Showing 192001 words to 195000 words out of 249515 words

Chapter 65 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1564

ne ke kiranta, ƙin dagawa tayi ta mayar da wayar tana duba cash din jakarta taga babu ma cash din sai dubu daya don kusan kullum idan ta fito tana siyan Energy drink biyu wani lokacin har uku saboda low bp dinta sannan tana yin transport din komawa gida shi yasa cash din bai dade mata, nan ta hau dube duben ATM card dinta bata gani ba a jakar sai na Usman kawai, tunanin inda ta jefa nata ta fara yi, ko dai ta bar shi a daki ne can gidan Ummi the last time da tayi using dinsa ko kuma ya fadi ne bata sani ba, tunanin faduwan yasa hankalinta ya tashi, ta rasa yanda zata yi gashi yau dama bata yi niyyar komawa gidan Ummi ba Suleja kawai zata wuce abun ta, can dai da ta gaji da tsayuwa ta ciro Atm card din Usman tana jujjuyawa tana nazarin tayi amfani da shi ko kar tayi a ranta, wani me adaidaita sahu ta tare tace masa inda zata cire kudi take son ya kai ta, tana shiga bayan sun yi tafiyar like 15 minutes yace "Ga wani banki Hajiya" Ta kalli bank din tace "Mu je dai, bana son cire kudi a wnn bankin din" Haka yayi ta tafiya da ita suna ta wuce bankuna da dama sai tace su je wani, har dai mai adaidaita sahun ya gaji yace "Hajiya kudin ki fa yawa yake, kar mu je muna wallahi tallahi a hanya" Mayraah tace "Ba damuwa mu je zan baka ko nawa ne" Daga karshe dai bayan tafiya me tsayi tace masa ya tsaya, ta sauka tana kallonsa tace "Amma zaka yi hakuri in cire kudin in dawo yanzu" Ya wani hade rai yana kallonta, can ya kashe napep dinsa ya sauko yanda zai dinga ganinta da kyau yace "Ina jira" Shiga bank din tayi ta tafi ATM machine din, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta saka ta fara cire dubu goma tukun, ai ko ya ciru, bayan nan ta sa 50k shi ma ta cire sannan ta maida Atm card din cikin jakarta da sauri ta fito ta dawo gun mai adaidaita sahun ta shiga tace "Mu tafi" Yace "Mu je ina?" Tace "Inda zan samu motar zuwa Suleja zaka kai ni" Yace "To bani kudin kawo ki nan da nayi tukun" Dubu biyar ta kirga ta basa amma duk ta kagu su bar wajen, yana amsan kudin bayan ya ga nawa ne ya tada adaidaita sahun suka bar wajen, sai kusan Magrib Mayraah ta iso Suleja a gajiye ga yunwa da take ji don har wani juya mata kanta yake, bayan ta sauka a daidaita sahun da ya kawota anguwan nasu don yace bazai shiga layin ba haka ta fara trekking zuwa cikin layin tana tafiya a hankali, tun daga nesa take kallon motar da ta hango anyi parking few houses before her's babu ko kiftawa.......
[7/23, 8:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Har Mayraah ta isa dai dai inda aka yi parking motar bata daina kallon motar ba, as if tana son tabbatar da motar waye, kasa ci gaba da tafiya tayi zuciyarta na bugawa ganin an bude kofar motar alamar wanda ke ciki zai sauko, idonta na kansa har ya sauko ya kulle motar ya rungume hannu yana kallonta without blinking, ta wani hade rai ta ci gaba da tafiya kamar zata tashi sama, zata wucesa yace "Ilham" a mugun fusace ta juyo tace "Me yasa kake bibiyata? And how did u get here??" Yana kallonta directly yace "Saboda tun daga first day din da Ahmad ya kawo ki hospital baki da lafiya na gano da yawa daga maganganunki karya ne, nasan karya kike tun a sannan, u never called ur people that very night da Ahmad ya baki waya ki kirasu, wasu nambobi daban da kika san basa amfani kika yi dialing, don har yau i have the 2 numbers na karba gun Ahmad kuma ina kira inji a kashe, wacece ke? Why did u chose to say all sort of lies about so many things to me? Take a look at ur self, baki yi kama da warce tasan wani abu wai shi wahala ba a rayuwa, baki yi kama da warce ta fito daga gidan da sai an tara kudin admission kafin ki taho makaranta ba, sannan a ilimin ki da wayewarki bazan yarda cewar baki san anyi terminating admission dinki kika taho Abuja ba, show me the admission list kin