Showing 111001 words to 114000 words out of 249515 words

Chapter 38 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1540

ta hau danna wayarta without raising her head, sannan ya kalli Badiyyah yace "Ohk, can you come back in the next 30 minutes?" Tana gyada kai tace "Sure sir, thank you" Ya gyada mata kai yana kallonta yace "You are welcome" Juyawa tayi ta fita ta kullo office din tana murmushi, Dr Musharraf ya kalli Mayraah yace "Go on dear, ina jin ki" Ta kashe wayarta without looking at him tace "I think a nan na tsaya, sai na ci gaba da karatun before going further, let me go and continue now" Yace "Haba sauran ma zaki iya mana, kawai ki ci gaba nasan ai kin karanta course din during test" Ta dau handbag dinta tace "I am serious nan na tsaya, yanzu zanje in ci gaba" Yayi shiru yana kallonta, sai kuma yace "Ohk, idan kin ga Badiyyah around the premises ki ce ta shigo" Mikewa Mayraah tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Ohk" Daga haka ta fita daga office din. Tana sauka downstairs taji gaba daya makarantar yayi mata zafi, ta kasa zama cikin department din har sai da ta fita waje, rasa inda ma zata je tayi, ta zauna karkashin wani bishiya, kawai sai taji hawaye ya cika idonta, nan da nan ta goge da sauri, ta ciro wayarta a jaka, tun da suka yi exchanging number da Maleeha basu taɓa waya ba sai chatting, yau kawai tayi dialing numberta yana fara ring ta daga, bayan sun gaisa Mayraah tace "Kin shiga school ne yau?" Maleeha tace "Aa ina gida wllh" A hankali Mayraah tace "Ohk, i tot u are in School" Maleeha tace "Why not come over to our house ba wani nisa fa daga school din" Mayraah tayi murmushi tace "Aa next time" Maleeha tace "No plss, don Allah ki zo tunda kinyi niyyar mu hadu" Shiru Mayraah tayi, Maleeha tace "Pls ki samu mai adaidaita sahu sai in gaya masa address, muna nan tudun yola fa, kinga ai ba nisa sosai" Mayraah tace "Ohk zan zo" Cikin minti sha biyar Mayraah ta isa gidansu Maleeha, Maleeha tayi farin cikin ganinta sosai, suka shiga parlonsu, Maleeha da mai aikinsu kadai ne a gidan duk parent dinta sun fita aiki, gisting with Maleeha made Mayraah felt relieved taji hankalinta ya kwanta sosai, tana gidan har aka yi azahar, bata yi niyyar cin abinci ba amma sai da Maleeha ta tursasa ta ta ci, suna cin abincin Mayraah tace "Plss Maleeha kar ki gaya ma Ya Usman na zo gidanku yau fa" Maleeha tayi shiru tana kallonta, sai kuma tayi murmushi tace "Ai muna dadewa bamu yi magana da shi ba" Mayraah ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "How?" Maleeha tace "Nothing.... he is just a frnd fa, Colleague din yayana ne, so i knew him through my brother, once in a while yana zuwa gidanmu" Mayraah tace "Wai ba soyayya ku ke ba?" Maleeha tace "At all, wai don coincidentally ya kai min abinci school ranan tare da ke? Yayana fa na kira ranan suna office tare sai nayi requesting abincin sai yayana yace he is busy, shi kuma sai ya kawo min amma wllh ba soyayya muke ba, ko chatting muna jimawa bamu yi ba" Mayraah was speechless, A hankali Maleeha tace "But i must confess to u Mayraah, i love ur brother amma shi bai san ina yi ba" Mayraah tayi murmushi tana kallonta tace "Then why not shoot ur shot dear" Maleeha tace "Hmmm, i am afraid" a hankali Mayraah tace "U need not to be Maleeha, zan so ace kun yi aure da yayana" Maleeha ta kauda zancen kawai ta kawo wani hiran. Karfe biyar saura Mayraah ta isa gida bayan ta bar gidansu Maleeha, tun fitowarta daga gidan gaba daya mood dinta ya canza, sai a sannan ma ta kara tuna cewar Dr Musharraf bai kirata ba all through, tayi kokarin yakice damuwar nan a ranta, bata ga motar Maheer a parking space ba bayan ta isa gida, ta zauna compound for some minutes don kawai sai taji bata son shiga gidan, kasa ci gaba da zaman tayi saboda damuwar dake tare da ita, taji kawai kwanciya take so tayi, mikewa tayi duk da yanda gabanta ke faduwa ta karasa balcony tayi using