Showing 159001 words to 162000 words out of 249515 words

Chapter 54 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1521

sai shegen tsada, dama dai Suleja kika ce to can ma ni nake, business dina ne kawai ke fitowa da ni cikin gari, ni nasan yanda za a samu gida me kyau a suleja, sai dai kuma Sulejan yayi maki nisa zuwa gwagwalada gaskiya, ga tsadan kudin mota" Da sauri Mayraah tace "Aa in dai za a samu bai yi min nisa ba" Mutumin yace "Atoh in zaki iya shikenan, ina daga nan zan sa a bincika min gida a can, ai garinmu ne Suleja iyayena da matana duk suna can" A hankali Mayraah tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, ka bincika min sai in bada kudin a kama min" Yace "In sha Allahu zan bincika a yau kuwa, amma dai yanzu makarantar zaki tafi? Kin dai ga garin kara lullubewa yake" Mayraah ta kalli sama da ya kara lullubewa tace "Eh tare min adaidaitan" Mikewa yayi ya fita cikin yayyafin ya samu adaidaita sahu sannan ya dawo yace "Ga can wani na tare maki har na maki ciniki da shi kudin kawai za ki basa" Ta mike tace "To nagode sosai" Yace "Yanzu lambar wayarki zaki bada a kira ki in an samu gidan ko ya za ayi?" Tace "Ai wayata ta mutu, goben dai zan zo in sha Allahu sai in ji ko an samu" Yace "To ba laifi, Allah ya kiyaye" Fita tayi daga shagon tana jin sanyi sosai ta tafi ta shiga adaidaita sahun da ya tare mata, bayan sun ɗan yi nisa Mayraah na kallon mai adaidaita sahun a hankali tace "Bawan Allah akwai hotel don Allah a unguwan da za mu je yanzu?" Yace "Kwarai kuwa, iri iri ma kuwa" Tace "Toh kai ni daya don Allah" Yace "Toh ba damuwa" Yana isa wani hotel yayi parking yace "Kinga ga wani nan, me kyau ne wannan naga yan mata na zuwa sosai" Mayraah na kallon hotel din tace "Toh Nagode" Ta sauka a daidaita sahun zuwa yanzu ruwan ya sake dawowa da karfi, tana kallonsa tace "Nawa ne kudinka" Ya fada mata ta ciro a handbag dinta ta basa sannan ta shiga cikin hotel din da sauri ruwa na jikata, a reception ta zauna bayan sun yi confirming payment dinta suka bata makullin dakinta ta wuce dakin, tana shiga ta kashe Ac din dakin ta kwanta ta rufa da bargo saboda sanyin da take ji sosai, har kusan magrib tana nan a haka gashi bata yi sallah ba, gashi tana jin kamar alamar cramps wanda hakan yayi mugun daga mata hankali, to yanzu ya zata yi ita kam, ta yunkura ta tashi ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta fara Sallah. Tun bayan da Abba ya gama karanta takardan da Hajiya Amina ta mika masa yake zaune parlor ya kasa cewa komai, ya furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya fi a kirga a zuciyarsa, ita dai Hajiya Amina na inda take a tsaye ita ma ta kasa cewa komai, daga karshe kawai ta juya ta bar parlon, kiran Maheer ne ya sake shigowa wayar Abba for the third time, Dagawa Abba yayi, calmly yace "Kana ina yanzu?" Maheer yace "Ni ina asibitin har yanzu, Ammin ma taki saurarata ta bar asibitin yanzu haka, ta ma ki jiran in tafi da ita a mota" Abba yace "Bayan kai babu kowa a asibitin?" Maheer yace "Eh yanzu wasu cousins dinta suka iso..." Abba yace "To ka taho gida yanzun nan" Daga haka ya katse wayar, Maheer didn't get dalilin da zai sa Abba yace ya taho gida yanzu bayan ga abinda ke faruwa, kawai dai ya tafi parking space din asibitin ya kama hanyar hoping all is well, Duk da rashin nutsuwan dake tare da Abba haka nan ya kira abokinsa wanda shi ma babban ɗan sanda ne, in brief ya sanar masa abinda ke faruwa, abokin nasa yace "Wani Division ne ranka shi dade?" Abba that was just confused don kusan Absentmindedly yayi masa bayanin yayi wani sigh yace "I don't really know" police officer din yace "To a wani anguwa abun ya faru, sai in kira division din anguwan with immediate effect" Abba ya fada masa anguwan da gidan Maheer yake, Officer din yace "Ohk, give me a minute" Daga haka ya katse wayar, Abba ya ciro handkerchief ya share zufar goshinsa ya mike ya fara safa da marwa a parlon yana sake nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, sake