Showing 138001 words to 141000 words out of 249515 words

Chapter 47 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1534

da ita, few hours ago ta tare, she will continue taking care of the house and the people in it kamar yanda ake yi a baya, for more than a month now the house lack this, zata ci gaba da kula da duk wani welfare din gidan nan, kaga kamar kai da ka biyo hanya tun karfe biyar u need something to eat, so akwai abinci a kitchen yanxu haka, Mayraah ma kaga bazata sake zaman hostel ba akwai warce zata sa mata ido a gida ko da bana nan, ku ma bakwa nan, Umar dake hanya gobe bazai dawo gida babu kowa ba, ka gane ko...." a takaice Usman yace "Allah ya sanya alkhairi, let me take a shower" Yana fadin haka ya mike yana kallon Hajiya Amina ya ɗan yi bowing yace "You are welcome Ma" Tana murmushi tace "Thank you so much dear" Juyawa yayi ya fice daga Parlon ya ciro wayarsa yana dialing number Maheer, Abba na kallon Mayraah yace "Mu je ki ga dakin ki daughter" Mayraah da jikinta yayi sanyi kalau, ta mike da kyar bata sake yarda ta kalli Hajiya Amina ba har suka fita daga Parlon Abba ya kai ta har dakin Maheer yana nuna mata yace "This will be ur new room" shiga dakin kawai tayi Abba ya bar wajen ta kulle kofa, Mayraah ta jingina da kofar hawaye cike idonta ta fashe da kuka, she still can't believe this, kishiya Abba yayi ma Ammi? Did this also happen because of her? Dama tun barin ta gidan nan Ammi bata sake dawowa ba kenan, ita all this while tayi zaton Ammi ta dawo gidan, yanzu fa duk ta dalilinta abubuwan nan ke faruwa kenan, tunanin hakan yasa ta kara fashewa da sabon kuka ta sulale kasa tana jin komai na duniyar ya isheta why is all this happening for her sake, why??? me yasa abubuwa ke ta faruwa because of her. Har kusan karfe goma Mayraah na zaune bakin kofar dakin ko motsi ta kasa yi tsabar yanda ta kidime, taji anyi knocking kofa, da sauri ta mike tana kallon kofar ta goge hawayenta kafin ta bude, Hajiya Amina ta gani tsaye sanye da hijab har kasa, Hajiya Amina na kallonta cike da kulawa tace "Kin ci abinci kuwa?" Mayraah ba ta yarda ta kalleta ba a takaice tace "Na ci" Hajiya Amina tace "Ohk to, sai da safe kenan?" Mayraah tace "Eh" Hajiya Amina tace "Toh Allah ya tashe mu lafiya" Tana barin bakin kofar dakin Mayraah ta hade rai ta kulle kofar ta tafi can cikin dakin ta zauna hawaye na sauka idonta. Washegari Aunty Mariya ta nemi izini gun mai gidanta na zuwa kaduna urgently, yana barinta kuwa ta kamo hanya, karfe tara da rabi ta isa kano ta nufi gidan Hajja, tana shigowa parlon Hajja, Hajja tayi sororo tana kallonta daga sama har kasa, can tace "Lafiya?" Er dariyar karfin hali tayi ta karaso ta zauna, ita kanta Ammi kallon Aunty Mariya take don sai da gabanta ya fadi, Hajja tace "Tambayarki nake lafiya??" Aunty Mariya tace "Wallahi ba komai kawai mun zo wani biki ne na family din mai gidan, tun jiya ai nake kano kawai nace bari in maku surprise shi da ban sanar maku ba" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "To kin zo a dai dai kuwa, sai ki raka er uwarki zata koma gidanta yanzu haka ma Maheer take jira na kirasa yace yana hanya, ko don saboda yaran nan gwara kawai ta koma dakinta baza a biye Mamuda ba, Umar din ma wai bai iso ba sai yau" Aunty Mariya tace "Kai Alhamdulillah amma naji dadin wannan labari wallahi ashe na zo a dai dai, dama abinda nake ta son ku gane kenan Hajja, ai ba saboda Alhaji Mahmud zata koma gidan nan ba ko don albarkacin 'ya yanta