Showing 72001 words to 75000 words out of 249515 words
faru ba? Me suka maki a gidan?" Still taki cewa komai don kukan ma bazai bari tayi magana ba, ya dawo yana facing dinta yayi kasa da murya yace "Tell me what happened???" Ganin bazata yi magana ba ya bude bayan motar yace "Shiga ciki" juya masa baya tayi ta hade kanta da motar taki shiga tana rusa kuka, Cikin calm voice yace "Mimi...." Sai a sannan ta juyo ta girgiza masa kai cikin rawan murya tace "Ina son zan je wajen Ammi" Shiru yayi yana kallonta, can yace "To shiga in kai ki" shiga cikin motar tayi hawaye na sauka idonta, ya kulle motar sannan ya shiga front seat ya tada motar suka bar layin, sai da suka hau main road ya kalleta ta madubi, zuwa sannan ta daina kukan ta jinginar da kanta da motar kana ganinta kasan tayi nisa cikin tunanin da ta fada, bai ce mata komai ba har suka isa gida don bai son ya mata magana ta fara sabon kuka. Mama Ladi tace "Ahaf... Ai dama tun suna yara suka iya munafurci, Mera da Usman ba? Sam ai zuciyarsu ba kyau, to banda rashin kyan zuciya mu taho tare rimi rimi ana hira a mota daga karshe ku zame ku yi tafiyarku ku bar mu? To da babu Maheer din wa zai maida mu gida yau, wallahi da na sani ma jiya da ban karesa wajen Hajja ba, don irin dukan da yayi ma Badiyya ya ci ace yana self din yan sanda yanzu haka, da ya sumar da er mutane sai yace me?" Haseenah dake tsaye parlon tana ɗan murmushi tace "Kiyi hakuri Umma, kilan wani uzurin ne ya taso masu" Mama Ladi ta ɗan kalleta tace "Ke kuma wannan magana ai ta pamily ce ba sai kin sako mana baki ba, sun ga za mu ɓata masu lokaci ne yasa suka yi tafiyarsu tunda suna da abun yi" Daga haka ta nufi kofa, tuni dama Aunty Mariya ta fita daga parlon, Haseenah bata ko damu da abinda Mama Ladi ta ce mata ba don ita yau ranta fari tass, tana kallon Maheer da ya bi bayan Mama Ladi cike da shagwaba tace "Sai ka dawo baby, amma don Allah kar ka jima" Yace "Ohk in sha Allah" Daga haka ya fita daga parlon, Haseenah ta zauna kan kujera tana wani murmushi, ita ta ma manta rabon ta ji ta cikin nishadi irin yau.... Maheer na ajiye su Aunty Mariya, Mama Ladi tace "Baza ka shigo ka gaida baabarka ba bawan Allah?" Yana ɗan murmushi yace "Zan shigo anjima da daddare in gaisheta ae" Mama Ladi tace "Duk barin jikin ka koma wajen wancan kodaddiyar matar taka ce haka?" Yayi er dariya yace "Aa ni dai ban ce haka ba" Sallama yayi ma Aunty Mariya yayi reverse ya bar layin.
Ko da ya koma gida Haseenah har tayi wanka sharp sharp ta bada tsadaddun turarrukanta a jiki sannan ta dauko wasu shegun kananun kaya ta saka, welcoming dinsa tayi tun daga bakin kofa ta rungumesa, yayi pecking dinta a goshi sannan ya karasa cikin parlon ya zauna, ita ma ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa tana kallonsa kamar mayya, ya kamo hannunta yace "What will we be taking for lunch" tana shafa beard dinsa tace "Abinda Babyna ya fi so" Yace "Ko muje eatry mu siya abinci?" Ta juya ido tace "Sure dear" Yace "To shirya mu tafi" Hijab dinta har kasa ta saka kan kayan jikinta sannan suka bar gidan, dama bai shigo da motarsa ba a waje yayi parking, duk ita ta zabi abinda za su ci, bayan sun bar eatry din yace "Zan biya gidansu Ahmad in bashi sako" Tace "Ohh bai koma Abujan bane shi?" Yace "Aa ya koma, kaninsa yace in ba zai je Abujan gobe" Tace "Ohk" Suna kusa gidan Haseenah ta kallesa tana murmushi tace "Kamar in shiga gida wllh" Murmushin yayi shi ma, don dole sai ka wuce gidansu kafin ka karasa gidansu Ahmad a layin gaba, saboda yawan zuwa gun childhood frnd din nasa da yake yi ne ma suka hadu da ita a unguwan, yana isa dai dai gate din gidansu yace "Ko zaki shiga ki gaida su Mumy kafin in dawo daga gidansu Ahmad din?" Ta zaro ido tace "Kai Baby dama ana haka?" Yace "Why not, ai kamar yanda kike yawan fada yanzu muna era din civilization and modernization" Tayi dariya tace "Kuma haka ne, to in ka dawo sai ka kirani in fito, amma fa zan ji kunya" Yana kallonta yace "Ba wani kunya baby, ki gaida su Mumy" Bude motar tayi tace "Alright sweet, amma kar fa ka dade don Allah" Yace "Ina mika masa zan juyo ai, kece ma zan ce ma karki ki fitowa da wuri ki shanya ni a nan" Ta sauka