Showing 78001 words to 81000 words out of 391264 words

Chapter 27 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2611





"Wallahi idan kina son zaman lafiya ki janye zancen hadani dake da gaggawa idan ba haka ba ciwon zuciyane zaiyi silar mutuwarki, saboda ni nan da kike gani na ba mutumin kirki bane Wan iska ne ni, sannan bani da mutunci .." Ras taji gabanta ya fadi, tunda yafara magana bai kalle ba, baima san wacece



wani irin wahalallan yawu ta haWiya, amatukar rude take kallon shi jikinta na kerma



"Nasan bazaki so ya'yanki su yi rashin dacen uba ba, shiyasa nake gargadinki, tun kafin kiyi danasani mara amfani, ke in banda ma haWama da rashin sanin ciwon kai ina ke ina Zayn pravin obinna? Nayi maki kama da sa'ar auranki? Wai ke yar wacece ma"?



Hawayen dake taruwa a cikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta

Hankalin shi kwance yaci gaba da cewa"Ni nasan ba hakanan kika kyale mommy ba, Allah kadai Yasan me kika kulla da har ta amince zata hada ni da ke, idan ma kwaWayin abun duniyane ya rufe maki ido to ki fadamin nawa kikeso tun daga miliyan biyar har abun da yai sama zan baki kije kija jari ki rufawa kanki asiri...." sautin shesshekar kukanta ne ya cika masa kunnansa, a zafafe ya juya da niyar ya dauke ta da mari kamar an ruke hannunsa ya dakata cak Yana huci idanunsa akan fuskar zahra da hawaye ya gama wanke ta, bakomai ne yaja hankalin shi ba face kyawun fuskarta ba laifi tana da sura dai dai wadaidai saidai baya jin zai iya kula macen da bata kai matsayinsa ba

Sassauta muryarshi yayi"ke, yi min shiru in ba haka ba zan 6ata maki rai"



yatsun hannunta na kerma ta toshe bakinta, sam takasa kallon cikin idanunshi gashi ya matso kusa da ita kamshin turarensa duk Ya gama kashe mata jikinta

"Idan kinason zaman lafiyar, Kije ki fada mata, baki sona banyi maki ba"muryarya da shesshekar kuka tace"kayi hakuri amma ni bazan iyaba, saboda ina ganin girmanta, sai dai kai ka je ka faWa mata" dakyar ta kare maganar tana faman jan numfashi



"Tausayinki nake ji bana so kiyi danasani, wallahi bani da mutunci, ni banma shirya yin aure ba, saboda baya agabana, Ni nafi sha'awar inyi sharholiya ta son raina" ya fada yana shafa sajen fuskarsa" yanzu ke kin yarda ki auri dan iska mai mu'amala da matan banza"? Ya fada yana cizon lips dinsa da masifa

Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ita kanta batasan tayi hakan ba, batasan ya akai zuciyarta take jin kaunarsa ba, a maimakon taji haushin kalamansa.



Dafe kanshi yai da hannu Waya kafin ya furta"look, Idan burgeki nakeyi naji zan baki kaina, amma ki janye batun nan, saboda ni ban shirya ma aure ba, ko auran zanyi bazan auri wadda batakai aji na ba, bana so ki jefa rayuwarki cikin hatsari, kada kiga kamar ina lallashinki mommyn mu kaifi Wayace idan ta furta magana babu wanda ya isa ya dakatar da ita, shiyasa nake lalla6aki saboda ke kadaice zaki canza ra'ayinta" zahra dake ta faman yin shesshekar kuka muryarta na rawa tace"har abada bazan iya tunkararta da maganar nan ba sai dai kai kaje ka fada mata..." bata ?are maganar ba ya daka mata tsawar data firgitar da ita

Nuna ta yayi da yatsan hannun shi"Share hawayen kan fuskarki, ki tashi muje ki fada mata baki sona banyi maki ba" muryarta kasa kasa tace"ay na fada maka bazan iyaba..." bata kare maganar ba, taji ya haWe bakinsa acikin nata, wani irin bugu zuciyarta tayi mata, gaba Waya takasa tabuka komai, har sai da Ya gama abunda zaiyi kafin ya zame harshensa, Yai saurin zuge glass din motar Ya tofar da yawun bakinsa.



tsabar wulakanci Ya zari hanky yana kara goge bakinsa kamar wanda ya ta6a najasa, rushewa tayi da matsanancin kuka ganin irin wulakancin da yai mata, abunda yafi ?ona mata rai sanya mata harshe da yai abakinta, arayuwarta ta tsani namijin da ba muharraminta ba ya ta6a ta,

Tsawa yakuma daka mata tuni ta shiga taitayinta.