spare key da Maheer ya bata ta bude kofar parlon, zaune ta tadda Haseenah da Badiyyah a parlon duk suka juya suna kallonta, ta sauke idonta kasa ta cire takalminta a bakin kofar parlon zata wuce dakinta Haseenah ta mike ta sha gabanta tana mata wani matsiyacin kallo tace "Ke gidan ubanki ne nan din da zaki shigo mana babu sallama sannan ki saka kai zaki wuce daki kamar kin ga marasu asali zaune a parlon? Are you mad?" Mayraah dai tayi shiru tana kallonta, Badiyyah tayi wani dariya ta mike tace "Kinsan duk inda mara galihu yake to yafi masu galihu iya shege banda haka mu sa'anninta ne da zata wuce bata gaishe mu ba? wallahi na rasa jin kan me yarinyar nan take har yanzu bayan tasan mummunan history dinta, da nine ita da nikab zan dinga yawo a gari on a serious note, duk department yanzu an san bata da asali kuma Shegiya ce" Juyawa Mayraah tayi da zuman fita ta bar masu parlon, Haseenah ta fizgota a fusace ta cakumi hijab dinta tace "Don ubanki mu zaki yi walk out on muna maki magana ko dai codeine kike sha ne??" Mayraah ta dinga kallonta babu ko kiftawa, can tace "Pls take ur hands off me" Bata rufe baki ba Badiyyah ta wanka mata mari me kyau a fuska, Haseenah ta kara mata a other cheek din tace "Ni kike gaya ma i should take my hands of u? How dare u talk to me like that?" Badiyyah ta cire dankwalinta ta daura a kugu ta finciko Mayraah daga wajen Haseenah tace "Dama har yau ban fanshe dukan da Usman yayi min a kanta ba, so this is the rightful time, kamar yanda ya dokeni ake ganin ya doki banza babu wanda ya dau mataki kema yau haka zan dokeki in doki banza babu abinda zai faru wallahi...." Mayraah na jin haka ta fara kokarin cire Hijab dinta don baxata bari haka kawai Badiyyah ta doketa ba, Badiyyah tayi using wannan opportunity din ta shakota da Hijab din ta fara dukanta ta ko ina tana cewa "Yau sai dai wata ba ke ba wallahi" Haseenah ta koma gefe tana kyalkyala dariya tana kallonsu tana hailing din Badiyyah, Sai da Mayraah ta san yanda tayi ta fizge Hijab din daga jikinta ta fara retaliating dukan da Badiyyah ke mata, nan suka fara kokuwa suna kai ma juna duka ta ko ina, Haseenah ta ga alamar at anytime Mayraah zata iya kai Badiyyah kasa ashe Badiyyar ba wani karfi ne da ita ba, kawai Haseenah ta shige kitchen da gudu ta kunna gas ta dau fry pan ta zuba manja ta daura kan wuta ta yanka albasa ciki sannan ta cika wutan gas din sai da taga ya fara hayaki sosai kitchen din ya turnuke ita kanta tari take sannan ta fito da fry pan din parlor ta nufo inda suka damben, Mayraah taji numfashinta ya fara tsarkewa ta fara struggling to breathe saboda manjan da Haseenah ta fito parlor da shi tana zagaya su, Badiyyar ma tari take amma hakan bai hanata dinga kai ma Mayraah duka ba har sae da ta kai ta kasa duk da yanda taga numfashinta na kokarin daukewa bata fasa dukanta ba, Haseenah na ganin haka ta ajiye fry pan din hannunta bayan kujera ta gudu daki ta dau wayarta tayi dialing number Maheer yana dagawa ta fashe da kuka tace "Baby kana ina ne don Allah? Ka bar ko me kake yi ka dawo gida ba lafiya" Maheer da fitowarsa kenan daga asibiti ya rage sautin karatun Alqur'ani da ke tashi a motarsa yace "Me ya faru???" Cikin Muryar kuka Haseenah tace "Wallahi ina zaune ko minti ashirin ba ayi ba Badiyyah ta zo wai shekaranjiya ta mance charger dinta zata dauka, to zata tafi kenan sae ga Mayraah ta dawo ita ma zata shigo parlor, kawai sai Mayraan ta bangajeta a bakin kofa, ni dai kawai sai gani nayi suna dambe, daga haka kuma numfashin Mayraah ya fara sama sama...." Katse wayar Maheer yayi, Haseenah ta koma parlor da sauri, zaro ido tayi tana kallon Badiyyah da ta mike tana huci tana kallon Mayraah dake kwance kasa kamar bata numfashi, Haseenah ta dafe kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kamar bata numfashi fa Badiyyah" Badiyyah ta dau Hijab din Mayraah da sauri ta saka don tuni shegun kayan jikinta suka yage kaca kaca, ta