Showing 234001 words to 237000 words out of 249515 words
takardunta yace "Hey get out" Juyawa tayi ta bar takardun ta fita daga office din.....
[8/6, 7:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na fitowa office din MD ta nufi office din Dr Khalil, zai fita suka hadu da shi a bakin kofa, yana kallonta yace "Har kun gama?" Mayraah ta taɓe baki tace "Ni dai in kaje office din ka dauko min credentials dina pls" Dr Khalil na jin haka yasan an samu matsala, yace "Tell me, ya ku ka yi da shi?" Tace "Ni yanzu na fara masa uzuri gaskiya, kamar fa ba shi da lafiya ne, but seriously bai kamata ana bari yana fitowa gida a wannan yanayin ba, his parent are not doing him good" Dariya Dr Khalil yayi ba tare da ya shirya ba, Mayraah ta sauke ajiyar zuciya ta koma gefe ta tsaya, har a zuciyarta ta fara tunanin da gaske MD na da problem may be in his brain or so, to ko dai karatu ne ya fara taɓa masa ƙwaƙwalwa, Dr Khalil that was just laughing ya dake yace "Amma dai ya maki tambayoyin da zai maki?" Mayraah ta daga kai ta kallesa tace "He was just talking gibberish and finding fault where there is no fault...." Dr Khalil na murmushi yace "Za ki jira har mu fito theatre?" Mayraah tace "Zan je office din Ceo ne yanzu, i am dropping my handbag in ur office" Dr Khalil yace "Kun hadu da ita ne?" Ta gyada masa kai tace "Ta shigo ne ta gan ni" Dr Khalil na murmushi yace "I love this bond that is forming gradually between u and Ceo, i like it, kuma fa bata da yarda matar, ke kuma gashi kamar taku ta zo daya, ko office dinta in ba MD din ba sai kilan Dr Ajay babu me zuwa, out of bound muke kiran wajen, you know she is so confidential...." Mayraah dai bata ce komai ba, ya mika mata makullin hannunsa yace "Idan kin ajiye jakan sai ki kulle min office" ta amsa tace "Ohk" Yana barin wajen ta shiga office dinsa ta ajiye jakarta sannan ta fito, ta kulle kofar ta tafi sama zuwa office din Ceo, Dr Elliana Alfred... Haka Mayraah ta fada a zuciyarta bayan ta ga sunan manne jikin kofar office din, ta kai hannu zata yi knocking kofar kenan taga an bude, ido hudu suka yi da MD, ita ta fara sauke idonta ta bi ta gefensa ta shiga cikin office din ta bar sa nan tsaye, kasa fita daga office din yayi, did he just open the door for this brat to come in? Kawai ya fice daga office din ya kulle kofar. Mayraah ta karasa har kusa da couch din da Ceo ke zaune da magazine a hannunta, har ta karaso kuma kallonta matar take, matar ta nuna mata inda zata tafi don making mata coffee din da coffee maker dake office din tace "The coffee maker is over there" Mayraah ta karasa wajen sai taga ba coffee powder a nan, dawowa tayi ta gaya mata, Ceo ta ajiye magazine din hannunta tace "Ki je office din Dr Aliyu ki amso, i took it home the last time i was here...." Mayraah tace "Ohk Ma" Daga haka ta juya ta fita, office din Dr Khalil ta tafi duk da tasan bazata gansa ba amma she wish he was there yaje ya dauko coffee din da kansa a wajen MD, ita dai bata son encounter da mutumin nan kwata kwata, avoiding dinsa ma ya kamata ta dinga yi don ta fara masa kallon mahaukaci, ganin babu wani alternative ta sake komawa sama zuwa office din MD din tunda babu yanda zata yi, tsaye tayi bakin kofar tayi knocking, taji yace "Who is there?" kawai ta bude office din a hankali ta shiga, tsaye ta samesa gaban table dinsa yana duba statement of result dinta, wasu takardu yayi saurin dauka a kan table din ya daura kan result din nata cikin few seconds, and she saw that, ta dai karasa cikin office din ba tare da ta bari ta kallesa ba tace "Ta ce wai ka bada coffee powder..." Shi ma without looking at her yace "Naga kamar kina nema ki dinga kawo min reni, don me za ki shigo min office kai tsaye kamar dakin ki? Are you okay?" calmly tace "I knocked first" ya kalleta a karo na farko fuska a daure yace "And who gave u the permission to