Showing 18001 words to 21000 words out of 249515 words
for peace kawai kamata yayi kace masa u are not interested shikenan" Musharraf yace "Mami ni fa as far as u are not against my marriage to babu wanda ya isa ya hanani abinda nake so, tun daga kan Daddy har su kawu da su Aunty Halima, nobody" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu ya batun lefen jiya baka ce min komai ba" Yace "I decided to give her the money su siya kayan" Mami tace "Nawa ka bata?" Yace "7M" Mami tace "Why not make it 10m?" Yace "Zan kara mata" Mami tace "To ka dai ce mata banda Abaya da akwati ko?" Yace "Yeah"
Badiyya na zaune dakin Haseenah tana goge hawayen da yaki tsaya mata cikin rawan murya tace "Haka kawai kun sa in koma gidan ni ban ga amfanin komawata ba yau kwana biyu kenan, tun da naje dama ta tattara ta koma dakin Maheer, ba wani information da nake samu banda numbersa da nayi snapping dazu da ya kirata tana bandaki, kuma kinga ai tun dazu muke kira baya shiga saboda settings dinsa da ya saka idan baya da numberka bazaka samesa" Haseenah tace "Kilan Private line dinsa ne, amma babu ta yanda likita zai sa wayarsa a wannan setting din, definitely yana da wani layin da kowa ke samunsa" Badiyya ta jinginar da kanta jikin gado tana shessheka tace "Wllh na gaji Haseenah, wasa wasa fa yau saura wata daya bikin" Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni zaki gaya ma sauran kwana nawa bayan rana daya ne da nawa da Maheer, ai ko nima an cuceni wannan damuwar da aka sa ki, banda haka da yanzu ai har dake zamu yi ta shirye shiryen bikina, amma ace ana ta abu ba ke" Badiyya dai bata ce komai ba sai hawaye take, Haseenah tayi kasa da murya tace "Toh kece da gaddamar tsiya, Nan nan Zaliha ta kawo mana shawara shekaranjiya kince ba haka ba, wannan kadai ne fa option dinmu yanzu Badiyya" Badiyya tace "Ke ni fa bazan dau kudina in kai ma wani kato wai Malami ba, wa enda na kai a baya wani result din na gani? Duk karyace da cin kudin jama'a in gaya maki, da zan gaya maki nawa Malamai suka ci kudina a shekaru na talatin da biyu a duniya wllh sai kinyi mamaki, ke bari kiji tun ina 22 years nake bin Malamai amma har yau ban ga out come ba, don haka wannan karan ma bazan yi asaran kudina ba, bayan samari haka na dinga ba malamai kudi akan in hada common degree din nan amma dubi sau nawa ana Withdrawing dina from this university to another, ta dalilin wannan Dr Musharraf din ne na gano ashe ina da ilimi rashin maida hankali ne kawai, ai abun akwai mamaki ace wai ni Badiyya ke final year a Nursing Science, alhalin Microbiology ma na kasa shekarun baya" Haseenah tayi wani murmushi tana girgiza kai tace "Uhumm Badiyya kenan, wllh baki dai samu na kwarai bane kawai" Badiyya ta zaro mata ido tace "Ke na fa ce maki duk karya ce Haseenah, haka nan ake cewa ba a samu na kwarai ba amma ni nayi harka da Malamai sun fi 50 kuma idan gaskiya ce ace a cikin mutum hamsin babu na kwarai ko daya? Aa wllh ba da kudina ba wannan karan" Haseenah dai tayi shiruu, Badiyya ta kalleta tace "Ko ke kinsan wani Malami ne?" Da sauri Haseenah ta zaro ido tace "Ah haba dai, wane ni??? ina nake zuwa da zan san Malamai, kuma su waye kawayen nawa banda ku? Ban san kowa ba wllh, kawai shawara na kawo amma ni ba malamin da na sani" Badiyya na goge idonta tace "Shikenan nasan abinda