dau handbag dinta da wayarta da gudu ta bar gidan, rikicewa Haseenah tayi ta nufi windows din parlon da sauri ta bude labule don hayakin manjan ya fita, ta kure fanka ta buda Ac sannan ta dau fry pan din shima da gudu ta kai kitchen ta zubar da manjan a sink ta fara wanke wanke, gaba daya a tsorace take, ta kara dawowa parlor tana kallon Mayraah that is lying almost lifeless a kasa, jikinta na rawa ta kara daukan wayarta tayi dialing number Maheer amma bai daga ba, da gudu ta tafi kitchen ta debo ruwa ta fara zuba ma Mayraah tana jijjigata, gaba daya ta tsorata ba kadan ba, ta fita a guje tana kwala ma Musa mai gadi kira tana cewa "Musa zo ka duba min kaddai mutuwa tayi" Musa na shiga parlon shima ya kasa karasawa ya dinga "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una" Tuni Haseenah taji hanjin cikinta ya kada ta daura hannu a ka ko ina a jikinta na rawa tace "Ta mutu ne Musa??" Dai dai nan Maheer ya shigo parlon, shi kansa bai san ta yaya ma aka yi ya iso gidan ba, dukawa yayi inda Mayraah ke kwance ya dagota yana kiran sunanta cikin tashin hankali, ganin she is unresponsive ya fara mata Chest Compressions da sauri, daga bisanni ya bude bakinta ya hade da nasa giving her mouth to mouth resuscitation, duk da tashin hankalin da Haseenah ke ciki sai da ta hade rai tana kallonsu ganin abinda yake ma Mayraah, nan da nan ta nemi fargaban da take ciki ta rasa, ganin bazata iya ci gaba da kallonsu ba ta fito balcony ta tsaya fuskarta a daure. Haseenah ta fi minti biyar tsaye a balcony taki shiga parlon, sai a sannan kuma ta fara addu'ar Allah ya sa Mayraahn ma ta mutu kawai, tana tsaka da wannan tunanin ne Maheer ya fito dauke da Mayraah ya nufi motarsa dake waje da sauri, Haseenah ta wani kyabe baki ta bi Mayraah da kallo ganin idonta a rufe suke ta fara wishing dinta mutuwa, can dai kuma ta bi su har kofar gidan da sauri, cike da damuwa kamar gaske tana yarfe hannu tace "Maheer hope she is breathing now? Hope kayi reviving dinta?" Ko sauraronta Maheer bai yi ba ya shige driver seat ya tada motar ya bar unguwan with speed, wani murmushi Haseenah tayi ta juya ta koma ciki tana ci gaba da yi ma Mayraah fatan mutuwa. Maheer na zaune ward din da aka kwantar da Mayraah wajen karfe tara na dare, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, kana ganinsa zaka san he is not himself, ba a jima da cire mata oxygen ba don breathing din nata ya dawo normal, lkci lkci yake tashi ya dubata a kan gadon, Usman ne ya shigo ward din, direct gadon da Mayraah ke kwance ya nufa ya tsaya yana kallonta babu ko kiftawa, Kamar yanda bai ce ma Maheer komai ba haka Maheer ma bai ce masa komai ba, ko minti ashirin Maheer bai yi da kiransa ya sanar masa da abinda ke faruwa ba, don ko Ammi bai gaya ma ba har sannan, after standing for almost 5 minutes yana kallon Mayraah, Usman ya juya ya kalli Maheer for the first time yace "Me ya kai Badiyyah gidanka har tayi mata haka?" Maheer dai bai ce komai ba, juyawa Usman yayi ya nufi kofa ya fice daga ward din Maheer ya bi sa da kallo. Usman na fita ko minti sha biyar ba ayi ba Mayraah ta bude idonta, Maheer ya mike da sauri ya duka kusa da ita ya kamo hannunta yace "Mimi how are you feeling?" Hawaye ya gani a idonta, lkci daya jikinsa yayi sanyi ya ma rasa abinda zai ce mata.... Badiyyah na kwance Hajja na gasa mata hannu da ruwan zafi sai ihu take duk ta cika gidan tana cewa wayyo mamana kamar gaske don babu abinda ya samu hannun, dama tana dawowa gida ta sanar ma Hajja karya zalla wai Mayraah ta rufeta da duka a gidan Maheer da kyar Haseenah ta kwace ta, daga dai Mayraan taga wannan lecturer din da ya fasa aurenta yana kula ita Badiyyar a school, ta dai yi fabricating lies ba kadan ba tayi feeding din Hajja da shi, wanda nan da nan Hajja ta kira Ammi tana vibrate, abinda ta manta ne kawai bata fada a wayar ba don in ance ma ta tsine ma Ammi ba mamaki, Hajja ta tafi ta dafo ruwan zafi ta hau