come in?" Ita ma kallonsa take taki cewa komai, sai kuma ta hango coffee powder din da ya hada dazu a kan table dinsa, zagayawa tayi ta tafi zata dauka, ya bi ta da kallon mamaki, bayan ta dauka zata bar wajen bata lura da laptop dinsa da ke caji ba kawai kafarta yayi tangling wayar chargern, force din ya jawo tsadadden laptop din tun daga kan table din har kasa, komawa baya tayi ta dinga kallon laptop din a tsorace, lokaci daya gabanta ya wani fadi, ta durkusa da sauri ta daga laptop din tana duddubawa, bayan few seconds ta mike tana kallonsa cike da karfin hali tace "I am.. am sorry...." Sai kuma ta ajiye laptop din tare da makullin hannunta ba tare da tasan tayi hakan ba kawai ta dau coffee powder din ta nufi kofa ya bi ta da kallo, tana fita ta kulle office din ta sauke wani ajiyar zuciya har sannan gabanta na faduwa, ko dai bai ga abinda tayi ma laptop din bane, da sauri ta bar wajen ta koma office din Ceo, cikin minti kadan ta gama making mata coffee din, duk inda ta bi sai Ceo ta bi ta da kallo ta ma daina karatun magazine din da take, daga karshe Mayraah ta kai mata coffee din a Tea cup da saucer dinsa, Ceo ta nuna mata table din gabanta, Mayraah ta duka ta ajiye a hankali, Calmly Ceo tace "Thank you dear" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "You are welcome Ma" Ceo tace "Are your parent here in Abuja?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yes Ma" Ceo tace "Mary Ann every movement of urs reminds me of my late friend, it's been long i felt heartbroken this way, har na koma England kina raina ban san me yasa ba, i think i asked Aliyu about you twice or so" Mayraah ta sauke kanta kasa, wani bugawa zuciyarta yake da ita kanta bata gane dalilin sa ba, Ceo ta dauki cup din shayin tace "You can take your leave, thank you dear" Mayraah ta kasa barin wajen, har sai da Ceo ta daga kai ta kalleta, sunkuyar da kanta tayi tace "But ma, kin ce za ki hada ni da relatives din friend din taki" Ceo ta ɗan yi murmushi tace "Sure i will, i am kinda busy now, gobe za mu je workshop Lagos, in 2 days time zan koma England ina da aiki a can" Mayraah ta gyada mata kai tace "Toh Nagode" Ceo tace "You are welcome" Daga haka Mayraah ta juya tana tafiya a hankali ta nufi kofa, matar ta bi ta da kallo babu ko kiftawa. Gaba daya Mayraah ta mance da batun makullin Dr Khalil har sai da ta sauko second floor ta lura she is not holding the key, nan hankalinta ya tashi don bata san inda ta bar makullin ba, ko a office din MD ko na Ceo, hango kofar office din tayi kamar a bude, hakan ya bata mamaki sosai ta dai karasa tana kallon kofar that was slightly opened, tura kofar tayi taga MD tsaye gaban table din Dr Khalil with her handbag in his hands, yana ganinta ya ajiye jakar keeping a straight face, ya kwashi wasu files kan table din Khalil, Mayraah ta kasa cewa komai don tsabar mamaki, to me yake nema a jakanta? Kofa taga ya nufo ta koma gefe tana kallonsa da mamaki tace "Meye kake nema a jakana?" Yace "Ohh jakarki ne ashe, ai na zata na Khalil din ne" Daga haka ya fice daga office din ta bi sa da ido, da sauri ta tafi gun jakar nata ta bude tana duba ciki, wayarta ne a ciki sai Atm card da glasses dinta, with oil perfumes, to me yake nema, is he even okay? Zaunawa tayi still tana searching jakan har sannan mamaki ya kasa barin ta, kenan a office dinsa ta bar key din. Sai kusan karfe daya Dr Khalil ya shigo office dinsa, Mayraah ta mike tana kallonsa tace "Uhnn I've waited all day" Dr Khalil yace "Wallahi muna fitowa kuma MD ya kirani office dinsa, kin samu kin ci abinci ma kuwa?" Mayraah ta dau jakarta tace "Dama kai kawai nake jira driver har ya zo yana jirana a waje, idan naje gida zan ci" Yace "Ohk, ina jin yayi imputing data dinki, so u are going to write me down ur account details, ur shift is from 8am to 6pm For now, resume work next week Monday" Mayraah