Showing 186001 words to 189000 words out of 391264 words

Chapter 63 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2638

ta taimaka mata suka nufi bedroom dinta...

Cike da jimami ummi da mami suka nufi dakunansu domin yin sallah....



Bayan shigarsu dakin, Anila ta zame hannunta daga na zahra, ta zauna gefen gadon, wani iri gumi ne Ya wanke fuskarta, Numfashin ta da hucin zafi yake fita. tsananin tausayinta ne Ya kama zahra, cikin sanyin murya tace"Aunty Anila dan Allah ki daure ki tashi ki shiga toilet kiyi alwalar, idan muka kammala sallar sai muyi masu addu'a...."



idanunta jawur ta kalli zahra, Cikin disasshiyar murya ta furta"Zahra ki barni kawai, Ni kadai nasan raWaWin da zuciya takeyi min! Zahra in har Ana bata dawomin da junaid ba, wallahi zaku iya rasa ni, saboda bazan iya rayuwa batare da yaron nan ba, zuciyata zata iya bugawa in mutu...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sar?e makoshinta, fashewa da kuka zahra tayi"Aunty Anila ki daina wannan maganar! Bana jin dadi, Kina karya min zuciya ta! In sha Allah babu abunda zai faru dake, ba zaki mutu ba, kuma in sha Allah ba abunda zai faru da junaid, Zasu dawo cikin koshin lafiya..." lallashinta zahra ta ci gaba dayi dakyar ta samu ta shawo kan Anila, harta hakura ta mike ta shiga toilet yin alwala, bayan shigarta zahra ta nufi wardrobe din kayan Anila, don ta Wauko mata hijabi, bayan ta bude murfin ta zura hannu cikin jerin hijaban Aneelarh dake a jere ta ru?o Waya tana kokarin janyota kwatsam! ba zato ba tsammani idanunta suka sauka akan Wan mutun dake kwance cikin shelve din wardrobe Ya kudundune kanshi atakure jikinshi duk ya sandare.



Rass taji gaban ta ya faWi nan take ta saki hijabin dake ruke a hannunta ya faWi ?asa ta runtse ido ta daddage ta fasa ?ara tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un jikinta ya fara kakarwa gaba daya tabi ta ruWe takasa gane wanene ma ita dai kawai taga dan mutun kamar aljani, banko kofar toilet anila tayi da gudu ta fito jin sautin karar zahra, gabanta na faduwa ta furta"Zahra! Meye faru? Lafiya kike ihu? La66an zahra na kerma sam ta kasa magana sai nuna mata cikin wardrobe din takeyi da yatsan hannunta wanda ke ta kerma..



Adabarbarce ta furta"Aun...Aun... aunty Anila mutun! ?an mutun a ciki! ...." a matu?ar ruWe Anila ta nufi wardrobe din ta kai idonta inda zahra ke nuna mata lokaci Waya ta waro idanunta waje da karfi ta furta"baby junaid..." sai lokaci zahra ta sake kallon shi dakyau taga fuskarshi sharkaf da gumi ya sandare kamar matacce duk ya takure kanshi a cikin shelve din da alama ya dade a ciki, wani abun daure kai towel ne Waure a jikin shi daga gani har wanka anyi mashi.



Allah kadai yasan meya faru da har ya 6oye kan shi cikin wardobe.. " A hanzarce Anila ta Wauko shi ta zauna kan floor tare da kwantar da kanshi saman kirjinta, ta shasshafa fuskarshi, muryarta na rawa tace ma zahra ta dauko mata ruwa, da sauri zahra ta fuce daga dakin jim kaWan ta dawo hannun ta ruke da bottle water mai sanyi ta mi?a ma Anila, yatsun hannunta na kerma ta buWe murfin ta gumtsi ruwan abaki ta watsa mashi saman fuskarshi, wata irin firgita yayi jikin shi ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama...nannauyar ajiyar zuciya anila da zahra suka sauke. Cikin sanyin murya anila ta ambaci sunan shi junaid! Firgigit ya ware idanun shi waWanda suka kaWa jawur har saida suka tsorata, Yana ganin fuskar mommynsa Ya ?an?ameta ya cusa kanshi cikin kirjinta Ya fashe da kuka mai sautin gaske ya dinga sambatu na fitar hayyaci, hakan ba karamin Waga masu hankali yayi ba...lamarin yayi matu?ar daure masu kai? Meya faru da shi? Ya akai ya shiga cikin wardrobe ya boye kanshiS'hatta bugun zuciyarshi bana lafiya baneW'

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.


Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK

COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright ? 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:05 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite

Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun ?addara Takun ?arshe page 38 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 02, 2024
Sponsored Link

Takun ?arshe
"Junaid Dan Allah ka daina kuka! Me ya faru dakai? Meyasa ka 6oye a cikin wardrobe? ina Anah? Kwata kwata baya fahimtar me take cewa, kuka yakeyi na fitar hayyaci hada kai hannu ya dunga bugun bayan ta, fashewa sukayi da kuka daga ita har zahra wani irin tausayin shine ya kama su, gashi sun rasa gane kan shi.



banko kofar dakin ummi da mami su ka yi daga waje suka jiyo sautin kukan junaid hakan yasa suka watso aguje suka fado dakin, lokaci Waya suka ci burki suna kallon Anila dake a rungume da junaid, waro idanu sukayi hadi da buWe baki tsabar mamaki da al'ajabi ne ya kama su! Sam sun kasa furta magana na dan wani lokaci kafin mami ta matsa kusa da su, muryarta da rudu ta furta"ikon Allah kamar junaid nake gani! a ina kuka gan shi ne"? Shuru ba wanda ya bata amsa har saida ta Wan daka masu tsawa saboda akagareta"bakuji ina magana bane? A ina kuka gan shi"? Dakyar Zahra ta tsagaita da yin kukan tana faman jan numfashi ta labarta masu komai.



Mami ta zagba salati tana tafa hannayenta, gaba daya sun shiga rudani, lamarin yayi matukar rikirkita tunaninsu sun rasa tunanin me zasuyi, kowa da abunda yake sakawa aranshi..."

Mikewa Aneela tayi Wauke da shi, ta nufi mami tana kuka Yana kuka an rasa me lallashin wani"mami ku taimaka ku lallashe shi ya?i yin shiru na rasa gane meke damun shi, junaid baya a cikin hayyacin shi, idanunshi sun kaWa jawur sai sambatu yakeyi mana"

mi?a hannu mami tayi zata dauke shi aikuwa ya ma?e kafaWa ya ?ara shigewa jikin mamanshi, sautin kukan shi ya cika kunnuwansu, sun rasa ya zasuyi da shi, gaba Waya suka yi mashi ?awanya suna kokarin shawo kanshi ta hanyar lallashin shi kwata kwata baya sauraron su, adai dai lokaci su abie sun dawo daga masallaci kwatsam sukajiyo kukan junaid mai ?araji, wani irin faWuwar gaba ne ya darsu a zukatan su, mahboob har yana tuntu6e garin saurin ya shiga ciki, gudu gudu sauri sauri uncle ?an iya da Abie Sukeyi suka nufi dakin Anila, suna shiga suka iske su mami tsaitsaye cirko cirko fuskokin su sharkaf da hawaye, kusan atare su abie suka kai dubansu ga junaid, arude mahboob Yace"Junaid! Aunty Anila a ina kuka gan shi? Ko Ana ce ta dawo da shi"? Abie ne yayi hamdala Yana fadin Alhamdulillah sun dawo kenan, dama saida raina ya bani wani wurin sukaje, Ina Anan take ne? Me kuma akayi mashi yake kuka.. "? Uncle Wan iya yace"lafiya kuke kuka?Shima Yana kuka babu mai lallashin wani? Ina ita Anan"?




cikin shesshekan kuka zahra ta sanar da su inda suka gano junaid





"Abie, junaid baya sauraron kowa, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, kuka kawai yakeyi, mun rasa gane kan shi..." tsantsar tashin hankaline akan fuskokinsu har sun fara murnar ganin shi azatonsu Ana ce ta dawo da shi ashe ba haka bane.



