Showing 168001 words to 171000 words out of 391264 words

Chapter 57 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2626

nima bana acikin hayyacina, lokacin da kikazo dakina na manta komai daya faru saboda bayin kaina bane sai daga baya nayi mafarkin abunda ya shiga tsakanin mu..." ya faWa yana haWiyar yawu mai Waci.



"Angel kinsan bani kadai bane kuma har yanzu elders suna bibiyar rayuwata ko su zasu iya shiga tsakaninmu don su rabani dake saboda sun san cewa ke daice lagona, ta hanyar shiga tsakanina dake ne kadai zasu iya cin galaba akaina.." wani irin faduwar gaba take ji, ita kanta bata son tayi silar da zai koma kurkukun ?addara, maganar tashi taso tayi tasiri azuciyarta....



Jin tayi shiru yasa shi tunanin ko ta yafe mashi ne, matsawa yayi kusa da ita, ya Wan kwantar da kanshi saman kafaWarta da sauri ta sanya hannu ta ture shi da karfi ta wurga mashi harara da kakkausar murya tace"kada ka ?ara gigin ta6ani! Idan har ba so kake inyi maka abunda baka ta6a tsammani ba! Kabarni inji da abunda ke damuna Danish! Ka nisanta kanka dani zaifi maka kwanciyar hankali"



Kamar karamin yaro haka ya fashe mata da kuka, bawan Allah Ya rasa meke yi mashi dadi a duniyar nan



"Ki tausayama rayuwata angel, ki yafe min koda ba zaki cigaba da kula ni ba, bana so kina fushi dani, na yarda na amsa laifina, ki yanke min kowani irin hukunci ne a shirye nake dana kar6e shi...."



Bata ta6a ganin tashin hankalin akan fuskarsa irin na yau ba, taji tausayin shi amma in ta tuna irin rashin imamin daya yi mata adaren shekaran jiya sai ta ji ta?ara jin tsanar shi, akan me zataji tausayin shi bayan shi bai tausaya mata ba? kalaman auntyn ummi ne suka fara dawo mata cikin kanta, idan har tabari namiji yana ta6a ta zata samu ciki, wannan maganar ta Waga mata hankali, tabbas in har ta cigaba da bashi fuska zaicigaba da kokarin kusanta kanshi da itane, wannan dalilin ne yasa tace"Zan yafe maka, amma abisa sharaWi Waya"? Jikinsa na kerma yace"wani irin sharaWi ne"?

"Kayi min alkawarin zaka yi komai nace"? Waga mata kai yayi alamar eh

"Daga rana irin ta yau bana so ka kara kusanta kanka dani...." kafin ta kare maganar yace"bazan iyaba angel..." da sauri ta daura yatsanta kan la66ansa da ruwan hawaye suka ji?a tsit yayi yana sauraronta

"Idan har dagaske kai garkuwa ne agareni mai bani kariya daga dukkan abun cutarwa toh inaso kabani kariya daga sharrinka danish! Ka nisanta kanka dani, in har kana son farin cikina, saboda ganinka da nakeyi a yanzu raina yana 6aci..." wasu zafafan hawayene suka kara wanke fuskarshi

"Baka da mafita data wuce wannan! In har kayi min hakan zan yafe maka.." runtse idanunshi yayi yana jin wani irin kunci da takaici kamar ya binne kanshi haka Yake ji, bakomai ya fado mashi aranshi ba face kalaman chief, dayace mashi ya bata tazara kada ya tursasa mata saboda ayanzu tana akan dokin zuciya!

Numfashi Yaja kafin a hankali ya buWe idanunshi a acikin nata, har saida gabanta ya fadi ganin yadda suka kaWa jawur tamkar an watsa mashi barkono a cikin su, kyakkyawar fuskarshi ta 6aci da ruwan hawayen shi har cikin ranta tana jin kamar bata kyauta mashi ba.

