Showing 27001 words to 30000 words out of 391264 words

Chapter 10 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

3514

kai chief owais yayi alamar eh

"Kasan ban ta6a ganin ta ba, saboda busy da nake shiga, amma tana araina, yau ka tabbatar tazo dinner din nan, Ina son ganin ta, ka kawo min ita gabana in sanya mata albarka"

"In sha Allah dad"

"Good, Ka shiga ka karasa shiryawa zan jira ka a dining room" amsa mashi yai da toh.



Har Ya buWe kofar zai fita ya Wan dakata tare da waiwayowa baya ya kalli chief dake kallon shi



"zan fada mata, tayi dacen miji," yana fada ya fuce daga dakin, qasaitaccen murmushi chief ya saki, fatan shi kamar yadda kowa ke fadin tayi dacen miji itama tayi alfahari dashi a matsayin a bokin rayuwarta.

Da wannan tunanin ya nufi walk-in closet dinsa, within minutes Ya kamma shiryawa cikin Jalabiya launin ocean blue.

A dining room ya taras da su gaba dayan su sun hallara, tun daga kan momynsa malikat tare da younger sis dinsa Hindu ?ar matashiya ce da bazata wuce 22 Years ba, Black beauty tana asanye cikin shiga ta jumpsuit Dark navy, kitson zanene akanta wutsiyar gashin har kan shoulders din ta, Allah yayi ta da ruwan kyau kamar ita ta zana kanta, Komai nata ?aramine Wan pink lips dinta da Asian eyes din ta, ga dogon hanci, Bata da ?iba siririya ce, a haka structure din jikinta ba karamin kyau ne da shi ba, Kamannin ta sak dana Mommyn su Gimbiya Malikat Sarauta.



Waya bayan Waya yayi hugging dinsu cikin mutunta juna suka gaisa, kafin ya zauna sukayi breakfast dinsu, daddy sharafudden yaji dadin cin abinci tare da Wan nasa, har abaki yake bashi bayan sun kammala yayi masu sallama agurguje Ya nufo gidansa.





_________________________
'?





A 6angaren su Unaisah kuwa bayan kammala sallar asuba, bacci mai nauyi yayi awon gaba da su kamar matattu, har wurin karfe tara babu alamun zasu farka, ummi sai faman yin zarya ta ke yi daga dakin ta zuwa nasu don ganin ko sun farka, saboda tana son ta fara gyara masu jikin su, ganin baccin nasu bamai ?arewa bane yasa tabi su Waya bayan Waya ta farkar da su, wani abu da ya Waure mata kai, duk wanda ta tada daga cikin su sai taga ya watsa da gudu ya nufi upstairs second floor, da sauri tabi bayan su don ganin ina za su je, a dakin danish ta same su zu?unne bakin gadon shi suna kuka kamar ran su zai fita, hankali a tashe ta tambaye su meya faru suke kuka? Cikin shesshe?ar kuka suka ce mata meyasa danish din su bai farka ba? Sun hana idon su bacci jiya sun ro?i Allah akan ya bashi lafiya amma shine Allah bai kar6i addu'arsu ba bayan wahalar da su ka sha ko dan saboda danish baiyi imani da shi ba ne....." waro idanu waje ummi tayi tana kallon su, ita dai unaisah ko magana ma takasa furtawa lamarin yafi karfin ta ashe har yanzu akwai sauran rina akaba, abun ka ga masu ?arancin ilmin addini


Lallashin su ummi da unaisah suka dinga yi suna basu baki, akan su yi hakuri su daina fadin hakan babu kyau, gaggawa aikin shaidan ne, indai sunyi imani da Allah to su bi komai a sannu in sha Allah Wan uwan su zai farka..." da?yar su ka shawo kansu har suka samu komai ya lafa, ta sanya suka fito daga dakin ta rufe mashi ?ofa

