Showing 120001 words to 123000 words out of 391264 words

Chapter 41 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2562

kukan da suke yi har lokacin,



Zeenatu sarkin tausayi har ta fara matsar ?walla, shi kanshi Dr shureim dauriya ce kawai Yake Yi, amma ba ?aramin tausayi suka bashi ba, bazai ta6a manta sha?uwar da ke atsakaninsu ba,




Fitowa Zahra tayi daga gidan karaf idanunta suka sauka akan su Dr shureim da Zeenatu Har saida taji gabanta Ya faWi ganin irin kyawun mutumin da kamalarsa da?yar ta janye idanunta daga kansu ta mayar da dubanta ga su Aneelerh,



Murmushi Zarah ta saki saboda taji daWin ganin aminnan atare,



"Ki daina kuka bana son ganin hawayen ki," Aneelerh ce tai maganar idanunta jawur Benazir tace "Idan kinaso In daina kema ki daina, taya bazanyi kuka ba Aneelerh? Nayi babban rashin da har abada bazan Iya ta6a yafewa kaina ba, laifina ne gani nake kamar nice silar da zumuncinmu ya tarwatse..." da sauri Aneelerh ta sanya hannu ta toshe mata bakinta "ki daina Waurawa kanki laifi, saboda bayin kanki bane tafiyar da kikai, kema bada son ranki aka raba ki da danginki damu kanmu ba...." lallashinta taci gaba da yi Zeenatu har ta fara gajiya da tsayuwa dama ita bata saba da wahala ba,

Tana faman jan ajiyar zuciya ta juya ta dubi su Shureim cikin sanyin murya tace"Aneelerh ga Yaya Shureim da Zeenatu Wiyar Uncle Wina" da sauri Aneelerh ta nufe su fuskarta da fara'a ta gaishe da Yaya shureim "sannunku da zuwa Yaya shureim ku shigo daga ciki" tay maganar tare da hugging Win Zeenatu tace "Yan mata sannunki kuyi ha?uri mun barku atsaye"

Kamar bata son haWa ido da shureim saboda girman shi da take gani, tun fil azal tana matu?ar jin nauyinshi kuma tana girmama shi,



"Yawwa anaeelerh mun same ku lafiya",



"Lafiyalou Yayanmu" tay maganar tare da ru?o hannun Zeenatu suka yi gaba Shureim Yabi bayansu tare da Benazir da sauri Zahra ta koma falo tana jiran su shigo don su gaisa,



Lokacin da suka shigo falon Mami da Ummi suna atsaye suna jiran shigowarsu don su tarbesu, koda Benazir tayi arba da Mami wani irin nauyinta da kunyarta ne suka kamata, Mami kuwa fara'a tasaki da sauri ta janyo Benazir ta rungumeta tana Wan bubbuga bayanta "marhabun lale ?ata, tsawon lokaci munyi kewar rashin ki" lokaci Waya Benazir taji hawaye sun sake wanke mata fuska

Muryarta da shessheka ta furta"Ma..mi " sam takasa ?arasa maganar,

"na fahimce ki basai kinyi min bayani ba, Aneelerh ta sanar dani komai, ki kwantar da hankalinki ba kuka yakamata kiyi ba, godiya yakamata mu yiwa Allah daya dawo mana dake cikin ?oshin lafiya" Mamin ta faWa tare da raba jikinsu ta sa tafin hannunta tana share mata hawaye

Kafin ta Wago ta dubi Dr shureim wanda tun da ya shigo ya sunnar da kanshi ?asa saboda nauyin Mami da yaji gani yake kamar har yanzu tabon da yai ma kansa zaisa su guje shi,



Da?yar ya motsa labbansa zai gaishe da ita Mami tayi saurin katseshi da cewa "Allah sarki Shureim kaine ka koma haka? Gaba Waya kun canzamin, Shureim Ka yada zumunci ?iri ?iri Ka guje mu ka koma Egypt ban ta6a zaton zakai mana haka ba"


Cikin sanyin murya yace"Mami ay min afuwa nima bada son raina ba nayi nesa daku, zaman ?asar ne Ya gagareni saboda abun da Ya faru, amma wallahi ko bayan da na tafi kuna araina..." bai ?are maganar ba Mami ta katse shi da cewa "bakomai Shureim, duk abun da Ya faru mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa Ya guje ma ?addararsa ba, naji dadin ganin ku cikin koshin lafiya sosae..."