duba takardan yayi for the countless time, kawai ya koma kujera ya zauna ya rike kansa yana kiran Allah a zuciyarsa, duk wannan abubuwan dake faruwa Abba bai taɓa jin haushin Ammi yanda yake jin haushinta yanzu a zuciyarsa ba, Bayan some minutes wayar Abba ya fara ring, ya duba ganin officer din ne ya daga, Officer din yace "Yauwa after making series of calls an samo division din yanzu, in sha Allah za a saketa sannan ayi sulhu a gida tunda Allah ya takaita ita warce aka ji ma raunin is responding to treatment, wannan family issue ne kawai dama a gida ya kamata a sasanta, Allah kuma ya kiyaye gaba" a hankali Abba yace "To nagode kwarai da gaske officer" Sallama suka yi Abba ya katse wayar ya sake mikewa yana zaga parlon, dai dai nan aka bude kofar parlon Mama Ladi ta shigo duk ta hada zufa, Abba dai kallonta kawai yake har ta Karaso cikin parlon tace "Mamuda yan sanda fa sun yi ramm da Hajja" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Wayyo Allahna, wayyo Allah, Allah sarki yayata, wallahi da dai ni suka tafi da suka bar ta amma suka ki sauraron haka, da kafa na taho gidan nan Mamuda tsabar gigicewa ga yunwa ko gidan ban rufo mata ba, unguwan nan ya cika babu matsaka tsinke in gaya maka, sai ga Hajja a motan yan sanda, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin irin wannan tashin hankali da bala'i ba sai yau, wai ace surkan jikanta suka dauko mata yan sanda kusan goma" Abba ya katseta don surutunta kara masa ciwon kan da yake ji yake, a takaice Abba yace "Nayi waya an saketa" Mama Ladi ta fashe da sabon kuka tace "Allah Ubangiji yayi maka albarka, in ba kai din ba wallahi sai dai ta kwana cikin barayi a self, tana kuka fa basu ji tausayin tsufarta ba suka dinga figarta har kofar gida, kuma ba kowa ya ja mata ba Badiyyah" Maheer ya shigo parlon da sallama, ya nufi Abba yana kallonsa ganin yanayinsa amma ya kasa cewa komai, Abba ya mika masa takardan hannunsa yana kallonsa ya girgiza kai sounding so pained yace "Ur mother failed me" Daga haka ya wuce sama, ita dai Mama Ladi sai zare ido take tana bin takardan hannun Maheer da ido, Sai da kan Maheer ya sara yana fara karanta first 3 lines din takardan kuma yaga writing din Mayraah, ya ji kafafuwansa sun kasa daukansa ya zauna kan kujera zuciyarsa na bugawa yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta zaro ido a tsorace tace "Lafiya, takardar mecece Mashir?" Kasa bata amsa yayi ya rike kansa. Hajiya Fauziyya da mukarrabanta dake cikin mota za su koma asibitin da aka kwantar da Haseenah bayan ta tabbatar mai gidanta ya bada order din kada a bada belin Hajja sai an kama Badiyyah tukun wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin mai gidan nata ne ta daga tace "Abban Ikram muna hanyar asibitin yanzu haka, don Allah ka kara jaddada masu kada a bada belin matar nan sai an kamo matsiyaciyar yarinyar" Mai gidan nata yace "Ai ina jin fa kawai hakuri za kuyi ayi sulhu Fauziyya, don yanzun nan wani officer da nake jin nauyinsa don gaba ma yake da ni gun aiki kawai dai na fi sa sanin Officers dinmu ne ya bugo min wai surkar abokinsa ce ita matar da yan sandan suka kama, yana kuma neman alfarman a rufe case kawai aje gida ayi sulhu" Hajiya Fauziyya na huci tace "Ban gane ba Abban Ikram, kana nufin an doki er mu an fasa mata kai a banza kenan? Wai kai kaga uban raunin da ta ji mata ne kuwa? Ko don ban dauka a hoto na turo maka ba?" Yace "Na dai gaya maki, ayi hakuri a je ayi sulhu don gaskiya ina bala'in girmama Mutumin nan kuma ina jin nauyinsa, don haka ni har na kira Dpo din division din nace masa a saki matar kawai....." Cikin daga murya Aunty Fauziyya tace "In mun yarda shegiya nake, in mun yarda Allah ya tsine mana, wallahi baza mu yarda ba, a tura mu kotu kawai alkali yayi mana Shari'a...." Katse wayarsa yayi, Aunty Farida tace "Lallai Baban Ikram, a saketa fa yace??" Aunty Fauziyya na huci tace "Kyaleni da shi kawai, a tura mu kotu a kwatar mana hakkin er mu kawai, babu wani sulhu da za