zan yi" Haseenah tace "Me za ki yi?" Badiyya ta mike ta dau handbag dinta tace "Ke dai kawai ki zuba ido" Haseenah tace "Toh Allah Ubangiji ya sa a dace, yanzu yaushe zaku fara final exams din ku?" Badiyya ta nufi kofa tace "Wa ke ta wani final exams" Haseenah tace "Aa Badiyya kar fa kije kiyi 2-0 gwara ki samu ki kammala degree din nan naki successfully, shekara biyar fa ba wasa ba" Badiyya ta hade rai ta juyo tana kallonta tace "Ai sai dai Mayraah tayi 2-0 babu degreen babu miji, tunda har ta shiga gonata... Wallahi in dai ina numfashi i can go to any extent na ganin auren nan ya lalace, kuma lalacewar auren zai yi distablizing dinta har sai ta kasa final exams" Tana gama fadin haka ta fice daga dakin tayi banging kofar, Haseenah dai ta taɓe baki, haka kawai tace mata ga malamin da ke mata aiki har ya karkato da hankalin Maheer gareta wataran abu ya hadasu ta tona mata asiri a familynsu ta shiga uku, waye bai san Badiyya da tonan silili idan abu ya hadaku ba....
Sai bayan Magrib Badiyya ta shigo gida, Ammi na zaune parlor tare da Maheer, ta gaida Ammi, sannan Maheer ma ta gaishesa ciki ciki, zata wuce yace "Zo nan" tsayawa tayi, sai kuma ta juyo tana kallonsa, yace "In taso in sameki ne?" Dawowa tayi ta zauna saman kujera bata ce masa komai ba, yace "Daga ina kike?" Ta daure fuska tace "Daga gidansu Haseenah nake muna shirye shirye" Maheer yace "This should be the last day da zaki fita ki kai magariba a waje, nan ba gidan Hajja bane da kike fita sanda kike so ki dawo sanda kika ga dama, sannan gidan nan ba a fita anyhow without control we are not animal, this should be ur first and last warning" Tuni ta kauda kai zuciyarta na tafarfasa, tabdijam banda su Haseenah da Zaliha da suka ja mata a ina wannan mutumin zai ganta ya dinga yanka mata warning haka kamar er cikinsa, duka duka da shekara nawa ya girmeta?? Ita dai Ammi bata ce komai ba, Lokaci daya ta mike fuuu ta wuce sama, Ammi na kallon Maheer tace "Allah ya shirya mana ita" Maheer yace "Allah abunta har da iskanci saboda taga babu me ce mata komai, gashi Hajja ta gama lalatata, su kansu dangin babanta are not helping matters at all, da anyi magana sai kuce marainiya"
Mayraah na zaune tana karatu a daki Badiyya ta shigo ko sallama babu, Mayraah na kallonta tace "Sannu da zuwa" Wani mugun kallo Badiyya ta watsa mata, daga nan ta hau tube kaya tana diresu kan gado, Mayraah dai ta ci gaba da karatun da take, Badiyyah na shiga bandaki Mayraah ta mike ta bar dakin, a stairs suka hadu da Maheer ta bi sa zuwa dakinsa kamar zata yi kuka tace "Yaya don Allah ka tayani yi ma Ammi magana ko downstairs ne in koma, wllh i can't stay in the same room with Badiyya, ko na mata magana bata kulani, and ta riga tayi occupying ko ina a dakin, ni tsoronta ma nake baxan iya kwana daki daya da ita ba, Ammi kuma tace dole sae na tsaya a dakin" Maheer yace "Leave Ammi alone, ki shigo nan kiyi duk abinda za kiyi, in few weeks time zaki bar mata gidan ita da Ammin ai" Yana fadin haka ya shiga bandaki, Mayraah ta karasa a hankali ta zauna gefen gado. Karfe bakwai na safe Mayraah ta fito daga dakin Maheer kafin Ammi tayi noticing a nan ta kwana, dakinta ta nufa da sauri ta buda kofar dakin a hankali ta shiga, bbu kowa cikin dakin tasan probably tana banɗaki, Mayraah ta fiddo kayan da zata sa yau don