Showing 135001 words to 138000 words out of 249515 words

Chapter 46 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1558

from no where, idan bamu ja ta jiki mun yi consoling dinta ba a wannan stage din depression ake son ta shiga at her young Age?? she neva bargained for this, ita haka Allah ya kaddara mata kuma babu bawan da ke wuce kaddararsa, wallahi Baabarka ta ban mamaki ainun, ba a taɓa disappointing dina irin yarda mahaifiyarka tayi disappointing dina ba, da wannan abun da tayi ma ni da Mayraah akan selfish interest dinta da relatives dinta wllh gwara ace asara nayi na miliyoyin kudi, ban taɓa expecting haka daga gareta ba ko a mafarki, kuma in har tana ganin ita bazata iya dawowa gidan nan don ta ci gaba da rike Mayraah ba to ta sha zamanta duk inda take, don ni a jiya na riga na auro warce zata zauna tare da Mayraah a gidan nan, na kara aure saboda Mayraah, da ban yi niyyar gaya maku ba sae dai ku gani da idonku amma ynzu na gaya maka zuwa anjima ita warce na auran zata tare in sha Allah, wannan ne dalilin da yasa nace ka dawo da Mayraah gida, ita kuma mahaifiyarka taje can ta karata for all i care, all this while da kaga na amince da zaman Mayraah a hostel saboda nasan bazai yiwu ta zauna ita kadae a gida ba ni na tafi sabgogina, kai kana gidanka Usman kuma bai gari, shi yasa kawai na hakura da zamanta a hostel...." Maheer ya dinga kallon Abbansa babu ko kiftawa, and u can see the shock written all over his face, kasa cewa komai yayi tsabar yanda ya girgiza, Abba yace "In kuma baza ka je ka daukota ba ni zan je in daukota da kaina a hostel din yanzu" Maheer ya mike still bai daina kallon Abba ba, he was speechless to ya ma rasa abinda zai ce, can ya juya ya fita daga parlon ya kulle masa kofa, sai a sannan yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Har ya fara sauka downstairs kawai ya juya da sauri ya sake komawa Parlon Abba, sosai hankalinsa ya tashi yana shiga parlon, Abba ya daga kai yana kallonsa, Maheer ya karasa ya zauna pleadingly yace "Abba don girman Allah kayi hakuri ka janye batun auren nan, wallahi yau Ammi tace in je in daukota zata dawo gida...." Abba ya dakatar da shi yace "Ohk ita kuma warce aka daura mana auren da ita jiya sai in saketa yau saboda mahaifiyarka zata dawo ko me kake nufi?" Maheer yayi kasa da murya cike da damuwa yace "Abba masalha fa ake nema..." Dakatar da shi Abba yayi yace "Bana neman wannan masalhar, da mutunci na da furfurata mahaifiyarka da danginta suka walakanta ni suka nuna ban isa ba duk akan son zuciya irin tasu, to ni ba karamin mutum bane Maheer, aure ne an riga an daura kuma yau matar zata tare na sa an mata furnishing dakin Mayraah, Mayraah kuma zata koma dakinka nan din ma na sa an gyara, kai kuma duk sanda ka zo da iyalinka zaku iya sauka Chalet din gidan, period, go and bring back my daughter home....




MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788




*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake*
[7/9, 9:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya jima zaune a parlor bayan ya sauka downstairs, gaba daya kansa ya ƙulle ya rasa wani tunanin zai yi, gashi da yamma yace zai je ya dauko Ammi yasan kuma in dai suka ji wannan abinda Abba yayi ba lallai Ammi ta yarda ya dawo da ita gidan ba, to amma me yasa Abba zai yi haka Ammi bata yi deserving haka daga garesa ba, rike kansa yayi, he is really confuse at this point don gaba daya he was short of idea, mikewa yayi a sanyaye, to wa ma zai gaya ma wannan maganar yanzu, Aunty Mariya ce ta fado masa ya fita compound yayi dialing numberta, tana dagawa bayan sun gaisa tace "Ka kai ta gidan ne Maheer?" Yayi wani ajiyar zuciya me cike da damuwa, duk da Aunty Mariya na kaduna sam bata jin dadin zaman da Ammi take tayi a gidan Hajja ta ki komawa gidanta for more than a month now, kusan kullum ita ke encouraging Maheer kar ya gaji da zuwa gidan Hajja ya dinga ba Ammi hakuri ta koma gidanta, ita dai fatanta ace Ammi ta koma dakinta a ko da yaushe addu'anta kenan, jin Maheer yayi shiru, Aunty Mariya da gabanta ya fadi tace "Ta canza shawara kuma ko?" Maheer ya girgiza kai a sanyaye yace "Aunty Abba ne ke sanar min ya kara aure.... He is just telling me now" a tsorace Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya kara aure kamar yaya Maheer? Aure fa kace" Maheer ya kasa ce mata komai, cikin kidimewa tace "Ban gane ya kara aure ba, shi Abban ya gaya maka haka?" A hankali Maheer yace "Yanzu haka daga parlonsa nake Aunty, ya tabbatar min yayi aure jiya kuma yau matar zata tare sannan kuma ni ga yanda muka yi da Ammi kan cewar yau zan je in daukota, akwai fa matsala Aunty, Ammi gani zata yi kamar nasan da auren Abba na mata shiru kuma na tilastata ta dawo, ni kuma wllh he is just informing me now" Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wani irin fitina ne daga wannan sai wannan duk Mama Ladi da Badiyyah suka ja mugayen abubuwan nan dake faruwa, yanzu ina Mayraah din? last time da na kirata tace min sauran masu 3 papers to ban sake waya da ita ba har yau, is she still in the hostel?" Maheer bai ma son ya furta ma Aunty Mariya kalman da Abba yayi wai zai kara aure saboda Mayraah don shi ma sai da abun ya dakesa, Abba look into his face yace zai auri warce zata rike masa Mayraah ya mance duk rikon da Ammi tayi mata kamar ita ta haifeta wanda ko da wasa su kansu basu san wacece Mayraah ba sai da wannan abun ya faru, kawai ya girgiza kai cikin sanyin murya yace "Sun gama on friday, yau kuma zan daukota daga hostel in maido ta gida" Aunty Mariya ta rasa abinda zata ce duk jikinta yayi mugun sanyi and she felt for her sister, ya da kuruciyarta ba a mata kishiya ba sai yanzu da ta fara ajiye surkai, nan da nan hawaye ya cika idon Aunty Mariya tana girgiza kai tace "Maheer this is seriously getting out of hand, yanzu sake blaming Mayraah din za su yi, dama suna ganin ta dalilinta komai ya dagule to ga uwa da uban dagulewa yanzu kowa zai gani, kaga shkkn sai su tabbatar da abinda suke tunani a ransu don yanzu ma cewa za su yi gashi Abban yayi aure duk a ta dalilin Mayraah, wannan wani irin fitina ce, me yasa Abba bai yi hakuri ba tun da yasan ba halin Ammi bane wannan, me yasa zai saka mata da haka bayan duk gwagwarmayar da suka sha tare a rayuwa, fisabilillahi sai da shekarunta zai kawo mata abokiyar zama saboda shaidan ya shiga tsakani??" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Maheer dai ya kasa cewa mata komai duk jikinsa yayi mugun sanyi, Aunty Mariya ta matsar da abincin da take ci don gaba daya ya fice mata a rai, hankalinta yayi mugun tashi da batun nan da Maheer ya kawo mata, ko ya Ammi zata dau wannan labarin, ita ma ji yanda taji balle Ammi, da ba don uwa uwa bace da sai tace duk Hajja ce ta ja ma Ammi, duk Hajja ta kara rikita wannan al'amarin haka, kuma Badiyyah ita ce babban silar faruwa komai, hawaye kawai take ta kasa magana tana jin zuciyarta na zafi kamar ita aka ma kishiya, suka yi shirun kusan minti daya ko wannensu da tunanin da yake a rai, Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Yanzu Aunty ki bani shawaran yanda za ayi, bana son Ammi taji