Ko da aka shirya masu breakfast kasa ci su ka yi saboda fargaba da zullumin kada su rasa Wan uwan su, Hankalin ummi duk ya tashi saboda tausayin su da ya kamata, Kamar marasa lafiya haka suka koma, lalla6a su ta dinga yi har ta samu suka ci abincin kaWan bayan sun gama ne ta tarasu a falo ta fada masu dangane da Farewell dinner din da zasu halarta na uncle din chief, sun ji dadi yau zasu shiga cikin family din chief koba komai zasu Webe kewar abun da ke damun su, duk cikin su mutun Wayace batayi farin ciki da fitarsu ba, hakanan take jin gabanta na faduwa, babban abun da take jimawa ba lallai su samu kar6uwa a wurin family din chief ba, bugu da kari rashin wayewar ?an uwanta, yafi komai Waga mata hankali, tana jin tsoron su shiga bainar jama'a su yi kauyacin da zaisa a gane jahilcin su harma a goranta masu ko a ?yamace su.

Hankalinta sam ya?i kwanciya, har sai da taja aunty umminsu gefe Waya ta faWa mata abunda take zullumi tace tana neman alfarmar abarsu su zauna a gida kada aje da su wurin dinner din nan.

Ummin tace ta kwantar da hankalin ta, ba abun da zai faru saboda basu kadai zasu tafi ba, hada su boss man kuma tasan bazasu bari a wulakanta su ba awurin taron zasu basu kariya, sannan tasha jin labarin familyn obinna mutanene masu karamci da daraja Wan adam don haka kada ta sanya damuwa aranta in sha Allah zasu samu kar6uwa a wurin su.

Jin wannan maganar ya sa hankalin ta ya kwanta, Har ta fara zumuWin lokaci ya cika don atafi da su.



Ba tare da 6ata lokaci ba, Ummi ta tattara matan suka shiga Home beauty saloon din gidan, domin gyara masu jikin su, mazan kuma taj ne ya tafi da su 6angaren jami'an isod na gidan acan za'a gyara masu sumar kansu, Waya bayan Waya ta wanke ma kowan nan su sumar kanshi tagyarata tsaf tayi masu hair style kala kala, Unaisah da batool kalar nasu gyaran gashin all layers around ne yayi bala'en yi masu kyau sumar kan har kyalli take yi tana Waukar ido saboda mayukan da aka yi masu amfani da su, gashin ya ciza launin shi dark brown yayi washar washar da shi daga baya ya lullu6e wuyansu da tsakiyar bayansu kamar hijabi, Azeeza da jemimah kuwa kalar nasu styal din braided bun ne, wanda ake dun?ule gashin daga tsakiya sai kaga ya yi kamar donut, gyaran gashin su yayi kyau sai ya ?ara fito masu da beauty baby face din su, sun fito a jar fatar su ta turawa, Parveen da Hannah su nasu gyaran gashin Classy ponytails ne yara sun fito suffarsu ta kyawawan ?an mata, Sai farin ciki sukeyi tamkar babu abunda ke damun su, bayan an gama gyaran gashin, ummi tafara gyara masu kafafuwansu da akaifinsu, Haki?a tayi kokarin yadda kasan ?a'?an ta haka ta dinga tsaftace su ciki da bai, har hakoransu bata bari ba sai tayi masu amfani da tooth care product wurin wanke masu su, dalilin dayasa take yi masu gyara duk da boss yace kayan da za'a sanya masu ya zamanto sun lullu6e ko'ina na jikin su, ita tasan ba yadda za'ay a shiga da yaran nan wurin dinner ta prime minister ba tare da security din dake tsaron wurin su sanyasu cire mask din fuskarsu ba, shiyasa ta dage damtse wurin gyara su, don agansu da mutuncin su, saboda itama maganar unaisah ta sosa ranta, batason ayi masu kallon ?as?anci, harta fatarsu sai da ummi tagyare masu ita, Kamar ?a'?an Furanni saboda tsabar Kyan da su ka yi, ita kanta da take kallon su ba karamin tafiya da imanin ta suke yi ba, inaga idan suka shiga wurin dinner din tabbas zasu Ja hankalin jama'a,