ki, wani school ne kin ki fada min, ke da kika tsaya tara kudin makaranta da kyar ta yaya ma za kiyi lodging hotel me tsadan nan, har kiyi ikirarin zaki iya kama gidan dubu dari uku a Abuja, so many unnecessary lies, kin ce sunanki Mayraah kin dawo kince Ilham u think i forgot, and worst of all ke kadai kike zaune gidan da zaki shiga yanzu not with anybody kamar yanda kika yi claiming cewar gidan stepmom dinki ne, har briefing dinki labarin rayuwata nayi duk don ki zama relax and tell me a little about ur self amma kin ki, ban san mission dinki a Abuja ba, amma baki yi kama da warce ta fito daga gidan da ba tarbiya ba, you look decent and well brought up, as a medical Dr na hango depression a idanuwanki, damuwa na daga cikin abinda ke contributing na low bp dinki.... Nayi kokarin ganin kin fara aiki a hospital din ko zai canza maki thinking dinki akan abubuwa da dama da ya shafi rayuwarki amma naga ba haka bane, and kin nuna u are not even after the job, u are not desperate about it, sannan u don't mind being fired, that aside kina da enough cash a tare da ke" Mayraah ta kasa ci gaba da kallonsa nan da nan hawaye ya cika idonta, kasa daurewa tayi ta hade kanta da motar ta fashe da kuka sosai, shi dai kallonta kawai yake, can ya sauke ajiyar zuciya yace "Zan je masallaci, ana kiran sallah, ki shiga ciki kiyi sallah, idan na dawo masallaci i will call u out" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta ta wuce sa ta karasa gate din gidanta ta ciro makulli a jaka ta bude ta shiga ciki, sai a sannan ya dauke kai daga kallonta ya karasa masallacin da ya ji ana kiran sallah. Mayraah na zaune kan darduma tun da ta idar da sallan magrib, har sannan ta kasa daina kuka don ya famo mata ciwon da ke cikin zuciyarta, bata taɓa sa wa a rai wai zata zauna ta gaya ma wani anything about her self ba, she just want to be, bata son tana tuna abinda zai dameta, juyawa tayi tana kallon wayarta dake vibrate, can ta jawo ta daga ta kai kunne, Dr Khalil yace "Ina jiran ki" Ta sauke idonta bata ce komai ba ya katse wayar, bayan few minutes ta mike ta linke darduman ta fita waje, tana tafiya a hankali ta karasa har gun motar yana zaune driver seat leaving the door open, hakan ya sa ta zaga ta bude front seat ta shiga ta zauna ba tare da ta kallesa ba tana fidgeting fingers dinta, shi dai kallonta kawai yake, can yace "Mayraah" Ta daga idanuwanta ta kallesa yace "Tell me who u are, me ya kawo ki garin Abuja" Nan da nan hawaye ya cika idonta, yace "Assuming i have any other intention toward u kinsan bazan kai ki gidanmu ba, ko ince gidansu matata, duk abubuwan nan da kika ga nake ta kokarin yi a kanki don bana son kije ki fada wani hali ne ba don komai ba, ni mutum ne me tausayi kowa ya sani so i have no bad intention toward u, don kin gaya min wacece ke iyaka idan naga da inda zan baki shawara sai in baki kuma bazan baki shawaran da zai cuce ki ba, idan kuma taimako ne da bai fi karfina ba sai in maki, trust me Mayraah" Ta goge hawayen dake sauka idonta ta gyada masa kai, a hankali tace "Sunana Mayraah Mahmud..." Ya gyada mata kai yana kallonta, tace "I was born and brought up in kano" Sai kuma ta fashe masa da kuka yace "Kin ga kiyi hakuri, be strong and tell me what u want to tell me" Nan ma kai ta gyada masa tana goge hawayen da ya ki tsaya mata.... Mayraah bata boye masa komai game da rayuwarta ba har zuwa ranan da ta bar garin Kano, she told him every single thing, shi dai Dr Khalil kallonta kawai yake cike da tausayinta, abu biyu kadai ne yaji tausayinta a kai a duk labarin nan da ta basa, na farko wa enda take kallo a matsayin iyaye tun tasowarta bayan shekaru 22 ta gano ba su ne iyayen nata ba, he can't imagine this great disappoinment, na biyu kuma fasa aurenta da aka yi saboda rashin sanin asalinta, shine kawai tausayinta da ya ji amma ita irin upbring din da ta samu ma mutane da yawa dake tare da iyayensu basu samu kwatankwacinsa