haushina in anyway, gani zata yi i know everything, kuma in dai tasan da batun kishiyar nan nasan bazata dawo ba Aunty" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tana share hawayenta tace "Kawai ka bari gobe lahadi zan shigo da safe zan nuna kawai na zo bikina, idan ya so sai in rakata gidan, in mun koma gidan we will sort things out a samu ta fara komawa gidan dai tukunna, don tabbas kana maidata gida Anjima duk bayanin da zaka mata bazata fahimceka ba za ku ma taga kamar da hadin bakinka aka mata haka, ka bari kawai ni zan zo gobe in rakata mu koma gidan, kawai ka basu wani uzurin ko na emergency a asibiti sai kace gobe zaka je ka dauketa ka kai ta gidan" A hankali Maheer yace "To Aunty, Allah ya kai mu goben" Tace "Umar din ya iso ne?" Ya girgiza kai yace "Anyi delaying Flight din nasu gobe zai iso in sha Allah" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya kai mu, ita ma Mayraah kar ka maidata gidan yau, it's better gobe ta same mu gidan ba mu sameta ba kilan abubuwan za su fi zuwa mana da sauki" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "But Abba insisted sai na maidota yau fa Aunty, instruction din da ya bani kenan" Aunty Mariya tace "Just find a way out Maheer, kayi duk yanda zaka yi sai gobe zata koma gidan, zan kira ka anjima har kaina ya fara ciwo wallahi, wannan wani irin jarabawa ne astagfirullah" katse wayar tayi, Maheer ya fita daga gidan ya shiga motarsa ya wuce gida ransa duk a dagule. Mayraah ta saka hijab dinta ta fito waje ta dalilin kiranta da aka yi, yana tsaye jikin mota ya rungume hannunsa, ɗan murmushi tayi ta karasa kusa da motar tana kallonsa tace "Ina yini Yaya?" Yace "Lafiya lau, how was the final exams?" Tace "Alhamdulillah" yace "Saura project" Ta gyada kai tace "I am submitting on monday in sha Allah, yaya yaushe ka dawo?" Yace "Not long ago" Tace "Ya aiki?" yace "Alhamdulillah" Ta jingina da motar tace "Ya Maheer yace min yau ya Omar zai dawo, is he back?" Usman ya girgiza kai yace "Sai gobe in sha Allah, ki shiga ki dauko kayanki, za mu tafi gida" Sosai gabanta ya fadi nan da nan mood dinta ya canza ta kafesa da ido babu ko kiftawa, shi dai kallonta kawai yake, haka kawai Mayraah taji da ma kawai ita dai ta ci gaba da zama a hostel din in ma na har abada ne, she is tired with the way things are happening all of a sudden, bata awa daya kalaman Ammi na karshe basu fado mata a rai ba, wani lokacin ta ɗan yi murmushi, wani lokacin kuma taji hawaye na sauko mata, sai taga kamar tafi samun rest of mind zaman da take a hostel din duk da ba wai damuwanta ya yaye bane, a'a har yanzu tana cikin damuwan sosai ma but baza ta so ace ta koma gidan nan ba ko a mafarki, Usman dake ta kallonta as if reading her mind yace "Ko nan din gidanku ne da baza ki bari ba Madam?" Nan da nan hawaye ya fara zuba idonta, ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yayi kasa da murya yace "Za ki koma gida Mayraah, it's still ur home baki da wani wajen da ya wuce can, baki san ko ina ba sai can, as far as we are concern bamu da wata kanwa da ta wuce ke, Abba yace in je in dauko ki, ko gida ban karasa ba na taho nan, so go and pack only ur clothes ki bar ma Ummi duk wani foodstuff ki zo mu wuce gida" Mayraah ta share hawayen dake ta sauko mata cikin rawan murya tace "Amma yaya ban gama project din ba fa, don Allah a bari in gama" Yace "Abba yace zaki gama a gida, be a good gal and do as i say" Juyawa tayi a hankali ta koma cikin hostel din ya bi ta da ido, bayan wani lokaci sai ga ta ta fito da jakarta Ummi ta dauko mata akwatinta biyu, har sannan hawaye ya ki tsaya mata, ita kanta Ummi jikinta yayi sanyi don ta zata Mayraah zata tsaya har nan da sati biyu kafin su gama da internal and external defense dinsu, Usman ya bude masu booth suka ajiye boxes din da jakar, Usman na kallon Ummi with smile on his face yace "Thanks for accommodating our sister Ummi, Allah Ubangiji ya baku sa'an exams, hope kun yi exchanging contact" Ummi na murmushin ita ma tace "Ameen, eh mun yi exchanging" Yace "Maa sha Allah, God bless you" Daga haka ya zaga ya bude ma Mayraah front seat yana kallonta, ta daga kai ta kallesa tana share idonta, bai taɓa bude mata mota ba sai ranan, Maheer kam sai dai in ita ta bude ta shiga amma he is never tired of