Showing 213001 words to 216000 words out of 249515 words

Chapter 72 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1552

downstairs zuwa kitchen, ko da ta fito wanka ta tarar Ammi ta dauko mata kaya daga dakinta ta ajiye mata gefen gado, bayan ta shafa mai ta shirya ta fito parlor, har a sannan Badiyyah na parlon Ammi a kwance ita kadai, Mayraah na tafiya a hankali ta karasa kusa da ita ta durkusa tana kallonta tace "Ya jikin?" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata, Mayraah tayi shiru tana kallonta hawaye na taruwa idonta, abubuwan da suka faru a baya ne da dalilin faruwansu kawai ke yawo mata a zuciya, da sauri ta goge idonta trying to shun away the thoughts off her mind, cikin sanyin murya tace "Kin yi breakfast ai ko?" Nan ma Badiyyah ta gyada mata kai tana kallonta, wani tausayinta Mayraah ta dinga ji har cikin ranta, she can't just imagine Badiyyah da ta sani ce wannan, a whole Badiyyah, Ammi ce ta shigo parlon, Mayraah ta juya tana kallonta, tana tsaye bakin kofar tace "Fito ki je wajen Abbanki Mimi, he is around" Mayraah ta mike tana goge wasu hawayen dake taruwa idonta ta nufi Ammi, a tare suka sauka downstairs, Mayraah na hada ido da Abba dake zaune kan kujera ya mike tsaye yana kallonta, sosai jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta and for the first time she felt guilty akan abinda ta aikata, for the first time ta ji bata kyauta abinda tayi ba, nan da nan hawaye ya cika idonta ta nufesa da sauri ta rungumesa sosai ta fashe da kuka tace "I am sorry Abba, don Allah kayi hakuri, i don't know what came over me, i was...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Abba yayi patting din bayanta a hankali bai ce komai, tayi kukanta me isarta sannan ta durkusa nan gabansa cikin rawan murya tace "Don Allah ka yafe min Abba" Har a sannan ta kasa hada ido da shi, Abba ya zauna kan kujera a karo na farko yayi magana yace "It's okay Daughter.... I am glad you are back home hale and hearty, that was our prayer and hope, Alhamdulillah" Ganin yanda take kuka ya shafa kanta yace "Nace ya isa haka my dear" Ta gyada masa kai tana goge hawayen dake sauko mata, gefensa ya nuna mata ta dawo ta zauna ta daura kanta a jikinsa, sai a sannan ta lura da mutanen dake zaune parlon, Mama Ladi ce dake ta taɓe baki tana hararanta sai Hajiya Amina dake ta kallon Mayraah tana murmushi, matar looks so happy da dawowar Mayraah, Mayraah ta kalli Abba ya gyada mata kai yace "Go and greet her" Mikewa tayi ta ɗan kalli direction din dining da ta hango Usman a zaune shi ma yana kallonta, ta karasa har gaban Hajiya Amina ta durkusa gabanta ta gaisheta, Hajiya Amina ta dago ta sitting her down by her side ta jawota jikinta tana amsa gaisuwar ta da fara'a, Ammi dai na tsaye stairs taki karasowa cikin parlon all her attention na kan Mayraah, Mama Ladi da take ganin abinda ake bai shafeta ba ta mike tana kallon Ammi tace "Ke har yanzu fa shegiyar me aikinki bata kawo ma bakuwar nan abinci ba, ko kafura ce mai aikin da bata san ance baƙon ka annabinka ba" Ammi bata tanka Mama Ladi ba, don dauke kai ma tayi, Hajiya Amina na murmushi tana kallon Mama Ladi tace "Ayya Mama nace mun yi breakfast kafin mu fito" Mama