Showing 222001 words to 225000 words out of 249515 words

Chapter 75 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

2368

na so ki ba da wani nufi ba, i resigned lecturing few weeks back, lecturing caused me all what i am going through now, i regret it, assuming a asibiti nake aiki may be sau daya zan ganki ki tafi shikenan ba lallai ki sake dawowa in ganki ba, amma as a lecturer, seeing you everyday made me fell in love with you without me realizing that, i never bargained for all this Mayraah, i am still yet to recover fully from the death of my father and only sister, then all of a sudden you...." Kasa ci gaba yayi, nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah jikinta yayi sanyi sosai ta kasa ce masa komai, ya katse wayar kawai, ta fashe da kuka, har ranta tasan she still loves Musharraf but su Abba baza su bari ta auresa ba, likewise his parent baza su bari ya aureta ba, kwanciya tayi tana kukan tausayin kanta. Wajen karfe hudu Maheer ya kirata, ta daga wayar tayi shiru, yace "Can i come over now?" A hankali tace "Yaya can i leave it tomorrow pls" Da mamaki yace "Why tomorrow?" Ta mike zaune tana dafe kanta dake mata ciwo tace "Kawai naji ina son in bari sai gobe da safe, ban san me yasa ba" Maheer yace "But are you okay?" Ta gyada masa kai tace "Ehh but deep down i want to leave tomorrow instead of today" Yace "Ohk then, zan gaya ma Ammi" Da sauri tace "How will you tell her?" Yace "Don't worry Mimi, zan ce mata ban baro asibiti da wuri ba" Tace "Yauwa yaya" Yace "Bacci kika yi ne?" Tace "Yanzu na tashi" Yace "Ohk, to bari in yi sallah it's almost time" Tace "Toh sai Anjima" Daga haka ya katse wayar ita ma ta mike ta shiga bandaki. Tana idar da sallah ta sake dialing number Musharraf, yana ta ring har ta fidda ran zai daga sai gashi ya daga, a hankali tace "When are you coming back?" Yace "To where?" Tace "Gidanka" Yace "I am home ae" tace "Naga ka fita dazu around 11:30" ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "How?" Tace "In ur white car, u were on either black or navy Blue polo" Musharraf that was very surprise yace "Wait! How did you know?" Tayi murmushi cikin sanyin murya tace "That shows i am with you now and always" Musharraf yayi shiru, can yace "I believe kin zo anguwan ne" Tace "Not at all" Yayi kasa murya yace "Pls Mayraah, for the sake of the love i have for you tell me where are you now? Ina kika tafi" Tace "Ina Miller road" Musharraf yace "Miller road? I don't understand" Tace "Yea" Yace "Wajen wa?" Tace "My aunt" Yace "But i am not too far from Miller, just few streets away" A hankali tace "I know" A bit confused yace "But which of ur aunt?" Tace "Baka san ta ba" Musharraf yace "Don Allah in da gaske kike send me the house address, don Allah ba don ni ba, don't play with my feelings Mayraah" Ta ɗan yi murmushi tace "I will send u the address" Daga haka ta katse wayar ta masa fowarding address da ta tura ma Dr Khalil jiya, tana tura masa ya kirata yace "Don girman Allah da gaske kike Mayraah" Tace "Toh shikenan" Yace "Ohk, ok i am on my way now, right away" Daga haka taji ya kashe wayar, nan gabanta ya fara faduwa, to wa zata ce ma Hajiya Amina zai zo, what if yana zuwa Maheer ko Usman suka zo fa, ko kuma Abba ya dawo, ya zata yi? wannan tunanin yasa taji hankalinta ya tashi sosai, tasan babu wani nisa daga gidansa zuwa nan, ta mike da sauri ta tafi ta samu Hajiya Amina, Hajiya Amina tace "What will u be making for dinner?" Mayraah tace "Akwai sauran abincin Aunty" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Sunkuyar da kai Mayraah tayi tace "Dama Aunty wani coursemate dina ne..." Sai kuma tayi shiru, Hajiya Amina tace "Feel free" Mayraah tace "Yana nan anguwan ne, zai zo mu gaisa" Hajiya Amina tace "It's okay, sai ki shigo da shi parlor ku gaisa ba komai" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa za mu zauna a compound" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Mayraah har ta juya sai kuma ta sake dawowa tace "Aunty