opening the car door for her, bayan ta shiga ya kulle motar ya zaga ya shiga driver seat Ummi ta dinga daga masu hannu har suka bar area din. Mayraah suna isa gida bayan Usman yayi parking ta bude motar ta sauka, haka kawai gabanta ke faduwa sosai, bata taɓa tunanin akwai ranan da zata shigo gidan da take ma kallon comfort zone dinta tun tana er yarinya ba ta dinga jin wannan faduwar gaban da feeling din kanta as a stranger, ya fito da akwatinta biyu bayan ya mika mata karamin jakar, shi kuma ya dau 2 boxes din suka nufi entrance din shiga gidan tana tafiya a hankali har sannan gabanta na faduwa, wnn ya sa ta fara addu'a a ranta har suka shiga parlon, gaba daya an canza fasalin parlon ba yanda yake a ɗa ba, parlon ya dawo sabo fil don har da sabon fenti aka yi, ga wani daddadan kamshin turare da ke tashi a each and every angle din babban parlon, turaren kuma babu hayaki ko kadan sai azababben kamshi me sanyaya zuciya, Usman ma dai ya ɗan yi jim a parlon don har a sannan yasan Ammi bata dawo gidan ba gashi rabonsa da garin kusan sati uku, yana ajiye Boxes din Mayraah wayarsa ya fara ring, ita dai Mayraah na rakube bayan kujera kamar bakuwa tana bin ko ina na parlon da kallo, kawai samun kanta tayi da tunanin she is not a member of this big house anymore fa, ita din bare ce kawai a cikin yan gidan, she is a total stranger yanxu ta kuma yi accepting haka, ta goge hawayen da ya taru idonta tana kallon Usman da ya ciro wayarsa dake ring, dagawa yayi ganin Abba ne, Abba yace "Ku kuka shigo yanzu?" Yace "Ehh" Abba yace "Ohk ku taho parlorna a sama" Usman yace "To" Katse wayar yayi ya kalli Mayraah yace "Meye kike yi haka kamar kin shigo gidan da baki taɓa shigowa ba?" Ita dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Mu je Abba na sama" Bin bayan Usman tayi suka haura sama, Mayraah ta dinga bin Corridor din da kallo don har nan ma anyi fenti, turaren wutan har sama, infact everywhere is soo cool sbda kamshin nan, tana biye da Usman har suka isa parlon Abba, Usman yayi sallama Abba ya amsa sannan suka shiga parlon, Abba na zaune Parlon rike da cup din shayi, Mayraah ta karasa ta zauna kasa kusa da shi tana murmushi ta a kallonsa tace "Abba ina yini" Abba yyi patting kanta yace "Welcome back home daughter, fatan kun gama jarabawan lafiya?" Mayraah ta gyada kai tace "Alhamdulillah Abba" Abba yayi murmushi yace "Maa sha Allah dear, Allah Ubangiji ya fiddo sakamako mai kyau in samar maki aiki a babban asibiti..." Murmushi Mayraah ta dinga yi don har ranta taji dadin wannan abinda Abba yace, Abba ya kalli Usman dake kallonsu yace "Ya gajiyan hanya barrister?" Usman ya dan shafa kansa yace "Alhamdulillah" Abba yace "Amma na hanaka tuƙin dare baka ji" Usman yace "Wajen 5 muka baro Kaduna, akwai matsala a hanya ne" Abba yace "Toh Allah ya tsare, a dinga kula dai da tafiyar dare pls" Usman yace "In sha Allah" Abba ya dau wayarsa yayi dialing number sannan ya kai kunne, ana dagawa yace "They are around" Daga haka ya katse wayar, ba a wani dau lokaci ba aka bude kofar parlon daga Usman har Mayraah suka daga kai don ganin wanda zai shigo, wata mace ce in her mid 40 ta shigo parlon da sallama, Usman dai sai kallonta yake haka ma Mayraah, matar ta zauna kan kujera cike da fara'a tace "Sannunku da zuwa" Usman ya kalli Abba, sai kuma ya kalleta yace "Ina wuni" Tana murmushi tace "Lafiya lau, barrister ko?" Yace "Eh" Ita dai Mayraah kasa ma gaisheta tayi ta kafeta da ido har sai da matar tace "Mayraah fatan a gama jarabawan lafiya?" Mayraah ta sauke idonta daga kallonta gaba daya she is confuse, can dai tace "Ina yini" Matar da fara'a yaki barin fuskarta tace "Lafiya lau dear, Allah ya baki sa'an jarabawa a fito da sakamako me kyau in sha Allah" Mayraah tace "Ameen" Usman dai yayi shiru, in ya kalli matar sai ya kalli Abba daga karshe dai ya mike da nufin barin parlon Abba yace "Aa zauna ai ban yi introduction ba" Usman ya koma ya zauna yana kallon Abba, Abba na nuna matar dake zaune yace "Sunanta Hajiya Amina, she is ur new aunt...." Usman ya dinga kallon Abba babu ko kiftawa haka Mayraah da ta jingina da kujera kamar idonta za su fito tana kallon matar da har a sannan take murmushi, Abba yace "A jiya friday aka daura mana aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login