da yanda hankalinsu ke a tashe ya kamata kawai tayi hakuri ta koma" Hajja tace "Yanzun ma saboda su din ne ai ba wani ba, bazan so wannan yaro Umar ya dawo bata gidan ba babu dadi haka" Maheer ne ya shigo parlon da sallama he look so down kawai karfin hali yake kiran da Usman yayi masa jiya ya basa sleepless night bai taɓa zaton haka daga Abba ba, kawai sai ya dinga tausayin Amminsa, da mamaki yake kallon Aunty Mariya bayan ya zauna yace "Aunty daga ina haka?" Tayi murmushi tace "Daga sama" Yace "Kai amma nayi mamaki fa, babu wanda yace min za ki zo" Aunty Mariya dai ta ɗan yi dariyan karfin hali tace "To ai babu wanda na gaya ma" Hajja ta nuna masa jakan Ammi tace "Ga kayan can ka kai mota" Mikewa yayi ya dau box din ya fita daga parlon ya fita kofar gida ya bude booth ya saka, ya rufe booth din kenan, ya ga adaidaita sahu ya tsaya dai dai gidan, ya dinga kallon adaidaitan don ganin wanene a ciki sai ga Mama Ladi ta sakko da kwarababben akwatinta tana ce ma mai daidaita sahun "To kai yaro Allah ya sa ina da dari biyar din da kace, don wllhi daga ni sai dari da hansin na sauka kano, in zaka hakura ka amsa haka gashi...." Mai adaidaita sahun ya kashe machine din nasa yana kallonta yace "Ban gane ba baaba" Haseenah na kallon Badiyyah dake cin dankali da kwai tace "Ke don Allah Badiyyah?" Badiyyah tace "Wallahi nake gaya makiz ai sai da na bi duk yanda na bi na gano daga inda take zuwa exams, har hostel din sai da naje da nose mask in gaya maki, kuma wallahi kullum sai Maheer yaje wajenta sau biyar a rana, ashe wannan fitan daren da yake wajenta ma yake zuwa ke kina nan kin saki baki sai karfe goma ya dawo mana nan" Haseenah ta dinga kallon Badiyyah with straight face, kamar wasa yau Badiyyah ta tashi da cewar sai Haseenah ta bata kudin gold, da yake Haseenah ta san ta kan dubara tuni ta san yanda ta shashantar da zancen ta shigo da zancen Mayraah shine har da debo ma Badiyyah dankali da kwai da hado mata shayi, shine Badiyyah take bata labarin tasan inda Mayraan ma take yanxu haka, Haseenah tace "Kuma su Ammi sun sani???" Badiyyah tace "Nima fa jiya nayi binciken na gano, har yanzu ban gaya masu ba, so nake sai naje gidan anjima, to ai yau ma Ammin zata koma gida" Haseenah ta zaro ido tace "Da gaske don Allah?" Badiyyah tace "Wallahi, ai shi yasa kika ga Maheer ya fita can gidan Hajja zai je ya dauketa ya maida ta gida" Haseenah ta fara sosa kai tana kalle kalle, can ta kalli Badiyyah da ta cika dankali da kwai a baki tace "To dai gaskiya zan je gidan in taya ta kwalema tun da kinga ko ina dole zai yi ƙura yanzu" Badiyyah ta kalleta da sauri sai kuma tayi dariya tace "Ji neman kugun zama da sabon salo, ance maki babu me aiki ne a gidan??" Mikewa Haseenah tayi ta wuce dakinta da sauri sai ga ta ta fito sanye da doguwar riga da Hijab hannunta rike da handbag dinta, Badiyyah ta saki baki tace "Ina za ki?" Haseenah tace "Gaskiya can zan je in taya su aiki, ko ba komai ai Ammi kamar mahaifiyata take, kuma zata ji dadi idan taga na rigasu ma zuwa gidan na fara mata gyare gyare...." Badiyyah tace "Tabdi, to kin gaya ma Maheer din ne?" Haseenah tace "Ba sai ma gaya masa ba, ai Mahaifiyarsa zan je in kyautata ma" Badiyyah tace "Toh bari in sa kaya mu je tunda bani da inda zan je yau" Haseenah tace "To don Allah kiyi sauri" a haka Badiyyah ta mike ta tafi dakinta ta shirya ta yafa gyale ta fito suka kama hanyar gidan a cikin adaidaita sahu, Haseenah sai fatan ta riga su Ammi zuwa gidan take......




MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*
[7/10, 9:17 PM] Khaleesat Haiydar💖: Duk yanda Hajja ta bi da Mama Ladi a kan kar ta bi su Ammi gida ƙin yarda tayi, don bata sake sauraron Hajjan ba ta sake fita da akwatin nata zuwa motar Maheer tana cewa "Ji min tsohuwa dai, to wajenki na zo da zaki ce min sae na zauna wajenki, bayan ni nasan me ya dawo da ni, ko kin zata yawon banza na zo yi Kano, kina zaune kara zube babu neman taimako babu komai sai surutu da isa da gadara, gashi da hannunki da bakinki kina neman tarwatsa zuri'arki" Bayan fitar Mama Ladi Aunty Mariya na kallon Hajja da ta cika tayi fam, ita a dole Mama Ladi baza ta bi su gidan Abba ba, Aunty Mariya tayi kasa da murya tace "Ae kafata kafarta Hajja baza ta zauna gidan ba in sha Allah, ko awa daya baxa mu yi a gidan ba za mu dawo nan tare da ita, haba ai yanzu kuma ba da bane da za ayi hakan" Ita kanta Aunty Mariya sae da taji wani iri da kalmarta na karshe, su kuma baxa su gane ma'anar yanzu ba ɗa bane da ta fada, Ita dai Ammi taki cewa komai a parlon amma sam ita ma bata son Mama Ladi ta bi su, shikenan ita danginta basu da zuciya kenan, me ma zai kara burgesu da gidan Abba, me Mama Ladi zata bi ta gidan su yi after all this that happened, Maheer dama bai bi ta kansu ba ya dinga danna wayarsa daga tsayen da yake kamar baya jin ma me suke cewa, haka kawai baza a dinga daura masa pressure daga wannan sae wannan ba, A fusace Hajja tace "In ban da ma rashin zuciya me kanwata zata sake koma yi gidan Mamuda, mutumin da har yau bai sake bi ta kanmu ba, wallahi in nace maku nayi farin ciki da dawowar Ladi garin nan to nayi ma Allah karya, sam bata da hankali bata da zuciya bata san inda ke mata ciwo ba, ta wani kwaso rubabben akwatinta ta kara dawo mana to me za mu mata??" Aunty Mariya dai tace "Ke dae Hajja kawai ki bar ni da ita nasan yanda zan bi da ita in sha Allahu" Aunty Mariya na kai wa nan ta mike ta dau handbag dinta, Hajja ta kalli Ammi tace "Ki tashi ku je Allah ya tsare" Ammi ta mike ta dau karamin jakarta tace "Ameen" Sai a sannan Maheer yayi ma Hajja sallama ya juya ya fita daga parlon, Mama Ladi na tsaye jikin mota tana ta jiransu sai ga shi sun fito, Mama Ladi tace "A saman motar za a daura akwatin Maheer?" Ya ɗan yi murmushi ya bude mata booth yace "Ai nan ba karaye bane da ake daura akwati a saman mota" Mama Ladi tace "Ƙul ɗan nan, wllhi karayen nan ba kauye bace" Shi dai bai ce mata komai ba ya dau akwatin karfen ya saka bayan motar ya bude mata kofar baya, ta shiga sannan Ammi ma ta shiga, Aunty Mariya ta shiga gaba, sai da suka bar layin Mama Ladi ta sauke wani ajiyar zuciya me karfi tace "Maganganu dai sanka sanka, babu dadin ji.... huhuhu" Babu wanda dai ya tanka Mama Ladi a motar, can ta kara sauke ajiyar zuciya tace "Mutum ba kyau, ku ji tsoron mutum, amma dai ba komai Allah ya kai mu gidan lafiya" Maheer na kusa gida duk jikinsa yayi sanyi, bai san yanda Ammi zata dau wannan lamarin ba, bai san yanda zata yi reacting ba, ita kanta Aunty Mariya tayi nisa tunanin da take, ita dai tasan koma meye bazata yarda ta bar Ammi tace zata sake barin gidan ba, she just have to let her stay by all means, tsoronta yanzu Mama Ladi tunda ba alkibla gareta ba kar ta kara ɓata abun ta rikita komai, Maheer yayi parking bayan mai gadi ya bude masu gate din gidan, nan bugun zuciyarsa ya fara tsananta, baya ma tunanin zai zauna gidan bayan ya ajiye su gwara kawai ya bar gidan duk ma abinda za ayi ya kasance baya nan, he is just tired of everything, ya kashe motar, Aunty Mariya ta fara sauka sannan Ammi, Mama Ladi ma ta sauko tana kallon Maheer tace "Fiddo min da akwatina Maheer, abubuwan ciki ba na wasan yara bane" Maheer ya bude booth din ya sauko da akwatin nata, Aunty Mariya da gabanta ke faduwa ita ma ta kalli Ammi da ta tsaya kamar tana jiran Mama Ladi tace "Ammi mu shiga akwai rana kamar ba safiya ba" da fara'a Ammi ta amsa gaisuwan Mai gadi da ya taho yana gaisheta cike da girmamawa, sannan ta bi bayan Aunty Mariya zuwa cikin gidan, Mama Ladi na biye da su a baya, shi dai Maheer na rike da akwatin Mama Ladi yana tafiya a hankali, Aunty Mariya na shiga parlon Ammi taga