ai Abba bazai dawo ba yau ko?" Hajiya Amina tayi murmushi tace "Bazai dawo ba, kar ki damu" Mayraah ta juya ta fita daga parlon, tana komawa dakinta taga miss calls din Musharraf har 4, Hijab ta sa ta sauka downstairs, tana isa gate bayan mai gadi ya bude mata ta gansa tsaye jikin motarsa, kallonta yake babu ko kiftawa kamar yanda ita ma take kallonsa, she just can't explain how she felt seeing him at the same time sai taga ya rame, kana ganinsa kasan ba shi da rest of mind, tayi karfin halin cewa "Ka shigo" Ya nufota har sannan yana kallonta, ta juya ta koma cikin gidan, wajen shan iska ta tafi yana biye da ita ta zauna, shi ma ya zauna yana facing dinta, a sanyaye tace "Good evening sir" kasa amsawa yayi ya dafe kansa, ta sauke idonta tana goge hawayen da ya fara taruwa da yatsunta, cikin rawan murya tace "Kayi hakuri, this our destiny" Yace "What is our destiny Mayraah?" Ta daga kai ta kallesa tace "Allah bai rubuta za mu yi aure yanzu ba" Yace "Sai yaushe?" Tayi karfin halin cewa "May be years to come, in dai da rabon za mu yi aure babu wani abu da zai hana hakan amma a yanzu kam ban ga alaman za mu yi ba" Yana gyada kai yace "Sai yanzu na sake tabbatar da baki so na Mayraah, i now believe ni ne kawai nake son ki, ni ne kawai nake bata lokacina" Ta fashe da kuka tace "Saboda me zaka ce haka? Iyayenka baza su yarda ka aureni ba, nima iyayena baza su yarda in aureka ba bayan duk abubuwan nan da suka faru a dalilin wedding dinmu that never occurred, and ah baya da nake tunanin zan iya bin ka mu tafi mu yi aurenmu a wani waje may be ban zauna nayi tunani da kyau bane a kan hakan, i get to understand that it's the biggest mistake da ni da kai za mu yi making idan mun yi hakan, aure babu albarkan iyayenmu bazai mana lasting ba, daga karshe duk za mu zo muna da na sani ne, but keep in mind sir, you still remain my first love, a kanka na fara soyayya akan ka nasan menene so ina alfahari da hakan, sannan kayi min so na tsakani da Allah, kayi min so na aure, kuma har gobe bazan taɓa daina sonka ba sai ma sonka ya karu a zuciyata, kawai mu jira lokaci Sir, ina ji a jikina we are meant for each other kuma za mu yi aure amma ba yanzu ba, may be sai a gaba ta yanda bamu yi zato ba, but for now let act just like frnds mu ci gaba da zumuncinmu da communication don mu samu sauki a ranmu...." Ya ɗan yi murmushi ya mike, a hankali yana kallonta yace "Thank you Mayraah" kallonsa kawai take ganin yanda idonsa ya kada, ya juya ya nufi gate, mikewa tayi da sauri tace "Sir..." Ko waiwayowa bai yi ba har ya isa gate din ya bude ya fita, wasu hawaye ne suka dinga sauka idonta ta koma ta zauna ta hade kanta da table tana kuka a hankali..... Ammi na zaune parlon Abba tana xuba masa abinci bayan magrib, bayan ya kunna TV yace "Mayraan bata dawo ba yau ne?" Ammi tace "Maheer din yace bai baro asibiti da wuri ba sai gobe" Yace "Ohk..." Bayan ta gama zuba masa zata fita ya bi ta da kallo yace "Za mu yi magana ne idan na gama" Tace "Ka kirani in ka gama" Daga haka ta fita daga Parlon, duk kwanan nan ko zama part din nasa bata son yi unlike before, iyaka ta shigo ta basa abinci ta koma bangarenta, ko kwana ta daina yi a part din, yana gama cin abincin ya kirata, bayan ta dawo parlon ta zauna, yace "Duk kwanan nan ina lura kin maida bangaren nan baƙon ki" ta wani hade rai tace "Don Allah bana son wannan maganar... In wata magana ce ka min amma ba wannan ba" Ya ɗan yi murmushi yace "Ohk" Ajiye ruwan hannunsa yayi yana kallonta, bayan few seconds yace "Akan Usman ne...." Ammi ta maida hankali kansa tana sauraronsa, cikin few minutes Abba ya gaya mata maganar da Usman ya samesa da shi, Ammi sai kallon Abba take without blinking, can ta girgiza kai tace "I will prefer Maheer, don ya fi sa sanyin hali da sanin ya kamata, kuma nayi magana da shi akan hakan few days back, don haka ka bar maganar Usman" Abba dake ta kallonta da mamaki yace "But Usman showed interest first, saboda me za ki ce Maheer? Saboda me zan bar maganar