Showing 369001 words to 372000 words out of 391264 words

Chapter 124 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

3581

zai biyo baya in mahaifinta yaji ta fitar da sirrin, aranar saboda fadan daya kaure tsakanin Benazir da anila saida mami da abie suka rabasu dakyar bayan sunci uban juna, abie ya tambayi meya hadasu faWa, anan Anila ta fayyace masu komai, hankalinsu ya tashi matuka basuji dadin abunda ya faruwa ba, Ita kuma Benazir acikin labarin da Anila tabada nan taji wani abu daya Waure mata kai tamau har ta kudiri aniyar saita gano koma wanene ya shiryama Aisha da yaya shurem makirci, saboda ta gane ba laifinsu bane, tuggune aka shirya masu, musamman ita Aisha da aka yi mata kullalliya tun a kasar germany, bayan Benazir ta dawo gida, batare da sanin kowa ba, ta shiga dakin zainab mai aikin su ta tsare ta da tambayoyi akan ta fada mata meye faru tsakanin shureim da iyayen su saboda taji aranta bakomai suka sanar da su ba, anan zainab ta fayyace mata komai, bayan ta baro dakin zainab din ta koma nata dajin ta dauki waya ta kira dr shureim a lokacin duk yana a egypt, cikin sa'a ya daga kiran bayan tayi ma shi ta'aziyar babaynsu da suka rasa ta bashi hakuri tare da lallashin shi, har ya tambaye ta agurin wa taji nan ta labarta ma shi komai, har tace yaya shureim meyasa baka sanar dani ba? bayan haka meyasa da suka matsa maka baka dauki yarinyar ka kaima Aneelerh don ta ruke maka ita ba? Yace mata baiyi tunanin hakan ba, saboda a lokacin baya acikin hayyacin shi komai ya faru, ta kuma tambayar shi meyasa me kira uncle musa ya nemi taimakonsa ba, yace mata ya kira amma baya samun shi, a karshe tace mashi kada ya damu, in sha Allah zata dawo mashi da farin cikin shi, a lokacin bai gane maganar ta ba, har dai su ka yi sallama da juna Sauran bayani game da abun da ya faru zamu ji ne abakin wanda ya dace muji=?M?)_

Gaba Waya suka bita da kallo yayin da take ?arasa saukowa daga kan stairs Win ta nufe su Jikinta na 6ari yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta.


cikin raunanniyar murya dr shureim ya furta"Aisha dama Kina nan"!

Muryar mutumin da yai silar tarwatsa rayuwarta, tun kallo daya da tayi ma shi tayi saurin kawar da idanunta akan su Benazir.


Anila data gama rudewa tace"Aisha kece dagaske Nake Gani? Aisha dama Kina nan da ranki da lafiyarki baki ta6a tunanin ki waiwaye mu ba? ko awaya baki taba kiran mu ba, ko mun kira bama samunki! kullum layinki a kashe! aisha Kinsan Irin radadin danaji saboda tafiyarki? Laifin me mukayi maki Aisha dayaja har Kika manta damu arayuwarki, kika zabi kiyi nesa damu bayan alkawarin da mukayi ma juna duk runtsi duk wuya zamu kasance atare, Why Aisha? Kinbar mu da zullumin ina kika tafi? Kina araye ko kin mutu? Awani hali kike Ciki...."?

Kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata kamar ranta zai fita.

Idanunta akan na Aisha wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa ya ke yi kamar mazari, ga hawayen dake yar tseral kan kuncin ta.


Cikin shesshekar Kuka Benazir tace"baki kyauta mana ba Aisha! Kinci amanar amintakar mu, a zatona In matsala ta same ki nice mutun ta farko daya kamata ki fara tuntuba sai bakiyi hakan ba, tsawon shekara goma sha takwas baki waiwaye mu ba, ban ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zatazo ki juya mana baya ba, sai gashi tazo Aisha.."!