karfe tara take da lectures, zaunawa tayi tana jiran fitowar Badiyya amma shiru, ta kalli agogo ganin she is been sitting for 30min ta kalli kofar bandakin, ita dai bata ji an buda ruwa ko kuma dai wani alama da zai nuna mutum na bandakin ba, tana ta zaune bayan wani minti goman ta mike tana bin dakin da kallo, to ko dai bata bandakin ne, Boxes din Badiyyah uku ne ranan da ta zo gidan, yanzu kuma maimakon uku Mayraah sai taga biyu kawai babu na tsakiya, kallon gaban mirror tayi da sauri taga babu wasu turarruka da kayan shafe shafen Badiyya, nan ta lura hatta Charger dinta da power bank dake bedside drawer babu su, kofar bandakin ta nufa ta ɗan tura kafin ta leka ciki taga wayam, fita tayi daga dakin ta tafi dakin Usman don can Maheer ya kwana, knocking tayi sai da ya amsa sannan ta bude ta shiga, ta samesa kwance, ta karasa kusa da shi da sauri tace "Yaya Aunty Badiyyah fa bata gidan nan" Maheer yace "How?" Mayraah tace "Wallahi kuwa, yanzu naje dakin nama yi zaton tana bathroom ina ra jiranta sai daga baya nayi noticing babu jakanta daya a dakin" Maheer yace "To me zanyi kika zo kika tasheni" Mayraah tace "To ko gidan Hajja ta koma?" Maheer yace "Da ya fi mata dai" yana fadin haka ya gyara kwanciyarsa ya juya mata baya, Mayraah ta ɗan turo baki, can tace "Zan je in gaya ma Ammi" bai ce mata komai ba, hakan yasa ta mike ta fita daga dakin, Hankali tashe Ammi ta nufi dakin Mayraah bayan Mayraah taje ta sanar mata Badiyyah bata gidan, Ita dai Mayraah na tsaye bakin kofar dakin nata tana kallon Ammi dake bin ko ina na dakin da kallo har da bude press taga Badiyya ta kwashe kayanta, Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ke yaushe kika lura bata nan?" Mayraah da gabanta ya fadi don bata son Ammi tasan ba a dakin ta kwana ba tace "Kawai ina tashi naga bata nan, ni na zata tana parlor ne at first" Ammi ta fice daga dakin ta koma nata dakin, wayarta ta dauko tayi dialing number Badiyyah taji a kashe, ta rasa yanda zata yi kawai ta kira Hajja, Hajja na dagawa bayan sun gaisa Ammi tace "Hajja Badiyyah ta je gidanki ne?" Hajja tace "Wacece kuma Badiyyah?" Ammi ta kasa cewa komai, nan taji dama bata kira Hajja ba, amma to duk ta rude, Hajja tace "Ban gane Badiyyar da kike nufi ba, bayan warce ke gidanki dama akwai wata Badiyya ne?" Ammi tace "To zan kiraki Hajja" Bata tsaya sauraron Hajja ba ta katse wayar ta ajiye kan gado ta fita da sauri zuwa dakin Maheer, ganin baya dakin ta tafi dakin Usman, Maheer da har ya ci gaba da baccinsa ya bude ido saboda irin kiran sunansa da Ammi take, ya mike zaune yana kallonta, hankali tashe Ammi tace "Maheer Badiyyah bata gidan nan fa" Maheer yace "Toh Ammi jaririya ce ita Badiyyar nan?" Rai bace Ammi tace "Wani irin magana kake gaya min haka, an tashi babu yarinya a gida kace min jaririya ce" Maheer yace "To nima haka na samu labari, kilan gidan kakarta ta tafi ba an mata fada jiya kan ta dawo da daddare ba" Ammi tace "To na kira Hajja kuma daga yanda take amsa min Badiyyah bata je gidanta ba" Maheer yace "Bichi ta tafi kenan" Da damuwa Ammi tace "Wayarta fa a kashe Maheer" Maheer yace "Don Allah kar ki wani damu kanki Ammi, Badiyya fa ba yarinya bace, inda baza a mata fada ba zata yi abinda ta ga dama ta tafi" Ammi ta kasa cewa komai, can ta juya ta fita daga dakin, Maheer ya koma ya kwanta...
