Showing 207001 words to 210000 words out of 249515 words

Chapter 70 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1565

ya dawo inda take yace "To ya ku ka yi da ita?" Mayraah tace "Kawai ta nuna min hoton matar da tace ne" Yace "Kuma kinga kuna kama?" Ta daga kai ta kallesa tayi masa nodding kawai, Dr Khalil yayi shiru with different thoughts running his mind kamar yanda ita ma tunani iri iri ke yawo a ranta a lkcn, can yace "Tace zata hada ku ne?" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah a hankali tace "Ae tace ta rasu" buda ido yayi sosai, can yace "To yaranta fa?" Mayraah na goge idonta tace "Tace zata hadamu" Khalil yace "Ita matsalarta shiririta ta da shauninta yayi yawa, yanzu tana iya kama hanya in ta tafi sai bayan shekara za mu ganta a kasar nan" Mayraah dai sai kallonsa take, yace "Amma ki kwantar da hankalinki kafin ta koma dai in tana ganin ki she will be remembering definitely" Mayraah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Zan wuce gida" Yace "Wani gida?" Ta daga kai ta kallesa, ya sauke idonsa yace "Zaman kan naki zaki koma Sulejan ki ci gaba da yi?" Ta wani kallesa, calmly yace "Mayraah" shiru tayi bata amsa masa ba, yace "Kamar yanda nace maki jiya, it's high time ki koma gida yanzu, you've given them enough space nasan yanzu komai ya daidaita in sha Allah" Mayraah ta girgiza kai tace "I will go back when i know it's right to do so" Da mamaki Dr Khalil yace "Abinda Ahmad yayi maki har yanzu bai zame maki darasi ba kenan, to let me tell you, ba Ahmad ba kowa ma kallon da zai maki kenan, don duk mace me mutunci ko gunduwa gunduwa da namanta iyayenta ke yi baxata bar gabansu ba, kuma duk warce kika ga ta bar gida ta tafi wani gari to babu wanda ya isa ya canza kallon er iskan da mutane za su dinga mata, ba ga su nan muna gani a Abuja ba sun tsallake sun bar gida sun dawo nan suna ta iskancinsu" Mayraah ta mike tace "Ni ai Allah ya san ba iskancin nake ba, kuma ban ce bazan koma gida ba, amma sai idan ta hadani da family din matar da na gani a hoto" Dr Khalil yace "Ai ko kina gida za a iya hakan, beside iyayenki na samun labarin kin samu aiki permanently a asibitin nan i know they will support u ki ci gaba da aikin ki, cause kowa yasan asibitin nan a kasar nan, it's ba privilege working here...." Mayraah tace "I will think about that" Dr Khalil yace "Kinsan menene matsalarki Mayraah?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa yace "Taurin kai" Zata yi magana aka bude office din duk suka juya, MD ne tsaye bakin kofar, Mayraah ta kauda kanta tana kallon Khalil tace "We will continue on phone" Daga haka ta dau pack din burger dinta da jakarta ta nufi kofa ganin babu hanyar da zata wuce tace "Excuse me pls" Dr Khalil ya koma kujeransa ya zauna yana kallonsu yana murmushi, MD na mata wani kallo yace "Zan ƙwada maki mari, ni kike ce ma excuse you pls? Or are you harebrained?" Bata ko kallesa ba ta raba ta gefensa almost touching him tayi ficewarta a ranta kuwa cewa tayi sai dai ya ci kansa. MD ya juya ya kalli Dr Khalil a fusace kafin yace komai Dr Khalil yace "Kasan me Dr Aliyu? Har nayi picturing ka mace ma yarinyar nan kun fara soyayya da zai yi leading to marriage, it will really make sense, dama naga kamar yanzu baka da budurwa ko?" Yana kai wa nan ya fashe da dariya not minding MD's weird facial expression a lokacin. Mayraah na isa Suleja bayan tayi share sharen gidan don ta kwan biyu bata zo ba ko ina yayi ƙura, tayi wanka sannan ta dafa Indomie ta ci, tun jiya da daddare ta kulle sim card din da ta kira Musharraf da shi saboda yanda ya dinga kiranta, dauko wayar tayi kamar zata bude sim din kuma kawai ta fasa ta ajiye wayar, tana ta zaune dakinta maganganun Zainab na mata yawo a kai, making her feel so hurt a zuciyarta, kawai sai tayi murmushi tana goge hawayen da ya cika idonta, hoton nan da ceo ta nuna mata ne kawai ya jinkirta abinda tayi niyya a ranta yau, she really want to know who the woman in the picture