"Bani shi nan" abie Ya fada tare da mi?a ma Anila hannu, a firgice baby junaid Ya ?ankameta alamar bazai je gurin abie ba, cikin murya kuka tace"abie ya ki yarda da kowa, su mami sunyi kokarin lallashinshi amma Yaki sauraron su...."



Girgiza kai abie yayi tare da ambaton Inna lillahi wa inna ilahirraji'un kafin daga basani ya kalli anila dake ta sharar kwalla, tana jijjiga junaid

"Anila ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan, Kina kara Waga mashi hankali, je ki zauna ki lallashe shi, ke kadai ce zaki iya shawo kan shi, kiyi mashi addu'a ita yake bukata ayanzu..." amsa mashi tayi da toh, da sauri ta koma gefen gadon ta zauna, tare da sanya hannu ta talla6o kan shi, ta fara yi mashi kira'ar alkur'anin a cikin kunnanshi, su mami sunyi zungudum suna kallon su gwanin ban tausayi, cikin ikon Allah taji ya fara tsaitsayawa da yin kukan kafin a hankali taji yayi shiru ya nutsa kan shi a kirjin ta, fuskarshi tabi da kallo kumtunsa sunyi jawur, la66ansa sun kumbura suntum, hatta ?warin idanun shi sunyi jajir, siraran hawayene ke ta zarya kan kun cin shi, lokaci Waya taji ya fara sauke ajiyar zuciya a jere jere, nunfashin shi ya fara daidaita ba kamar Wazu ba.




bata dakata da yi mashi kira'ar ba har saida ta tabbatar ya daina shesshekar kukan kafin tayi shiru tana duban shi, ajiyar zuciya su mami suka sauke hankalin su ya dan kwanta jin yayi shiru

Cikin sanyi murya ta furta sunan shi"junaid" motsa la66ansa yayi batare daya firta kalma ba...

"Dan Allah ka daina kuka, kasan bana son 6acin ranka, nasan nice na bata maka rai na tafi anguwa nabarka, ka yi hakuri ka yafe min junaid, wallahi bansan za'a tada ku da wuri ba..." shiru yayi bai tanka mata ba...

"Babyna, bazaka mun magna ba? Fadamin meke damunka? Kanka yanayi maka ciwo? Ko kana jin yunwa? Ina Ana? Meyasa ka yin kuka..." duk tabi ta rude sai surutu takeyi mashi, shidai yayi shiru bawan Allah shi kadai yasan bala'in da idanun shi suka gane mashi.



"Kada ki takura mashi Aneelarh, tun da mun samu yayi shiru, ki kyale shi Ya huta, Allah kadai yasan meya faru da shi wanda yayi silar rikicewar shi"! Mami ce tayi maganar

Ummi tace"ni ban ma san tunanin me zanyi ba wallahi, hankali na Ya tashi! abun da ya Waure min kai meya faru da su? Taya akai junaid yayi wayon 6oye kan shi a cikin wardrobe? To ko dai wani mugun abunne Ya faru da su bayan tafiyar mu, gaskiya ina ji araina Ana ce ta boye shi don kada a cutar da shi ko kuma shi ya boye kan shi sakamakon wani mugun abun daya gani, Allah daga ganin halin da junaid yake a ciki bana lafiya bane, Yaga wani abune daya razanar da shi" ta ?are maganar tana kallon su



Jinjina kai uncle dan iya yayi"nima abunda nake tunani kenan, amma taya za'ay mu san ainihin abunda ya faru bayan tafiyarmu? Cikin shesshekar kuka Anila tace"Junaid zai iya fada mana idan Allah yasa ya dawo hayyacin shi"