daga motar tana dariya tace "Haba ai ni bana ma sha'awan zaman gidan namu yanzu tunda na dandani zaman gidan ka, ae gidan miji daban ne" Kulle masa motar tayi tana masa kallon kauna tace "Sai ka dawo my hubby" Yace "Ohk, but ji mana" Har ta fara tafiya ta juyo tana kallonsa, ya gyara zamansa yace "Go inside and explain to ur parent where u lost ur virginity cause u didn't bring it to my house, after that they should do better akan tarbiya da manners din da suka baki don ya maki karanci, idan kin masu bayanin na farkon wanda shine main issue a nan, sa iya nemana in saka masu convenient lokacin da zan zo su min bayanin da kansu, that is idan ina da lokacin ma kenan, sannan a dawo batun rashin tarbiyyarki da manners dinki, wannan kuma ban san for how long zae dauka a koya maki ba, though my main concern ynxu is how and where u lost ur virginity i really want to know that from ur parent daga nan ne zan iya deciding fate din aurenki a kaina..... ita warce kika kira tsintattciya mara asali i can swear with my life virgin ce, she is intact, cause she is my mum's training, she is my training, i raised her since from when she was a toddler, kin ga kuwa ba standard din ku daya ba" Yana kai wa nan ya tada motarsa yayi zoom off ya bar ta tsaye a ƙame a wajen kamar statue ko kifta ido bata yi.
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Plss ayi hakuri aji tsoron Allah a sauke haƙƙi.....
[6/20, 9:01 PM] Khaleesat Haiydar💖: Haseenah ta dinga bin motar Maheer da kallo ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take tsaye har taga ya bar layin nasu, bayan few seconds ta hadiye wani abu da ya makale mata a makogwaronta da kyar, gani take kamar fa mafarki take ba gaske ba, ta kikkifta ido ta bude still dai ta ganta tsaye a kofar gidan nasu, nan fa ta tabbatar ba mafarki bane da gaske ajiyeta Maheer yayi a gida, tayi karfin halin juyawa ta kalli gate dinsu dake a kulle, bata san sanda ta fara tafiya ba da sauri ta bar bakin gate din tana tafe tana harhade hanya kamar mara gaskiya, da hijab dinta ta dinga rurrufe fuskarta don kada wani a layin ma ya ganta ya ganeta, a haka har ta bar layin gaba daya ta isa bakin titi, zufa ne ke keto mata a goshi ga cikinta dake murda mata, sai a sannan ta daura hannu daya a kai cikin tashin hankali tace "Na shiga uku" tunanin inda zata nufa yanzu ta fara yi, Zaliha ta fado mata, sai kuma ta girgiza kai da sauri don tasan tana zuwa gidansu Zaliha yanzu dole su hadu da mamar Zaliha, matar da wuni tayi a gidansu ranan bikinta, gashi banda wayarta babu ko sisi a hannunta, gefen ta koma jikin wani shago ta shiga kiran layin Badiyya, har ya katse bata daga ba, ta sake kira tana addu'ar Badiyya ta rufa mata asiri ta daga kiran don ita kadai ce mafitar ta a yanzu, Badiyya na dagawa kamar warce ke cikin maye tace "Account din zan turo?" Sai a sannan Haseenah taji hawaye ya cika idonta, ta fashe da matsanancin kuka tace "Badiyya na shiga uku, don Allah kina ina yanzu?" Badiyya dake kwance bakinta yayi suntum ta mike zaune da kyar don duk jikinta ciwo suke mata wai a haka Hajja ta kai ta chemist an mata allura an bata magani, Badiyya tace "Me ya faru??" Cikin kuka Haseenah tace "Ni dai don Allah gaya min kina ina, in fara barin nan kafin wani da na sani ya gan ni, in ma Bichi kike sai in taho kawai yanzu" Badiyya ta zaro ido tace "To fa... To me ya fito dake? Jiya fa muka kai ki Haseenah" Haseenah ta rushe da sabon kuka tace "Ni dai ki fara gaya min inda zan sameki Badiyya" Badiyya tace "Ke ni fa gani a gida ba lafiya fa" Haseenah tace "Innalillahi, Badiyya kin dai san bazai yiwu in zo gidan ba kada kakarku ta gan ni ko, Badiyya gidanmu Maheer ya maido ni yanzun nan" Badiyya ta zaro ido tace "Gidan ku kuma? Garin yaya?" Cikin kuka Haseenah tace "Wallahi, yanzu haka gani a junction din gidanmu na rasa inda zanje, gashi ina tsoron kada wani ya gan ni, ko kuma wani ɗan gidanmu ya zo wucewa" Badiyya tace "To gashi ni bazan iya fitowa ba bakina yayi suntum baki ji yanda nake maganan ba ma, sannan duk jikina yayi tsami ko daga hannu da kyar nake yi wllh, da sai ince mu hadu a hotel, amma kawai yanzu ki samu adaidaita sahu ki taho idan ya so sai in