na kallonsa tace "Ohk, thank you" Yace "Scrubs dinki kamar suna can gidan Ummi, so zan dauko maki a office din MD yanzu tunda kin ce driver yana jiranki...." Daga haka ya fita daga office din zuwa na MD, yana shiga MD dake tattara laptop dinsa da wasu textbooks yace "We are leaving together with Ceo now, idan an ajiyeta bazan dawo nan ba, sai after the workshop, na kai mata list din da muka yi creating na Dr's da 3 nurses da za aje Lagos din gobe, pls ka taho min da motata gida anjima...." Dr Khalil yace "Kana gida ai da daddare?" MD ya kallesa yace "Ka manta za mu fita tare da daddaren zuwa hotel din da frnds dina turawa suka sauka, kasan ban cika son driving at night ba, sorry for always inconveniencing you pls" Dr Khalil yayi murmushi yace "Su abokan naka turawa me yasa basu sauka gidanka ba?" MD zai yi magana Ceo ta shigo da list din da ya kai mata tana mika masa ya taho ya amsa da ladabi, tace "I saw just 3 nurses in the list, why is that?" Ya sunkuyar da kai yace "We chose just them Ma'am" Tace "Why not make them 4, include Mary Ann to the list pls" Ya daga kai yana kallonta da sauri, sai kuma ya ɗan shafa kai yace "But Ma'am, babu ticket for that same flight... Sai dai wani jirgin, wannan da muka yi booking jirgin ya cika, sai ma da muka yi contacting dinsu suka soke wasu ticket din aka samar mana 10 din da muke bukata...." Dr Khalil ya saki baki yana kallon MD don ko booking ticket din basu kai ga yi ba tukunna, Ceo tace "Ohk, that's fine" Daga haka ta juya ta fita daga office din, Dr Khalil na girgiza kai yace "Ka ji tsoron Allah Dr Aliyu, what's there idan anje workshop din da ita, ai ire irensu ma ya kamata...." Dakatar da shi MD yayi yace "Baza ta je ba, yaushe ma aka bata cikakken aiki a nan din da zata je workshop din manyan likitoci a Lagos, wa enda suka yi shekara da shekaru a nan ma basu je ba sai ita mara kunya da ko fara aikin bata yi ba" Dr Khalil yace "Toh dai Ceo da kanta ai tace aje da ita kuma ta san sabuwa ce" MD yace "To ni kuma as the MD of this hospital nace banda ita, baxata je ba, kuma abinda baka sani ba ni ba full employment na bata a asibitin nan ba, she will just work as an Intern in here, not a staff, beside ko service fa bata yi ba daga amsan statement of result kawai sai aiki?" Dr Khalil yace "Thank God dai ba government hospital bane nan din balle kace, kuma wannan kamar bakin ciki kake mata...." MD yace "Shi din ne ma" Juyawa Dr Khalil yayi zai fita, MD yace "Book the flight immediately pls... 10 seats" Dr Khalil yace "Ohk" Daga haka ya fita ya kulle masa kofa. Yana komawa office dinsa yace "Mayraah if it's okay anjima idan na amso su daga gida Ummi ko da daddare ne sai in kai maki gida, cause kamar babu scrubs din available yanzu" Mayraah ta mike tace "Ohk nagode" Yace "You are welcome, ki gaida su Ammi" Tace "Za su ji" Daga haka ta fita daga office din don tun dazu Drivernta ke waje. Wajen karfe biyu Mayraah ta isa gida, tana bude kofar parlon ta ga Usman a zaune shi kadai, sau biyu yana daga kai yana kallonta wanting to be sure ita din ce, ta karaso parlon ta ɗan yi murmushi tace "Yaya yaushe ka zo?" Ya hade rai yace "Yaushe kika fara wannan dressing din in zaki fita?" Tayi kasake tana kallonsa, can ta zagaya inda yake zaune, ya dinga kallonta daga sama har kasa, tace "Yaya me ya faru da dressing din?" Yace "Tambayata kike? Ok barin hijabs din naki kika yi a kano kenan?" Ta ɗan turo baki tace "Yaya Abaya ce fa ba wani abu ba, beside....." Calmly yayi shutting dinta yace "Keep quiet" Ammi ce ta fito daga kitchen ta tsaya tana kallonsu, A nutse yace "Kar ki sake wannan dressing din a gidan nan, were you trying to get someone impressed a hospital din?" Ammi tace "Ban gane kar ta sake wannan dressing din ba, meye da shigar tata da bazata sake ba?" Ya ɗan daga kai ya kalli Ammi don bai ma san ta fito daga kitchen din