Showing 3001 words to 6000 words out of 249515 words

Chapter 2 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1494

amsa ita ma tayi, ta ba warce ke kusa da ita, har ta fara sauka stairs zata koma gun su Hamida wayarta dake hannunta yayi vibrate alamar shigowar message, duba wayar tayi... "Stay behind" shine content din message din, jingina tayi da stairs din kamar zata yi kuka don bata so haka ba, can dai ta koma daya bangaren corridor din stairs din ta tsaya, tana ganin Coursemate dinta duk suka sauka kasa bayan sun rubuta attendance din, babu kuma wanda yayi noticing dinta a cikinsu a hankali ta fara tafiya zuwa office dinsa, tana isa kofar ta kwankwasa a hankali, jin bai amsa ba ta yi sallama, sai da taji ya amsa sannan ta shiga ba tare da ta kallesa ba ta kulle masa kofar, kallonta kawai yake, tana tafiya slowly ta isa gaban table dinsa without looking at him ta ɗan risina tace "Good morning sir" Calmly yace "Mayraah" ta ɗan kallesa, sosai gabanta ya fadi taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, bata san sanda ta zauna kan daya daga kujerun dake facing dinsa ba amma bata bari sun kara hada ido ba, yace "Why were you late to my class?" Ta girgiza kai tace "Sallah naje yi" Bai ce mata komai ba, bayan few seconds yace "Look at me" Da kyar ta dago ta kallesa suka hada ido, da sauri ta daura goshinta kan table dinsa tana jin wani sabon kunyansa da bata san dalili ba ita ma, ɗan murmushi yayi bai dai ce mata komai ba, ganin taki dagowa bayan kusan 40 seconds yace "Shikenan... Idan baza ki dago ba tashi ki tafi" Kamar jira take ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi kofa ya bi ta da kallo, kafin ta fita yace "Sai ki nemi wanda zai duba maki Defense slide dinki" Da sauri ta juyo ta kallesa ta marairaice tace "Don Allah kayi hakuri" Yace "Toh dawo" Ba musu ta dawo tana sinne kai ta zauna, yace "When next ku ke da lecture yau" Tace "Sai 2" Yace "Ohk, kin zo da laptop din ki?" Ta girgiza masa kai, yace "Turo min slide din naki ta Email yanzu" Tace "Toh" Slide din ta shiga nema a wayarta zata tura masa, shi ko sai kallonta yake, can a hankali yace "Kwana nawa su Ammi suka gaya maki anyi fixing?" Sosai gabanta ya fadi, taki dago kanta balle ta basa amsa, maganar da take ta fatan kar yayi mata kenan, yayi murmushi yace "Look Mayraah...." Still taki dago kanta sai ma hade rai da tayi, yace "Toh tashi ki tafi" Da sauri ta kallesa tana buda manyan idanuwanta ta marairaice tace "Duba maka slide din nake fa Sir" Murya can kasa yace "I love you" sunkuyar da kai tayi har da rintse ido, kawai jin kamshin turarensa tayi sharply hakan yasa ta bude ido da sauri ta gansa a gabanta, ta fara kiciniyar mikewa tsabar rudewa ta harde kafa sai ga ta a kasa, ya koma baya da mamaki yace "Meye haka kike yi, do u want to injure ur sef?" Tuni ta mike tsaye kamar zata yi kuka tace "Na tura maka sir" ya duka yana kallon kafafuwanta to be sure bata ji ciwo ba, sai kuma ya mike yace "Ta fi kiyi wucewarki, gobe ki kawo min hardcopy uku na slide din" Da sauri tace "Ok Sir" Sai kuma ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, zaunawa yayi saman kujeran da ta tashi yayi letting out sigh, wondering if she will ever change, ya ga kamar kullum abun ta kara gaba yake. Karfe daya da 'yan mintuna Mayraah na zaune tare da su Hamida a class suna jiran lokacin next lecture dinsu yayi taji wayarta yayi vibrate, dauka tayi ta duba taga sako ne ya shigo, bude message din tayi tana kallo, "Ina jiranki a parking space" shine abinda ta gani a rubuce, ta kalli su Amira da Hamida ta mike tace "Ina zuwa yanzu" Bata jira cewarsu ba ta nufi kofar fita, Mayraah na isa parking space ta karasa har inda ya ajiye lafiyayyen motarsa wanda babu tantama yana ciki a zaune, zagawa tayi ta daya side din amma bata bude motar ba har sai da ya bude daga ciki sannan ta shiga ta kulle motar, maimakon ta kallesa sai ta fara wasa da Hijab dinta, ledan eatry dake back seat ya dauko ya mika mata ta ɗan kallesa sannan ta amsa tace "Nagode" Yace "Duk sanda kika gama lectures ki kirani, am going home now" Ta gyada masa kai, yace "Sai anjima" Bude motar tayi ta sauka tace "Allah ya saka da Alkhairi" Ta kulle masa motar ta nufi cikin department ya bi ta da ido.