Kasa karasa maganar tayi saboda zafin da zuciyarta tayi mata ta fashe da kuka, Taj dake ta kallon su duk da baisan me ya faru da su ba, jikin shi yayi sanyi kawas, zuciyarshi ta kwaWaita da son jin labarin Alakar dake a tsakanin su, Ummi tana ?arasowa gaban su Benazir da Anila suka rungumeta kamar zasu mayar da ita cikin su, Jikinta ne yayi sanyi lakwas tausayin junansu ya kamata, they had deeply missed each other, more than words could express cike da sanyin jiki a hankali ta daura hannayenta akan bayansu, suka haWa kawunansu Jikin na juna suna ta kuka babu mai lallashin wani, idanunsu arurrufe sai ruwan hawayen da ke shararowa ta cikin su.


"Aisha, ashe da rabon zan sake ganin ki a rayuwata"? Ya faWa yana kallonta har time din bata raba jikinta daga nasu Benazir ba, tsawon mintuna kafin a hankali suka raba jikinsu daga na Juna.


Komai daya faru arayuwarta take tunawa, gani take kamar a yanzu komai ke faruwa, Kallon kallo suke jefawa Junansu tsakaninta da Anila da Benazir, sunyi mamakin haduwar bazatan da sukayi.

Taj dai Ya rasa gane takan maganganunsu, duk yabi ya rude sai binsu da kallo yakeyi ..


Dr shureim duk ya Sha jinin jikin shi ganin kamar bata son kallon shi, fargabansa kada ace har yanzu bata yafe masa ba.

Lokacin da Idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassaruwa, tayi mamakin manyantakarsa, ba kamar yadda ta tafi ta barshi ba, Ya ?ara girma ya kuma ?ara kyau, su ma sunyi mamakin Sauyawar da Aisha tayi, ta zama babbar mace, dirin jikin nan nata yana nan ya ma kara ninka na da.

Dakyar ya iya furta"Aisha, na gaza yarda cewa kece nake gani, dan Allah ki yi min magana ko na gasgata kaina" Ya faWa idanunsa cike tab da kwalla.


"Nice ya Shureim..." bai jira ta karasa maganar ba, ya furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! ya ambaci hakan Yafi sau a kirga kafin ya zube kan gwiwowinsa tare da daura goshinsa kasa yayi sujudusshukur cikin harshen larabci yake yiwa Allah kirari tare da hamdala saboda bayyana masa Aisha da yayi,.Lamarinsu Ya daurewa Taj kai Ya rasa gane meke faruwa, sun bar shi a duhu.

Mikewa yayi ya mayar da duban sa agare ta, Cikin karyayyar murya dr shureim Yace"ba irin neman da banyi maki ba, Allah bai nufa zan ganki ba, har yau bandaina kallon hutunanki ba, kuma har yau bandaina jaraba kiran layin wayarki ba don inji ko zai shiga amma ban ta6a samun ki ba Aisha, Kin manta damu, amma ni ban manta dake ba, You're always in my nightly prayers"

Lumshe Idanunta tayi tare da bude su A hankali kan fuskar shi, Ji yake kamar yayi hugging din ta ko ya samun sassauci nadaga abunda Zuciyarshi ke ji a game da ita, Sam sun kasa Daina kallon juna, ita kadai tasan me take ji

"Dan Allah Aisha ki bude baki kiyi magana ko munji sanyi a cikin ranmu" Aneelarh ce ta fada tana share kwalla.

Numfasawa tayi kafin ta furta"Ya shureim Where's my baby, ina Fatima Batool dina? Has she grown up? Is she attending school? Have you told her about me? Does she know about me?"

Gabansu ne Ya faWi rass! gaba daya suka sha jinin jikinsu, Da jin abunda tace sun fahimci bata su take ba, Yar da ta bari itace aranta.

Sunkuyar da kanshi yai kasa sam Ya kasa bude baki Ya furta kalma saboda fargaban halin da zata shiga! Hankalinta ne Ya tashi jin yayi shiru bai furta mata kalma ba.

"Ya shureim kayi shiru bakace komai ba? Inason ganin ta fiye da komai na duniyar nan! Nasan yanzu ta girma, a lissafina zata kai shekara goma sha takwas...."

bata ?are maganar ba, ganin hawaye na shararowa kan kuncinsa, aruWe ta dubi su Benazir daga yanayin fuskarsu ta fahimci wani abu ya faru.

