Showing 42001 words to 45000 words out of 249515 words

Chapter 15 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1520

don tun asali baka bi ka'idar da ya kamata ka bi ba while giving out the girls hand in marriage tunda kasan da wnn babban issue din a kasa, in other words an yaudaremu an kuma yi playing with our intelligence an mayar damu kananun mutane, sannan an cuci ɗan mu, a lamari na aure babu amfanin shigowa da rashin gaskiya cikinta saboda gudun abinda zai je ya dawo, domin haka muke son sanar da kai cewa a yanzu mun janye daga wannan auren da muka nema ma ɗan mu ake kokarin daura sa gobe, sadakinmu da duk wani abu da aka kawo gidan nan za mu aiko a amsar mana in sha Allah, gatan da ko wani uba zai yi ma ɗan sa kenan a issue irin wannan, mun bar ka lafiya Alhaji" Abba was speechless, har duk suka mike suka fara fita daga parlon, Maheer da gaba daya ya dinga jin maganganun Uncle din Musharraf kamar a mafarki yayi saurin daukan takardun da Abba ya ajiye a gefensa yana dubasu daya bayan daya, kallon Abba yayi, lkci daya ya duka nan gabansa hankali a tashe yace "Abba ban gane ba, what is all this? Me yake faruwa??" Abba ya kasa ce masa komai don yayi nisa tunanin da ya tafi, Maheer that is getting impatient don har wani zafi yake ji duk da AC dake kunne parlon yace "Don Allah kace min wani abu Abba, i am loosing my self, I can't stand this anymore, me ke faruwa?" Abba ya sauke ido ya kallesa, bayan few seconds ya fara magana Calmly yace "Haka ne.... Mayraah isn't my biological daughter Maheer, ba ni da Ammi muka haifi Mayraah ba, bamu san ta yaya ma aka sameta ba, mu dai kawai...." Kasa ci gaba Abba yayi, Maheer that was dumbfounded and shock ya dinga kallon Abba kamar ranan ya fara ganinsa it felt like mafarki yake kawai, bayan shirun kusan minti uku tsakaninsu, Maheer yayi karfin halin mikewa with breaking voice yace "Ni da Usman kuma su waye iyayenmu? If Mayraah isn't ur child then mu ma ba yaranku bane" Yana kai wa nan ya fice daga parlon Abba ya kasa ce masa komai...
Mayraah ta mike zaune tana kallonsu Hamida dake ta harkan gabansu a dakinta, waya ne kare kunnenta suna magana da Musharraf da ya kirata ko minti biyu ba ayi ba yanzu, a hankali tace "I will call u back, i am not alone" tana fadin haka ta katse wayar ta fita zuwa corridor din dakunan, sake dialing numbersa tayi yana dagawa ta marairaice tace "But sir kasan bazan iya fitowa yanzu ba ai, they are people everywhere a gidan, i will be noticed idan zan fita" Musharraf yace "Plss Mayraah find a way da zaki samu ki fito it's urgent plss" She couldn't resist because of the urge in his voice, cike da damuwa tace "But are you okay sir?" Yace "No i am not" Tace "Ohk, yanzu kana farkon shigowa layinmu kace?" Yace "Eh" Tace "Toh i will be coming right away" Katse wayar tayi ta fara tunanin ta yaya zata fita gidan nan without being noticed, daga karshe dai she successfully found her self outside ba tare da an lura ita bace don Nikab ta saka, ko su Hamida basu son ta fita daga gidan ba, inda yace mata yayi parking ta nufa, taga Motarsa ta karasa ta bude front seat din ta shiga tana kallonsa da damuwa, kafin ta ce komai taga ya fara driving motar, da mamaki tace "Sir ina kuma za mu je?"


Payments before end of free pages, to avoid going for break...

07087865788✍🏻

WhatsApp only, no phone calls pls
[6/6, 4:38 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖


_By khaleesat Haiydar_✍🏻



Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga one and only Maman Khadee me sabon kasuwar dutse😁 (Aunty Zahrah) da Er ta Deejah me lamurje a ɗa kafin ta fara siyar da namijin goro yanzu, sai kuma me cikin shekara uku da taki haihuwa har yau har gobe (Matar Babana Ummu Nabila🙄) khaleesat Haiydar na maku fatan alkhairi a ko da yaushe😁

This page goes to you Zainurah Yazeed Ahmad, u are one of the die hard fan i am opportune to meet, Allah Ubangiji ya raya maki zuri'a, and i do appreciate u now and always dear, Allah ya biya maki bukatunki na alkhairi....
Sauran fans da suka yi patronizing dina even before in gama free pages wllh i really appreciate u people, ina maku fatan alkhairi duniya da lahira, Allah ya raya maku zuri'a, ya kara ma iyayenku lafiya da tsawon rai me amfani, Ameen.