Bari dai in takaice maku zance, Ummi har yadda zasuyi magana ta ?an gayu wayayyu da yadda zasu yi tafiya mai jan hankali sai da ta koya ma su, duk don kada suyi kauyacin da za'a tozarta su, sai wuraren sallar Juma'a ta sallame su tace suje su yi sallah after sun kammala su kwanta su huta kafin lokaci ya cika, A lokacin itama daki ta shiga don ta yi sallah ta kuma kwanta ta huta, fatanta Allah yasa taj ya nema mata alfarma a wurin chief ko ta samu ta fita yawo anjima

Badajimawa ba, Su sajeed suka dawo atare da taj, Wa'iyazubilla yadda kasan mazan hurul aini a kyau, Musamman masu tarin sumar cikin su, Sajeed da Naufal sai Javed, wani hadadden gyaran suma akayi masu irin na gayun nan, yadda kasan ya'yan wani shege mai ji da naira, shi kan shi haris da bai kai su sumar kai ba, gyaran gashin da akayi mashi ya kara fiddo mashi da Inner beauty dinsa, bayan taj ya rako su sun dawo gidan basu taras da ?an uwansu a falon ba duk suna a daki suna hutawa A falo suka zauna suna jiran lokaci ya ?arasa cika, dadi suke ji za'aje da su wani wuri kamar su zuba ruwa ?asa su sha tsabar murna.



*DINNER HALL*



Wuraren karfe huWu da wanu abu.



Katafaren ?akin taro ne dake a cikin Obie Estate, Aljannar duniya ce mai zaman kanta, saboda tsabar haduwar Hall din idan Ka shiga ciki gaba Waya zaka rude ka kasa tantance a ina kake ma, musamman a yanzu da yasha uban decoration an kawata shi da kayan ado masu ?yal?yali da Waukar ido, gaba Waya kewayen hall din Fusatattun sojoji ne majiya ?arfi ke tsaron shi tare da Canadian polices ga kuma gwarazan jami'an Isod, bayan ga wadannan jami'an hada na'urorin cctv dake a kowace kusurwa har ta cikin fitilun lantarki da jikin kofafi, ciki da wajen Wakin taron domin ba su tsaro daga dukkan wani abun cutarwa, yadda aka sanya tsaro a hall din bana tunanin ko sauro zai iya haura ?afa Ya shiga batare da alburushin bindiga Ya tarwatsa kan shi ba, Entry way na shiga hall din tana a cikin Garden din gidan An kawata saman ta da gefenta da adon string lights mai walwali da daukar ido, ga wani shamfidaddan carpet da zai isar dakai cikin dakin taron lallausan gaske daga saman Entry door din anyi wani rubutu da adon furanni aka sanya



*Welcome to the farewell dinner of Prime minister Hateem Obinna*



Idan muka koma cikin hall Win kuwa sai dai muce masha Allah, Zahra world of beauty interior designers sun baje basirar su wurin ?awata cikin Wakin taron, wasu haddun dinner tables ne rukuni rukuni a kalla sun kai set hamsin kowani table yana a kewaye da rantsastsun kujeru masu nunfashi zubin bean bag chairs, daga kan kowani table an ?awata shi da Centerpiece wanda ya kunshi Glass candle sticks An kunna wutar su gawanin ban sha'awa a kewaye da containers na furanni launuka daban daban, ga wasu jerin Crystal glasses ?an uban su masu Waukar ido, bayan su kuma akwai Silverware and napkins with table ware a kowani dinner table hada menu card ajiye bisa tables din, komai fa ya tsaru ga wasu Crystal Sparkling chandiliers masu haskaka tsakiyar Wakin taron da wani irin twinkling lights hakan ba?aramin ?awata Wakin taron yayi ba, ga wata ni'ima dake kurWaWowa ta cikin na'urorin A.c mai ratsa sassan jikin mutun, idan muka koma 6angaren abun da za'aci hohoho duniyar dadi wato daga can 6angare guda dinner buffet ne jerin nau'ikan abincine da aka killace su a cikin chafing dishes wato wani irin aroma ne ke tashi na daddaWan kamshin abinci mai cika makoshi, ga jerin large glass bowls na kayan marmari da zungura zunguren glasses na Juice masu sanyi komai fa an tanada, babu ce kadai ke babu a dakin taron, anyi 6arin dollar, naira kuwa ta raina kanta a wurin, dukiyace aka narkar wurin ?awata ko'ina, idan kuwa nace zan fayyace komai dake a hall din tabbas zamu ?are takun karshe ne wurin kwatanta haduwarshi shiyasa na takaita da bayani don mu shiga kaitsaye cikin taron.