Cikin rauni na murya yace"na amince in har hakan zaisa ki yafe min, bazan ?ara takura maki ba" dakyar ya kare maganar, kafin ya kifa kanshi saman laps dinshi

"Danish! Ta ambaci sunan shi bai amsa mata ba,

"Bana so wani yaji abunda ya faru atsakaninmu! Koda chief ne! Duk da bansan ko ka riga da ka faWa masa ba" muryarshi kasa kasa yace"ban fada masa ba" ajiyar zuciya ta Wan sauke, da sauri ta share hawayen ta kafin ta kuma cewa"don na yanke alakar dake atsakaninmu hakan ba yana nufin bana sonka ba! Kawai bana son ka akusa dani ne, sannan bana son hukuncin da na yanke ya shafi rayuwarka! kada ka hana idon ka bacci saboda dani, kuma kada ka ?i cin abinci, idan kayi hakan bazan ji dadi ba..." tana magana hawaye na kara wanke fuskarta, kasan hijab din jikinta ta sanya ta share hawayen kafin ta daidaita nutsuwarta.







Kafin Takai hannu ta zuge window glass Win motar, tayi ma chief magana don ya buWe mata car door Win da ta gaza buWe wa, dagangan Ya datse kofar motar shiyasa ta gaza buWe, yanzu daya tabbatar sun gama magana, da kanshi ya buWe mata, ta fito idanunta cike tab da kwalla dakyar ta haWiye kukan da take ji, haWa ido sukayi cikin na juna, muryarta ?asa ?asa ta furta"mun gama magana inaso zan tafi" bata san hawayen da take 6oyewa sun fara sintiri kan fuskarta ba, hanky ya zaro mika mata"ki share hawayenki"! Kar6a tayi a hankali ta fara share kwallar

Iphone dinta dake a hannun shi ya mi?a mata"na sa maki card, zan kira anjima zamu yi magana, ki koma ciki yanzu" amsa mashi tayi da toh nagode, kamar karta tafi haka take ji tana tafiya tana waiwayon motar zuciyarta cike fal da tunanin shi....



*AFTER SOME DAYS*



(Bayan wasu kwanaki)



tun daga ranar da chief Ya kawo danish asibitn bai ?ara matsa mashi akan ya kawo shi ba, daga shi har ita unaisah din sunji jiki ba kaWan ba daurewa kawai sukeyi, sau?in su Waya kowannansu Ya samu abunda Yake Webe mashi kewa, chief ya zama tamkar abokinshi baya barin shi acikin damuwa, sai da yasan ta yadda yai harya samu kar6uwa a wurin danish, kullum suna atare abinci ma atare suke cin shi, abu uku ke raba su lokacin sallah, lokacin zuwan chief wurin aiki da kuma lokacin bacci, wani lokaci har ?arfe shabiyu na dare suna kaiwa adakin danish harya fara koya mashi yadda zaiyi rubutu da yadda zaiyi amfani da waya harma da laptop, saboda yana son su fara making phone call da prime minister hateem, su big guy har mamaki sukeyi idan suka ga chief da danish suna magana cos basu ta6a tsammanin yaron zai iya sakar ma wani jiki acikin su har haka ba, bawan Allah Danish dannewa kawai yakeyi ba dan chief yana kokarin lallashinsa da debe mashi kewa ba da tuni ya jima da zaucewa, saboda rashin ganin unaisah ba karamin illa yakeyi mashi ba, duk daren Allah sai ya farka da radadin rashin ta, shi kadai yake haukanshi kafin Allah ya kawo mashi sau?i, bai ta6a bari chief yaga gazawarshi ba tun da ya fahimci mutumin baya son damuwarshi kuma yana bashi kyakkyawar kulawa...