12....


Mami was speechless, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi, banda kallon Alhaji Mansur babu abinda take, Alhaji Mansur ya ci gaba yace "Don haka mun sanar masa za aje karbo mana duk wani kaya da aka kai gidan da sunan aure, kudin da muka kai kuma Faisal zai koma ya amso su" Mami ta girgiza kai cike da damuwa tace "Ba sai an amso komai ba Alhaji, mu bar masu ko don...." Ya wani hade rai ya dakatar da ita a fusace yana kallonta yace "Akan me zaki ce ba sai an amso komai ba? Mu bar masu saboda muna tsoronsu? Mutanen da basu san mutunci ba, mutanen da suka yaudaremu suka maida mu yan iska, ai basu cancanci ko tsinke a bar masu ba wlh, komai sai sun fito da shi idan ba haka ba hukuma ta rabamu da su" Mami dake masa wani kallo ta kasa jurewa tace "Ku ko ina sai kun nuna wannan halin naku na karanta? Idan shi wanda ya siya kayayyakin da kudinsa yace a bar masu fa?" Alhaji Mansur ya mike yace "Shi wanda ya siya kayan ya ci kaza kazansa, ai ba shi ke da iko da kansa ba, Kuma wallahi wallahi kin ji rantsuwan musulmi ko? To sai an amso kayan nan gaba daya, yanzun nan za a tura su Halima tunda dama su suka kai, don haka su za su koma su amso, aikin banza kawai" Yana kai wa nan ya fice daga parlon yana muzurai, tashin hankalin Mami ya kashi biyu yanzu ta ma rasa wani tunanin zata yi in particular, babban damuwarta na farko Musharraf, she don't know how he will take this and cope don ta ga yana son yarinyar, na biyu kuma ita a rayuwarta bata son taga an ci ma mutum mutunci, she detest that, babu tantama tasan an tara jama'a gidansu yarinyar nan, a haka su Halima za su je su gwada halinsu na rashin tarbiyya da rashin mutunci cikin taron jama'a, mikewa tayi ta dauko wayarta tayi dialing din number Alhaji Saminu wanda shine babba a family din and he resides in kaduna, kuma duk suna shakkarsa suna jin maganarsa, yana picking bayan sun gaisa ta fara masa bayanin abinda ke faruwa, ya katse ta yace "Duk na san da batun nan an kirani an gaya min komai, ashe kananun mutane ne makaryata, kinga kuma baza mu bari ɗan mu ya auro warce bata da asali ba, dama an san su waye iyayen nata ne to da sauki, kinga kuwa ai baza mu yarda a kawo mana irin wannan cikin zuri'ar mu ba" A hankali Mami tace "Haka ne, amma yanzu Alhaji Mansur ya bar nan wai za a tura su Hajiya Halima su je can gidansu yarinyar su amso kayan aure da aka kai, ni kuma naga hakan bai kamata ba tunda nasan wacece Hajiya Halima nasan kuma me zata je ta aikata a gidan, kasan cin mutunci bashi da dadi Alhaji" Alhaji Saminu yace "Shikenan shi Faisal da zai koma amso kudin auren sai ya karbo har akwatunan, zan kirasu in sanar masu kada a tura kowa in ba shi Faisal din ba" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, Mami ta ɗan ji hankalinta ya kwanta don baza ta so a walakanta kowa ba a kan Musharraf, kara kiran layin Musharraf tayi for the countless time amma still a kashe, she felt so disturb and worried for him, ta zauna saman kujera ta dafe kanta.... Ammi ta kasa nutsuwa tun bayan da ta shigo parlon baƙi ta dalilin kiran da Abba yayi mata a waya, Abba ya bi ta da ido har ta nemi waje ta zauna tana kallonsa ita ma, da kyar tayi karfin halin cewa "Lafiya dai ko Yallabai?" Abba ya kasa ce mata komai ya dauke idonsa daga kallonta, nan taji hankalinta yayi mugun tashi don kana ganin Abba kasan he is not himself, Ammi ta kasa jurewa tace "Don Allah ka gaya min abinda yake faruwa Yallabai ko yaron cewa yayi ya fasa auren ne??" Abba ya kasa bata amsa don a duniya baya son duk wani abu da zai daga mata hankali sanin condition dinta, but he have no choice dole zata sani, Ganin yanda Ammi ta rikice masa yayi ta maza yace "Haka ne" Ammi was shock, ta dinga kallon Abba ko kiftawa babu, lokaci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Kana nufin ya fasa auren?" Abba ya gyada mata kai, Ta fashe da kuka tace "Meye