Ladi tace "Aa ko farfesun ne bari inje in debo maki da burodi mu bamu gaji rowa ba a pamilyn mu" Daga haka ta wuce kitchen da sauri, Ammi ta juya ta wuce sama Abba ya bi ta da kallo, Mayraah na son tashi daga kusa da Hajiya Amina ta bi Ammi amma sai ta kasa, gaba daya she is not comfortable sitting down with her, mikewa Abba yayi ya wuce sama. Sai kusan karfe sha biyu Hajiya Amina da Abba suka bar gidan har sannan kuma Ammi bata sauko kasa ba, sai upstairs Hajiya Amina ta tafi tayi mata sallama a part dinta, Mama Ladi kuwa babu wanda zai ce ba wajenta Hajiya Amina ta zo ba don babu labarin karaye da bata ba Hajiya Amina ba, saboda ita ne ma har Hajiya Aminar ta iya kai wa karfe sha biyu a gidan, tunda ita kadai ce downstairs sai Usman dake aiki da laptop dinsa a dining area. Mayraah ta shiga dakin Ammi bayan tafiyar Hajiya Amina ganinta kwance har a sannan ta zauna gefenta tana kallonta tace "Ammi ko dai baki da lafiya ne?" Ammi ta sakar mata murmushi tace "Aa kawai hutawa nake Daughter" Mayraah tace "Toh ba abinda za a kawo maki?" Ammi tace "Aa... i am okay" Shiru Mayraah tayi, tun dazu take zaune dakin da Badiyyah take kwance bayan Ammi tace ma Badiyyar ta koma can za a gyara mata part dinta, ita dai ta rasa wani irin tausayin Badiyyah take har cikin ranta, sai Mama Ladi ce ta zo ta kirata taje suyi sallama da Hajiya Amina tana mata mitar meye hadinta da Badiyyar zata ne ta makale mata kowa na baya baya da ita salon ta shafa mata wani cutar, ita dai Mayraah bata ce mata komai ba, bayan tafiyar Hajiya Amina ne ta hauro sama ta shigo part din Ammi, mikewa Mayraah tayi after some minutes, Ammi na kallonta a hankali tace "Anjima idan na tashi ki zo in gyara maki gashin ki" Mayraah tace "Toh Ammi" Fita tayi daga dakin ta koma dakin da Badiyyah take, Badiyyah na kallonta da kyar tace "Baƙin sun tafi? Ina son in je parlor na gaji da nan din" Mayraah tace "Eh sun tafi" Ita kanta Badiyyah yau ta ɗan samu sukuni tunda ba ayi neglecting dinta as always ba, yau gashi har ruwan wanka sai da Mayraah ta tara mata ta samu tayi wanka, hatta Ammi bata bi ta kanta a gidan iyaka ta ajiye mata abinci in ta ga dama ta ci, wanka ma idan ta ga dama taje ta tara ruwa tayi, sai kuma Maheer da ta saka yake bata medication shi ma yana ajiye mata magani yake fita, Mama Ladi kuwa sai dai bata kyallara ido ta ganta ba, munanan kalamu sai wanda ta manta ne bata sakar mata, hakan kuma ke sa Badiyyar kuka sosai taji kamar ta mutu ta huta kawai, yau kuwa tun da Mayraah ta dawo take by her side even if she is not saying anything to her, Mayraah tace "Sun tafi, za ki iya saukowa, ba kowa a parlon" Da kyar ta lallaba suka koma downstairs ta kwanta nan tsakar carpet, sabuwar mai aikin gidan ce ta kira Mayraah da ladabi tace "Hajiya ta hanata saukowa ta kwanta nan saboda baƙi masu shigowa fa" a hankali Mayraah tace "Ba jimawa zata yi a nan ba" Suna cikin magana Haseenah ta leko Parlon don tabbatar da Mama Ladi bata ciki kafin ta shigo, tana ganin bata parlon ta shigo zata kitchen ta debi abincin rana, dama yanzu ko gas bata kunnawa sai an girka a nan ta faki idon mama Ladi ta shigo ta diba tunda ba wai kanta ya gama healing bane ita ma har yanzu jinya take, tana