Idan muka koma 6angaren Benazir jikinta yayi sau?i sosai, tana samun kulawa a wurin mutane ukun nan da suka tsaya mata, dr jzz, hajiya layla da kuma unaisah, cikin ?an kwanakin nan ta dawo hayyacin ta sai dai babu wanda Ya lura da hakan kuma bata nunama kowa ba, ita kanta tasan dalilin ta nayin hakan, dagangan take yin pretending, kusan kullum ne sai su anila sunzo dubata, haka zalika Alhaji ubaid da shureim basa gajiya da zarya wurin zuwa asibitin, har ila yau Alhaji ubaid bai haWu da unaisah ba, ba su ta6a cin karo ba, duk lokacin da zaizo tana a toilet, ko tana bacci, itama Hajiya sarah tana kokarin zuwa asibitin duk da ayyukan office da suke yi mata yawa, sau Waya suka ta6a haWuwa da unaisah har suka gaisa da junan su wani abu daya daurema unaisah kai muryar matar tayi shige data cousin din aunty pretty da ta ta6a kira, aikuwa aranar har jaraba kiran layin aunty pretty tayi saboda ta tuna da ita, sai dai kash ba'a Waga kiran ba, saboda wayar ta koma hannun zeenatu dr shureim ne ya bata donsu dinga gaisawa, ita kuma dama bata cika ruke waya a hannunta ba, sai ta wuni bata dauketa ba sai in ta tashi kiran dr shureim tukunna take daukarta..



Alhaji musa tun zuwan da yayi sau Waya, bai ?ara zuwa asibitin ba, ko awaya baya kira balle har yasan wani hali suke a ciki, gashi har dr ya fara tunanin sallamar su saboda taji saukin jikin ta sosai..



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE
'?*



*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MAY LIKE THESE POSTS
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright ? 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:05 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite

Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun ?addara Takun ?arshe chapter 34 Complete
by
Novels Elite Admin
August 30, 2024
Sponsored Link

Takun ?arshe

'?

EPISODE 33

Kwance take tana sharar bacci cikin kwanciyar hankali, cikin bacci ta yi kwakkwaran juyi zata gyara kwanciyarta kwatsam tayi arba da fuskar mutun wani irin firgita tayi a haukace ta zabura zata mike da sauri Benazir ta cafko hannun ta ta ru?e shi gam, suka ?urawa juna ido batare da ?yaftawa ba, Hankalin Unaisah ba ?aramin tashi yayi ba, ta rasa gane meyasa cikin ?an kwanakin nan matarke tsareta da ido kamar zata lashe ta, aranta ta ayyana kodai ta6in hankalin nata ne Ya motsa? Kada fa ta hau ta da bugu tun ba hankaline da ita ba..tuni tasha jinin jikin ta, tana faman haWiyar yawu kutt murya na rawa ta furta"am..um.. mamana! Tun yaushe kika farka"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda Benazir tayi mata rumfa kamar zata danne ta, babu alamun zata tanka mata tayi shiru tanata kallon ta...babban tashin hankalin unaisah hajiya layla bacci takeyi balle ta kawo mata Wauki, tuni ido ya raina fata.

"Dan Allah na ro?e ki, ki daina kallona haka, babaynki ce fa, ki na bani tsoro. .." sai da tay wannan maganar, Benazir ta saki murmushin gefen fuska har dimple

dinta ya lotsa...

"Babyna ne"? La66an unaisah na kerma tace"ni ce, dan Allah kada kiyi min komai..." ?ar dariya benazir tayi, wani irin nishadi take ji..

Shafa sumar kanta tayi har wani kyafkyafta idanu take Yi kamar wata mara gaskiya


Unexpected ta ji ta manna mata sumbata kan kuncinta, kafin tayi wani yunkuri ta kara mata wani kan la66anta, runtse idanu tayi kamar zata fasa ihu ta furta"na shiga uku, tawa ta same ni"! dariya benazir tayi kafin ta janye jikinta daga na unaisah ta koma kan gadonta ta kwanta idanunta na fuskantar ceilling..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarta da sauri ta cusa kanta jikin pillow,

Satar kallon ta unaisah tayi, ta rasa gane meke damun matar, ta fara tsorata da lamarinta, kwanakin nan ta canza mata, ba kamar farkon da tafara jinyarta ba, ko meyasaS'



Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta sauko daga kan gadon, ta lalla6a cikin sanWa take tafiya, backpack dinta ta buWe ta curo wayarta ta nufi toilet ta shige ciki,



Text message ta tura ma daddynta



"Daddy, barka da dare, daddy ni dai nagaji da zaman asibiti, gida nakeso in dawo" tana tura mashi text din jim kaWan saiga kiran shi, tayi mamaki saboda batasa rai zai bata amsa ba kusan karfe shabiyu na dare, tayi zaton yayi bacci.