lallaba in fito mu shiga gidan Maman Bala, wannan gidan dai da nake shiga in canza kaya wani lokacin in za mu fita" Haseenah ta gyada kai da sauri tace "To, to gani nan zuwa yanzun nan" Daga haka ta katse wayar ta tsayar da adaidaita sahu ta shige da sauri tana zazzare ido ta gaya masa inda zata. Suna isa layin Haseenah ta kira Badiyya, babu bata lokaci Badiyya ta daga kiran, Haseenah tace "Gani a kofar gidan, don Allah ki fito masa da kudi babu ko sisi a hannuna" Badiyya tace "Toh gani nan" Hajja da ta gama dama ma Badiyya kunu kenan ta juyo tana kallonta da mamaki tace "Ina kuma za ki Badiyya?" Da kyar Badiyya tace "Zan ɗan motsa jiki na ne ko zan ji dama dama, daga nan sai in shiga gidan Maman Bala" Hajja tace "Ki shiga gidan Maman Bala a wannan yanayin Badiyya, a'a da dai kiyi hakuri ki koma ki kwanta ga kunun na dama maki" Badiyya tace "Ke dai ba ruwanki, tunda kika ga zan fita ae zan iya ne" Daga haka ta fice daga parlon Hajja ta bi ta da kallo. Badiyya ta ba mai adaidaita sahu kudinsa tana kallon Haseenah da ke ta hawaye tace "To wai me kika masa haka? Ko da yake mu je gidan Maman Balan tukun" tana dingishi suka shiga gidan Maman Bala tare da Haseenah da ko lura da jikin Badiyya da bakinta bata yi ba tsabar tashin hankalin da take ciki, Dakin yaran Maman Bala suka shiga Badiyya ta zauna tana kallon Haseenah tace "Amma Maheer mahaukaci ne, me kika masa har yake da mind din mayar dake gida daga tarewarki jiya??" Haseenah ta zube kasa ta fashe da kuka sosai tace "Na shiga uku Badiyya, babban tashin hankalina kar ma Mumy ta samu wannan labarin, wallahi nasan kasheni kawai zata yi" Badiyya tace "To kin ki gaya min me ke faruwa, sae kuke kuke da kame kame kike, wani abun kika masa ne?" Haseenah ta hadiye wani abu da kyar tana nazari, ita dai tasan ko karen hauka ya cijeta bazata yi gigin gaya ma Badiyya da kowa yasan bata da sirri abinda ya sa Maheer ya maida ta gida ba, can dai tayi karfin halin cewa "Wai daga yarinyar nan Mayraah sun zo dazu da safe na nuna masa bana bukatarta a gidana shkkn fa Badiyyah, shkkn Maheer ya maida ni gida" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Badiyya ta rike haɓa cike da mamaki tace "Lallai yarinyar nan ta zama annoba a al'umma, saboda ita fa Usman yayi min wannan dukan jiya da daddare a gidansu, Allah Allah nake in samu kaina in san ta inda zan billo ma matsiyaciyar, yanzu kema a kanta aka maida ke gida??" Sai a sannan Haseenah ta kula da yanda halittar Badiyya ya canza gaba daya, amma da yake ba shi ne gabanta ba bata bi ta kan hakan ba sai kuka take, cikin shesshekan kuka tace "Badiyya ki taimaka ki gaya min yanda zan yi, gaba daya kaina ya ƙulle, wallahi kasheni yan gidanmu za su yi in suka samu wannan labarin, zuwa fa kawai yayi ya ajiyeni a bakin gate dinmu daga fita mu siyo abinci a eatry, ashe yasan plan din da ya hada min" Badiyya da taji zuciyarta na tafarfasa tace "Tashi mu shiga wajen Hajja, yanzun nan kuwa zata kira uwarsa...." Da sauri Haseenah ta rikota tana zare ido tace "Don girman Allah ki rufa min asiri bana son kowa yasan abun nan da ya faru banda ni da ke, na yarda dake ne yasa na zo har nan na sameki" Badiyya ta buda baki tace "To yanzu ya kike son ayi? In ba wajen Hajja za mu je ba ta kira uwarsa ni kinga da wani abu da zan iya yi a nan? Ai dole kuwa uwarsa tasan abinda yake faruwa" Haseenah ta girgiza kai da sauri tace "Aa gaskiya ni dai nace maki bana son kowa ya sani, let sort this out without involving anybody" Badiyya ta taɓe baki tace "Cabb, ashe kuwa baza muyi sorting dinsa ba har abada, an gaya maki suna jin maganar kowa banda na uwarsu ne? Ai in ba Ammi bace ta saka baki a maganar nan wllh Maheer bazai saurari kowa ba, ke ma dai da nacin ki sai da na nuna maki illan auren Maheer kika ki saurarata to yanzu ga irinta nan daga kwana daya ya koro ki gida" Haseenah na goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Ni dai Badiyya ki min alfarma kar ki gaya ma kowa wannan abun, bari in kira Zaliha ta same mu a nan inji ita kuma shawaran da zata bada" Badiyya ta kyabe baki tace "To kuma babu abinda ya shiga tsakaninku??" Haseenah tayi kamar bata ji ta ba tana kokarin dialing number Zaliha.