kyallara ido taga Badiyyah ta fara wakar habaici tana taunar cingam wai wata tayi cikin shege don ta ci ragon suna.... Can kuma ta hango Mayraah wani matsiyacin kallo ta mata ta shige kitchen bata fasa wakar da take ma Badiyyah ba, Mayraah dai ta bi ta da kallo, ita dai Badiyyah dama ko kallon direction dinta bata yi ba don duk haduwar da za su yi da Haseenah a gidan wakar da take mata kenan, to tana fama da kanta ina taga ta kulata. Washegari wajen karfe goma na safe Mayraah ta tashi daga baccin da take, har ta mance rabon da tayi bacci peacefully kuma me tsayi haka, wanka tayi ta shirya sannan ta gyara ma Ammi dakinta ta fito parlor, Maheer ta gani zaune parlon shi kadai, ta karasa kusa da shi ta zauna kasa tace "Yaya ina kwana?" Yana kallonta yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kan ya daina ciwo?" Ta ɗan buda ido sannan ta cire dankwalin kanta don gashinta suka zubo kasa tace "Ya daina" Tun jiya da Ammi tayi mata kitson kalaba take complain din ciwon kai don ta dade bata yi kitso ba, hakan ma yasa ta kwanta da wuri jiya da daddare, yanzu kuma da ta tashi taji babu ciwon, yana kallon kitson nata yace "Yayi kyau" Murmushi tayi tace "Thank you, yaya result dinmu fa?" Sai bayan da tayi tambayar gabanta ya fadi sosai she can't imagine her spilling, ya ɗan yi shiru yana kallonta, nan da nan hawaye ya cika idonta, yanzu gaba daya hawaye baya mata wahala nan da nan take hawaye, cikin rawan murya tace "I had issues ko?" Yace "Nasan tsohon saurayinki ya gaya maki ai" Har sannan gabanta na faduwa tace "Wallahi yaya A'a, babu ta inda zai yi accessing dina ya gaya min" Yace "Ai na zata kin ga result din naki tuntuni" Ta girgiza masa kai tayi narai narai da ido, yace "To bari in nuna maki, but...." Hankali tashe tace "But what yaya??" Yace "Promise me u will be calm ko me zaki gani, kuma ki gode Allah" Wasu hawayen ne suka taru idonta, yace "Toh shikenan" Da sauri ta goge idonta tace "I will be calm plss" Yace "Good, dawo nan" Mikewa tayi ta koma gefensa da ya nuna mata ta zauna sai tsuru tsuru take da ido, ya shiga WhatsApp dinsa ya nemo chat dinsa da Hamidah da ta turo masa result din, Mayraah da duk jikinta ke bari don bata san me zata gani ba ta rufe fuskarta da kujera, ya dubo result din da Hamidah ta turo masa sannan yace "Here...." Ƙin dagowa tayi tace "Kawai ka gaya min plss" Yace "Toh shikenan bari in ajiye wayar" Dagowa tayi da sauri ta amshi wayar cikin dakiya tana kallon screen din, wani kara tayi ganin pass, ta maida dubanta da sauri gun CGPA dinta kawai taga da first class dinta ta fita, ai bata san sanda ta rungumesa ba cike da farin ciki, ya ɗan buda ido yace "Ke... baki da hankali ne" She was soo happy ta zamo kasa tace "Alhamdulillah" Sai kuma tayi sujud shukr, yace "To abinda ya kamata kiyi kenan kike shirme" Mayraah ta dade bata yi farin cikin da tayi a moment din nan ba, amma fa can kasar zuciyarta tunanin ta yanda za ace ta fita da first class take, ita fa tasan abinda tayi a exams din, how comes Kuma ta fito da first class dinta still, but all the same she is soo Happy, mikewa tayi ta dawo gefen Maheer ta zauna tace "Yaya how about sis Badiyyah's result?" Yace "She was expelled" Jikin Mayraah yayi