"Ku mu zauna" ta faWa tare da nuna masu sofas, Bayan kowa Ya zauna Ummi da Zahra suka yi masu barka da zuwa



"Muyiwa Annabi salati" acewar Mami gaba Waya suka yi atare kafin daga bisani Mami ta dubi Zeenatu dake ta faman zare blue eyes Winta, gaba daya tarasa sukuni saboda bata saba shiga mutane ba kamar tana jin tsoron su,



"Tabarakallahu ahsanul khaliqin, ?ata wacece wannan bakuyi min bayani ba, gata dai masha Allah daga gani ba jinsin ?asar mu bane" murmushi Zeenatu tayi,



Ummi tace"kin riga ni faWa, tun da suka shigo ta tsole min ido, kamar in sace ta" dariya sukai cikin raha,



"Sunanta Zeenatu, Wiyar Uncle Wina ce" waro idanu Mami tayi haWi da jinjina kai,



"Masha Allah, sannu Zeenatu" amsa mata tay da "yawwa"



"Dan Allah ki saki jikinki, ki Wauka kamar kina agidanku ne, don na fahimci kamar kin takura"

Murmushi Zeenatu tayi har dimples dinta suka lotsa,

"Ina su Maminku ina fata duk suna lafiya" cikin kulawa tayi Maganar tana kallon benazir"

"Suna nan lafiya, sunce mu gaishe daku, taso mu zo tare amma tace sai zuwa na gaba",

Murmushi Mami tayi "Allah Ya kawo ta Lafiya in ma batazo ba ni na fidda lokaci inje gidan naku"



Shiru sukayi na wani lokaci, kowa da abunda Yake sa?awa aranshi, Benazir ta ?osa su ke6e da Aneelerh don su ?ara jajantama junansu.

Fitowa daga kitchen Ana tayi hannunta Wauke da tray na kayan abincin da suka shirya masu har zata gifta ta Wan dakata tare da kallon ba?in nasu karaf idanunta suka sauka akan fuskar benazir, tsabar kiWima da ganin Benazir ?iris Ya rage ta saki kayan abincin hannunta Jikinta Ya hau bari da sauri takai abincin Dining ta nufo su, gaba Waya ta zube kan carpet tana ambaton sunan Benazir,



Kusan atare suka Wago suna kallonta duk tabi ta ruWe muryarta na rawa take faWin "Aunty Benazir! Kece? Ko dai makuwa nayi ne?"

Hawaye ne suka ciko idon benazir bakomai Ya faWo mata aranta ba face Irin azabtarwar da tayi ma yar'uwar Ana mai aikin gidanta Janet taci azaba a hannunta in tai mata laifi hada duka take haWa mat?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 a,

Cike da jin kunyar Ana tace"Ni ce Ana, ba makuwa kikai ba, fatan na same ki lafiya? Ina yar uwarki janet"

Matse ?walla Ana tayi "Allah Sarki Aunty Benazir Ina nan lafiyalou, Janet tana a Jos tare da Esther ni kaWai ce anan, Aunty Benazir Ina kika shiga tsawon lokaci bamu ji Wuriyarki ba..."

Kafin benazir ta bata amsa Aneelerh tayi saurin tarar numfashinta da cewa "Ana kije ki ?arasa shirya masu abincin, zanyi maki bayanin komai" ta faWi hakanne saboda bata son ana tayi maganar 6acewar su Angel gudun kada Benazir taji hankalinta Ya tashi,



"Kada ki damu, zuwa anjima kafin mu tafi zan nemeki..." amsawa Ana tayi da toh, Jiki asanyaye ta mi?e tana tafiya tana waiwayon su Benazir tana mamakin Matashiyar da suka zo da ita, aranta ta ayyana watakil itace Yar uncle Winsu da taji ance zasu zo da ita...har sai da ta shige kitchen tukunna ta daina kallon su,



Mi?ewa Aneelerh tayi tare da kallon Benazir tace "mu shiga daga ciki",

Mami tace "kuyi me? Ba zaki bari su ci abinci ba, salon ki cika ta da surutu"

"Ba daWewa zamu yi ba Yanzu zamu fito"

Ummi tace"ke ko an daWe ba'a haWu ba, tana son su Wan ke6e ne ay firar yaushe rabo",

mi?ewa Benazir tayi suka nufi bedroom Winta hannunsu cikin na juna,



"Shureim ya'yanka nawa Yanzu" sunnar dakai ?asa yai jin tambayar da Mami tayi masa,