is, amma da ta tuna Ceo tace mata ta rasu sai jikinta yayi sanyi sosai, Ahmad ne ya fado mata, ita fa ta dade bata yi mamaki irin mamakin abinda Ahmad yayi mata ba, to gani yayi tayi kama da yan iska ne ko kuma ya taɓa ganin tayi wani action da yayi kama da na iskanci? Har cikin ranta taji tana appreciating Dr Khalil kuma tana jinsa kamar Ya Maheer because he was there for her always, kiran azahar ya sa ta tashi taje tayi alwala, sai da tayi sallah sannan ta kwanta tayi baccin da bata samu tayi ba jiya. Bayan la'asar Mayraah na wanke plate din da tayi amfani da shi a kitchen taji ana knocking gate din gidan, so tari idan Maman Hanan ta lura ta dawo suleja ta kan shigo mata su yi hira, wani lokacin kuma daya neigbor dinta Harira ma na shigowa duk sanda suka ga ta dawo, Hijab dinta ta saka ta fita, tana tsaye jikin gate din gidan tace "Waye?" taji muryar namiji yace "Assalamu alaikum" Mamaki ne ya cikata, tace "Waye?" Yace "Baƙi ne ki bude gate din ki fito" Sosai gabanta ya fadi tace "Baƙi kuma? Ni bana expecting baƙi daga ko ina" Mutumin yace "Eh mu ma dalili ne ya kawo mu, bamu yi tunanin za mu zo anguwan nan yau ba" Kasa cewa komai Mayraah tayi don gaba daya ta tsorata, mutumin yace "To cut everything short don naga kamar kin tsorata, mu jami'an tsaro ne... We are not here to harm u Madam, amma idan kika ki bude gate din, we are sorry there is nothing we can do about it za mu bude gate din by all means" Mayraah that was so afraid tace "But what did u want from me?" Yace "Open the gate" ƙin budewa tayi ta koma ciki ta dau wayarta ta fara dialing number Dr Khalil a tsorace.
[7/29, 3:44 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan wani ɗan lokaci Mayraah ta dawo bakin gate din, tayi gathering courage duk da yanda gabanta ke faduwa tace "Sorry... brother na yace i shouldn't open the gate till he comes" shiru duk ta ji sun yi bayan ta gaya masu haka, sai kuma taji mutumin yace "Ki bada number brother din naki" Mayraah tayi tsuru tsuru jin abinda yace, sake maimaita maganar yayi, cike da karfin hali tace "Aa ni bazan bada ba sai na tambayesa tukunna" Mutumin yace "Kirasa yanzu kice we are requesting for his number, call him immediately" Komawa cikin gidan Mayraah tayi ta sake kiran number Dr Khalil, yana fara ring ya daga yace "I am on my way now kar ki bude gate din" Kamar zata yi kuka tace "Wai sun ce in basu numberka kuma" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Number na?? ohk ok basu kawai, but do not open the gate, just call out the number for them" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Kin ji me nace?" A hankali tace "Toh" Komawa gate din tayi bayan ya katse wayar, cikin karfin hali tace "Yace in baku number din, zan kira maku digit din yanzu" Mutumin dake bata amsa yace "Ohk, do so now" Kiran numbers din khalil ta shiga yi har ta gama, mutumin yace "Good" Ji tayi kamar sun bar bakin gate din, ita dai sai zare ido take har taji tafiyar motarsu, duk da haka bata yarda ta bude gate din ba ta koma cikin gidan duk hankalinta a tashe, gaba daya ta rasa wani tunani ma zata yi, tana ta zaune cikin fargaba har wayarta ya fara ring wajen karfe biyar da wani abu taga Dr Khalil ne ke kiranta, dagawa tayi ta kai kunne da sauri, yace "Fito ki bude gate din" Tace "Ka zo ne?" Yace "Eh ina waje" mikewa tayi dama har sannan bata cire hijab din jikinta ba ta fita zuwa bakin gate din, bugun zuciyarta ya tsanata cike da karfin hali ta makale jikin gate din tace "Ka kadai ne?" Yace "Ni kadai ne mana Mayraah" a hankali ta bude gate din with throbbing heart, tsaye ta gansa bakin gate din, ta marairaice masa tace "Did they call u pls?" Yace "Yea they called, but it's not even something serious" Tace "Toh me suka zo yi? Me ya faru? Did commit any offense?" Yace "Za mu je station din yanzu, kawai tambayoyi za su maki...." Ta fashe da kuka sosai tace "Toh ba sai mutum yayi laifi ba ake kai sa station, ni me nayi? Don Allah kar ka boye min ka gaya min" Yace "Nace maki