Usman?" Ammi tace "Eh Maheer nace, saboda duk nasan halinsu ai, ita ma kuma nasan halinta da wanda zai iya hakuri da ita, ya kuma fi sanin ciwonta...." Abba yace "To tunda haka ne duk a bar zancen, daga Usman din har Maheer nayi cancelling maganar, tunda naga abun naki kamar son kai ne" Ammi tace "Babu batun son kai, future din yarinyata nake dubawa da inda zata samu kwanciyar hankali... Kuma duk yaran nan dai naga nawa ne babu wanda zai ce ya fini sanin halinsu gaba daya su ukun, kuma kayi hakuri zance dai baza a bar shi ba Yallabai, dama Maheer din ba wai yayi dacen mata bane, Mayraah kuma zata fi dacewa da shi don ina ga ko ni ban san halinta yanda Maheer ya sani ba" Mikewa Abba yayi ya bar mata parlon ya shige daki don baya son biye ta, ta kwashe warmer din abincin ta fita ita ma. Karfe tara na safe Mayraah ta sakko downstairs da jakarta, Hajiya Amina dake ta kallonta tace "Ko dai baki jin dadi ne, tun jiya naga you are not ur self, is anything wrong?" Mayraah tayi murmushin karfin hali tace "Ba komai Aunty, ciwon kai ne amma yayi sauki yau da safe" Hajiya Amina tace "Maheer din na waje ne" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina ta dau ledan dake gefenta ta mika mata tace "Ga su nan turarruka ne, though they are not much" Mayraah ta risina ta amsa tace "Nagode Aunty" Hajiya Amina tayi mata murmushi tace "You are welcome, ki gaida Amminku da Mama" Mayraah tace "To za su ji in sha Allah" Daga haka ta nufi kofa ta fita, tana isowa kofar gida ta tadda Maheer a mota, ta karasa ta bude front seat ta zauna tana kallonsa tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" A hankali tace "Yaya baza ka shiga ka gaisheta ba" Ya ɗan yi murmushi yace "Kin ga na makara, sai naje nayi dropping dinki sannan in tafi aiki" Mayraah tace "Just 2 minutes fa is enough yaya, kuma tasan kai ne ka zo daukata" Yace "Ohk i will do that next time in sha Allah" Bude motar tayi ta sauka tace "Ni dai sauko kaje ka gaisheta sai ka fito mu tafi" Shiru yayi yana kallonta, can ya kashe motar ya bude ya sauka ya zagayo, tana murmushi tace "Yauwa ko kai fa" Hancinta ya ja sannan ya shiga cikin gidan ta bi bayansa, har sannan Hajiya Amina tana zaune parlor tana kallo, Maheer ya karasa ciki bayan ta amsa sallamarsa, ya zauna sannan ya gaisheta ta amsa da fara'a tace "Ya aikin Dr" Yace "Alhmdlh" Tace "To maa sha Allah, ya su Ammi da Mama" Yace "Suna nan lafiya" Ta mike tace "Bari a hado maka breakfast" Yace "Aa i am okay, aiki zan tafi" Daga haka ya mike, Tace "Toh shikenan, Nagode kwarai, Allah ya tsare" Yace "Ameen" har balcony ta rakasa ya mata godiya ya sauka, Mayraah dake zaune inda ake shan iska ta mike ganin ya fito, ta jira har ya karaso inda take suka fita gate din a tare, suna barin anguwan tana kallonsa tace "Yaya" Ya juya ya kalleta sannan ya ci gaba da driving dinsa yace "Mimi" a hankali tace "You know what?" Yace "No Mimi" Tace "Kwanan nan naga u are somehow, is there anything wrong? You are not longer lively like before, baka magana sosai, you are always silent, why is that?" Maheer ya kalleta yace "Ba komai, i will be fine in sha Allah, stress din aiki ne" Mayraah tace "Ko har da na matarka?" Ya girgiza kai yace "Not at all, ai bana shiga harkanta, i have nothing to do with her, i am just waiting for time" Mayraah tace "To koma menene yasa kake zama silent kayi hakuri ka ji" Yayi murmushi yace "You are funny Mimi, ba komai kawai yanayin aiki ne" Murmushin tayi ita ma duk da nata damuwar da yayi mata yawa a zuciya ɗon ko baccin kirki bata yi ba jiya saboda tunanin Musharraf amma tun dawowarta gida bata jin dadin yanda ta lura Maheer bai cika son magana ba unlike before, she missed the old him, a haka har suka iso gida wanda in da ne ko bata basa labari ba shi zai dinga bata har su isa inda za su, bayan yayi parking kofar gida ta juya tana kallonsa tace "Take care of ur self" Yace "Toh Mimi" Bude motar tayi ta sauka ta dau jakarta a back seat sannan ta shiga cikin gidan, yayi reverse ya bar anguwan.