"KaWan kika gani, wannan so mun ta6ine idan har baki janye kudirinki akaina ba, zan cigaba da amfani dake ne" ya faWa yana mai kara jaddada mata

"Ki share hawayen nan, Ki tashi muje ki faWa mata kinjanye" muryarta na kerma ta amsa mashi da toh, shu'umin murmushin gefen fuska yasaki, dama yasan zata amince ko dan saboda abinda yai mata don ya fahinci ba yar hannu bace tana da kamun kai shiyasa ya tsorata ta.



Hanky ta zaro ta share hawayen fuskarta, sannan ta daidaita nutsuwarta, kafin ta buWe motar, ta fito shima ya fito ta Wayan bangaren suka nufi hajiya saratu dake atsaye can nesa da su.



Tunkafin su karaso ta nufosu, fuskarta da fara'a tace"Son, Ina fata kun sasanta kanku"!

Nunata zayn yai"ki fada mata abun da kika gaya min acikin mota" amsa mashi tayi da toh kafin ta kalli hajiya saratu zuciyarta cike fal da tsoronsa ta ce"Mun gama magana dashi, Kuma mun fahimci juna" a gigice zayn yake kallon zahra jin abunda tace, zuciyarsa ba karamar hasala tayi ba, bai ta6a tsammanin yarinyar zatay taurin kai ba.



"Zahra kin tabbata yayi maki? Amma meyasa naga idanunki sunyi ja"? Da sauri zahra tace"kaina ne keyi min ciwo, har fada masa nayi, shine yace yakamata na tafi gida na huta, zamuyi magana awaya..." da tsantsar mamaki zayn yake kallonta, gashi ba halin Ya karyatata, don ya fahimci ta kama zuciyar mommynsu.



"Naji dadi my son, dama nasan bazaka ?i tayin da nayi maka ba, da ace zaid ne ba lallai ya amince ba saboda shi na daddynsa ne kai kuma nawa ne, hakika yau ka faranta raina my son, Allah yayi maka albarka, zahra kema nagode maki sosai da kika aminta da tayina in sha Allah ba zakuyi danasani ba, Ina da tabbacin hakan, Ta fada tare da janyo zayn da zahra tayi huggin dinsu tana Wan bubbuga bayansu, sai faman farin ciki takeyi yayin da su kuma zuciyoyin su suke a kuntacce da bakin ciki.



"Zayn ko zaka kaita, Gida"? Ta fada bayan ta raba su daga jikinta, da sauri zahra tace"mommy kin manta nazo da mota dina"

"Oh eh hakane, na shafa'a, Muje son mu rakata ta tafi gida" atare da zayn suka raka zahra bakin mota bayan ta shiga ta zauna, hajiya saratu tace"surukata, Anya zaki iya driving dinnan kuwa? Ko dai zayn yakai ki" wani irin mugun kallo zayn ya watsama zahra da sauri tace"a'a mommy, wallahi zan iya, ay ba sosai nake jin ciwon kan ba"



"Toh zahra Ki kula min da kanki sannan ki gaishe min da mutanan gidan"



"In sha Allah ngde ssae"



Harara hajiya saratu ta watsa ma zayn"kai bazakai mata bankwanan ba, ahaka zakuyi auren" yana faman yamutsa fuska yace"bye, sai mun yi waya" aran shi ya furta "zakiyi danasani,"



Bayan ta baro estate din har ta hau kan titi tana driving, zuciyarta bata daina tariyo mata kalaman zayn ba.



Uban tagumi aneelerh ta zabga da hannu Waya, tana kallon zahara data kammala bata labari



"Zahra kinyi kuskure wlh, meyasa baki Wauki shawararshi ba kin fada mata baki son shi? Zahra ina guje maki auran mutun mara kunya irin shi! Kowace uwa burinta ta sama ma ya'yanta uba nagari wanda zasu koyi da shi su kuma yi alfahari da shi ba irin zayn ba, sam bai dace dake ba" zuciyarta ajagule tafada, kwata kwata zayn bai kwanta mata aranta ba, tun kafin ma ta ganshi.