it's not something serious Mayraah, yanxu haka daga station din nake, kawai suna daukan statement dinki zan dawo da ke gida, kar ki wani daga hankalinki" Cikin kuka tace "Statement of what? What wrong have i committed?" Yace "Na fa ce ki kwantar da hankalinki, i am with you, yanzu ba daga Abuja nake ba saboda ke?" Share idonta tayi tana kallonsa, yace "Dauko wayarki mu tafi lokaci na wucewa" A hankali ta juya ta koma cikin gidan, wayarta ta dauko da handbag dinta ta fito, a cikin motarsa ta samesa yana jiranta, bayan ta kulle gidan ta tafi ta bude front seat ta shiga motar, kana ganinta kasan duk jikinta yayi sanyi sosai kuma a tsorace take, bayan sun bar layin ya kwantar da murya yace "Pls calm down Mayraah, kema kinsan bazan bari ayi harming dinki ba, beside i told u it's not something serious, u need not to worry kar ki je jininki yayi kasa" Ta fashe da kuka tace "But i want to know what i did, ina son sanin menene ya sa suka zo za su tafi da ni, wani laifin nayi? I know kasani tunda kaje station din, definitely u are aware, you are just hiding it from me, don girman Allah ka gaya min menene ko zan samu relieve" Dr Khalil ya ɗan kalleta, sai kuma yace "Ohk bazan boye maki ba, kinsan me ke faruwa?" Ta girgiza masa kai da sauri zuciyarta na bugawa, ya ɗan yi shiru sai yace "Kinsan ko wani society or rather community, da irin ka'idarsu ko kuma ince da irin way of life dinsu, da yanda suka ba al'adarsu da addinin su muhimmanci, right??" Shiru tayi tana kallonsa waiting for him to go straight to the point, ya sauke ajiyar zuciya yace "To kin dai ga garin nan da kike ciki yawanci majority dinsu musulmai ne, sannan akwai Hausawa babu laifi, so the community are against gidan da kika kama kina zaune ke kadai kina zaman kanki don suna da yara kuma suna duba tarbiyar yaransu suna tsoron kada yaransu suyi tunanin hakan abu ne me kyau mace ta kama babban gida irin wannan tayi zamanta, sannan sunce ke kince kina karatu amma sun gano ba karatu kike ma a garin Abujan ba, iyaka idan kinje kinyi abinda za ki yi a Abuja sai ki dawo nan ki bude gida ki shiga bayan kwana biyu ki sake komawa cikin Abuja, sannan a complain dinsu sun ce akwai saurayin da ma yake zuwa ya sameki a nan din" Sake baki Mayraah tayi tana kallonsa har zuwa sanda ya dasa aya, she was so shock and speechless, yace "To ban san ko bayan zuwan da nayi last week ko akwai wani wanda ke zuwa wajenki ba" Mayraah bata san sanda ta fashe da kuka ba tace "Allah ya saka min, wallahi bazan yafe masu ba, tunda na dawo nan babu wanda ya taɓa zuwa wajena sai kai, bazan taɓa yafe wannan kazafin da suka min ba" Dr Khalil ya langwabar da kansa yace "Kinga abinda nake gaya maki ai ko, mutuncin ya mace gaban iyayenta, in ko ba gaban iyayenta ba to gidan mijinta, in dai a arewa ne duk inda za ki je to wallahi kallon da za a maki kenan baza ki taɓa canza su daga maki kallon nan ba, a takaice gani suke sharholiyarki kike shigowa kiyi a Abuja sai ki dawo nan Suleja ki fakee, let me tell u something.... kiwon mutane ake yanzu ba fa dabba ba, duk footstep dinki a kan idon mutane yake" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kukan bakin ciki da takaici take, har suka iso garin Abuja ta kasa daina kukan da take har ya ma daina lallashinta, wani station taga sun zo, bayan yayi parking a waje yana kallonta yace "Kiyi hakuri in sha Allah komai ya zo karshe daga yau, wipe off ur tears and trust me I will be by ur side" A hankali ta goge idonta tana kallonsa cikin rawan murya tace "Toh yanzu me zan ce masu idan mun shiga?" Yace "Kar ki damu, na riga na masu bayanin komai, iyaka Statement dinki za a dauka, shikenan" Daga haka ya sauka daga motar ita ma ta sauka har lkcn hawaye ya ki tsaya mata, she felt so hurt da irin kallon da mutane suke mata, ga Ahmad, Zainab, and now sulejan da take, calmly yace "Na fa ce ki daina wannan kukan" Ta gyada masa kai da kyar tana kara goge idonta, ya nufi cikin station din tana biye da shi a baya. Dr Khalil ya