Badiyya na isa gida ko sallama babu ta shiga parlon kakarta, hankali tashe ta jefar da jakan hannunta tare da siririn mayafinta, Hajja kaka dake zaune parlon ta bi Badiyya da ido tace "Ke kuma lafiyar ki?" Badiyya ta zube gabanta ta fashe da matsanancin kuka, Hajja ta yi saurin dauke kopin kunun dake gabanta tace "Subhanallahi, lafiya Badiyya? Wani abun suka maki a can Bichin?" Cikin kuka sosai Badiyya tace "Wai Hajja da gaske an kai kudin auren Mayraah?" Hajja na kallonta da mamaki tace "Kudin Mayraah? Ina ruwanki kuma da wata Mayraah, yarinyar da ko ga maciji bakya yi da ita, kudi kuma ai yau kwana uku kenan da kawowa, shawara kika so ayi dake kafin a amsa kudin ne ko ko?" Badiyya ta daura hannu a ka ta kara rushewa da kuka tace "Amma Hajja na taɓa ce maki ina son mutumin fa amma kika bari aka amshi kudin nan, wayyo na shiga uku na lalace" Hajja ta koma baya a firgice tace "Anya kanki daya kuwa Badiyya? Me ya sameki haka? Ina ruwanki da mutumin da bai ce yana son ki ba? Ba ga ki da samarin barkatai na banza da na kirki ba, meye sai na Mayraah zaki sa ma ido fisabilillahi? Me yarinyar nan ta tsare maki a duniya ne?" Badiyya tace "Wallahi sai dai ita ma kar ya aureta duk mu hakura..." Hajja ta matsa daga kusa da ita a tsorace tace "Lallai ban san baki da hankali ba sai yau, ita er uwar taki kike ma baƙin ciki kiri kiri babu sakayawa Badiyya?" Mikewa Badiyya tayi tana kuka tace "Ni ba er uwata bace, babu abinda na hada da ita" Daga haka ta shige dakinta da sauri, Hajja ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace "To Allah ya sa ki gane, idan ba haka ba ai sai ki zama masifa da annoba a al'umma, ni dai ban taɓa ganin haka ba tun zuwana duniya...."



WhatsApp Via 07087865788

No phone call pls, just WhatsApp.
[5/27, 11:56 AM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖





By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻





2.....