Zahra Tana shesshekar kuka ta ruko hannunta"ki tayani da addu'a, ita nafi bukata, Aunty aneeleeh bawai nakasa fada mata bane, Ina son shi ne"

Jinjina kai aneeleeh tayi"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Shikenan, zan tayaki da addu'a Idan alkhairi ne shi agare ki Allah Ya tabbatar mana dashi, idan kuma akasin hakan zan roki Allah Ya shiga tsakaninku, bayan haka dole su mami suji maganar nan"



kwantar mata da hankali aneelerh tacigaba dayi saida komai ya lafa tukunna aneelerh tace"Ina alkwarina? Kince zaki Waukar min hotunan dinner in gani, Jiya da su na kwana araina, ganin kin kwaso gajiyane yasa ban takura maki ba"



Murmushi zahra tasaki tunawa da Unaisah, yarinyar data kwanta mata aran ta.



"Aunty aneeelerh, akwai labari, zaki sha kanun labarai, " ta fada tare da janye baby juanid dake langwa6e ajikinta, kamar maijin bacci Yai shiru Yanata sauraronsu.



Gado Ta nufa ta dauko purse dinta ta curo wayarta donta nuna ma aneeleeh hotunan da ta dauka tare da unaisah



Kwatsam wayar ta fara ringing, da sauri tayi picking ganin sunan abie

Barka da safiya abie ina kwana"?

"Lafiyou, zahra, Ina aneeleeh ne"? Da sauri tace gatanan adakina



"Okey ki fada mata, ?awarta ta turo min da sako ta layina, ta zo ta same ni a daki ina jiranta!" amsa mashi tayi da toh bayan ya kashe kiran ta dubu Aneelerh dake kallon ta, cike da son jin me abie Ya faWa mata.





"Abie ne ya kira, yace in faWa maki Kawarki ta tura mashi da sako ta layin shi kije ki same shi adaki"



Da alamun mamaki Aneeleerh ta furta"?awata kuma? Anya kuwa abie ya karanta sakon dai dai? In bahaka ba ni wata ?awace gare ni da zan bata layin abie"



"Aunty Aneelerh kije kawai ki gani, bamusan menene aka turo ba" amsawa tayi da toh a hanzarce ta mike ta bar junaid adakin.



Ruko hannun shi zahra tayi"zonan In nuna maka hotunan dinner,"

Gefen gado ta zauna tare da daura shi kan laps dinta, ta buWe gallery tana nuna mashi hotunansu, lokacin data buWe hoton Unaisah, wuff Junaid Ya fusge wayar daga hannunta Yana fadin"Angel! angel! angel"! Har saida gaban zahra Ya fadi, a matukar rude take kallon shi ba tare data fahimci me yake nufi ba.





*SALSABEEL=ث?*



Zaune Yake kan sofa hannun shi ruke da wayar shi, Har ya kammala shiryawa, sai faman duba agogo Yake yi, Har ya fara gajiya da jiran su, Wagowa yai tare da kallon su, suna a zaune tsakar falon suna cin abinci, mutun Waya ce ke babu acikin su, Khadeeja dake acan cikin toilet tana wanka, a kalla ta shafe kusan awa Waya da rabi har yanzu bata fito ba, gashi har yan uwan ta sun kammala shiyawa.



"Dan Allah ku yi sauri ku ?arasa, kun ga har karfe sha biyu ta buga" amsa mashi sukayi da toh

"Yaya salsabeel, Khadeeja fa? Har yanzu bata fito ba, ko ban da ita zamu tafi" rubeena ce tayi maganar.





"Bansan ya zanyi da ita ba, so take ta 6ata mana lokaci, bari naje na dubo ta" ya fada tare da mi?ewa Ya nufi upstairs.