Abba na zaune parlon Ammi tare da Usman da Maheer, sai Ammi da Mama Ladi dake parlon su ma, Mayraah ce ta shigo karshe bayan Mama Ladi taje ta kirata a wajen Badiyyah, Mayraah ta zauna kasa kusa da Ammi wondering why she saw everyone sitted kamar ana meeting, Mama Ladi tace "To kai yanzu Mamuda a ina ka taɓa jin an bar ya mace tayi aiki? Ni dai tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin haka ba gaskiya, kyan ya mace ai dakin mijinta, sannan kace Habuja kana nufin mu sake sakinta kamar akuya ta koma Habujan kenan, abinda fa hankali zai dauka shi ake yi Mamuda, ya mace take faa" Maheer dake ta kallon Mama Ladi yace "Wa yace maki mace bata aiki?" Mama Ladi tace "Aa ba ruwana, ba a pamilyn mu ba wallahi, yanzu duk abun magana ai kamata yayi mu gujesa, har yanzu fa bamu gama farfadowa daga bakin fentin da Badiyyah ta goga ma pamilyn mu ba, in ku kun farfado ni ban farfado ba wllhi, tunda gashi har yau bana iya fita sai ina boye fuska kar a danganta ni da Badiyyah" Shi dai Usman bai ce komai ba, Ammi ma tayi shiru amma kana ganin mood dinta kasan batun aikin bai mata dadi ba ko kadan duk da Maheer ya mata maganar jiya, Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk abinda kika fada gaskiya ne Mama, amma dama ai baza ta fara aiki haka kawai bata da kowa a garin Abuja ba, duk sai da na gama tsarina da Usman sannan na tara ku a nan...." Ammi ta daga kai tana kallon Abba, Abba ya ci gaba yace "Babban asibiti ne kuma sananne a Nigeria, ba kowa ake bama aiki a asibitin ba, na taɓa wani aboki likita yayi aiki a asibitin shi ma kafin ya koma kasar waje, shi yasa naji bazan bari damar nan ta subuce ma Mayraah ba...." Mama Ladi tace "Naga abinda ya isheni, to me zata yi da aiki? Ba ci ta rasa ba, ba sutura ba, ba komai ba" Abba yace "Aa zata yi aikinta in sha Allah...." Mama Ladi tace "Toh aure fa? Kana ta maganar aiki kamar wasu kafurai, haka za mu sa ta gaba sai ta tsofe a gida mu shiga uku Mamuda, aure fa shine martabar ya mace ina tunatar da kai" Abba yace "Aure ai lokaci ne Mama, wuyarta lokacin ya iso za ayi, aiki kuma baya hana aure, mutane da yawa na neman aikin basu samu ba" Mama Ladi ta kyabe baki tana girgiza kafa alamar ita fa batun aikin bai gamsar da ita ba, Abba yace "Saboda haka na yanke shawaran Amminta zata koma Abuja da zama gaba daya, don har na siya gida a can an zuba komai, tarewa kawai ya rage, tun da idan nace a fara ginin filina dake can din zai iya daukar lokaci kuma Mayraah zata yi resuming aiki next week" Mama Ladi dake gwalo ido tace "Ka siya sabon gida a Habuja Mamuda?" Kabbara Mama Ladi ta saki cike da farin ciki sannan tace "Alhamdulillahi, dama ance mahakurci mawadaci, shikenan Ammi zata koma er Habuja duk me son ganinta sai ya shirya nan kuwa ko wani kare da doki shigowa yake, dama Allah na tuba anguwan nan in ba dole ba me mutum zai yi da shi duk ɗoyin ƙwata, duk lungun da ka bi warin ƙwata, kai maa sha Allah amma nayi farin ciki da wannan labarin kuma ka kyauta Mamuda" Abba ya ciro wayarsa dake ringing yayi picking call din abokinsa, Mama Ladi da farin cikinta ya kasa boyuwa ta mike ta lallaba ta tafi kusa da Maheer tace "Mashir a ina zaka samo min wani akwatin wallahi na gaji da wannan dama" Maheer yayi murmushi yace "Usman ne yasan inda ake siyarwa" Zata koma gun Usman taga Abba ya gama wayar da yake ta koma da sauri ta zauna tana washe baki, Abba ya ajiye wayarsa yace "Amma magana ta gaskiya Mama baza ayi tafiyar nan da Badiyyah ba, tun da can kadunan ance Hajjan ba lafiya to ina ga in zaki koma Karaye zaki koma can tare da ita kawai, don zuwa jibi za su bi jirgi in sha Allah, kayan sawansu kawai za su dauka..." Sake baki Mama Ladi tayi tana kallon Abba bata ko kiftawa.
[8/3, 8:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mama Ladi na gyara shimfidar da zata kwanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login