dalilinsu Yallabai? Sai ana gobe daurin aure an tara jama'a za su zo yau su ce sun fasa, me aka masu haka?" Kuka take sosai tana kallon Abba da ya kasa cewa komai don zuciyarsa ya gama karaya, he is just trying his possible best to be stable, yasan in dai ya sanar ma Ammi dalilin fasa auren nan sai ta fadi kasa yanzu, she won't be able to take it ya sani... Abba ya dake yace "Ya isa haka Hajara, dama Allah ya riga ya rubuta Mayraah ba matar yaron nan bace, shi yasa kika ga hakan ya faru ana gobe daurin auren, kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, duk abinda Allah yayi mana dai dai ne kada mu masa butulci, sai dai bana son ki sanar ma kowa an fasa auren nan tukunna" Cikin kuka sosai Ammi tace "To me ya rage yallabai, gobe ne fa auren? Meye amfanin boye boye, ba gwara a sanar ma kowa ya kama gabansa ba? babban damuwata halin da Mayraah zata shiga idan ta samu wannan mummunan labarin don ban ga alamar ta sani ba..." Ammi ta kasa controlling kanta a parlon sai kuka take kamar ranta zai fita, Jikin Abba ya kara sanyi, he wish yaron nan bai sanar ma Mayraah ya fasa auren ba da kuma dalilinsa na fasawar don duk abu da ya taɓa Mayraah yasan shi ya taɓa, shi kansa bai san irin son da yake ma Mayraah ba, bai taɓa mata kallon ba shi ya haifeta ba, Abba yayi kasa da murya yace "Na dai ce maki kar ki ce ma kowa komai, kuma kin manta daurin auren biyu ne? Ai akwai na Maheer, so for now kiyi shiru don Allah, and pls ki kwantar da hankalinki ki koma ki ci gaba da sabgogin ki" Sai da Ammi ta ci kukanta na kusan minti biyar a parlon sannan ta share hawayenta ta mike a hankali ta fita a sanyaye, Abba da gaba daya tunaninsa ya dagule ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ransa, waye wannan da yasan da batun ba su suka haifi Mayraah ba har ya je ya sanar ma family din Musharraf?? Waye yayi wannan danyen aikin, baya tunanin zai taɓa yafe ma kowa waye wannan, da zai san waye sai ya sa an dauresa even if da last card dinsa ne, asalin Mayraah abu ne wanda su kansu are still very surprise ta yanda suka ajiyesa babban sirri a zuciyoyinsu for almost 22 years now, ko da wasa basa tada zancen tsakaninsa da Ammi, sai dai in ya siya kaddara da sunan Mayraah ya bata ta ajiye sai yaga mood dinta ya canza don hakan na tuno mata da cewar ba fa su suka haifi Mayraah ba sannan Mayraah bata da gadonsu, ita ce ma ta kawo masa shawaran dinga siyan property da sunanta tun yarinyar na shekara sha biyu, duk sanda kuma Abba yayi hakan takan kwana ta yini cikin damuwa a zuciyarta ranan, ya san duk son da yake ma Mayraah bai kama kafar na Ammi ba, don Ammi ta dauki son duniya ta daura mata, yanda ta saka Mayraah a rai ko su Maheer bata saka haka ba, kawai Allah yayi Mayraah bazata sangarce ba saboda su Maheer da Usman da basu bada space din haka ba especially Usman that was so strict on her, Abba ya kasa ci gaba da zama ya mike ya dinga safa da marwa a parlon, shi dai yasan a garin Kano babu wanda yasan da cewar Mayraah isn't their Biological daughter, a takaice ma bayan shi, Ammi, Hajja, sai iyayensa kafin rasuwarsu, sai kilan ko Aunty Mariya babu wanda yasan da wannan secret din, ko da kuwa cikin abokansa da yan uwansa maza, Ammi ma yasan hatta kawayenta basu san ba ita ta haifi Mayraah ba, Abba ya kusa minti sha biyar yana zaga parlon, bai taɓa shiga damuwa da rudanin da ya shiga a wannan moment din ba, abu ne da ya zo unexpected kamar daga sama, Daga karshe ya dau wayarsa yayi dialing number Maheer, sai da ya kusa katsewa Maheer ya daga, amma bai ce komai ba, Abba yace "Kayi hakuri ka dawo mu yi magana Maheer, we need to talk pls" Abba bai jira jin me Maheer zai ce ba ya katse wayar, komawa yayi ya zauna yana ta sake sake a ransa har Maheer ya shigo parlon, Abba ya bi sa da kallo ganin yanda duk ya dawo wani iri a cikin ɗan kankanin lokaci, har ya samu far end of the parlor ya duka kasa ba tare