"Wallahi Dama mu tafi mubar ta a gida, kada ta mana hauka, tun da ya salsabeel Yace wurin gasar kyau zamu je kuma in muka ci za'a bamu kyautar wani abu" acewar hibba.



rubeena na murmushi tace"ni zan cinye ma gasar saboda nafi ku kyau" harara hawwa ta galla mata"a haka din? Dubi kumatunki, kuma ay cewa yai sun fi son mace doguwa mai gashi, mara jiki, me dogon hanci" daure fuska rubina tayi rai a6ace tace"wlh indai bani zanci ba sai dai kowa ya rasa" ta fada tare dakai hannu ta dauki robar zuma ta dinga watsa masu akan rigunansu, azabure suka mike suna faman zare idanunsu ganin ta 6ata wankan su.



"Wallahi baki isa ba, Saina rama mana" sarah ce ta fada da sauri ta fisge zumar ta matsa mata a jikin rigarta, fashewa tayi da kuka tana fadin wayyo Allah ya salsabeel sun 6ata min kayana, shikenan ni bazanci gasar kyau ba, zu?unnawa tayi gaban kayan abincin tana haki ta dauki coke da niygar ta watsa masu, dam?o hannunta Hawwa tayi nan fa faWa ya kacame a tsakaninsu, daga wadda za'aja ja ma gashin kai sai wadda aka ca6e ma kwalliyar fuskarta, Mubeen dake a zaune yana kallon su sai faman tikar dariya yakeyi



Duk wannan budurin da sukeyi salsabeel bai sani ba, Yana atsaye bakin kofar toilet din dakin su khadeeja, ba irin bugun kofar da baiyi mata ba akan ta fito, amma ta?i ko tanka mashi.



Rai a6ace yace"wallahi idan kika bari nasa kafa nabar dakin nan sai dai ki zauna agida, Babu inda zaki je" muryarta da shesshekar kuka tace"wayyo Allah ya salsabeel ba kaine kace zamuje gasar kyau ba, shine fa nakeso in koma fara" waro ido waje yai jin soki burutsin ta, cike da takaici ya furta"Baki da hankali ne? Tayaya za'ai ki koma fara? Waya fada maki sai farare suke cin gasar kyau? to bari ki ji in fada maki bakake sune suka fi lashe gasar" muryarta da shagwa6a tace"ni dai Allah ba wani nan wayo kakeso kai min don kada inci"

Dafe kanshi yai da hannu Waya"ke zaki fito ko ba zaki fito ba" shiru tayi bata tanka masa ba,

Buga kofar yai da karfi"Khadeeja ranki zai 6ace in baki fito ba" still bata tanka mashi ba

Banko kofar dakin akay, Mubeen ne ya fado ciki kamar an wurgo shi, Rigar shi duk ta 6ace da jan bakin su rubina

A ruWe salsabeel ke kallon shi Yama rasa ta ina zai fara



"Yaya salsabeel, Kaga su rubina sun 6ata min kayana da jan bakinsu, kawai saboda nayi masu dariya suna fada" bai karasa sauraren shi ba yai saurin fucewa da sauri mubeen Yabi bayan shi tunkafin Ya sauko down Ya hango su manne da juna, sun kacame kamar irin kifin gwangwanin nan sai ihu suke Yi,



Wata irin tsawa mai sauti Ya daka masu a firgice suka saki junansu, suna ganin shi suka fara kokarin bare baki zasuyi kuka

Nuna su yai da yatsan hannun shi"kar wadda ta kuskura tayi min kuka" ya fada yana zare masu idanun shi da alama ranshi ya 6aci, Yaji haushin yadda suka 6ata kayan su, abu tun karfe kusan tara na safe ake ta fama yaki ci yaki cinyewa

Sam yakasa yi masu fada, baisan meyasa yake jin nauyin ya furta masu kalma mara dadi ba.

"Yanzu abun da ku kayi kun kyauta"? Sunnar dakai kasa sukai har suna hada baki wurin fadin"dan Allah ka yi hakuri ba zamu kara ba" ta6e baki yai" a haka zamu tafi,tun da kunfi son aganku a haukacen ku"

"Ya salsabeel dan Allah kabari mu canza wasu kayan," harara ya watsa masu, rai a6ace Ya kama hanyar fuce wa daga falon Yana Fadin"ni na tafi sai kun taho"

Watsawa su ka yi aguje suka nufi bedrooms dinsu, Jim kadan suka fito har sun canza kayan jikin su..



