mutumin yace "I no dey hear hausa madam" Turanci tayi masa ta gaya masa inda zata je, yace ta shiga, tana shiga bayan tafiya me nisa ya tsaya dai dai wani babban shopping Mall ta sauka ta ciro kudinsa ta basa sannan ta shiga ciki. Bangaren mayukam shafawa ta nufa don bata dau cream dinta ba a gida, ta dau cream din da shower gel ta koma side din turarruka tana zaba kamar ance ta juya......
[7/17, 6:50 PM] Khaleesat Haiydar💖: Da sauri Mayraah ta dauke kanta kafin ya kalli direction din da take tsaye ta bar wajen ta koma wani section din mall din gabanta na faduwa tana zare ido, wani lecturer dinta ne Dr Nasir which is a very good frnd of Musharraf don su biyu kadai ne young Dr's din department din nasu as at then, farko da Musharraf ya fara sonta yayi discussing hakan da Dr Nasir din ne, yawanci sai Dr Nasir ya kira ta office din sa as if zai yi mata tambaya ko kuma ya ce zai tura mata Pdf na handout in kuma taje office din tare zata gansa da Musharraf da baya ce mata komai a lokacin, nan kuma shi yake sa Dr Nasir din ya kirata office din kawai don ya ganta, that was 2 years back don tuni Dr Nasir ya bar department din nasu yana Uni Abuja yanzu, Mayraah duk ta rikice ta fara tunanin yanda zata bi ta maida kayan da ta zuba a karamin shopping cart dake hannunta don tana tsoron kar ace taje wajen biya su hadu da shi a can, da ta sani da ta fito da nose mask, cikin dubara ta ɗan sake leka section din da Dr Nasir din yake taga yana tahowa, da mugun sauri ta juya zata bar wajen ta ci karo da wata mata rungume da babynta, zaro ido Mayraah tayi tana kallonta ganin alamar bahaushiya ce matar tace "Don Allah kiyi hakuri...." Matar tayi mata murmushi tace "Ba komai" Ko rufe baki matar bata gama yi ba Mayraah taga Dr Khalil bayan matar rike da wata babyn mai kama da warce matar ta rike alamar dai yan biyu ne, Dr Khalil ya ɗan buda ido alamar yana son tuna sunanta yace "How are you" Matar ta juya ta kallesa, ita dai Mayraah duk a rikice take kar Dr Nasir ya zagayo ya ganta, kamar mara gaskiya tace "Ina yini" Dr Khalil yace "Lafiya lau ya jikin, hope kin ji sauki gaba daya yanzu?" Mayraah tayi saurin gyada masa kai, Dr Khalil ya kalli matarsa yace "Patient dita ce, dazu muka sallameta a asibiti" Matar na kallon Mayraah tace "Allah sarki, Allah ya kara lafiya" Mayraah na murmushin karfin hali tace "Ameen Nagode" Dr Khalil ya lura da how tensed Mayraah is don ta kasa tsaye waje daya kamar mara gaskiya, matarsa na kallon Mayraah tace "To sai anjima" Mayraah ta gyada mata kai da sauri ta bar wajen, Dr Khalil suka wuce tare da matar sa, wani ajiyar zuciya Mayraah ta sauke batan ta hango Dr Nasir can bakin entrance din mall din zai fita da sauri yana waya kuma babu komai hannunsa alamar kilan ya fasa siyayyan, har dai taga fitar sa, gaba daya sai ta dawo uncomfortable a mall din don gani take kamar zata sake haduwa da wani wanda ta sani, da kamar ta fasa siyayyan kawai ta koma hotel dinta sai kuma ta tuna ba fa ta da mai da zata shafa gobe, kuma har pad tana son siya with few junk food don ba ko da yaushe take jin cin abinci ba, kamar mara gaskiya haka ta dinga shopping din nata being very cautious, duk inda kuma taga alamar za su hadu da Dr khalil da matarsa sai tayi maza ta canza route dinta har dai ta gama picking few things da take bukata sannan ta nufi counter inda zata biya, tana hango Dr Khalil da wife dinsa tsaye wajen su ma sun gama siyayya sai taki biyan kudin kayan nata a nan, ta koma next counter din, Dr Khalil na gama biyan kudin abubuwan da suka siya, dai dai sanda aka zo kan Mayraah dake daya side din, tana kokarin bude handbag dinta ta ciro Atm card dinta ya mika ma mutumin Atm card dinsa da turanci ya ce masa ya cire kudin, Mayraah ta daga kai ta kallesa da sauri tace "Aa Dr kar ka