ba, Mayraah dai sai turo baki take, can dai yace "To gidan biki za ta Ammi, haka ake zuwa interview dama?" Ammi tace "Aa ba ruwanka, let her dress the way she wants as far as ba wando ta saka ta fita ba, meye laifin Abaya?" Mikewa yayi ya bar parlon ya shige daki, Mayraah ta bi sa da kallo, Ammi tace "Rabu da shi ki tafi kije ki yi wanka ki sauko ga abinci na gama" Mayraah ta gaisheta a hankali sannan ta wuce sama, wajen karfe uku ta sake saukowa downstairs bayan tayi wanka tayi sallah sannan ta canza kayanta, dinning area ta tafi ta debi abincin da Ammi ta ajiye a nan, spoon daya ta ci, sai kuma kawai ta mike ta nufi dakin da taga Usman ya shiga dazu, a hankali tayi knocking kofar dakin, tana ta tsaye taji ya bude kofar ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta bi ta gefensa ta shiga cikin dakin ta juya tana kallonsa ta marairaice tace "Yaya did i dress indecent?" Kulle kofar yayi ya koma ya zauna, ta bi bayansa tana kallonsa, yace "Amminki ta ce ba indecent bane... She gat your back" Murmushi tayi ta durkusa gabansa tace "Toh kayi hakuri yaya bazan sake ba, kuma ma ai uniform zan dinga sa wa ba kayan gida ba daga yau" shi dai kallonta kawai yake, ta mike tace "Have you eaten?" yace "Yeah" Tace "Toh zan je in ci abinci" Daga haka ta juya zata fita yace "Mayraah" Juyawa tayi ta kallesa, ba haka nan duk brothers dinta ke kiran sunanta kai tsaye ba, yace "In kin gama abinda kike yi da daddare ki shigo za mu yi magana" Da mamaki take kallonsa wondering maganar me za su yi, sai kawai tace "Toh in sha Allah" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Bayan magrib Mayraah na zaune kan darduma wayarta ya fara vibrate ta dauko a zaton ta Maheer ne don tayi masa kira har biyu bai yi responding ba, Dr Khalil ne ke kiranta, ta daga kiran bayan sun gaisa yace "Na dauko maki Scrubs din a gidan Ummi, can i come over yanzu in kawo maki, kin san za mu je lagos gobe da safe and probably monday za mu dawo" Mayraah tace "Ohk to Nagode" Yace "Address din fa?" Tace "Bari in tura maka" Katse wayar tayi ta tura masa address din, bayan minti sha biyar ya sake kiranta yace gashi a kofar gida, mikewa tayi sai da ta fara zuwa ta gaya ma Ammi sannan ta fito daga gidan sanye da hijab dinta har kasa, tana ta kallon motar wondering ko ya canza mota ne, ta dai karasa ya sauke glass din yana kallonta da murmushi yace "Good evening" MD ta gani zaune front seat ya wani hakikance, Dr Khalil ya sauko daga motar ya zagayo back seat ya dauko mata uniform din ya mika mata yace "Sai fa da yan sanda suka tsayar da mu kafin mu shigo nan, wai wajen wa za mu" Mayraah tayi murmushi tace "Sai kace masu wajena mana" Dariya yayi yace "Eh lallai kam wajenki" can yayi kasa da murya yace "Baki gaida boss dinki ba Hajiya" Mayraah ta sake kallon MD da yayi kasa da kai yana kallonta ta Mirror, don unguwan haske tarrr kamar da rana ko ina fitilu ne, yana ganin ta juyo ya dauke kai yana danna waya with a serious face, a takaice tace "Ina yini" jin bai amsa ba Khalil ya karasa har kusa da door din motar yayi knocking yace "Ana gaisuwa Oga" MD yace "Dalla ka zo mu tafi kana bata min lokaci kasan ana jirana" Mayraah na kallon Dr Khalil tace "Nagode Dr sai da safe" Ya mata murmushi yace "Ki gaida su Ammi" Tace "In sha Allah" Daga haka ta shige cikin gida, Dr Khalil ya zagaya ya shiga driver seat, MD ya kallesa yace "Burin ka kawai ka dinga ja mana raini wajen yarinyar nan, yanzu sai ta ga kamar biyoka nayi fa in her stupid mentality, ji wani iyayi da take, to meye da Unguwan nan?" Dr Khalil yace "Aa bawan Allah, sai da nace in ajiye ka eatry ka jirani in zo in kawo mata sakon kafin in koma in daukeka muje inda za mu kace no way sai ka biyo ni" MD yace "To ni ɗan iska ne zan yarda ka ajiyeni eatry ba abinci nake ci a eatry ba?" Dariya Dr Khalil yayi yace "To nan dai ne gidansu incase....." MD ya