"Benazir, Ina fatima na? Nasan kin kula min da ita, saboda na yarda dake, nasan ba zaki taba bari jinina ya wulakanta ba, dan Allah ki fada min ina take? Inason naganta! Ku kai ni gurin ta! Sunkuyar dakai kasa Benazir tayi, idanunta cike tab da kwalla.


Hankalin Ummi ba karamun tashi yai ba, hannayen Anila ta ruko a cikin nata..


"Anila, nasan ba zakiyi min karya ba, pls ina babyna dana barma ya shureim? Keda Benazir wanene Ya shayar min da ita uhm? Waye ya raine ta har ta girma? Na yarda daku nasan ?ata tana samun kulawa a gurin ku, Dan Allah ku fada min tana ina"?

Kamar mai faman da tabin hankali, sam babu nutsuwa atare da ita, Yar ta kawai take son gani.

Gaba daya maganganun Aisha sun ruWa Taj, sai binsu yakeyi da kallo daya bayan Waya, ya rasa gane inda suka dosa.

Dakyar ya iya furta"pls ku zauna, sai kuyi magana atsanake! Kukan Ya isa Haka, bana so inganku a cikin damuwa, duk da bansan meya hada ku ba"


"Daddyn Angel, kace suyi min magana Ina babyna take? Sunyi banza sun kyale ni suna ji ina magana"!

Tausayin ta ne ya kama Taj, yace"dan Allah ku fada mata Ina babynta ta ke"!

In a cool voice shureim yace"kiyi hakuri Aisha, fatima ta koma ga mahaliccinta tun bayan da kika bani ita, badajimawa ba ta rasu....."

kasa ?arasa maganar yayi ganin yadda ta dafe kanta da tafukan hannayenta labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un..


"Kiyi hakuri Aisha, wlh Yaya shureim yayi iyakar bakin kokarinsa gurin ganin ya ruke amanar da kika bashi, amma Allah bai nufa Batool zatai zawaicin kwana ba..."

Benazir bata ?arasa maganar ba, Aisha ta soma ja da baya tana girgiza kanta, wani irin kuncine Ya mamaye zuciyarta, Taji zafin mutuwar yarinyar data kwalla fa rai akai, tayi azan ta girma har ta zama budurwa ashe ma ta rasu.

"Pls Aisha, Ki tsaya zamuyi maki bayani, pls, kiyi hakuri ki jure, mu ma munji zafin mutuwar ta, ba yadda zamuyi ne Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan.."

Aneelerh da ta dauko maganar, bata kaiga dire ta ba, Aisha ta juya da gudu tana kuka kamar zatayi tuntube yayin da take taka stairs, cikin sauri suka bi bayanta sai dai kafin su karasa tuni ta shige daki ta kuma datse ?ofar.


*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*





*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: =?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???

_*~....................................................................~*_


~___________________________________ '?~





Around ?arfe 10 na safe, Kiran Chief Ya shigo wayar ta, a lokacin tana a zaune kan prayer mat ta nutsu tana yin karatun alkur'anin da ta buWe akan qur'anic stand, bayan da ta kai aya mi?ewa tayi daga kan Prayer mat din, ta Wauko wayarta da Waura kan Pillow ta yi picking Call din tare da kara wayar a kunnanta.



"My babe, how're you? i hope you slept well "?



Sa'ilin da muryarsa ta ratsa kunnanta wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta.



"I'm doing well, thanks hubby,



"Okay, Idan baki komai ki same Ni a part Wina"



"Okay Sir" rejecting call din ta yi.


da sauri taje gaban prayer mat din ta rufe qur'anin, Bayan ta saka High heels dinta ta fuce ta nufi part dinsa.



yana a kishingiWe kan bedmattress dinsa, single da short ne a jikin shi Ya mike kafafunsa yayin da idanunsa ke a lumshe kamar na mai jin bacci, yau tun da ya farka daga bacci Omar ke ta faWo masa arai, saboda a duk ranar birthday dinsa Omar ne mutun na farko da ya ke fara turo ma shi happy Birthday greetings tare da Birthday gift, Omar baya so wani ya riga shi taya Chief murnar birthday dinsa, wannan karan Allah bai nufa za'ayi da shi ba.