Wajen karfe uku da wani abu Mayraah na gyara Bedroom dinta don jiya da shekaranjiya duk a dakin Ammi take kwana, yau kuma dakin nata take son ta dawo, aikin kawai take amma ba wai hankalinta na kan aikin ba, tunani kala kala ne cunkus ke yawo a ranta, gaba daya ji take kamar zata yi zazzabi, the fact that nobody is even saying anything to her akan issue din nan dake faruwa ya sa taji ta fara tsanar kowa a gidan, they are all acting like everything is normal, babu wanda ke son tada maganar ko da wasa, it's more like an bar ta a duhu kawai babu wani bayani from anybody and that's beginning to hurt her deeply, ta goge hawayen da ya taru idonta ta tafi jikin window ta tsaya tana kallon waje, Then who is she? Menene asalinta? Why was she dumped right from birth? Me ye laifinta da aka yi abandon dinta tun daga haihuwa? Tunanin hakan yasa taji wasu sabbin hawayen na sauka idonta, bude kofar dakin aka yi, bata juyo ba ta goge hawayen dake sauka idonta da sauri, jin shiru bayan some seconds ta juyo a hankali don ganin wanda ya shigo, ya jingina da kofar dakin yana kallonta yace "Kukan me kike dazu a gidan Maheer?" Kamar baxata ce komai ba, sae kuma ta girgiza kai tace "Babu komai, i just saw my self crying" ya mata wani kallo yace "That's a lie" tayi murmushin karfin hali tace "Da gaske nake yaya, babu komai" Zai yi magana aka bude kofar dakin ya koma gefe, Aunty Mariya ce ta shigo tana kallonsa tace "Kai Mama Ladi na ta nemanka tun dazu fa" Ya hade rai yace "Kai, gaskiya this old woman is stressing me seriously, me kuma zan mata?" Aunty Mariya tayi dariya tana kallon Mayraah tace "Hajiyata ban ga kin fito kin diba abinci ba har yanzu, ko kawo maki zan yi" Mayraah tayi murmushin karfin hali tace "Zan zo in diba Aunty" Aunty Mariya tace "Better" daga haka ta juya ta fita dakin tana cewa "Kai kuma bari in je ince ma Mama Ladi kace tana damunka" Bai ce mata komai ba ya maida dubansa kan Mayraah yace "Je ki debo abincin" yana fadin haka ya juya zai fita tace "Yaya ka ara min wayarka don Allah" ya juyo yace "Ina naki wayar?" Tace "I lost it" Ya ciro wayarsa a aljihu ya ajiye mata gefen gado sannan ya fita daga dakin, ta karasa ta dau wayar ta zauna gefen gado ta fara dialing number Musharraf, a ranta ta fara addu'ar Allah ya sa ya kunna wayar yanzu, amma unfortunately aka ce mata a kashe, nan da nan hawaye ya cika idonta damuwarta ya karu a kan na da, what is happening? Baya son magana da ita ne yake kashe wayarsa kenan, Kwanciya tayi edge din gadon hawaye me zafi na sauka idonta. Karfe biyar Mayraah ta shigo parlon Ammi ta dalilin kiranta da ta yi, tun da ta shigo Ammi ke kallonta, ita kanta Ammin ta kasa samun nutsuwa har sannan a zuciyarta daurewa kawai take duk abin nan, Mayraah ta durkusa gabanta a hankali tace "Ammi ga ni" Ammi tace "Me za ki girka ma Abbanku?" Mayraah tace "In masa tuwo da vegetable?" Ammi tace "To je kiyi" mikewa tayi ta nufi kofa zata fita suka kusa cin karo da Maheer, ta koma gefe ba tare da ta kallesa ba tace "Sannu da zuwa" daga haka ta fita daga parlon ya bi ta da kallo kafin ya karasa ciki