Mayraah na zaune parlor tana danna wayarta wajen karfe biyar da rabi na yammacin ranan aka bude kofar parlorn, tana daga kai taga Hajja ce ta shigo da sallama rataye da jakarta, Mikewa tayi ta nufeta tana murmushi ta amshi jakar tace "Hajja sannu da zuwa" Hajja tace "Yauwa Mayraah, kwana biyu shiru baki je min ba, ko duk karatun ne" Mayraah tace "Dama wannan weekend din nake son zan je in sha Allah Hajja" Hajja tace "Toh Allah ya kai mu, ina Amminki?" Mayraah tace "Tana daki bari in mata magana" Daga haka ta tafi sama dakin Ammi, Hajja ta zauna a parlon tana gyara yafin gyalenta, ba a dau lokaci ba Ammi ta sauko tana ma mahaifiyarta sannu da zuwa, Hajja tace "Yauwa sannu, ya gida ya yaran?" Ammi tace "Alhamdulillah" Mayraah ta tafi ta dauko ma Hajja ruwa, Ammi na kallon Hajja tace "Ba ku zo tare da Badiyyan ba ko bata dawo Bichin ba har yanzu?" Hajja tayi kasa da murya tace "Wace Badiyya, Badiyyar da ta zama abar tsoro Hajarah, dalilin zuwa na kenan ma yanzu haka" Ammi da sai da gabanta ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Me kuma tayi Hajja? Ai da kin kirani ma na je ba sai kin taho da yamman nan ba" Hajja dai ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba tana bin Mayraah da kallo har sai da ta ajiye mata abincin da ta debo mata, Hajja tace "Ai da baki zubo min abincin ba ma, a koshe nake Mayraah" Mayraah tayi murmushi tace "Aa ki dai ci ko kadan ne Hajja" Daga haka ta bar masu parlon ta wuce sama. Ammi dai sai kallon Hajja take tana jiran jin me Badiyyan ta kuma yi, lamarin Badiyya na damunta don iya bakin kokarinsu suke yi a kanta amma abu sai gaba yake, dama tunda Mayraah ta zo ta sanar mata zuwan Hajja ta san ba lafiya, don Hajja sai tayi shekara ma idan ba da wani dalili me girma ba baza ta zo masu gidan ba, Hajja ta kara sauke ajiyar zuciya ta labarta ma Ammi yanda suka yi da Badiyya dazu da safe, Shiru Ammi tayi tana kallon Hajja da mamaki sosai, gaba daya ta ma rasa abinda zata ce tsabar yanda lamarin ya birkita mata lissafi, Hajja na girgiza kai tace "Yanzu da za ki bi ni mu koma gida sai kin ga abun ba kyau, tana can ta cika gida da kuka har sai da mai gadi ya kasa hakuri ya leko yana tambayar ko lafiya, sai nace masa bata jin dadi ne, har zuba mata abinci nayi na kai mata dakin wai duk don in fita hakkinta amma wllh bata ci ba, abun ya isheni na rasa yanda zan yi shine nace bari in zo ko hadani da Maheer za kiyi mu koma ya zane er banza, don in nace Usman sai ya iya ji mata ciwo" Ita dai Ammi ta kasa cewa komai, can dai ta dauke idonta daga kallon Hajja, Hajja tace "Ba shiru za ki yi ba Hajara, idan ba ke din ba wa zan je in tunkara da wannan magana" Ammi ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya tace "Ai da zai yarda shi bawan Allahn da sai ayi auren da ita kawai Hajja, in dai hakan zai sa hankalinta ya kwanta, ita kuma Mayraah tayi hakuri Allah ya fiddo mata da wani" Hajja ta hade rai tace "Amma ban san baki da hankali ba Ammi, in zo neman mafita gunki ki dankaro min wannan magana ba dadin ji haka, ce maki aka yi abinda na zo ki gaya min kenan, wato ina ma goyon bayan taɓaran da Badiyya tayi kenan, ni zaki yanko ma lafiyayyen baƙar maganar nan..." Da sauri Ammi tace "Aa wllh ba haka nake nufi ba Hajja, baki