Lokacin da ta karaso bakin Door room din, sau Waya tayi knocking kofar ta buWe, sallama tayi mashi daga ciki tajiyo voice dinsa ya furta"Come In babe"



Walking slowly ta nufe shi ta dan tsaya daga gaban Gadon, idanunta akan fuskar shi still bai buWe eyes dinsa ba suna a lumshe.


sumar kan shi tabi da kallo ganin hadadden ducktail haircut din da akayi masa, ya ?ara ?awata kyawun fuskar shi, ya yi mata kyau daga gani yau akayi masa shi.



Sau uku tana gaida shi bai amsa mata ba, tayi azan bacci yakeyi amma sai ta tuna before ta shigo saida ya bata izni.



"My Chief, ko ka yi bacci ne? Nayi magana naji ka yi shiru, pls kayi min magana"



bata ?arashe maganar ba, taji ya furta"kin bata min rai Unaisah, fushi nake da ke" Ya faWa tare da buWe idanunsa akan fuskarta.



Gabanta ne ya fadi adabarbace tace"I'm sorry ban fahimce ka ba, Meyasa ka ke fushi da ni? Laifin me nayi maka"?



Saukowa yayi daga kan gadon, hannun sa ruke da wayar sa, ya juya ya nufi tattausan rug din dakin sa, a ruWe tabi bayan shi da kallo, gently ya zauna akan rug din tare da nuna mata gabansa da yatsan shi"sit here Babe"

jiki asanyaye ta zauna tana fuskantar shi, jikinta duk yayi sanyi ganin mood dinsa ba walwala.



Kasa jure kallon da ya ke yi mata tayi, slowly ta kawar da idanun ta gefe daya..



"Meyasa kika tsani mahaifiyar ki? Laifin me ta yi maki?

nan take bacin rai ya wanzu akan fuskar ta, her voice barely above a whisper tace"Because she doesn't love me, she hates me, That's why lokacin da ta haife ni ta jefa ni a cikin bathtub, sannan ta gudu ta tafi batare da ta sake waiwaye na ba...."

tun da ta fara magana ya nutsu yana kallon smooth pinkin lips dinta har saida ta kai aya tayi shiru tana jiran amsar shi..

"You were rude to her, banji dadin maganganun da kika gaggayawa mahaifiyar ki ba!" ya fada yana mai nuna bacin ran shi

"uwa uwa ce koda ta banza ce It's not acceptable to disrespect her!"

"Amma bata sona meyasa tayi watsi da ni"?

"Ki daina cewa bata sonki Unaisah"!

Da yar tsawa ya fada, har saida ta zare mashi gray eyes dinta hakan yasa shi sassauta muryarsa saboda baison ya daga mata hankali



"I know you're intelligent and thoughtful, Don't you think there's a reason your mother ran away from you? pls kiyi tunani ta haife ki a tsakar dare a cikin toilet ta kar6i haihuwarta da kanta, ta saka ki a cikin bathtub ta gudu daga gidan ba tare da sanin mahaifin ki ba..."

arude ta dube shi gabanta na faWuwa



"Nasan bakomai kika sani dangane da tafiyarta ba, kamar yadda shima mahaifinki bakomai ya sani ba, rashin sani ne yasa kuke fushi da ita saboda kunyi tunani ta gudu ne saboda bata son zama da ku bayan ba haka bane....." gaba daya Unaisah ta rude da jin maganar shi.



Audio Recording din da ya Wauka na Labarin Ummi da Benazir ya kunna mata a wayarsa, ashe ya yi recording batare da sanin su ba.



Tun da ta fara sauraran shi yanayin fuskarta ya canza zuwa rudani da tashin hankali, aranta ta ayyana dama Aunty Ummin su Malama ce? Bata taba jin mace mai tausayi da kamun kai da tsantsar ilmin addinin islama irin ta ba, baiwar Allah ashe kaddara ce ta yi silar canza rayuwar ta.

