Showing 66001 words to 69000 words out of 249515 words

Chapter 23 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1519

daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta sauke idonta tace "Ina yini" Yace "Kin gama?" Ta gyada masa kai, yace "To tashi mu je ki fadi abinda kike so a siya maki" Ta ɗan kallesa tace "Ai na ci abinci" Shiru yayi yana kallonta, don komin abincin da ta ci bata taɓa ƙin bin sa ya siya mata ko ice-cream or shawarma in zai fita siya ma Ammi fruits da daddare, jin yayi shiru ita dai taki dago kanta tana ta wasa da fingers dinta, she was soo uncomfortable, a hankali taji yace "You are now trying to tell the world i am no longer ur brother Mimi, and u forgot i have been ur brother for good 22 years, me yasa kike son canza hakan yanzu?" Hawaye ya kawo idonta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya dago ta, ta kwace hannunta tana hawaye, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, cikin rawan murya tace "Kayi hakuri" Ya ma rasa abinda zai ce mata, bayan few seconds a hankali yace "Mu je" Bata bari sun hada ido ba tana goge hawayen dake sauka idonta ta nufi kofa ya bi bayanta, suna fitowa parlor Ammi ta dinga kallonsu, yace "Ammi i want to get her something sai in dawo da ita yanzu" a hankali Ammi tace "Ka bar er mutane fa a gida Maheer..." Yace "Ai kawayenta suna nan, kuma sai naje ma zan maida su various houses dinsu" Ammi ta kalli Mayraah tace "To sai kun dawo Mimi" yana gaba ta bi bayansa suka fita daga parlon, mamaki bai cika Maheer ba sai da yaga all through the ride ko tari bata yi ba, Mayraah da har sai ya gaji da labarinta idan suna mota tare, sosai ya ji abun ya damesa yanzu, yayi parking dai dai wani eatry yana kallonta a hankali yace "Shawarma da me zan siya maki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Anything" Bayan few seconds ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido, yana dawowa motar ya ajiye mata abinda ya siyo mata sannan suka bar wajen, duk da hanyar da ta ga ya nufa da ita bata ce komai ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin yayi parking dai dai gate din gidansa, wayarsa ya dauka yayi dialing number Haseenah tana dagawa yace "Tell ur frnds ina jiransu zan ajiye su gida yanzu" Da mamaki Haseenah tace "Ban gane ba, ina abokan naka? Kana nufin yanzun ma baza a siyi baki ba da sauransu?" Maheer yayi shiru kafin yace "Bakin wa za a siya?" A fusace Haseenah tace "Ni wallahi na gaji da walakancin da kake min Maheer dama ba sona kake ba ka aureni?" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, yace "No.... it's not like that Haseenah, kinga frnds dina yawanci a Abuja suke so duk sun koma saboda aiki, kiyi hakuri kawayen naki su fito in maida su gida, sannan su fadi nawa za a basu sai su turo account number" Cike da shagwaba Haseenah tace "Za ku yi magana da Zaliha idan sun fito" Yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, juyawa yayi ya kalli Mayraah, if it was before yanda tayi shiru haka da ya ja hancinta amma yanzu kam bai yi hakan ba, yayi kasa da murya yace "Tunanin me kike?" A hankali tace "Bacci nake ji" Yace "Ohk, yanzu zan maida ki gida ki kwanta, hope kina shan magungunan da na siyo maki tunda baki son alluran?" Ta gyada kai tace "Ina sha" Yace "Ohk" kawayen Haseenah hudu suka fito daga gidan har da Badiyyah, Maheer ya hade rai ganinta, Zaliha ta bude front seat tana washe baki tace "Ango ka sha kamshi" Gaba dayansu suka yi turus ganin Mayraah gaban motar, barin Badiyyah da ta bude baki da mugun mamaki, Maheer yace "Ku shiga in ajiye ku gida, it's getting late" Zaliha ta kirkiri murmushi ta koma back seat tare da sauran frnds din nasu, Badiyyah ta zaro ido tace "Aneesah na baki wayata kuwa?" Aneesah tace "Aa" Da sauri ta juya ta nufi cikin gidan tana cewa "Lahhh ban ciro sa a caji ba kenan" Badiyya na tuntube ta koma dakin Haseenah, tsaye ta ganta gaban madubi tana gwada kayan baccin da zata sa tana murmushi, Badiyyah tace "Ke kinsan da wa Maheer yake a cikin mota kuwa?" Haseenah ta juya da sauri tace "Aa" Badiyyah tace "Wllh er tsintuwar nan muka gani zaune gaban motarsa, wato duk maganganun da muka maki kan cewar ki ja masa aji yau akan abubuwan da ya dinga maki a biki har kin watsar kin wani kwaso kayan bacci kin zube kina zaba ko? To ai shikenan" Sosai gaban Haseenah ya fadi jin warce Badiyya tace mata sun gani a motar Maheer, ta dinga kallon Badiyyah ko kiftawa babu, tuni Badiyyah ta juya ta fice daga dakin ta koma compound tana ma mai gadi sallama sannan ta fita kofar gida, still tayi bakin gate ganin babu motar Maheer alamar ya tafi ya bar ta.