gasa ma Badiyyah hannunta da tace ya goce, a cikin ihun da take ne take cewa Hajja ita Bichi kawai zata tafi, Hajja tace "Ki tafi ina a haka? Ae wallahi in har Hajarah bata dau mataki a kan wannan abinda aka maki ba sai dai ta nemi wata uwar kuma ba ni ba, saboda ta nuna min iyakata shine ta sa Maheer ya tafi da yarinyar gidansa, to wllh yau za ayi ta ta kare, su zabi ko ni ko yarinyar nan, ae ita ke da iko da Maheer ba shi ke da iko da ita ba...." Hajja na kai wa nan ta mike tana huci ta shiga daki zata dauko man zafin da zata shafa ma Badiyyah amma ta neme sa ta rasa, fitowa tayi ta dau gyalenta tace "Bari in amso man zafi nan makota in dawo" Badiyyah na ganin fitar Hajja ta mike da sauri ta shige daki ta dau karamar jakarta ta saka kaya kala biyu da kayan shafe shafenta ta zuge jakar har wani rawa jikinta yake don ita gani ma take kamar za a kira ace Mayraah ta mutu, da ta tuna yanayin da ta bar ta sae gabanta ya fadi, tana fitowa parlor ta nufi kofa zata bude aka riga ta budewa, duk a tunaninta Hajja ce amma tana daga kai taga ba haka ba, a cikin minti biyar zuwa shidda ya gama mata abinda ya kawosa ya bar ta kasa ko kwakkwaran motsi bata yi tsabar duka, ya fice daga parlon.... Maheer na tsaye kan Mayraah dake zaune kan gado wajen karfe goma, tun dazu yake lallabata ta gaya masa menene ya faru dazu amma taki cewa komai, a haka Usman ya shigo ward din ya same su, Maheer ya dinga kallonsa don ko ba a gaya masa ba ya ma san daga inda yake, Usman ya nemi kujera ya zauna as if everything is okay, Maheer ya kalli Mayraah dake kallonsa, sai a sannan ta bude baki a hankali tace "Aunty Haseenah ce da sis Badiyyah" da wani expression Maheer ke kallonta, can dai yace "Haseenah?" Mayraah ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, juyawa yayi ya fita daga ward din.... Haseenah na zaune parlor tana cin Indomie din da ta dafa, zuwa yanzu har ta gaji da addu'ar Allah ya kashe Mayraah, banda ma ta gigice ai da taga ta shiga comma kamata yayi ace ta dau throw pillow ta danne mata fuska da shi da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, ta kyabe baki tana cin Indomienta da soyayyen kwai, tun da taga har goma da rabi tasan Maheer ba lallai ya dawo ba kenan tunda kanwar uwarsa na kwance asibiti, tana cikin tunanin nan ya bude kofar parlon ta daga kai da sauri, ganinsa ta mike ta nufesa da damuwa tace "Baby ya jikin nata, har na gaji da kiranka a waya baka dagawa, kaga tun dazu sai yanzu na iya dafa Indomie zan ci...." Takardan dake hannunsa ya jefa mata ya juya ya fice daga parlon, ta dinga kallon takardan gabanta na wani irin faduwa, da kyar ta durkusa ta dauka ta warware tana duba content din, wani ihu ta fasa ta bi sa a guje tana cewa "Maheer ka sakeni saki daya kamar yaya??? ban gane ba Maheer, ni din ka saka?" Amma tuni ya shige motarsa ya bar layin, shi dai mai gadi sai zare ido yake.



MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788



*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*
[7/2, 6:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya kalli agogon wrist dinsa dake nuni da karfe sha dayan dare sannan ya kalli Usman dake danna wayarsa yace "It's getting late, baza ka tafi gida ba?" Usman ya daga kai ya kallesa yace "I should be asking you that kai da kake da iyali a gida" Maheer yayi shiru bai sake ce masa komai ba, lkci lkci yake kallon Mayraah da ta koma bacci tun dazu, ganin har sha biyu Maheer ya mike ya dau makullin motarsa without looking at Usman yace "Sai da safe" Usman yace "Allah ya tashe mu lafiya" Bai ce masa komai ba ya fice daga ward din ya kulle kofar... Through out night din Usman bai yi wani bacci ba, he kept a close eyes on Mayraah dake ta bacci just to make sure is okay, karfe biyar saura na asuba aka bude kofar ward din ya daga kai ya ga Maheer ya shigo, Ajiye ledan hannunsa me dauke da hijab din Mayraah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login