Picking call din tayi tare da kara wayar a kunne"My daughter! Me kike yi har yanzu baki kwanta bacci ba? Wani abu ya faru ne"?



Cikin muryar raWa ta furta"ba abun da ya faru, kawai bana jin dadin yawan kallona da matar takeyi, duk in na farka tsakar dare saina ganta akaina ta tsare ni da idanunta"



Sautin dariyar shi ce ta ratsa kunnanta aiko ta haWe fuska kamar tana agabanshi tace



"Daddy dariya kake yi min?




"Sorry daughter, maganarki ce ta bani dariya, but ki ?ara hakuri Anila ta fada min next tomorror za'a sallame ta"



Shagwa6e fuska tayi, ko tsoro bata ji ita kadai a toilet





"daddy ina yan uwana? Yau banji muryoyin su ba"



"Suna nan cikin koshin lafiya, basu da wata damuwa"



Shiru sukayi na wani lokaci, zuciyar ta sai azalzalarta takeyi akan ta tambaye shi ina Danish amma ina takasa furtawa...



Kamar taj ya karanci abunda ke zuciyarta sai taji yace"Daughter, labari me dadi, dan uwanki Danish ya fara koyon rubutu da karatu a wurin chief, abun saiya baki mamaki yana da kaifin basira, kamar ke lokacin da kina ?arama, kwakwalwarsa tana ja, abun burgewa sun shaku sosai da chief in kika gansu kamar ?an uwan juna, tare sukeyin komai......." batasan ya akai ta tsinci kanta da sakin murmushin gefen fuska ba, har cikin ranta taji dadin jin labarin nan da daddynta ya bata..



"Daddy, na taya shi murna, kuma naji dadi wlh, Allah ne kadai zai iya biyan chief, yayi mana hallacci arayuwar mu, ina jin dadin kyautatawarshi agare mu, Allah yasaka mashi da mafificin Alkhairinsa....." addu'o'i ta cigaba da yi mashi daddynta yana amsa mata da ameen



Kafin daga bisani yace"daughter, ki koma bacci, bana so ki makara sallar asuba, kiyi addu'a kafin ki kwanta sannan ki kula min da kanki"



"Toh daddy, kaima ka kwanta kayi bacci, ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama da juna, kasa motsawa tayi daga cikin toilet din, wani irin yanayi take jin kanta mara misaltuwa, tanaji aranta kamar tayi missing din wani abu da zuciyarta take muradin son gani, ta wani bangaren taji dadin labarin cigaban da danish ya samu sosai har wani dan murmushi ta saki



Lumshe idanu tayi tare da jingina bayanta jikin wall na tsawon mintuna kafin ta juya ta buWe kofar, cikin sanda take tafiya tana satar kallon gadon benazir, ta lullu6e jikinta da bargo da alama ta koma bacci, hakan ba karamin dadi yayi ma unaisah ba..

Kan gado ta haye ta kwanta tare da jan duvet tayi covering jikin ta wani baccin ne ya kuma daukarta...



_________________________________
'?



*Hajjaty*



Tun da sanyin safiya bugun kofa Ya farkar da ita, tana tsaka da jin dadin baccin ta, da wata irin kasala ta mi?e ta sauko daga kan gadon tayi mi?a haWi da yin hamma, ?ar rigar bacci ce a jikin ta, sai da ta fara daukar hula ta lullu6e kanta kafin ta nufi kofar tana tambayar wanene"?



Daga waje tajiyo muryar sofia cikin tashin hankali tace"Aunty ni ce sofia, ki buWe min kofa" da sauri hajjaty ta buWe kofar ta le?a kai tana kallon sofia wadda gaba Waya babu kwanciyar hankali atare da ita ..tunkafin taji me zata faWa mata gabanta ya fara faWuwa.