Dariya tayi "dan Allah kada kace min bakai aureba"

Cike da jin kunyarta Yace "banyi ba Mami, amma nakusa in sha Allah" tayi mamakin jin maganarsa gashi har ya fara manyanta baiyi aureba koda Yake komai sai Allah Ya nufa,

"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" amsa mata su kai da ameen,

Shigowa Ana tayi "Mami na gama shirya abincin"

Mami tace"toh, ku tashi mu ?arasa Ciki" Dr Shureim Yace"Alhamdulillah, bana Jin yunwa sai dai ko Zeenatu in zata ci"

Ma?e kafaWa Zeenatu tayi "nima bana jin yunwar ay naci abinci agida" yadda tai maganar yaso basu dariya har sun gane shagwa6a66iyace

"Ha?uri zukuyi ku tashi muje, Nasan baza'a rasa space a cikin ku ba ko ruwan zumunci ne ku sha" lalla6a su Ummi tayi har dai suka mi?e suka bi su Mami zuwa dining..



A 6angarensu Benazir bayan sun shiga Waki da Aneelerh, cike da zumuWi suka zauna daga gefen gado

Sai faman bin juna da kallo suke yi kamar yau suka fada haWuwa

"Kinga yadda kika canza? Kin ?ara girma kinyi kyau abunki, bani labari bayan kin tafi ina kika faWa"?

Numfasawa tay kafin tace"Wani bawan Allah ne Ya taimaki Rayuwata, Mutumin kirki, Wan family Win Obinna nasan ba zaki rasa saninsa ba, sunan shi Zaki Mubarak Obinna A ?asar Canada Yake..." gaba Waya Benazir ta bata labarin Yadda suka haWu da zaki a Abuja bayan ta gudu daga jos da yadda harya taimaketa suka bar kasar atare..

Jinjina kai Aneelerh tayi har cikin ranta taji dadi da rayuwar benazir bata wula?anta ba,



"Koma wanene Yayi miki wannan aika aikar in sha Allah sai yaga sakayya, tun agidan duniya, anso a cutar da rayuwarki, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane cikin ikonsa kin faWa hannu nagari",



"Ni inda nagode ma Allah, ban tafi da tsohon ciki na ba, da bansan a Ina zan haife shi ba, ba rabon ?ata tasha wahala wlh banyi zaton zata rayu ba, inaji ina gani nabarta a kwamin wanka tana kuka tana kallona..." kuka ne Ya ci karfinta da sauri Aneelerh ta fara lallashinta

"Ni damuwana wanene yake kokarin ganin ya rabani da dangina? Me na masa Aneelerh? Nasan bana jin magana tun a ?uruciyata inada jan faWa da masifa, mutane da dama na sanya su ciwon kai har da masuyi min mummunan fata amma wallahi ban ta6a zaton za'a samu wanda zaiyi min asiri, to waini me nayi masu haka??" idanunta jawur ta faWa.



Dafa kafadarta Aneelerh tayi"in sha Allah duk wani mai nemanki da sharri kanshi zai koma, ubangiji Allah Ya tona asirin su"

"Ameen Aneelerh nagode sosai da kulawarki agareni, ni wlh banyi zaton zaku kar6e ni hannu biyu idan na dawo ba, ko gida da zan dawo nayi fargaban haWuwa da su Daddy amma saina ga kowa Yana murnar gani na ba ?aramin daWi naji ba, yanzu damuwana Waya shine mijina da ?ata ina matu?ar jin shakkarsu saboda nasan da wuya su kar6eni hannu biyu kamar yadda kukai min..."



"Meyasa zaki ce haka? ay su sai sun fi kowa murnar ganinki"

Girgiza kai tay"ba zaki gane ba Aneelerh, bayan tafiyata lokacin ina agidan zaki, kwatsam wata rana saiga sa?on saki daga Taj hakan Ya tabbatarmin da yaji haushin abun da na masa" da mamaki Aneelerh tace"kina nufin bake kika nemi saki daga wurinsa ba?"