ayi a gida, idan ko ba haka ba idan ban kira Yaya Abdurrahman soja an kai Badiyyar barikin sojoji ba sun kakkarya mana shegiya ku ce ba ni bace......." Haka Ammi ta dinga yawon police stations tana neman Hajja, in ta hau wannan adaidaitan ta sauka ta hau wannan a haka dai har Allah ya kai ta division din da aka kai Hajja, Hajja na zaune gaban yan sandan sai zare ido take, tana hango Ammi ta fashe da matsanancin kuka, Ammi ta nufeta ita ma ta fara kuka, wata police woman tace "Ku tun dazu an kawo tsohuwar nan station amma babu wanda ya biyota kamar bata da gata kusan awa biyu kenan......" Ammi na kallonta cikin kuka tace "Tun dazu na fito wllhi, nayi ta duba stations don ban san wanda aka kawota ba, da muna gidan ai sai dai ko ni a tafi dani baza mu bar haka ta faru ba" Police woman din ta taɓe baki tace "To za ku iya tafiya kawai an rufe case din, wai ku je gida ku sulhunta kanku" Ammi tace "Toh mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Ammi ta kama hannun Hajja dake kuka har sannan saboda takaicin wai yau ita ce a motar yan sanda har police station, adaidaita sahu Ammi ta samar masu, ta dinga bata hakuri amma Hajja ta ki daina kuka don kamar ma dada tunzurata take, cikin rawan murya Hajja tace "Kar ma ki maida ni anguwan nan don yanxu ban san da idon da zan kalli yan anguwan ba wannan abun kunya har ina? Da tsufana da mutuncina a min wannan cin mutuncin Ammi, wallahi ko yarinyar nan kadai ta rage a duniya Maheer bazai zauna da ita ba" Ammi ta rasa ma me zata ce jin furucin Hajja na cewar kar a maidata gidanta, to yanzu ina zata kai Hajja, da ace da ne dama gidanta kawai zata tafi da ita amma yanzu ba da bane, tunanin hakan yasa hawaye ya kawo idon Ammi ta rasa tunanin da zata yi kuma, tana kallon mai adaidaita sahun kawai ta gaya masa unguwan Maheer tace "Can zaka kai mu kawai" kafin su karasa ta kira Maheer, yana dagawa tace "Kana ina ne?" Maheer da har a sannan ya kasa motsi yana rike da takardan da Abba ya basa cike da karfin hali yace "Gida" Ammi tace "Wani gidan, mu gashi muna hanyar gidanka da Hajja yanzu tace bazata koma gidanta ba, ya za ayi da makulli?" A hankali yace "A bude gidan yake" Ammi ta katse wayar, wato bazai ma tambayeta ya aka kare ba, a haka suka isa gidansa ranta a bace, babu wanda ya nuna concern din abinda aka yi ma Hajja daga shi har uban nasa, suna shiga parlon Hajja ta zauna kan kujera ta fashe da sabon kuka, cike da damuwa Ammi tace "Don Allah kiyi hakuri Hajja" Cikin kuka Hajja tace "Ni abinda ya ban takaici da aka ki bin ba'asin ma abinda ya hadasu tun asali, wllhi da muka shigo nan da Ladi shake Badiyyah matar tayi tana neman kasheta har Allah ya ba Badiyyar sa'a ta bugata da bango, da kuma Badiyyar bata yi haka ba da ta dade da mutuwa a hannunta wllh, yanzu da ita matar ce ta kashe Badiyyar sai ace yaya? Ban shiga uku ba idan hakan ta kasance me zance ma dangin ubanta daga sun bar min amanar yarinya? Ashe matsiyaciya ce matar Maheer duk bamu sani ba tace Mayraah kaza, Mayraah kaza, Mayraah ta zageta, Mayraah ta ci mutuncinta, Mayraah ta tara mata kawaye a gida ita da kawayen su yi ta shewa, bayan ni dai nasan ba tarbiyyar da muka yi ma Mayraah ba kenan, yarinyar da kowa ya shaida nutsuwarta amma azzalumar matar nan ta dinga mata sharri tana kawowa kunnenmu, to wallahi Maheer ya gama zama da ita har abada kuwa, muna zaman zaman mu lafiya ta shigo ta tarwatsa mana Pamily, ta lalata komai, ashe ita ce ibilishiyar cikinmu daga aurota ko wata uku ba ayi ba ta tarwatsa komai, idan an bibiya wllhi ita ta dinga zuga Badiyyar ma take ta kawo wasu mugayen maganganu kan Mayraah, don da ai ba haka Badiyyah take ba, to yaushe ma ta zauna dindindin a kano balle ta shiga sabgar Mayraah har tace ta mata wani abu, tsakaninsu fa gaisuwa kawai ba wani shiga harkan juna suke ba duk mun sani, suna zaune lafiya kuma, Tun a sannan sai abun yayi ta daure min kai don nasan Mayraah dai da na sani a baya ba haka take ba, amma sai nake tunanin canzawa tayi kawai don