da ya bari sun hada ido da Abban ba, Abba felt so guilty a moment din nan, in ma basu gaya ma kowa ba bayan wasu shekaru da suka ga Maheer ya mallaki hankalin kansa ai da shi sun sanar masa basu boye masa ba, Abba ya ma rasa ta inda zai fara, Shi dai Maheer ya sunkuyar da kansa bai yarda ya kalli Abba ba, kana ganinsa kasan ya shiga damuwa sosai ba kadan, it's something that hit him so hard kamar a mafarki, Abba yayi kasa da murya yace "Ina son ka fahimce mu Maheer, mun yi abinda muka yi ne for the Sanity of Mayraah, muna son ta taso like every other child cikin so da kauna, ta yaya za a so yarinya kamarta ta taso da damuwar ba mu ne iyayenta ba? How will she cope with that? Sannan wllh mu kan mance ba mu muka haifeta ba tsabar yanda muka dauketa...." Shi dai Maheer bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba, Abba ya ci gaba yac "Maheer ban kiraka a yanxu don gaya maka yanda muka samu Mayraah ba, duk da nasan dole a yau ko gobe kowa zai san wacece *MAYRAAH* kuma ya aka yi ta shigo rayuwarmu har muka ga gwara mu boye ma jama'a, don yanzu babu wani batun boye boye kuma, amma Maheer ina son ka sa a ranka Mayraah isn't ur Biological sister, er uwarka ce kawai ita in islam, baya nan babu wani alaka ta jini tsakanin ku, kuma ka sani cewar da aure tsakaninku...." Maheer ya daga kai da sauri ya kalli Abba jin furucinsa na karshe, bai san sanda ya mike ba yana girgiza kai yace "Abba har abada babu aure tsakanina da Mayraah, kuma har gobe zan ci gaba da yi mata kallon kanwata ta jini ne warce muka fito ciki daya, bayan wannan bazan yi ma Mayraah wani kallo ba, she still remains my blood" Shiru Abba yayi yana kallonsa don gaba daya ya gama discouraging dinsa akan abinda ke zuciyarsa, bayan few seconds Abba ya sauke kansa kasa yace "Haka ne, And i am happy u said this..." Maheer yace "Kuma tunda aka fasa aurenta nima a daga nawa kawai, dan i won't have the rest of mind of getting married tomorrow bayan damuwar da nasan kanwata zata shiga" Abba ya girgiza kai yace "Baza a daga naka ba, in sha Allah gobe ne daurin auren ka babu fashi"
Aunty Mariya ta dinga salati a rikice a dakin Ammi bayan Ammi ta kirata ta sanar mata abinda ke faruwa, Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a saboda wani dalili yace ya fasa? Mun shiga uku" Cikin kuka Ammi tace "Ni dai kawai Alhaji ce min yayi an fasa amma ban san dalili ba" Aunty Mariya da har hawaye ya cika idonta tace "Da kyar in ba yan uwan nan nasa da suka kawo lefe ne suka lalata auren nan ba, kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu ta ina za a fara Ammi? Ina Mayraah din, anya ma ta san abinda ke faruwa kuwa?" Hankalin Ammi ya kara mugun tashi da ta tuna Mayraah, ta yaya zata dau wannan lamari, Ammi ta kalli Aunty Mariya cikin kuka tace "Ban san ko ya gaya mata ba, amma dai sun cutar min 'ya ta, kuma Allah ya saka mata" Aunty Mariya ta share hawayen dake sauka nata idon ta mike ta fita daga dakin, can dakin Mayraah ta tafi ta bude kofar, ganin su Hamidah kadai ne a dakin tace "Ina Mayraah?" Hamidah tace "Kilan tana dakin Yaya Maheer, waya take yi ta fita saboda hayaniya" Aunty Mariya da jikinta yayi sanyi ta juya ta bar bakin kofar, dakin Maheer ta tafi, ta gansa shi kadai a dakin nasa zaune gefen gado ya dafe kai, Aunty Mariya ta karasa cikin dakin ta kulle kofar cikin damuwa sosai tace "Maheer amma me yasa suka ce sun fasa? Wani laifin aka masu ne?" Ya dago kansa yana kallon Aunty Mariya da idanuwansa da suka kada sosai yace "Aunty...." Sai kuma yayi shiru, Aunty Mariya dai ta kasa cewa komai ita ma duk zuciyarta ya karaya, Cike da karfin hali Maheer ya ci gaba yace "Aunty wacece Mayraah?" Sosai gaban Aunty Mariya ya fadi, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, and u can see the shock a fuskarta, Bakinta na rawa tace "Ban gane ba Maheer, wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login