"Sofia! Meke faruwa ne? naganki kamar ba lafiya"? Yarfa hannu safiya tayi murya na rawa tace"marwa! Aunty mun shiga uku, kizo kiga abunda ke faru ! Marwa ta kuturce. .." aruWe hajjaty ta ce"bangane me kike nufi ba? Meya faru da ita? Wata irin kuturta . "? Bata jira hajjaty ta kare maganar ba, taja hannunta da sauri suka nufi dakin marwa dake anan corridor din da Wakunan house maids din gidan su ke..



Shigarsu ke da wuya hajjaty tayi arba da ?an aikin gidan gaba dayansu, sun hallara, fuskar kowan nansu sharkaf da hawaye cikin tashin hankali suke sallallami idanunsu akan marwa.



Suna ganin hajjaty suka buWe mata hanya don taga abun tashin hankalin da suke kallo,

Lokacin da ta sauke idonta kan marwa dake nannaWe kan katifarta rass taji gabanta yayi mata wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali, ta waro idanu waje, agigice ta daura hannayenta biyu saman kanta, ta zabga salati tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'u!!



la66anta na kerma ta furta"Mar..marwa! Meya faru dake? Ya akai kika koma haka? ta faWa tana kallon yatsun marwa da suka dunkule irin na kutare ga wani ruwa mai yau?i dake gangarowa ta tsakaninsu,, la66anta sun shafe babu hudar baki kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba, wani irin nishi take saki, idanunta sun kaWa jawur ga zufa data wanke jikin ta baiwar Allah ita kadai tasan azabar da take ji, sai faman zare na mujiya takeyi jikin ta nata kerma.



Fashewa hajjaty tayi da kuka, gaba daya sautin koke koken su Ya cika dakin

"Wayyo Allah! Na shkga uku! Dan Allah ku fadamun meya faru da ita? kaina ya kulle nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Jiya jiyan nan mukayi aikin dinner tare da ita lafiya lou muka rabu da ita...taya akai ta samu wannan lalurar ta kuturta? Ina bakinta yake"? Cikin shesshekar kuka tayi maganar

Abla tace"Aunty bamusan meya faru da ita ba, yau da safe mun tashi zamu fara aikin breakfast, mun ga bata fito daga daki ba, shine nace ma sofia taje tayi mata magana kada mu makara, bayan tafiyar sofia har mun fara aiki muka jiyo sautin ?ararta daga dakin marwa shine muka taho da gudu mu duka dan muga mike faruwa a nan muka tarar da marwa cikin wannan halin.. ." ta ?are maganar tana kuka

Sofia tace"wlh bansan meya faru da ita ba, Nima haka na sameta, ina shigowa dakin na isketa a nannaWe kan kafita, har ina zolayarta nace mata bana son iya shege kina ji inata ?wala maki kira kinyi shiru baki ce min komai, wlh aunty dana zo gaban katifar naga hawaye idonta gashi babu hudar baki, yatsun hannunta sun kuturce bansan sa'adda na fasa ihu ba, ni ban ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba, Allah daga gani Aljanune suka shafe ta . ..." gaba daya duk sunbi sun ruWe, hankalin su Ya tashi, jikin hajjaty na 6ari tace"ba kallonta yakamata mu tsaya munayi ba, bari inje in sanar da mutanan gidan..." da sauri ta fuce daga dakin... .



Kafin wani lokaci gaba Waya mutanan gidan suka hallara a dakin marwa, da sauri maids din suka basu hanya don su shuga ciki, baba obie ne kan gaba jikin shi sai 6ari yakeyi, Pravin da twins suna abiye da shi, har sunyi shirin zuwa office wannan abun tashin hankalin Ya ris?e su, hada Hajiya saratu ta shigo ta zumbula buba ajikinta, sai faman raba idanu takeyi tun kafin ma taga meya faru da marwan!!



lokacin da sukayi arba da marwa gaba Waya hankulansu suka tashi, sunyi matu?ar razana da ganin yadda halittar marwa ta canza, kowa sai tambayar ba'asi yakeyi, Tafa hannu hajiya saratu tayi"La'haula walakuwata illa billahil azim! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni filmusibati.. Gaba Waya tabi ta rikice, "Ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login