sanyi tayi shiru tana kallon sa, shi ma kallonta yake, can ta sunkuyar da kanta, yayi kasa da murya yace "Je ki amso breakfast dinki" Mikewa tayi ta fita daga parlon ya bi ta da kallo. Bayan 4 days da dawowan Mayraah tana kwance dakin Ammi da rana wayarta ya fara vibrate, dubawa tayi taga Dr Khalil ne ke kiranta tunda ta dawo sau daya ya kirata sai yanzu kuma, dagawa tayi ta kai kunne tayi masa sallama, bayan ya amsa ta gaishesa, yace "Ya kike ya gida?" Tace "Alhamdulillah, ya Ashnaah da Ashfah" Yace "They are fine, kin koma gida kin mance mutane ko" Murmushi tayi tace "Aa ni ban manta ka ba...." Yace "Gashi nan ko hello babu" Tace "Ai bana son in kiraka ne saboda mom twins" Yace "I understand Mayraah, ya Umminki?" Tace "She is fine Alhamdulillah" Yace "Ranan ai Barrister ya hadani da ita mun gaisa" Tace "Da gaske??" Shiru Dr Khalil yayi saboda bude office dinsa da aka yi, ganin wanda ya shigo yace "I will call u back" Daga haka ya katse wayar ya ajiye, Files din hannunsa yayi dropping masa kan table yace "I will be flying to Adamawa later, attend to this files and submit them to me before evening" Dr Khalil yace "Ohk sir, zaka je wajensu Mama kenan" Bai ce masa komai ba yana duba wani textbook dake kan table dinsa, Shi dai Dr Khalil kallonsa kawai yake, after checking the textbook ya daga kai ya kalli Dr Khalil yace "At last ka hakura ka samar mata aikin a wani asibitin kenan, but i was surprise da naga baka yi resigning ka bi ta can ba" Dr Khalil yayi kamar bai gane maganar da yake ba yace "Wa kenan?" MD na kallonsa yace "Ka fi ni sani" Dr Khalil ya fashe da dariya yace "Wait!!! Are you trying to ask for her whereabout in disguise?" MD ya hade rai kafin yace komai Dr Khalil yayi saurin cewa "She is being sick, very sick, ko picking call bata yi.... Kuma as our boss ya kamata kai da any other Dr or Nurse including me mu je mu dubata, she is seriously sick, an tafi da ita kano gun iyayenta...." Juyawa MD yayi ya fita daga office din, Dr Khalil ya bi sa da kallo yana murmushi. Bayan magrib Mayraah ta sauko downstairs ta shiga kitchen don dafa ma Ammi shayin da ta saba yi mata, bayan ta daura tea din ta zuba duk kayan kamshin da zata saka aka bude kofar kitchen din ta juya da sauri, ya shigo kitchen din suna hada ido tace "Ina yini" Bai sake kallonta ba yace "Lafiya lau" Rabonta da ganinsa tun jiya da safe, plate ya dauka zai debi abinci ta bi sa da kallo jin yanda yake wani kamshi tace "Yaya Maleeha fa?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Wacece haka?" Ta wara ido tace "Ita Maleehar ce baka sani ba?" Yace "Tuna min dai" Dariya ta fara yi sosai, ya juya yana kallonta tayi dariyar me isarta tayi shiru, still shi dai kallonta yake, tace "Kilan ma daga wajenta kake yanzu haka yanda naji kana kamshi shine kake min pretending" Yace "Haba" Ta kara kyalkyala dariya tace "I am sure" Yace "Aa sai dai ki rakani mu je yanzu" Da sauri tace "To don Allah mu je, bari inyi sauri in gama yi ma Ammi shayi sai in kai mata kafin nan ka gama cin abincin sai mu tafi" Yana kallonta ya mayar da abincin da ya fara diba a warmer yace "Sai mun dawo zan ci" Ta ɗan buda ido tace "Toh kaci ko kadan ne mana" Girgiza mata kai yayi without saying