ba, ta taso cikin gatanta da soyayya ta ko ina, she lived a comfortable life har zuwa sanda calamity din nan yayi befalling dinta, can ya tallabi chin dinsa yace "Mayraah" Ta daga jajayen idonta tana kallonsa yace "Ur story is not enough to leave home, baki ma Abbanki halacci ba, ita ma Ummin baki mata uzuri ba, da kin tuna irin soyayyar da ta maki tun baki san kanki ba na tabbatar babu abinda zai yi motivating dinki ki bar gida, sannan yayyinki maza su ma baki masu halacci ba" Cikin kuka tace "May be u are saying all this because u are not in the shoe, kowa zai dinga gani kamar it's easy but u promise u it's not, it's painful, i tried my best to be fine with them amma daga karshe kawai naga idan na ci gaba da zama zuciyata zata iya bugawa at anytime, i can't stand Ammi not talking to me a gidan bayan ba haka na taso take min ba, at the end su ma yayyin nawa avoiding dina suka fara yi ai, Abba did marry because of me...." Ta kasa ci gaba ta fara wani kukan, Dr Khalil yayi kasa da murya yace "Zaki koma gida Mayraah! dole za ki koma gida" Ta share idonta tana kallonsa tace "Bazan koma ba anytime now, idan kuma kace zaka takurani i am leaving Abuja.... i promise u" Da mamaki yake kallonta, can yace "To ke yanzu halaccin da zaki masu kenan? Kika san halin da suke ciki bayan barin ki gida?" Tace "Ba halaccin da zan masu ba kenan, i will never forget their good deeds and they still remain my parents har ko da yaushe, bani da kowa sama da su, kawai dai ina son in bada space ne zuciyar kowa yayi sanyi... Ina son komai ya dawo dai dai a family din, tunda ta dalilina kaga yanda abubuwa marasu dadi suke ta faruwa, i am the caused of everything, tun daga sanda aka fasa aurena abubuwa ke ta faruwa, i am blaming my self for everything" Dr Khalil yayi shiru kamar me nazari, can yace "Ya ma kika ce sunan yayan naki that is a Medical Dr?" Ta wani kallesa tace "I don't think that is necessary" Ya ɗan yi murmushi wanda iyakarsa lips yace "Ohk then, kin samu labarin fitowar result dinku na makaranta?" Ta girgiza kai a hankali tace "Bani da contact din kowa yanzu" Ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan" Bai sake cewa komai ba ita ma haka, and they were silent for almost 3 minutes kowa da tunanin da yake a ransa, A hankali tace "It's getting late, kuma zaka koma Abuja" Gyara zamansa yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "Haka ne, amma don Allah ina son kiyi hakuri ki daina dawowa Sulejan nan kwata kwata saboda ke macece bai kamata ki kama gida ke kadai ki dinga rayuwa ciki ba, don't forget everyone is watching u, za a maki fassaran me zaman kanta...." Mayraah ta kallesa tace "How did u find out nan da nake?" Yace "Nace maki tun farko dama ni ban taɓa yarda dake ba ko na second daya, though confidently kike karyanki but facial expression dinki ke exposing dinki, ina me baki shawara next time ki daina karya bai yi fitting dinki ba kuma za a gano ki cikin few minutes...." Ta sunkuyar da kanta, yace "I came here through ur neighbor's Husband, yarinyar da ta rasu kwanaki a hospital, i had to trace the man's number, don ranan da za su zo daukar gawan yarinyar yayi ta kirana ban daga ba ina aiki, sai yayi min text message, so sai da nayi tracing text message dinsa sannan na samu number" Mayraah ta wani hade rai tace "To banda sa ido irin na mutane shine har yace maka ni kadai nake rayuwa a gidan nan?" Yace "Aa bai ce haka ba, ce min yayi according to his wife ke student ce a jami'a, weekend kawai kike dawowa yi a gidan" Mayraah bata sake cewa komai ba, Dr Khalil yace "And lastly yanzu idan na bar nan zan je gidan MD, i will beg him on ur behalf cause dazu bayan tafiyarki ya shigo har office ya sameni, ke da nace kije ki basa hakuri sai kika ki basa kika yi masa kerere a bakin kofa, why Mayraah..." Da sauri ta wani hade rai tace "Ta yaya zan basa hakuri bayan yace in fita daga office dinsa" Dr Khalil ya ɗan yi murmushi