Wajen karfe tara da rabi Mayraah na tsaye a kitchen kusa da gas tana dafa ma Ammi shayin da ta saba yi mata, dafa shayin take amma gaba daya hankalinta baya jikinta, rashin samun wayar Musharraf ya dameta sosai don har wani zazzabi take ji yanzu, to ko dai he doesn't need her anymore because of who she is, tunanin hakan yasa taji hawaye ya kawo idonta, sai yanzu ta sake tabbatar da son da take ma Musharraf na gaske ne, tana kokarin zuba shayin a cup bayan ta gama taji an bude kofar kitchen din ta juya, sosai gabanta ya fadi ganin Badiyya ce ta shigo, Mayraah tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take tana goge idonta zuciyarta na bugawa, dawowar Badiyya kenan gidan tun bayan da Maheer ya tafi ya bar ta, Badiyyah tayi wani dariya tana kallonta tana tafe hannu, can ta rike haɓa tace "Ohh wai Shege ya fi ɗan masu gida, to in ji dai yanzu kin gane cewar matsayina da naki ba daya bane a family dinmu, don ke ba kowa bace facce tsintattciya walakantacciya warce karuwar uwarta ta wuragar da ita a gefen masallaci! Banda ma rashin sanin wacece ke ai da baza ki fara soyayya da Musharraf ba don yafi karfinki nesa ba kusa ba, shima kuma ko a mafarki bazai so ya kula irin ki ba mara asali, dama ance rashin sani yafi dare duhu, ai irin su Dr Musharraf sai mu masu asali gaba da baya yan dangi yan gata ba wa enda aka jefar tun suna tsummam haihuwa ba...." Mayraah kasa juyowa tayi sai hawaye kamar an bude famfo, ihun da taji Badiyya ta kwala ne yasa ta juyawa da sauri, da kafa ya sa ya kwasheta sai ga ta rigijib a kasa sannan ya kulle kofar kitchen din, Mayraah ta tsorata sosai ga koma gefe tana kallonsa, tuni ya zare belt dinsa ya fara lafta ma Badiyya ta wajen kan belt din kamar an aikosa, Ihu Badiyya take iya karfinta tana kokarin tashi amma ta kasa tsabar yanda belt din ke shigarta ta dinga birgima kamar macijiya tana cewa "Na shiga uku na lalace, Hajjaaaa" Mayraah da duk ta gigice ta tafi kofar kitchen da zai yi leading dinka zuwa backyard din gidan zata bude ya daka mata tsawa yace "Kina budewa zan hada da ke" Makalewa tayi jikin kofar zuciyarta na bugawa tana kallon yanda yake dukan Badiyya ba kakkautawa, bude kofar kitchen din Aunty Mariya tayi a gigice don tana saukowa parlor ta fara jiyo ihu kamar daga kitchen, a sama kuma ba a jin komai, Badiyya na ganin Aunty Mariya cikin gigicewa ta dinga cewa "Wayyo Aunty ki shigo ki taimakeni zai kasheni, wallahi kasheni zai yi ki kira har da su Hajja da Ammi" Aunty Mariya na ganin abinda ke faruwa ta kullo kofar kitchen din tana murmushi ta koma parlor ta zauna, Sai da yayi mata lilis ya farfasa mata duk jikinta da belt har bata iya motsin kirki tsabar dakuwa sannan ya duka yana kallonta cikin husky voice da idanuwansa da suka canza launi yace "Ko kallon banza ki sake yi mata a gidan nan ki ga" Daga haka ya tsallaketa ya nufi kofar kitchen da Mayraah ke kokarin budewa ya hanata, da sauri ta koma gefe ta basa waje gabanta na faduwa, ya bude kofar ya nuna mata waje yace "Fita mu je" Ba musu ta fita da sauri, shi ma ya fita ya kullo kofar.....



MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788 aji tsoron Allah a sauke hakkin marainiya😥 amma fa ba irin maraicin Badiyya ba🙄
[6/19, 12:43 AM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyya ce ke rusa kukan azaba ga bakinta yayi suntum tana biye da Hajja dake rike da hannunta suka nufi kofa, Mama Ladi ta ajiye kwanon abincin hannunta tace "O'o Hajja ba haka zaki ce ba, yaran nan fa duk daya suke a wajenki, ni wllh abinda yasa hankalina bai tashi ba saboda nasan ba wani can bare bane yayi mata wannan mugun bugu haka, ɗan uwanta ne na jini fa, zuciya ce kawai ta debesa yayi mata wannan aika aikan, kai har ma da sharrin shaidan don ni nasan ba haka yayi niyya ba" A mugun fusace Hajja dake huci tace "Babu abinda ta hada da shi banda uwarsa da take kanwar uwarta, don haka kar ki sake ce masa ɗan uwanta Ladi" Aunty Mariya dai na makale dakin baƙi tana jiyo duk abinda ake a parlon amma taki fitowa, Mama Ladi ta kyabe baki ta jawo kwanonta ta ci gaba da tsotsan ƙashin hannunta tace "To ke yanzu da kika figeta haka a ina za ku samu abun hawa da talatainin daren nan, wannan ai sai mai adaidaita sahun ya tsorata ya zata barauniya ce ta tsere daga hannun jami'an tsaro.... Wai anya ma Badiyya ce wannan ko dai kawai haukanmu muke, ya za ayi daga ɗan duka baki yayi suntum haka kamar leben rakumi?" Mama Ladi na kai wa nan ta tuntsire da dariya har da kwanciya tana kyakyatawa tace "Hajja duka ne fa an riga an nakada mata shi babu yanda muka iya sai dai muce Alhamdulillah, komai Allah yayi dai dai ne, kawai hakuri zaki yi idan Allah ya kai mu gobe da asuban fari sai ki ja ta ku tafi duk inda za ku amma yanzu dai ku rufa mana asiri don kuna fita idan Allah ya sa ku ka hadu da yan sanda cikin daren nan duk bayanin da zaki masu baza su gamsu ba, cewa za su yi sata taje tayi aka mata haka...." Cikin kuka Hajja ta katse ta tace "In kwana su karasa kasheta Ladi? In kwana saboda gidan ubana ne nan din ko kuma gidan ubanta? Ae wllh da dai ni da Badiyya mu kwana gidan nan gwara ko titi ne mun je mun yi shimfida mu kwanta, kuma ba laifin kowa bane laifina ne don dazu da safe da ta bukaci in bata makulli da na bata da duk haka bazai faru da Marainiyar nan ba, sannan da ace nayi tafiyata tun safe naje nayi abinda zai fi min alkhairi a gidana da hakan bai faru da Marainiyar ba, ko dabba baza ayi ma wannan dukan da aka mata ba, ki dubi jikinta fa duk a farfashe, dubi bakinta fa, kafarta kuwa da kyar idan bata yi targade ba, yanzu idan dangin ubanta suka ce sai sun dau mataki akan wannan abinda aka mata ni na isa in hanasu? Ko barawo dai baza ayi ma wannan tsinannen dukan na rashin imani ba balle ita da ba sata tayi ba ba kuma ɗan mutum ta kashe ba kawai tsabar zalunci da zuciyar kafirci yasa aka mata haka, kuma in dai burin mutane ne cin mutuncin maraya su walakantasa to wllh wllh baza su wanye lafiya da duniya ba, sannan ko ma wanene ya mata wnn aika aikan Allah ya isar mata cikin gaggawa, babu yafiya tsakanin ta da koma waye, ni ma kuma ba yafe masa zan yi ba tunda amanata ce ita" Ammi dake tsaye parlon ta kasa cewa komai sai hawaye, gaba daya jikinta yayi sanyi, she is soo speechless, Mama Ladi dai sai fama take da ƙashin hannunta tana lullumshe ido tana kallon Hajja, Hajja ta figi hannun Badiyya dake dingishi tana rusa kuka har sannan, za su fita daga parlon, Ammi tayi karfin halin bin su tace "Don girman Allah Hajja kiyi hakuri ki bari...." A fusace Hajja ta dakatar da ita tace "Ba abinda zaki ce min, inyi hakuri in bari a kasheta ki huta 'ya yanki su huta? kuma kije ki rungumi warce zaki runguma da ta fiye maki Badiyya tun asali dake da yaranki, ai tun ba yanxu ba dama kike nuna baki hada komai da Badiyya ba, ni kadai ce dolen Badiyya a duniyar nan tunda ni na haifi uwarta...." Mama Ladi ta buda baki tace "Kaji wata magana kuma, to wai ita Badiyyar er gwal ce da baza a doketa ba, ni wani irin duka ne ban sha a wajenki ba ina karama duk da bani da uwa bani da uba a lokacin, kin dubi maraicina da kike nakada min duka? yarinya munafuka kawai mara tsoron Allah kiyi ta daure mata kugu, wato dai duk