anything, tace "Toh bari in baka shayin Ammi kadan ka sha" Daga haka ta maida hankalinta kan shayin da take, shi dai yana tsaye yana kallonta, cikin few minutes ta gama dafa shayin ta dauko karamin tea cup da saucer dinsa ta fara zuba masa, sannan ta nufesa tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta, mika masa tayi a hankali tace "Here" taga bai amsa ba kuma kallonta yake, tace "Yaya" Sai da ta sake kiransa yayi saurin mika hannu ya karba, tace "Why are u absentminded? Tunanin me kake yi" Bai sake kallonta ba yace "Nothing, idan kin gama ina jiranki" Daga haka ya fita daga kitchen din ta bi sa da kallo, wani mug ta dauka ta zuba ma Ammi shayin bayan ta kashe gas din ta goge wajen ta fita daga kitchen din, tana ajiye ma Ammi shayin tace "Ammi gashi na gama" a hankali Ammi tace "Allah maki albarka" Mayraah tayi murmushi ta mike tace "Ammi zan raka ya Usman wajen wata frnd dinsa yanzu" Ammi ta kalli agogo tace "Frnd kuma?" Dariya tayi tace "Eh" Ammi tace "Toh sai kun dawo amma plss kar ku jima dare yayi" Hijab Mayraah ta shiga dakin Ammi ta dauka, sai da ta fara shafa turare a jikinta, har ta mance rabon da tayi amfani da wannan special turaren nata tun kafin a fasa aurenta ta daina amfani da turaren sai yau kuma da ta daukosa cikin kayanta, bayan ta gama shafa turaren ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita tayi ma Ammi sallama, sai da ta fara shiga dakin da Badiyyah take ta sameta tana bacci, abincin da ta kawo mata ma kadan ta samu ta ci, Mayraah ta rufe sauran sannan ta fita downstairs, zaune ta tadda Usman a parlon yana jiranta ga tea cup din da ta zuba masa shayi ya sha rabi ya ajiye sauran, tana kallon sauran shayin a hankali tace "Yaya bai maka dadi bane?" Yana kallonta yace "Yayi" Tace "To naga baka shanye ba" Yace "Ya isa" Karasawa tayi ta duka gabansa ta dau sauran shayin ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, Mayraah na shiga kitchen din ta shanye sauran shayin ta wanke cup din da sauce ta ajiye inda sauran suke sannan ta fito, tana kallonsa tace "Yaya mu je" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi bayansa. Suna fita compound din bayan sun bar anguwan taji yace "Kar ki sake saka turaren da kika saka yanzu" Mayraah ta juya tana kallonsa da mamaki, can tace "Saboda me yaya?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Kar ki sake kawai nace" shiru tayi bata ce komai ba, bata ce masa komai ba, ita dai tana ta zuba ido ta ga ta inda za su billo gidansu Maleeha tunda ta san gidan kuma taga sun wuce hanyar gidan, bayan sun yi nisa sosai da anguwan ta kasa daurewa ta juya tana kallonsa tace "Yaya sun tashi ne daga gidansu?" Yace "Ehh" Tace "Ayya, i was wondering naga mun wuce unguwan tun dazu" Ya juya ya kalleta yace "Kin taɓa zuwa ne?" Ta zaro ido tace "Gaya min fa tayi" Yace "Ohk" after almost 30mins ride ta gansu a wani anguwa na masu shegen kudi, ta dinga bin manyan gidajen da kallo har taga yayi horn bakin wani gate mai gadi na lekowa ya gansa ya buda gate din ya shiga yayi parking yana kashe motar ya sauka, Mayraah ma ta sauka ya kulle motarsa, ganin ya nufi entrance din gidan da sauri tace "Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login