yace "Ai yana cewa ki fita baxa ki fita ba zaki fara basa hakurin cikin ladabi, not to just walk out don yace ki fita" Mayraah ta kauda kai, Dr Khalil yace "Ba aikin kike bukata ba sbda ke ba shi ne ma a gabanki ba shi yasa u won't mind ko kin rasa aikin da thousand of people ke nema, but i wont allow that happen sbda bana son ki sake zama Sulejan nan, ban ga alamar an maki tarbiyar da zaki zama me zaman kanta ba" Ita dai bata ce komai ba, yace "Ki shiga gida sai da safe, gobe ki shirya ki taho asibitin" A hankali ta bude motar ta sauka, sai da ya ga shigarta gidan sannan ya bar layin a ransa yana nanata sunan Maheer da ta ambata masa a labarin da ta basa, sai kusan karfe tara saura ya shigo Abuja, yana parking bakin gate din gidan MD wayarsa ya fara ring, yana dubawa yaga Zainab ce, murmushi yayi, yayi silencing wayar don yasan taga bai dawo bane yasa ta kirasa, ya lura da ita duk kwanan nan she is acting insecured akansa, ya gaisa da mai gadin gidan ya shiga, a parlor ya tadda MD with different textbooks a gabansa da laptop, Dr Khalil yace "Mun kusa fara ce maka professor fa mutumin nan" MD ya daga kai ya kallesa, Murmushi khalil yayi ya zauna yana facing dinsa yace "To ya ake ciki?" MD ya rufe laptop din gabansa yace "Next week fa zata shigo, ina ga her plan is to meet the workshop" Dr Khalil ya bude ido yace "Really, i tot kace makarantar da take lecturing za su yi commencing exams" MD yace "To haka dai ta ce min" Dr Khalil yace "Kace akwai ƙura kenan" MD ya daga kafada yace "Ita da Dr Ajay kenan, yaushe rabona da asibitin, ai ta sani" Dr Khalil yace "Lallai kam, MD alfarma na zo nema don Allah" MD ya kallesa, nan da nan ya hade rai yace "Ba dai maganar fitsararriyar yarinyar nan ya kawoka gidana ba" Dr Khalil ya girgiza kai yace "Wallahi kayi misperceiving dinta ne MD, she is so good sannan ta iya aiki" MD ya girgiza kai yace "Ban ga alama ba, wai ba ita bace ta kasa ba ma yarinya common injection ba a ward ranan, sannan muna aiki a theatre tayi contaminating mana equipments, how is she good, don Allah do not spoil my mood Khalil, kai ma kasan bamu da vacancy" Dr Khalil yace "Na sani, shi yasa nace alfarma pls" da mamaki MD yace "To ko dai budurwarka ce yarinyar nan?" Dr Khalil yayi dariya yace "Kai ma kasan daga Madam dita ai babu kari" MD ya ɗan yi tsaki yace "Wallahi i hate dealing with rude human beings, zaka takurani Khalil" Dr Khalil yace "Ka dai yi hakuri don Allah" MD ya kara jan tsaki, bayan few seconds yace "Ina CV dinta?" Khalil ya shafa kansa yace "Za a kawo" MD yace "Till then" Khalil yace "Don Allah kafin su Madam su shigo kasar nan ka bata aikin nan, kasan in suna nan it will be hard wllh" MD yace "Ka ma maida ni ban san abinda nake ba Khalil, ta yaya zan bada aiki babu CV?" Khalil yace "Ko Hafsat ba sai daga baya aka kawo ba, kuma me wuyar dama mutum yayi graduating ko" MD yace "Don Allah lokacin kwanciya na yayi, in dai yarinyar nan ne bazan bata aiki babu takardu ba, apart of takardu sai nayi interviewing dinta, kuma idan naga she is not fit for the job Billah sai dai kayi hakuri bazan bata ba kaji har na rantse, even after the interview idan tayi passing kenan she will be starting as an Enrolled nurse" Khalil yayi shiru yana kallonsa, can a hankali yace "Enrolled nurse kuma MD" MD ya fara tarkata textbooks dinsa da nufin barin parlon, Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan ba matsala, amma a fara interview din tukunna pls" MD yace "Then she should come together with an apology letter in 2 days time, gobe bani da lokacinta haka ma jibi, sai ta bari on Sunday kenan idan Allah ya sa na shiga Asibitin" Yana gama fadin haka yace "I will be going to Bed Khalil" Khalil ya ɗan yi murmushi ya mike yace "To shikenan, thank you sir, Allah ya tashe mu lafiya" Daga haka ya bar parlon. Maheer dake zaune dakin Usman sai kallonsa yake har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login