Wata dattijuwa ce tsaye kofar gidanta da wani bugujejen riga dake ta zamewa daga shoulder dinta, ga wani uban dankwali ta kima a kai hannunta rike da tsintsiya, fada take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cikin daga murya take cewa "Sannan a karshe sae dae ince Allah ya isa tsakanina da ku, Allah ya saka min wannan cutata da sa ni magana da kuke ba dangin iya ba na baba, kuma ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba bishiyar nan ta girmi iyayen kakanninku, wllhi ban yafe ba har karshen duniya...." Wata mata dake wucewa da kayanta dukundukun tace "Baaba Ladi ina kwana, wani barnar aka maki halan" Mama Ladi ta juya tace "Sai ma kin tambaya?? yaran da kowa yasan Allah ya riga ya tsine masu albarka tun a nan duniya, yanzu don Allah ke a ina kika taɓa ganin an sha rake a karkashin bishiya Delu? Ba fa iyayensu masu zaman kashe wando a kauyen nan suka dasa bishiyar ba, nima gadonsa nayi gun mijina shi ma kuma gun iyayensa da suka gada wajen nasu iyayen ya gada, kinga kuwa ae ba banza bishiyar take ba, tun fa asuba nake aikin share wajen nan sae yanzu na gama, ai kinga an cuceni an ci amanata, sai cikin dare ko wani mahaluki ya tafi ya kwanta ya bai ma hakarkarinsa hakkinsu sai shaidanun yaran su hada daba karkashin bishiyata suna shan rake suna cin gyada, kuma in sha Allahu ƙara zan sa a zagaye min bishiyar da shi, sai in ga ta inda 'ya yan banza za su zauna karkashin bishiyar" Matar dake tsaye tana sosa kanta tana sauraron Mama Ladi tace "Ai ko kawai yanda kika ce ya kamata ayi, abi duk a zagaye wajen kawai da kara, sai dai fa wannan zai ci damin ƙara ba kadan ba tunda bishiyar tsamiyar kin ga ai tana da girma, kina yin haka kuwa kin yi maganinsu, kin ma huta da masu bi maki kofar gida kullum" Machine ne ya tsaya kofar gidan aka sauko rike da akwati, Mama Ladi tayi shiru tayi mitsi mitsi da ido tana kallon warce ta sauko daga saman machine din, can dai tace "Wacece wannan?" Warce ta sakko bata ko kalleta ba ta ja akwatin zuwa cikin er tsakar gidan, Matar dake tsaye tare da Mama Ladi ta washe rubabbun hakoranta tace "Baƙi aka yi daga birni kenan Baaba Ladi" Mama Ladi ta kalleta tace "Ke dai tseguminki yawa ne da shi Delu, nan kika gama bani shawaran banza wai in zagaye bishiya da ƙara kamar don ni kadai aka halitto bishiyar, to ai mugun halina bai kai haka ba da zan ki bari a zauna a sha iska in samu lada a karkashin bishiyata, kawai mata kiyi ta yawo kina doyi kina shiga hakkin jama'a, ke baki jin warin jikinki ne baiwar Allah, ke wari mijinki wari, aa to Allah ya mana tsari... Tafi ki ban waje munafuka" da sauri Delu ta yi gaba, Mama Ladi ta shige gidanta, haɓa ta rike tace "Wa ya maki kwatancen nan Badiyya?" Badiyya da har ta tube kaya ta watsar kasa tace "Nan din ne bazan gane ba Mama Ladi" Mama Ladi tace "Ai ko gaki nan kin kawo kanki tubarkallah, naga baki taɓa zuwa ke kadai bane sai da Hajja kuma kuna zuwa