Mahboob daya gama razana dakyar ya iya bude baki yace"ni damuwata yanzu ina Ana? Ga junaid ya bayya??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na saura ita baiwar Allah, bamusan meya faru da ita ba! Bamu san awani hali take a ciki ba..." bai kare maganar ba, Abie yace"in har wani abunne ya faru da su, zai iya yiwuwa itama ta boye awani wuri kamar yarda ta 6oye junaid..." jin wannan maganar yasa mahboob ruko hannun zahra yace mata tazo suje su kara nemo ta, da sauri suka fuce daga dakin bedroom dinta suka shiga, suka fara nemanta sako da lungu har karkashin gadon ta, da cikin wardrobe dinta amma basu ganta ba, sun duba ko'ina tun suna sa ran zasu ganta har suka fidda rai, kafin su fito daga dakin sai da mahbbob ya shiga toilet dinta Ya kashe shower din da aka bari a kunne da faucet, ruwa harya fara taruwa sosai har cikin dakin ta ya fara gangarowa, basu bar dakin ba sai da mahboob ya taimaka ma zahra suka gyara mata shi, kafin suka fito da sauri suka nufi sauran dakunan suna duddubawa, duk wani wurin sirri da mutun zai iya 6uya saida suka duba ko zasu ganta sai dai kash bata nan, ceilling ne kadai basu tsaga sun bincika ba don sunsan ba tayadda za'ay ta iya shiga ciki ta buya.

Badan sunso ba dole suka hakura da nemanta, jikinsu yayi mugun yin sanyi, zuciyarsu ta karaya, gani suke kamar ba zasu kara ganin Ana ba.





Anila taso takai baby junaid asibiti adaren saboda aduba mata lafiyar shi amma abie ya hanata yace mata ta cigaba da yi mashi addu'a in sha Allah zai samu lafiya, taruwa sukayi akan shi Waya bayan Waya kowannansu saida yayi mashi addu'a suka tottofa mashi a jikin shi, har indomie zahra ta dafa mashi ta kawo masu a plate amma ya?i ci, ta koma kitchen ta haWo mashi tea dakyar anila ta samu yasha tea din, jikin shi ya danyi sauki, zuciyar shi dai ce take bugawa da karfi, duk yadda taso ya bata hadin kai suyi magana don taji meke damunshi ya?i mata magana kamar kurma sai dai yabi ta da ido, don dole ta hakura, gashi ya hanata sukuni ya manne mata kamar anta da jini, ko da zata shiga toilet ta karasa alwala sai dai ta shiga da shi, bayan ta fito ta goya shi abayanta ahaka tayi sallah =ؔ?



___________________________________
'?



*ALHAJI MUSA=ت?*



Da sassafe ya shigo katafaren falon gidan, jallabiya ce a jikin shi grey colour, ta Wanyi tighting arms dinsa, kamar kullum fuskarsa a daure ba fara'a, ya zuba hannayenshi cikin aljihun jallabiyar.



Cikin takun izza yake tafiya yan aikin gidan dake kai komo suna yin aikace aikacen gyara falo dakai abinci dining suna ganin shi, suka fara gaishe da shi, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye ya nufi dining room ya tsaya bakin glass door din yana kallon zungureran table din dake a kewaye da kujeru ancika shi da kayan breakfast, wani abu da ya Waure mashi kai babu kowa a kan kujerun yayi mamaki sam ya manta da abunda ya faru jiya, saboda bayan ya gama balbalin bala'in shi gidan ya bari gaba daya bai ?ara dawowa ba, sai yanzu daya shigo da safen nan,baisan awani hali mutanan gidan suka kwana ba.



Agogon hannunsa ya duba don yaga ko time na yin breakfast dinne baiyi ba sai kuma yaga lokaci yayi

Ta6e baki yayi kafin ya dago ya kalli yan aikin, Tani ya hango da hannu yai mata alamar tazo, jikinta na bari ta nufe shi"yalla6ai gani"

"ya akai banga mutanan gidan ba? Ko baku fada masu an shirya masu breakfast ba"?