fahimce ni bane...." Hajja ta katse ta tace "To bari kiji ba komai ya sa na zo na sameki na gaya maki ba sai don ayi ma lamarin tufkan hanci tun wuri a taka mata burki ta dawo hayyacinta, in ma akwai wani abu dake damunta a kanta ne sai a nemo mai magani ya cire mata, amma ta yaya zaki yi furucin cewar Mayraah ta hakura ta bar mata? Ina ruwan Mayraah da katuwa Badiyya can, shi yaron dama ita yace yake so ne da zaki ce haka?" Ammi tayi murmushi tace "Toh me zance Hajja, yanda fa Mayraah take 'ya ta, haka Badiyya ma 'ya ta ce, abinda zan so ma Mayraah shi zan so mata..." Hajja tace "Kwarai kuwa er ki ce, don ke kika sha Mama kika sakar ma uwarta, kuma yau nasan da Rukayya na da rai ai Badiyya bata isa ba" Sai kuma Hajja ta fara matsar kwalla tace "To duk mutuwa ce ta ja hakan, ke kuma idan kina cewa Mayraah ta hakura gani nake kamar kin mayar da Badiyya bare ne, don da er ki ce ai zaki mata hukuncin da ya kamata ki taka mata burki baza kiyi wannan furucin ba, banda lalacewar zamani yaushe ma za ki ce haka, ai hukuntata ya dace kiyi don wannan babban kuskure ne" Ammi tace "Kiyi hakuri Hajja, ki bari Maheer ya kusa shigowa yanzu, sai ku tafi gidan tare" Hajja tace "To ya dai fi, idan ko ba haka ba ni sai ince ta tattara ta koma can wajen dangin ubanta a Bichi bazan iya wahala ba, kai ba ma Rukayya ba hatta ubanta da ace yana da rai yau da sai ta gane kuranta, to mutuwa ce me tonan asiri, sai dai mu ce Allah ya gafarta masu" A hankali Ammi tace "Ameen" Ammi ta mike tace "Mu je sama kiyi alwala magariba ta gabato" Hajja tace "Aa gaskiya, son samu ne ma ni bana son Mamuda ya dawo ya sameni gidan nan, bar ni inyi sallan a nan, Maheer din na shigowa mu tafi kawai" Duk yanda Ammi tayi da Hajja bata yarda ta hau sama ba ta shiga bandakin dake nan parlor zata yi alwala.... Hajja na zaune saman darduma, Ammi da Mayraah na kitchen Ammi na hado ma Hajja abinci, Maheer ya shigo gidan da sallama, mikewa Hajja tayi da sauri tace "Yauwa ɗan albarka mu tafi ka kai ni gida dama kai nake ta jira tun dazu" Maheer yace "Ikon Allah yaushe kika zo Hajjaju?" Hajja tace "Ban jima ba, mu tafi kawai dare yayi kar Mamuda ya dawo ya sameni" Bata jira cewarsa ba ta nufi kofa da jakarta a hannu, Ammi ta leko parlon tace "Don Allah Hajja ki tsaya ki ci abinci gashi nan yanzu zan kawo, shi fa Alhaji sai tara zai shigo yau ya tafi daukan karatu" Hajja tace "Banda lalura tsohuwa kamar ni me zan fito yi warhaka ina galantoyi a titi ko wacce tsohuwa na killace a gida Ammi? kawai in anyi niyyar bani abincin a zuba min ko a leda ne in tafi gida, Allah ya amfana" Ammi tasan ko me zata ce ma Hajja bazata yi convincing dinta ta tsaya ta ci abincin ba, hakan yasa tace "Toh bari a juye maki a Cooler Hajja" Mayraah tace "Hajja zan raka ki sai mu dawo tare da yaya Maheer tunda shi zai kai ki" Hajja ta juya ta kalleta, Ammi tayi saurin cewa "Aa baza ki je ba, baki ganin dare yayi" Hajja tace "kyaleta mu je kawai sai su dawo tare, abinda a mota za su kai ni su dawo" Ammi na kallon Mayraah tace "Tafi ki juye abincin a cooler...." Mayraah ta koma kitchen, Ammi ta nufi inda Hajja take tace "Hajja da dai ki bari naji tace ran sati zata je gaisheki ae..." Hajja tayi wani murmushi tace "Nasan kin fadi haka ne saboda Badiyya ko? amma kin manta ni babba ce Ammi, ai bazan ma Maheer magana a gaban Mayraah ba, tunda tace zata ki bar ta kawai mu je ba komai" Maheer dake kallonsu yace "Me Badiyyar tayi?" Hajja tace "Ka bari mu je gidan sai in maka bayanin komai"