Hawaye ne suka cika idanunta tab, tsananin tausayin Aunty ummin su ya kamata, ga wani kaunarta daya shiga zuciyarta, abun daya yafi ta6a zuciyarta a cikin labarin Hukuncin da sheikh Imam ya yanke ma ta, da kuma binne yarinyar da wan mahaifiyar yayi, Abun ya ta6a Zuciyarta sosai, muryarta na rawa tace"ban ta6a jin labarin daya taba zuciyata ba, irin wannan, kuma banyi zaton sheikh Imam zai iya yin hakan ba, a matsayin shi na malami, Aunty ummi ta bani tausayi ita da ya ya shureim, amma banji dadin binne yarinyar da yayi ba" muryarta na rawa ta ?arashe maganar.

"Yanzu inaso ki fadamin, Kafin ki saurari wannan labarin Wani irin kallo ki ke yi ma Aunty Ummin ku"?

tamkar zata fashe da kuka tace"tun kafin na santa, Dr. Laura ta america ce ta fara bani labarin ta, tace min karuwace ita, bata da kamun kai, kuma tayi kaurin suna a america, kawai dai ba mutuniyar kirki bace, amma da zama ya hada mu da ita sai na gane tana da sau?in kai, ba kamar yadda na zata ba, a ranar da ta fara yin karatun al'qur'ani agabana, na razana sosai, har nayi tunanin meya sa bata amfani da saninta take aikata sabon Allah ashe ba halin ta bane, kaddara ce ta afka mata...." ta karasa maganar cikin sanyin murya.



"Yanzu fada min meyasa ki ke yi mata kallon mutuniyar banza"!



"Rashin sani ne,"



GyaWa kai Chief yayi"haka zalika, itama mahaifiyarki rashin sanine yasa ki ke tunanin ta gudu ta bar ki saboda bata sonki, bayan ba haka bane, itama bada son ranta ba"

waro idanu waje tayi, jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, ni na hana mahaifinki yayi maki magana, saboda na daukarwa mommynki alkawarin zan sasanta tsakanin ki da ita, tun shekaran jiya da su ka zo bayan sun tafi, a daren ranar mommyn ki ta kira dad din ki, ta fada masa komai da ya faru da ita, har ma sunsasanta tsakanin su saboda ya gane ba laifin ta bane, may be bai fada maki ba, saboda nace yabar komai a hannu na"

ya ?arasa maganar tare da kunna mata audio din da Taj ya tura masa ya mika mata wayar

"Calm down and listen, zaki samu amsoshin tambayoyin da kike nema a gurin mommyn ki..."


yatsun hannunta na kerma ta kar6i wayar daga hannunsa tare da kangata saitin kunnanta don ta samu damar ji da kyau.



A hankali Chief ke kallon fuskarta yadda take zazzare gray eye balls dinta tare da moving lips dinta ba ?aramin tafiya yake da shi ba.



Bai aune ba Yaga ta zabura ta mi?e, Jikinta na kerma yadda kasan wadda Electric shock Ya kama, wayarsa dake a hannunta sai kerma take saboda jikinta dake kakarwa, Dafe kanta tayi da tafin hannunta, Labbanta na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"!


Ganin ta juya arude yasa shi sauri kiran sunanta"Unaisah Ina zaki je ne"?

Yarfa hannun ta Waya tayi, ta kamo gaban hijab din jikinta ta soma fifita da shi saboda zafin daya taso mata gaba daya ta rude.

"Calm down babe, dawo ki zauna muyi magana mana"

Calmly ya faWa idanunsa akan fuskarta dake fitar da gumi kamar babu A.c a dakin.

Lokaci daya ta fashe da kuka tana fadin wayyo Allah na, na shiga uku, ina son naga momnyna, Ina son in nemi ya fiyarta, Inaso na bata hakuri! i love her, i really wanna see her..."

ganin yadda ta daga hankalinta yasa Chief Ya mi?e tare da kar6ar phone din gudun kada ta kayar da ita kasa, Cikin boxer pocket dinsa Ya zura phone din, kafin ya tallabo fuskarta da tafukansa.

"Kalli cikin idanuna Unaisah" dakyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login