"Wallahi mun yi masu magana, ita zeenatu tace mun bazata ci ba, nayi nayi da ita taki kula ni, shi kuma shureim da naje dakin shi na iske shi kudundune cikin bargo kamar baida lafiya nayi mashi maganar breakfast yace min baijin yunwa in tafi kawai..."



bata kare maganar ba, rai a6ace ya Waga mata hannu da sauri taja baki tayi shiru duk tabi tasha jinin jikin ta, wucewa yayi azafafe Ya nufi upstairs, ya ture kofar dakin zeenatu ya shiga daga ciki, tana a zaune kan prayer mat, hannunta ruke da al'kur'ani tana karantawa sam bata ji motsin shigowar shi ba.



"Zeenatu"! Kakkausar muryarshi ce ta daki kunnanta, bata kula shi ba, tamkar bataji kiran da yayi mata ba, hakan ba karamun fusatashi yayi ba, kwatsam taji ya dauke kur'anin dake a hannunta, azabure ta mike idanunta sharkaf da hawaye ta furta"Daddy, give me my Qur'an..." ko kula ta baiyi ba ya rufe kur'anin ya nufi bookshelf din dakin ya daura shi asama kafin ya juyo ya kalle ta"fushi kike dani? Rai a6ace tace"daddy ba iya fushi nake da kai ba, haushin ka nake ji, dan Allah ka kyaleni in cigaba da karatuna ko na samun saukin abunda ke damuna..." fashewa tayi da kuka gaban hijab din jikin ta ya jike sharkaf da ruwan hawayen ta



"You don't want my happiness, Daddy. You don't want peace kullum burinka ka 6ata min rai, a haka kake son inyi alfahari dakai amatsayin mahaifina!"



ta faWa tana zare mashi blue eyes dinta wadanda suka kaWa jawur, ko kadan baiyi mamakin kalaman data furta mashi ba, ya riga da yasan meke damunta, wato saboda ya bata ma shureim rai jiya shiyasa take fushi da shi.



Matsawa yayi kusa da ita da sauri taja da baya tana girgiza mashi kai, wani irin fargaba da tsoron shi ne suka kamata tayi zaton zaiyi mata wani abune. Batai aune ba taji ya dam?i arm dinta ya janyota kan broad chest dinsa yayi hugging dinta.



softly yace"fadamin laifin me nayi maki? Meyasa kike fushi da daddynki? Cikin shesshekar kuka tace"ka 6ata ma ya shureim rai, jiya banji dadin kalaman daka gaya masa ba, daddy ya shureim baiyi maka laifin komai ba, amma ka rufe shi da fada harka shake wuyan rigar shi, baka dubi girman shi ba..." dakyar ta ?are maganar, shafa bayanta yayi cikin sigar lallashi yace"yanzu me kike so nayi? Don in wanke laifina"? Ya faWa tare da dago da fuskarta suka haWa ido sai taji yayi mata kwarjini da sauri ta kau da idonta gefe murya na rawa tace"kaje ka bashi hakuri, idan yace ya yafe maka nima zan daina fushi dakai" Waure fuska alhaji Musa yayi jin abunda tace wai shi zaije yaba shureim hakuri, girman kanshi ba zai barshi ba, amma dayake shu'umun kanshi ne sai yace mata"okey, mu sauka down, muje kici abinci" ma?e mashi kafada tayi"bazan iya ci ba, in ba atare da ya shureim ba"



"It's okey, muje sai in bashi hakurin" tace toh, ya ruko hannunta suka sauko downstairs.



A dining room ta tsaya kamar yadda ya bata umarni, Shi kuma Ya nufi dakin shureim time din daya shiga da sallama abakin shi, bai taras da kowa ba adakin, sautin ?arar zubar ruwa yajiyo daga bathroom, alamar yana aciki yana wanka, zama yayi gefen gadon shi yana jiran fitowarshi,

Almost 15 mins yana jiran shi, har ya mike zai tafi don bayason jira arayuwarshi sai dai ajira shi, jin motsin buWe toilet door dinne yasa shi dakatawa ya tsaya yana kallon shureim dake fitowa waist dinsa daure da towel, gefen fuskarshi yayi jawur kamar jini ya kwanta, hada sahun yatsun Alhaji musa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login