?aga mata kai tay alamar eh, shiru Aneelerh tayi jikinta Ya ?ara mutuwa lakwas saboda taj da kanshi Ya ta6a faWa mata Benazir ta tura masa text message tana neman ya saketa, to kenan wanene Ya shirya wannan tuggun?" Ta jafe ma kanta tambayar da bata da amsarta,



Ru?o hannayenta Benazir tayi a cikin nata ta dam?e su sosai cikin sanyin murya tace "Dan Allah Aneelerh ki taimaka min Inason yin magana da tajuddeen, naji kince baki da layin da Yake amfani da shi, tun da suna a tare da mijinki dan Allah ki kira Uzair Win sai mu yi magana da shi..." Rass Aneelerh taji gabanta Ya faWi, tuni ta nemi nutsuwarta ta rasa, batasan taya zata shawo kan Benazir ba sam ta manta da jiya ta faWa mata hada mijinta suna a South Korea,



"Kinyi shiru baki ce min komai" ta faWa idanunta acikin na Aneelerh, farat Waya ta fahimci wani abu daga yanayin da ta nuna, Wani irin kwarjini Benazir tayi mata muryarta da inda inda ta shiga faWin "am..umm..bani da layin shima uzair...au wayarshi ta lalace zan ce....." bata ?are maganar ba ta katse ta da cewa "Kada kiyi min karya Aneelerh ba halinki bane, dan Allah ki faWamin gaskiya ni dama najima ina kokwanton maganar mami, daga baya sai da raina ya bani akwai wani abu da take boyemin don itama lokacin dana tambayeta lambar Taj tunda nasan bata rasata ba kamar da suka bayyana man cewa suke kula da yarinyata lokacin dana dawo amman sai ta nuna man basu da lambarshi ta inda yake, tun nan na fara shakkun maganar ta tunda ko don saboda yarinyar tawa ai ya kamata ace suna da lambar tashi da suke magana, kawai ki faWamin in da akwae wani abu nayi maki alkawarin bazan tada hankalina ba, boyemin bashi da amfani tunda duk min daren daWewa zanji ne kuma bazan ji daWin ?in sanar man da kuka yi ba...."

Jinjina kai Aneelerh tayi tuni taji ?walla ta cika idanunta don har yanzu zuciyarta da ciwon abun,

Numfashi taja kafin ta fara bata labarin abun da Ya faru na 6acewar su Tajudeen,

Tsabar tashin hankali Yasa Benazir saukowa daga zaunan da take a gefen gadon ta dawo kan floor dirshan ta Waura hannayenta biyu asaman kanta muryarta cike da tashin hankali take faWin "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN! INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN......" Misalta tashin hankalin da zuciyarta ta fuskanta ba abune mai sau?i ba, Idanunta sun kaWa jawur facial muscle dinta har kerma take gaba Waya jikinta ya Wau wani irin mahaukacin zafi kamar mai fama da zazza6i sai kerma take,

Dafa kafaWarta Aneelerh tayi muryarta a raunace ta furta "Innallaha ma'assabirin Iya abun da zan iya furta maki kenan, abun da Ya faru Ya riga daya faru Benazir, illa iyaka mu cigaba dayi masu addu'a ubangiji Allah Ya bayyanar mana da su tunda har Yanzu babu labarin suna araye ko sun mutu,

Cikin shesshekar kuka Benazir take faWin "nashiga uku Aneelerh! Meke faruwa da rayuwata ne? Da farko An rabani da dangina hakan bai isa ba sai da akayi silar da ?ata da mijina suka 6ace! Wai wanene ke bibiyar rayuwarmu ne? Uban me muka masa...." jin Yadda take Waga Murya Yasa Aneelerh saurin toshe mata baki da tafin hannunta gudun kada su Mami su jiyota....

A ?arshe ma sai ta rungumeta saboda ta samu relief Win abunda ke damunta

Allah kaWai Yasan tafarfasar da zuciyarta keyi mata kamar numfashinta zai Wauke bakomai take tunawa ba face fuskar Taj dana yarta Unaisah yanzu shikenan ta rasa su?