Karfe takwas da yan mintuna Maheer ya isa gidan Hajja, Mayraah dake zaune gaban motar ta sauko ta bude ma Hajja back seat sannan ta dau abincin suka wuce cikin gidan, a nan parlor ta ajiye warmer din ta zauna... Hajja ta ja Maheer zuwa dakinta, nan tayi masa bayanin abinda ya faru dazu da safe tsakaninta da Badiyyah, Hajja ta kara yin kasa da murya tace "Ka ga ai taki fitowa taga wa enda ma suka shigo gidan ko da barayi ne, kuma tana nan dakin har yanzu ga takalmanta can bakin kofa, don haka ni ban san kan komai ba ban san me ya shiga kanta ba, hankali na yayi mugun tashi me babban suna" Maheer was totally speechless ya dinga kallon grandma din tasa, wato iskancin yarinyar nan gaba ma yake karawa maimakon ya ragu, Hajja tayi narai narai da ido tace "To ai ba shiru zaka yi ba" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma Hajja bai kamata ki bari Mayraah ta biyo mu gidan nan ba ai..." Hajja ta daga hannu tace "Aa to kai da uwarka kamar akwai munafurci a lamarinku, ni fa wllh duk daya kowa da kowa yake a gu na, babu abinda ya isa ya lalata mana zumunci, don me za ku dinga abubuwa haka kamar Badiyyar da Mayraah wasu bare ne?" Maheer ya mike ya fita daga dakin ya bude kofar dakin Badiyya, ta juya ta kallesa daga kwancen da take, lokaci daya ta kauda kai tana gyara kwanciyarta ganinsa, ya shiga dakin ya kulle yace "Ke dama rashin hankalin naki da rashin tunaninki ya kai haka?" Badiyya ta wani murtuke fuska taki cewa komai, ya gyada kai yace "Zan yi maganinki, Allah ya kai mu gobe" Daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da wani harara sai kuma ta ja tsaki. Sallama kawai yayi ma Hajja yace sai gobe zai dawo, a hankali Hajja tace "Toh Allah ya kai mu" Yayi hakan ne don baya son Mayraah ta fahimci komai don kiris ya rage ya cire belt ya zane Badiyya a dakin barin yanda ta wani juya masa baya saboda rainin wayo, Mayraah ta shiga dakin Hajja don mata sallama bayan da Maheer ya fito, Hajja tace "Toh Mayraah, Allah ya kai mu ran asabar din ina nan in zuba ido" Mayraah tace "In sha Allah, Na leka dakin Aunty Badiyya dazu naga kamar bacci take idan ta tashi kice ina gaisheta" Hajja tace "To zan gaya mata, sai da safe" Suna barin compound din Mayraah na kallon yayan nata dake driving tace "Yaya is anything going on?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Like?" Ta ɗan buda ido tace "Kawai dai nayi sensing kamar wani laifin Aunty Badiyya tayi ko?" Yace "Ai da kin shiga dakin kin tambayeta" Mayraah ta zaro ido tace "Tabb" Ya kawar da zancen ta hanyar cewa "Yanzu dai wasa wasa in less than 5 weeks zaki bar mu Mimi" Marairaice masa tayi tace "Ni bana son kana ce min haka yaya" Yayi er dariya yace "Toh ma dai su waye kawayen amaryan ke da baki da wasu kawaye??" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace "Ko Badiyya?" Nan ma dai murmushi tayi tace "Wannan ai senior sis dita ce" Yace "But.... Musharraf din yasan Badiyya ne?" Mayraah ta kallesa, sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login