Haseenah da Badiyyah zaune parlon ko kadan ganinsu bai mata ba, Ammi ta karasa cikin Parlon ita ma, Haseenah na ganin Ammi ta zamo kasa daga kan kujera tana sinne kai tana ma Ammi sannu da zuwa tare da gaisheta, Ammi ta amsa da ɗan fara'arta, Haseenah ta gaida Aunty Mariya ma, Aunty Mariya ta amsa, Badiyyah ma duk ta gaishesu, Mama Ladi ce ta shigo parlon ta gwale ido tana bin ko ina da kallo tace "Nan gidan ne kuwa naga kamar ba nan ba fa, ko idona ne? auuu kamar dai fenti aka canza da kujerun gidan fa" Aunty Mariya na kallon Ammi a sanyaye tace "Ina makullin part din ki Ammi?" Ammi ta mika mata handbag dinta, Haseenah dai sai wurga ido take kamar warce tayi ma sarki karya, Mama Ladi ta cire gyalenta ta jefar kan kujera tace "Ina Salibar ta kawo min abinda zan ci" Aunty Mariya ta wuce sama jiki duk ba kwari Ammi na biye da ita a baya, Mama Ladi ta bi bayansu tana cewa "Salibar ta kawo min kumallon saman bene kawai, kai amma Mamuda ya kyauta yanzu duk saboda dawowar naki yayi wannan gyaran haka?" Haseenah na ganin sun haura sama ta mike da sauri za ta bi bayansu ita ma taji ance "Me kike yi a gidan nan Haseenah? Da izinin wa kika fito?" Strictly yake tambayar, Haseenah ta juya tana kallon Maheer da ya shigo parlon da akwatin Mama Ladi ta ɗan hade rai tace "Yan gyare gyare na zo taya Ammi mana Maheer, zuwa muka yi ni da Badiyyah mu tayata kaga baxa mu bar ta tayi aikin ba ai" Maheer ya wani hade rai yace "Zo ki fita ki bar gidan nan kar ki tunzura ni, baki da hankali ne zaki kwaso kafa without informing me kice kin zo taya Ammi gyare gyare? To ba a son gyaran naki, sae kece zaki mata gyara aka gaya maki, i am giving u 5 minutes ki bar gidan nan kada ranki ya bace wllhi" Ransa a bace yake maganar, Haseenah ta wani taɓe baki tace "To ai ba don saboda kai na zo ba Maheer, don in ta kai ne ma bazan yi ba wallahi, gani nayi kawai ya kamata tunda Ammi abinda take min ko Mumy sai haka, sannan da hankalina ni ba yarinya bace ba sai wani ya sa ni ba shi yasa na zo kawai, kuma naga Mahaifiyarka ce Ammin nan kyautata mata kawai na zo yi kamar yanda zan yi ma tawa Mahaifiyar, to meye kuma abun tashin hankali a nan" Bata tsaya ta sake sauraronsa ba ta wuce sama da sauri, Badiyyah dai sai tauna chewing gum take tana jin su a parlon, Maheer da yaji zuciyarsa na tafarfasa ya bi bayan Haseenah sama da sauri dolenta kuwa ta bar gidan nan, Badiyyah ta kyabe baki, to ita bata ma ga amfanin biyo Haseenah da tayi ba gashi bata da kudin motar komawa banda haka yanxun nan ma sai ta tashi tayi tafiyarta, ko minti ashirin basu yi da isowa gidan ba amma tun da suka zo basu ga gilmawar kowa ba ga ko ina tsit, har sama Badiyyar ta tafi ta murda kofar dakin Mayraah a hankali ta bude duk da tasan bata gidan, zaro ido tayi ganin wasu tsadaddun furnitures masu shegen kyau cikin dakin, zanin gadon saman katifar ma kadai abun kallo ne ga wani kamshi dake ta tashi a dakin, ko ina na dakin ya canza ya dawo sabo fil kamar na amarya, ga sabbin akwatina da ta gani, a ranta tace to kuma dakin waye wannan haka, har zata karasa ciki ta yi ɗan hali ganin handbag ajiye a dakin sai kuma ta tuna ta fa ga motar Usman a parking space, a hankali ta jawo kofar ta kulle tana tabe baki ta nufi bangaren Ammi ta murda kofa taji a kulle, sauka downstairs tayi tace ma Haseenah ai fa gidan daga Usman sai Abba tunda motarsu ne kadai parking space sai na Ammi da ake kai ta anguwa a ciki, Haseenah na kallonta tace "Kuma bangaren Ammin ba a bude yake ba?" Badiyyah tace "Ai fa kamar ta kulle ne ta tafi da makullin" Ko kadan Haseenah bata ji dadin jin haka ba, amma dai tayi shiru suna ta zaune parlon suna jira, a haka ne su Ammi suka shigo gidan suka same su. Aunty Mariya na bude part din Ammi suka shiga ciki gaba daya har Mama Ladi, Aunty Mariya ta kaƙƙabe masu kujerun parlon suka zauna, Mama Ladi na girgiza kai tace "Mutum mugun icce" Bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Haseenah ta shigo tana ɗan murmushi tace "Ammi akwai abun shara a nan kuwa?" Mama Ladi ta tsuke fuska tace "To sai aka yi yaya in akwai? Don Allah ki rufa mana asiri kiyi tafiyarki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login