damu, i will pay" Dr Khalil yace "Ai na riga ma basa card din...." Mayraah ta kalli matarsa dake kallonta, hakan yasa matar ta sakar mata murmushin karfin hali, Mayraah ta mayar mata da murmushin tace "To Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Tuni aka yi ma Mayraah packaging few abubuwan da ta siya ta amshi ledan, matar kadai tayi ma sallama ta fita daga mall din don su kayansu da yawa ba a gama masu packaging ba, Zainab ta kalli mijin nata tace "Kai kowa dai patient dinka ne Dr" Yayi murmushi yace "Amma kamar patient yan matan sun fi tsaya maki ko...." Tace "Not at all nasan halin ka ai, and i trust u" Yace "Double that trust girlfriend" Tayi murmushi tana kara rungume daughter dinta dake bacci. Washegari karfe goma saura Mayraah ta fito daga hotel room dinta bayan sun gaisa da ma'aikatan wajen ta fita ta tari adaidaita sahu tace masa tasha zai kai ta, ya tambayeta wani tashar, nan ta hau kalle kalle don bata san ma sunan tashar da aka sauketa shekaranjiya ba, can dai ta shiga tana kallonsa tace "Kai ni ko wanne" a traffic ta siya nose mask ta saka don bata son taking risk yau, luckily kuwa mai adaidaitan ya kai ta tashar da aka sauketa Shekaranjiya, ta sauka ta basa kudinsa sannan ta karasa shagon mai pos din ranan, yana ganinta ya gane ta, bayan sun gaisa yace "Har ina tunanin kilan kin samu gidan ne da na ji ki shiru" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta zauna kan kujera tace "Aa ban samu ba, jiya ban ji dadi bane shi yasa baka gan ni ba" Yace "Allah sarki, Allah ya sauwake" Tace "Ameen, ka duba min gidan kuwa don Allah?" Yace "Kwarai kuwa an bincika har an samu biyu, duk wanda yayi maki a ciki shi za ki zaba" Tace "To ba damuwa, kuma nawa ne sai in tura kudin?" Yace "Toh Hajiya yanzu dai kowa yasan yanda duniya ya dawo babu gaskiya, daga haduwa da ni ba haka nan zaki yarda dani har ki bani dukiyarki ba duk da dai kowa yasan nan ne wajen neman abinci na, amma abinda ya kamata yanzu kawai zuwa can sulejan za mu yi tare da ke, bayan kin duba gidan kin ga wanda yayi maki sai ki bada kudin a baki makullin gidan" Mayraah tace "Aa ni kam ba sai naje ba, kar ka damu kawai a zabar min duk wanda aka ga yafi, but pls ya kasance da ruwa kuma da wuta a anguwan" Yace "Ai kar ki ji komai Hajiya ni ma bazan kai ki anguwan da zaki jigata ba don naga baki yi kalar wahala ba, wuta har sai kin gaji da shi, sannan babu matsalar ruwa gida me borehole aka duba maki" Mayraah tace "Toh nawa kudin hayan?" Yace "Toh amma ke irin gida me part part na haya kike so, ko kuma karamin self contain wanda ke kadai zaki zauna ciki?" Mayraah tace "Eh ni kadai nake so, bana son me mutane" Mutumin yace "Toh me daki daya suna bada shi akan naira dubu dari biyu da hamsin har agreement, in kuma daki biyu kike so har dari uku da hamsin ana bayar wa, dari hudu dai a takaice in da agreement, tsakar gidan ma zaki gansa ba lefi mota daya zata shiga ta zauna lafiya lau" a hankali Mayraah tace "To duk wanda dai aka samu ba damuwa" Yace "Amma fa gaskiya me daki biyun nan deal ne Hajiya, in dai da kudin kawai ki rufe ido ki amshe sa don anguwa ce me kyau akwai kuma jama'a kintsatsu ba laifi" Mayraah tace "To shikenan, a ina za a tura kudin" Yace "Ki saka a account dina don cash zan kai masu kar a zo ana dogon zance" Mika masa Atm card dinta tayi, don kudin ciki zai kusa 1.3 tunda babu abinda take da kudi ko Abba ya tura mata sai dai yayi ta zama a account din tunda su Maheer duk wani abun bukatarta su suke siyo mata, ya amshi Atm card din hannunta ta gaya masa pin tana kallonsa tace "Ka cire dubu dari hudu da talatin, sai ka rike dubu talatin din Nagode sosai" Godiya sosai mutumin yayi mata yace "Don dai kin ki ne Hajiya da akan idonki za ayi komai na gidan, har kudin in basu a gabanki" Tayi