ta gano ba mune asalin jininta ba bari ta gwada mana halin ɗan Adam, ashe shegiyar matar Maheer din nan ce duk ta hada komai, duk ita ce ta hada fitinar nan ta rikita mana komai, to da yake Allah me gafara ne sai gashi cikin gaggawa asiri ya tonu tun bamu shiga hakkin Mayraah ba, to wallahi sai Maheer ya saki annobar nan, ya rubuta mata takardanta kawai a gadon asibitin ya bata ba sai ma anje da nisa ba, a duk duniya babu cin mutunci da ya wuce wanda dangin Haseenah suka min yau don har in koma ga mahaliccina bazan manta ba wallahi, da mutuncina da girmana wai yau ni aka saka cikin motar yan sanda" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta ci gaba tana cewa "Wai fa a haka Allah ya rufa mana asiri an dauke Mayraan daga nan gidan bata kasheta ba, a yanda naga ta shake Badiyyah wllhi zata iya kisa matar, Allah dai shi yasan dalilin faruwan komai wallahi" Ammi dai kanta na kasa duk tana sauraron Hajja, lokaci daya hawaye ya kawo idonta, Hajja na share idonta tace "Duk ma abinda kika ma Mayraah ai er ki ce halaq malaq babu me ce maki don me tun da ba shi ya maki rikonta ba ya sha wahala da ita har zuwa yau, kuma 'ya bata fushi da uwarta koma me zata mata dole dai uwarta ce bazata canza haka ba, nakudarta ne kawai baki yi ba amma babu wanda ya kai ki sanin zafinta, ba kuma wanda zai nuna maki ya fi ki sonta daga 'ya yan naki har uban nasu, shi kuma Mamuda dama can da niyyar aurensa kece kawai baki sani ba, a yawace yawacensa ya samo Bazawararsa suke tadi ke kina gida kin saki baki, shine da ɗan matsalan nan ya faru yayi maza ya aureta ya fake da matsalar, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba yana da niyyar auren ya dai rasa yanda zai gaya maki ne, ni fa ba yarinya bace" Ita dai Ammi bata ce komai ba kuma har sannan bata dago kanta ba, hawaye kawai ke zuba idonta, Hajja ta cire dankwalinta ta share hawayen fuskarta tace "A samo min ruwan zafi in je inyi wanka in hadiyi panadol, wallahi duk jikina ciwo yake" Ammi taji baza ma ta iya shiga kitchen din ba, banda lalura me zai kawota gidan matar Maheer har ta zauna, rabonta da gidan tun ba a gama gini ba almost a year ago da ya kawota ta gani, ta dau wayarta ta mike ta fita balcony hawaye na sauka idonta ta sake dialing number Maheer, yana fara ringing ya daga, sai da tayi controlling kanta sannan ta iya cewa "Ka taho da Mayraah" Duk da Maheer ya ji ta ya kasa ce mata komai, kuma yana dai dai gate din gidansa ta kirasa, bude gate din yayi Ammi na ganinsa ta katse wayar, zata juya ta koma parlor kira ya sake shigowa wayarta ta duba taga Abba ne ke kiranta, sai da gabanta ya fadi don wata daya kenan rabon da kiransa ya shigo wayarta, ta daga kiran ta kai kunne ba tare da ta ce komai ba.
[7/15, 5:30 PM] Khaleesat Haiydar💖: Abba yace "Na kira ne in sanar maki burin ke da danginki ya cika a kan Mayraah, You and ur relatives have succeeded into pushing her, dama duniya ae kuke so ta shiga ko? To hakan ya faru sai ku zuba ruwa ƙasa ku sha..... amma ina son ki sani, idan wani abu ya samu yarinyar nan a duk inda take bazan taɓa yafe maki ba, i will never forgive u, duk halin da ta shiga ke da danginki ne sila saboda selfishness dinku, alhaki a kanku kuma ina me tabbatar maki Allah bazai bar ku ba....." Abba na kai wa nan ya katse wayarsa, Ammi dai ta ƙame a inda take tsaye as if trying to assimilate all what Abba is saying, after few second da katse wayar da Abba yayi ta juya a hankali tana kallon Maheer da ya iso balcony din, Har a lokacin bata cire wayarta a kunne ba, tana kallon Maheer ko kiftawa babu cikin karfin hali tace "Ina Mayraan?" Maheer bai yarda sun hada ido da ita ba ya mika mata takardan hannunsa, Ammi ta amsa da sauri tana duba takardan, lokaci daya ta juya ta koma parlor gun Hajja ta durkusa gabanta ta fashe da matsanancin kuka, Hajja ta gigice ta mike tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, lafiya? Me kuma ya sake faruwa?" Takardan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login