Sannu a hankali dan?ara dan?aran motocin su na alfarma zubin Mercedes benz S. Class suka soma shararowa izuwa cikin garden din a jere suke tafiya yayin da jami'an sojojin dake take masu baya suke bin motocin da kafafuwansu suke tafiya gefe da gefen su, hannayen su ru?e da jibga jibgan bindigu ga wasu kuma soke a qugunansu sai faman mazurai su ke yi, tamkar a filin daga.



?arasowar motocin ke da wuya A hanzarce Sojojin suka buWe back seat na motar farko, A hankali sheikha mujeedat ta zuro kafarta dake asanye cikin hadaddun takalman alfarma wadanda kudinsu kadai ya ishi wani talakan jari, kafin ta ?arasa fitowa tabarakallahu ahsanun khalikin gaba Waya sojojin dake a wurin saida suka saki baki kamar lehen sakarai saboda tsabar kallon ta a fakaice.



Embell??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ished abaya ce a jikinta launin royal blue anyi mata adon stones work, fuskarta tana asanye da Gold chain mask, adon dake akan fuskarta kaWai abun kallo ne, tayi masifar haduwa, daga ?asa har sama ta ca6a ado nasu na sarauta tamkar Wawisu a fagen haWuwa, bata jima da fitowa ba, jami'an suka budewa Prime minister hateem other side din motar ya fito tamkar tauraro a cikin taurari yayi shiga na mutunci, hadaddiyar shadda ce a jikin shi gezna launin blue anyi amshi senator style abun ka ga dogon namiji ga kira kayan sun zauna mashi kamar a jikin shi aka dinka su, wata expensive watch ce a hannunsa sai kyalli take tana daukar ido, Yatsun hannunsa na sanye da zoben azurfa mai shegen kyau, sumar kannan tashi tasha gyara har ta gaji da haduwa,

Bayan fitowarsu motar dake abayansu tasu Yazrin da Nazli ce, Lokacin da suka fito Kiris Ya rage zuciyoyin wasu su buga saboda tsabar haduwar wankan dasuka dauka na emirati abaya launin Silver, kowaccensu ta manna glasses a idanuwanta, ga adon gold knucles rings dake a yatsun hannayensu, sun yi rolling veils a kansu yadda kasan asace su saboda kyau.



Bayan fitowar su Nazli, sojojin suka cigaba da buWe ma sauran motocinsu, gaba Waya zaratan samarin family din maza da iyayensu ankon shadda gezna su ka yi, matasan ?an matan kuwa arab abaya suka sanya masu kyau da tsada na alfarma na kuma kece raini da fita tsara, wasu sun sanya lace abaya, wasu embellished abaya wasu open front abaya, wasu kaftan abaya, wasu egyptian abaya kowa da kalar nashi wankan, kowaccen su tayi lagin gyale akanta, wasu ma babu gyalen zallar sumar kansu ce har gadon baya kamar indiyawa, duk wadda ka kalli wuyanta zaka ganshi manne da ziririyar sarka ta diamond wasu kuma ta zinari, gayu mutanan Allah, Hajiya saratu fa ta dauki kur adakanta rantsastsiyar dubai abaya ce a jikinta tsadaddar gaske launin maroon rigar harta gaji da haduwa abunka ga manyan mata masu dirin jiki kayan sun ladabtu a jikin su kamar donsu aka kera su, kwansu da kwarkwatansu suka jera izuwa cikin hall din, iyayen su maza kowannansu yana ruke da hannun matarshi, wani irin daddaWan sautin kiWe kiWe da raye raye ne ya karaWe ko'ina na Wakin taron, Hada wani irin busa tamkar na sarewa Suna tafiya suna taka rawar dattako, cikin nishadi da raha, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki da annushuwa.