Gunjin kuka taci gaba da yi, kwantar mata da hankali Aneelerh ta shiga yi, suna haka Mami ta shigo ganin halin da suke ciki yasa ta nufosu da sauri tana tambayar lafiya mike faruwa ne ta gan su haka da alamun tashin hankali, zama tayi a bakin gadon ta dafa kafaWar Benazir tana faWin "mike faruwa ne na gan ki cikin wannan halin??" Aneelerh ce dake ?walla ta faWi mata dalilin shigarta halin, yanayin damuwa ne ya bayyana akan fuskar Mami tace ma Aneelerh tunda bata sani ba ai da bata sanar mata ba, shiru Aneelerh tayi cikin kuka Benazir tace "Mami nice na matsa mata ta sanar man, 6oye mani baida amfani don koda yaushe ina sa ran haWuwa dasu ashe ba rabo, an raba ni da mijina da kuma ?ata, Mami suwaye waWannan azzaluman da suka tarwatsa kan iyalin mu, mi mukai masu ne don Allah" gaba Waya ta gama karya masu da zukatansu itama Mami har idanunta sun ciko da ?wallan, rarrashinta ta shiga yi tana karfafa mata gwuiwa kan inda rabo sai suga sun bayyana tunda har yanzu ba'a da tabbacin ko sun mutu har ta bata misali da ita yadda ta 6ace 6at ba'asan ina take ba tsawon lokaci gashi yanzu Allah ya bayyanar masu da ita don haka ba abunda zasu yi sai suci gaba da yin Addu'a, a tare suka cigaba da rarrashinta har saida suka ga ta Wan samu nutsuwa Mami tace ta taso suje taci abinci dama shi ta shigo tayi mata magana, idanunta sunyi jawur ta girgiza mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace bazata iya cin wani abu ba a yanzu, dole Mami ta ?yaleta Benazir Win ta bu?aci shiga toilet da sauri Aneelerh ta mi?e tana nuna mata toilet Win ta mi?e jiki ba ?wari ta shiga, bayan shigarta Mami ta mi?e cike da tausayinsu ta fita, wanko fuskarta tayi bayan ta fito akan gadon aneelerh ta kwanta kamar ba laka a jikin ta, tsananin tausayinta duk Ya kama Aneelerh tana ta kallonta, bayan wani lokaci ta mi?e taje ta kawo mata abinci da juice don tasha tace mata bazata iya cin komai ba, lalla6ata tay dakyar ta samu tasha juice Win, shiru sukai can Benazir din tace "Ina yaronki? Naga bangan shi ba? Ina abie?"



"Bayanan sun tafi unguwa tare da Mahboob ?anin Zahra, su abie suma basa nan amma nasan zuwa anjima kaWan zasu dawo gidan"

"Allah Ya dawo da su lafiya" amsa mata tayi da Ameen daga haka bata ?ara magana ba har bacci Ya Wan dauke ta a Wakin.



____________________Chief



Around 5 na marece Ya fito daga Gym room Winsa, daga shi sai short ba?i a jikinsa, Ya haWa uban gumi zufa ta ko'ina take tsatstsafo masa, Hannunsa Waya ru?e da short towel da yake goge gumin jikinsa,



Bathroom Ya shiga, within 15 mins Ya fito daga wanka ya nufi walk-in closet dinsa cikin kankanin lokaci Ya kimtsa cikin suit navy blue sunyi bala'en Yi mashi kyau da alama zai fita wani wuri ne, hadaddiyar agogon hannunsa sai salki take, kafafunsa na sanye da hadaddun leather shoe ta ko'ina kamshin turarensa Ya karaWe Wakin,



Wayarsa ce ta fara ruri ya Wauko tare da duba sunan mai kiran sa, hidding number ce nan take Ya gane mutumin nan ne daya saba yi mashi kiran sirri,



Picking call din Yayi tare da kara wayar a kunne,



"Naji daWi da ka fara yadda da maganata, Yanzu Ya rage naka Owais kai kokari wurin gano su wanene miyagun dake a family Winka tunkafin lokaci Ya ?ure maka"



"Sai yaushe ne zaka bayyana min kanka? Ina son sanin Wanene kai?And how did you know everything that's happening with my fam?


Sautin dariyar mutumince ta cika masa kunnansa "sanin wanene ni bai da amfani, idan kuma ka damu da son sanin wanene to ka fara kawo ?arshen miyagun dake a cikin zuri'arku" runtse ido Chief Owais yai har cikin ranshi bai son jin Ya ambaci miyagu a family dinsa zuciyarsa karaya ta ke yi kalmar bata masa dadi,



Rai a6ace yace "babu miyagu a family dina, ka kiyaye kalamanka," dariya mutumin yayi "shiyasa nake jin tausayin ka Owais saboda ka yarda da kowa na family Winka, me zai faru a ranar da ka gane gaskiyar da nake kokarin ganar da kai" a fusace Ya daka masa tsawa baima tsaya ya ?arasa jin zancen mutumin ba Ya wurgar da wayar kan Gadonsa, Yana faman fitar da huci Ya furta "bazai ta6a yiwuwa ba, na yarda da family dina, babu bata gari


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login