baki wuce awa daya kike wucewa ki bar Hajja tunda ita har sati tana iya yi a kauyen nan, ke sae kice baxa ki iya ba" Badiyya tace "Yanzu dai wanka nake so inyi, wannan garin naku zafi kamar oven...." Mama Ladi tace "To Hegen almajirin me debo min ruwan a rafi bai zo ba, amma akwai ruwan da na adana bari in kai maki kiyi wankan" Daga haka ta fita daga bukkar, Badiyya ta bi ta da kallo, katon drum da ta sa ma kwado ta bude ta dau bokiti ta cika da ruwa tace "Banda ke ma wa ya isa yasa in bude wannan ajiyar tawa, ruwan nan yafi wata shidda komin rashin ruwan da nake bana taɓa sa, sai dae rashin ruwan ya kasheni babu ruwana, nasan wataran zai min amfani, to yau ga amfaninsa" Badiyya ta fito da sosonta da Sabulu ta wuce ɗan karamin bandakin dake tsakar gidan bayan Mama Ladi ta kai mata ruwan, Mama Ladi tace "Allahu Akbar, wllh sak marigayiya, bana mantawa haka take zuwa ta min sati a garin nan tun ma bata yi aure ba, ita kadai ce bata kyamatar inda nake sae er uwata Hajja kaka, Allah dai ya ji ƙan Rukayyah, shi yasa komi na samu er ta Badiyya nake ajiye ma idan na samu me shiga kano in basa amana ya kai mata" Badiyya na fitowa daga wanka ta tarar Mama Ladi ta ajiye mata kunu da kosai, ta ɗan yi shafe shafenta sannan ta fara cin abinci don karfe biyu na rana ake nema, Mama Ladi har da shimfida mata sabon zanin gado a kan gadon karfenta, Mama Ladi ta dawo ta zauna gefenta tace "Ban ji kince er uwata Hajja tace ki gaisheni ba" Badiyya ta fashe da kuka kamar jira take, a gigice Mama Ladi ta saki kara tace "Wayyo Allahna, mutuwa Hajjan tayi? Na shiga uku na lalace, ta mutu ne?" Cikin kuka Badiyyah tace "Tana nan Mama Ladi ba abinda ya sameta, kawai dama na zo in gaya maki abinda ake min ne saboda an ga bani da kowa, anga Abbana da Ummata basu da rai" ta kare maganar tana kuka sosai, Mama Ladi tace "Subhanallahi me ake maki Badiyya, su fa mutane har yanzu basu gane rikon maraya akwai tsarkakkiya ba shi yasa da yawan jama'a wuta za su, wa yace masu ana ma marainiya haka? Yanzu basu san ta dalilinki duk sai su shiga wuta ba" Nan Badiyya ta gyara zama ta labarta ma Mama Ladi duk abinda ke faruwa, na karya da na gaskiya, wanda na karyar ma yafi yawa, Mama Ladi tayi shiru tana kallonta baki bude, can ta gyada kai a hankali tace "Tabbas Hajja ta kirani ta sanar min da wannan biki har nace idan Allah ya nufa in zo to zan zo, don gaskiya naci alwashin sai bikinki zan je garin kano don kece tawa, Ita kanta Ammin ta kirani ta sanar min da batun bikin na mata Allah ya sanya alkhairi kawai, ko ba komai hakan ma zan samu lada, to da naji har da na Mashir ne ma yasa na canza shawaran zanje bikin don Mashir nawa ne, ashe kwace suka maki suka makala ma ita meran, ikon Allah, mutane sun zama abinda suka zama a harkan rashin tsoron Allah... Amma Ammi ta bani mamaki ainun, wllh ta ban mamaki, ita Hajja dama bazan kullaceta ba tunda nasan Ammin ce ke juyata yanda ta