Salsabeel Yana atsaye gaban motocin da za su shiga,, Jami'in da zaiyi driving din su Har Ya hallara a mazaunin driver, da gudun gaske khadeeja ta fito hannun ta ruke da takalmanta, har tana bangaje Su Yasmin, kamar a filin Yaki, gaba daya hankalin Jami'an dake tsaron gidan sai da ya dawo kanta, wani burgujejen wando tasanya yadda kasan kafafuwan agwagwa, ga wata yar yaloluwar riga mai hannu daya, Ta dambara jan baki akan la66anta har saman kumatuntu, mascara din data sanyawa eye lashes dinta ya zazzago har kasan idanunta, babu wanda bai firgita da ganin ta ba, Jami'an sai faman kunshe dariya suke yi a bakunansu, ko mayafi babu akanta sai wannan guntun gashin kan nata mai Wan yawa data fake shi da ribbom Ya karkarce gefe Waya.



Ko ta kansu bata bi, Tana isa bakin motar, ta jefa takalmanta cikin car window, kafin ta daddage ta kama glass din Ta zura kanta aciki ta soma kiciniyar kutsawa ta karfi, dafe kai salsabeel yay da hannu Waya tamkar zai fashe da kuka, ya ma rasa me zaiyi, su rubina duk sun bude bakunansu asake suna kallon ta.



A hanzarce Ya cafko kafafuwanta, Ya zarota daga tagar, tana ta faman haki ta dube shi idanuwan nan nata kamar na babie sai kyaf kyafta su takeyi



_"Ya salsabeel baka ce nayi kyau ba" Cikin sanyi murya yace"kyawun ne ya ruWe ni shiyasa nakasa magana" ya fada tare da bude mata murfin motar, ta shiga ciki ta zauna, Bayan kowan nan su Ya shiga, A jere suka fuce daga gidan kai tsaye suka haura kan titi_





*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*



Mu HaWu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya



*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*



3196407426



First bank



Bature Hafsat Muhammad,



*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MAY LIKE THESE POSTS
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
SUBSCRIBE USNovels Elite

Home
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 19 Complete
by
Novels Elite Admin
June 15, 2024
Novels Elite English
_*~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?*~_







3,F 'DB/=؋?=?%?=؞?





~Takun ?arshe=?%?~







Dedicated to Aunty Kubra=؋?=؞?







B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??





An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?







Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'





____________________________________
'?



ANEELERH



Bakinta Wauke da sallama ta shiga dakin abie, yana daga zaune gefen gadon shi sanye da farar jallabiya, idanunsa a manne da farin glass, yayin da hannun shi ke a ru?e da kur'anin da yake karantawa, sai da yakai aya kafin ya Wan Wago yana dubanta tare da amsa mata sallamar da ta yi



A tsanake ta shiga ta zauna daga kasan gadon kusa da kafafuwan shi, cikin girmamawa ta gaishe da shi

Fuskar shi dauke da murnushi yace"oum junaid, kin tashi lafiya" sunnar da kanta kasa tayi fuskarta da murmushi tace"lafiyalou abie"



"Ina jikallan nawa? Maimakon ki tafo min da shi? ko dai rowar Wan za'ay min ne" cike da jin kunyarshi tace"a'a abie, ni na isa in hana ka jikanka"



Murmushi yayi kafin ya Mi?a hannu ya Wauko wayarsa dake ajiye kan side drawer ya mi?a mata



"Kar6i nan, Ki duba sakon da aka turo miki" da sauri ta sanya hannu ta kar6a, kafin ta Waura idanunta kan screen ta soma karanta sakon



_Assalamu Alaikum, barka da rana abie an wuni lafiya, ya iyali, ?awar Aneelerh ce benazir matar tajudeen, Ina son yin magana da ita sai dai bani da contact dinta, dan Allah a hadani da ita, nagode sosai, ku huta lafiya__





Lokacin da ta kai ?arshen Sakon Idanunta azare, baki a buWe da tsantsar mamaki take kallon screen din wayar, sam takasa gasgata abun da aka rubuta mata, Muryarta ?asa ?asa take maimaita sunan Benazir Benazir!



Abie dake ta kallon ta, ganin tayi kasa?e


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login