gaisa da yan sandan cikin station din yace "Za mu iya shiga office din Dpo din?" Police officern yace "Ehh suna ciki har yanzu, You can go in...." Ya kalli Mayraah dake tsaye gefensa kamar warce tayi ma sarki karya gaba daya a tsorace take don bata taɓa shigowa police station ba, calmly yace "Mu je" Bin bayansa tayi har xuwa office din Dpo din, ya bude kofar ya fara shiga da sallama sannan ita ma ta shiga gabanta na faduwa sosai, makalewa tayi jikin kofar tana kallon wanda ke zaune kan Sofa a office din babu ko kiftawa, can ta juya a hankali ta kalli Dr khalil kamar idanuwanta za su fito, Dpo ya daure fuska yace "Kee, shigo ki kulle ma mutane office" Ji tayi kamar ta zura a guje, ta dai kulle kofar da kyar ta sunkuyar da kai, amma ta kasa karasawa ciki don gaba daya tayi shock a wajen, tuni Dr Khalil ya tafi ya zauna kan kujera, Dpo ya bata thumbs up yana gyada kai cikin jinjina yace "The runaway girl!!" Kasa daga kai tayi, cikin daga murya yace "Ya sunanki?" Da kyar ta daga kai ta kallesa cikin karfin hali tace "Mayraah" Yace "Mayraah the runaway girl.... to nemi kujera ki zauna" Ta saci kallon wanda ke zaune kan sofa din, ai tana ganin irin kallon da yake mata tayi saurin dauke kai kamar munafuka ta tafi ta zauna kan kujera ta takure waje daya, shi dae Khalil murmushi kawai yake, Dpo yace "Kin san wannan da yake zaune?" Sunkuyar da kai tayi, ya mata tsawa yace "Ke..." Cikin rawan murya tace "Yayana ne" Yace "Ya sunansa?" saboda tsoron kar ya sake mata wani tsawan cikin rawan murya tace "Ya Usman" Dpo yace "Yau kwananki nawa da barin gida?" Ta fashe da kuka ta kasa cewa komai, yace "Ba kuka nace ki min ba malama, warce ta iya tsallakawa ta bar gida ai zuciyarta ya kekashe kenan babu wani batun kuka, kwananki nawa yau da barin gida?" Cikin rawan murya tace "Kamar 3 weeks" Yace "Kuma baki da intention din komawa anytime soon ko?" Daga kai tayi tana kallonsa hawaye na sauka idonta, Dpo din yayi shiru, sai kuma ya nuna mata kujeran dake gaban table dinsa yace "Dawo nan ki zauna" Mikewa tayi tana kuka ta tafi ta zauna kan kujeran, yace "Mayraah" Ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta, yace "Abinda kika yi kin kyauta kenan? Saboda wasu unforseen circumstances sun faru that doesn't mean it is the end of life my dear, what if hannun mutanen banza kika fada? Did you know the type of era we are in now? Kinsan irin munanan cases da muke dealing da kullum a wajen nan? me yasa za ki zabi kawai ki bar gida saboda an samu matsala? pls nan gaba ko wani kika ga zai yi abun nan da kika yi ki basa shawaran kar yayi ba shi da amfani, ita dama rayuwa kowa da ƙaddararsa taki a haka ta zo sai kiyi hakuri ki zama me imani ki amshesa hannu bibbiyu, ko da wasa karki sake tunanin wannan shine solution dinki ke macece, leaving home is never a solution, ke baki tunanin halin da iyayenki da yan uwanki za su shiga saboda abin nan da kika aikata? Ko ke ba musulma bace? Don duk musulmi an san sa da tawakalli ne" Ita dai kanta na kasa hawaye sai sauka idonta yake, yace "Yanzu kin san ta yanda aka bi ki har Suleja?" Ta girgiza masa kai, ya dauko wani kwali ya ajiye mata a gabanta, kallon kwalin ta dinga yi sai kuma ta saci kallon Usman dake kallonta tayi saurin dauke kai, Dpo yace "Ko da wasa next time do not try this nonsense again pls" Sai kuma ya kalli Dr Khalil yace "Kai kuma Allah ya saka maka da alkhairi for all ur effort, ni yanzu zan fita, za ku iya tafi Allah ya tsare gaba....." Har suka fito daga office din Dpo Mayraah bata yarda ta kalli Usman ba, sai makalewa kusa da Dr Khalil take, bayan sun fita daga police station din, Dr Khalil na kallon Usman yace "Ina kuka nufa yanzu, don naga it's almost magrib" Ita dai Mayraah na can gefe tsaye gabanta sai faduwa yake, ta saci kallon Usman yafi a kirga, Usman yace "Ba komai, na saba driving din dare, i will drive to kaduna in sha Allah" Dr Khalil yace "Toh ba damuwa, idan ka isa kadunan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login