wannan tsiyar da ta tafka so kika yi a zuba mata ido saboda ga ta munafukar Marainiya ko? To wai ma uban waye ba maraya ba a zamanin nan na yanzu, ni iyayen gareni? Bakina fa da nata na bata labarin yanda aka samo Mera da zuciya daya wllh, sae ga labari a duniya an kasa a faranti ana ta yawo da shi, to wani marayan arziki ne zai yi wannan mugun abu? A marayun ma Badiyya er iska ce kawai...." Hajja tace "Ke ma Allah ya isa wannan kazafin da kika mata Ladi, in sha Allahu sai Allah ya saka mata, za kuma ki gani a kwaryar ki" Mama Ladi ta kyabe baki ta koma ta ci gaba da taune ƙashinta tana hararan Badiyya, Hajja tace "Kuma ina ce dai saboda ni kika zo garin nan ko? To ki koma inda kika fito ba a bukatarki, bana son ma kice zaki kara zumunci da 'ya ya na, ni da na zame maki dole kiyi da ni amma ba 'ya yana ba...." Hajja na kai wa nan ta fice daga parlon tana rike da hannun Badiyya, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "To ko dai wiwi Badiyyar ta banka mata ne" Ammi dai ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna kan kujera tana kuka sosai, Mama Ladi tace "Ko ma dai waye yayi mata wannan jibgar Allah yayi masa albarka, kyau ace ma ya cire mata haƙora biyu na sama da na kasa ta dawo kamar mujiya...." Mayraah dai ta gaji da zaman parlon baƙi ga baccin da ta fara ji, she is been sitting for almost an hour now a parlon, ta kalli agogo dake nuna karfe goma da minti arba'in, sannan ta ɗan kalli inda yake kwance, waya yake amma duk da babu wani tazara tsakaninsu bata jin abinda yake cewa, she just notice he is on phone call, a hankali tace "Ina jin bacci Yaya" Ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike zaune ya katse wayar, after few seconds ya tashi, tana ganin haka ta tashi ita ma, ya nufi kofa ta bi bayansa, sai da ta fito parlon ya kashe Ac da wutan parlon sannan ya kulle kofar ya fara sauka porch din building din tana biye da shi, suna shiga main parlor din gidan suka tadda Ammi da Mama Ladi har sannan a parlor, ita dai Aunty Mariya daga karshe dama kwanciyar ta tayi a dakin baƙin ta fara bacci don bata da strength din fara lallashin Ammi, kallo daya yayi masu zai wuce sama fuskarsa a murtuke, Mama Ladi tayi saurin cewa "Yauwa Usuman don Allah nace gobe zaka kai ni gidan Mashir kasan ba dani aka je kai amaryarsa ba, daga shiga makota in fito na tarar wai an tafi kai amarya, kaga Mashir ae bazai ji dadi ba ace ban je ba ko? To ina gudun kar ya kullace ni shi sa gobe da sassafe zaka kai ni gidan" Usman yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya wuce sama, Ammi ta bi sa da wani kallo shi kam yaki kallon ma inda take dama, Mama Ladi tace "Kya wani bi sa da harara, me yayi maki? Ance maki kowa ne baya son gaskiya kamar ke da uwarki?" Mayraah ta juya a hankali ta tafi kitchen don sake dafa ma Ammi shayin da take dafa mata dazu.
Ammi na zaune Bedroom dinta da safe, waya ne kare a kunnenta cikin sanyin murya tace "Wallahi ban yi wani baccin kirki ba jiya" Daga daya bangaren Maheer yace "Pls ki kwantar da hankalin ki Ammi, in sha Allah zuwa anjima zan je can gidan nata, ke ba sai kinje ba tunda ranta ya baci haka" Da damuwa Ammi tace "Amma shi Usman bai duba halin da nake ciki ba ya kara dauko min wannan maganar bayan yasan halin Hajja? Me yasa bazai yi considering din condition dina ba?" Maheer yace "To kika san abinda tayi masa, ke dai kawai ki bar zancen, shi da ba shiga harkanta yake ba kika ga yayi mata haka ai kinsan dole da abinda tayi masa" Ammi tace "Ya wuce wannan abinda tayi a kan auren Mayraah? Bayan shi ai ba wani abu da ya hadata da shi na ga, burinsa kawai ya ga ya janyo min magana, shekarun baya haka yarinyar nan ta nuna tana sonsa ita in ba shi ba bazata yi aure ba, amma duk irin lallaba Usman da nayi daga karshe ai kaga abinda yayi mana gaba daya, shi yasa har yanzu Hajja ke kullace da shi ba kuma fita ranta abun yayi ba don har gobe cewa take saboda Usman taki tsayar da miji, sannan kwanaki kiri kiri ya daukota a motarsa ya ki, babu abinda Hajja ta manta bata gaya min a waya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login