Prime minister Hateem ne yafara shiga hannun shi ru?e dana gimbiya mujeedat, daga bayan su Nazli da Yazrin ne, bayan su sai Mai girma sharafuddeen shima ya shiga hannun shi ru?e dana gimbiya malikat, Wayan hannun nashi ya ru?o hannun uwargidansa Hajiya laurat daga bayan su Chief Owais ne wanda zan iya cewa shine farkon haduwa saboda kyawun surar shi, Shaddar jikin shi ta bayyana zazzafan kyanshi kamar shi ya ?era kanshi, hannun shi yana a ru?e dana kanwarshi Hindu itama ta dauki wankan abaya.



Bayan wucewarsu Sir mubarak Ya shigo hannun shi ruke dana Mom turai, daga bayan su Zaki ne tare dr Jazz sai Ibad.



Fuskar kowan nan su da fara'a, bayan shigarsu Senate lateef ya shigo shima tare da Mom madina hannun su ru?e dana juna, Yayin da zulaihat da Ziyad suke abiye da bayan su.



Abun gwanin ban sha'awa, bayan suma sun shiga His excellency abdul Razak ya shigo tare da her excellency Muhibbat, suma sun dauki nasu wankan, atare da ya'yan su suka shigo Captain Yaseer da Yusra.



Daga su sai His excellency Deen Ya shigo fuskar nan awashe da annuri yayin da yake a ru?e da hannun her excellency Hajiya Jameela, daga bayan su Dr nawaz ne da Wan uwansa justice Nadeem sun dauki nasu adon.



Basu jima da wucewa ba, Hajiya saratu tamu ta mutunci ta shigo hannunta ru?e dana Pravin sunyi matu?ar haWuwa abunka ga ba'indiye shaddar tayi mashi kyau.



Daga bayan su Twins ne zayn da zayn wohoho wanka Yabi jiki, na madina masu kamshin zamzam tsayawa fasalta kawunsu a cikin shadda 6ata baki ne, Hannayensu na ru?e dana kanwarsu Faryat, ta ca6a uban ado ciki riga red colour duk matasan wurin babu wadda tayi shigar fitsara irinta, abayar jikinta ta matse kirjinta, ko arzi?in Wan kwalli babu akanta sai zallar kitson kalabarta, gaba dayan ?amshin turaren su ya gauraya da na iskar A.c wata irin ni'ima ke tasowa.



Har sun nufi inda aka tanadar masu kowa ya nannaWe rigarsa zai zauna, kamar daga sama muryar Mc ta katse su da cewa"ban bada iznin a zauna ba"! Gaba Waya suka kai idanunsu gare shi don ganin wani isasshen ne mai walkin Sa, Ruke yake da mic can saman step fuskar nan ta shi a murtuke tsoro tukuf da shi, gashin kanshi duk hurhura hatta jagirarsa da gashin bakin shi hurhurar ce ga wani dogon gemu har kan cikin sa, daga ganinsa Wan drama ne, ganin shi bakuwar fuska yasa suka soma tunanin wanene wannan?



Hajiya saratu har ta fara karkata baki zata fara zabga mashi masifa muryarshi ta katse mata hanzarinta



Kirari ya soma korowa yana nuna hanyar shigowa hall din da mic din hannun shi, gaba Waya suka kai idanunsu don ganin mai shigowa Obinna ne Ya shigo Cikin shiga ta alfarma tare da Babban amininsa Jan kunne.



Lokaci Waya suka sauke ajiyar zuciya, tare da sakin murmushi, saboda jin yadda ake yabon mahaifinsu bayan mc din yagama da baba obie Ya koma kan prime minister ya soma koWa shi yana fadin.



_Tsakin tama gagara tauna Prime minister Hateem Obinna, Shugaba mai cikakken iko, na Mujeedat ba maza a gabanka. Kasar Canada taka ce, Namijin duniya Taka lafiya, hasken wata sha kallo, fari mai farar aniya, adalin shugaba namu na mutun ci_



sautin tafin hannayensu ne ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login