Showing 225001 words to 228000 words out of 391264 words

Chapter 76 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2582

in yi tunanin koya maku girkin"



Hannah tace"wai komai saida ilmi, to a jika abamu musha sai mu haddace" tuntsirewa ummi tay da dariya, Sajeed dake sauraron su baisan sa'adda ya fashe da dariya ba



"Aunty ummi dama kin daina wahalar da kanki gurin yi masu bayani, ba zasu fahince ki ba, har yanzu da sauran su" acewar Sajeed, tsagaitawa tay da yin dariya cike da nishadi tace"wani lokacin kamar masu hankali, wani lokacin kuma wlh kamar in hada ku da tsumagiya inta jibga" dariya sukayi gaba dayan su



"Ina Unaisah da Batool? Banga gifcinsu ba, ko suna adaki ne"??



Hawwa tace"basa nan tun dazu muka je neman Unaisah don ta bamu notebooks dinmu mu yi karatu bamu ganta ba kuma bata a toilet sai dai muka Wauko books din"?



"Kun duba ko'ina baku gan su ba? Ko dai sun je dakin Danish ne"? Haris Yace danish Yana atare da chief suna karatu bana tunanin sun je dakinsa"



"To Ina suka je ne"? Ta fada tana kallon su



Yasmin tace"kila sun fita waje ko dai muje mu nemo su"!



Shiru ummi tay bata amsa ba tunani tay ko dai sun shiga bangaren daddyn unaisah ne"?



Da sauri ta zaro wayarta daga aljihu ta lalubo contact din unaisah ta kira layinta tana ta kira ba'a picking har ta katse almost 3 times



Yanke shawarar kiran taj tay har wayar ta ?are ringing ba'a Waga ba



"Nafi tunanin suna acikin gidan nan, ku tayani neman su" amsa mata su kai toh, da gudu wasu suka nufi bangaren hagu wasu dama Suka fara bin sako da lungu suna neman su.



?_________________________
'?





Bayan dr shureim ya isa gidan, a hanzarce Ya fito daga motar Ya nufi Cikin main falo Yana ta sauri saboda Hankalinsa Ya tashi Da halin da Zeenatu take a ciki Ya kosa Ya ganta ko hankalinsa ya kwanta har ya kusa fita daga falon muryar Tani? ta katse mashi hanzarin shi.



"Shureim har an dawo" dakatawa yai tare da kallonta"Tani na same ku lafiya" da fara'a tace"lafiyalou, "



"Ina mutanan gidan"?



"Hajiya layla tana aWaki, zeenatu kuma bata jin dadi amma na kira daddynta awaya na faWa mashi, Yanzu haka ya turo family doc din su Yana aWakin Yana duba lafiyarta..."



tun kafin Ta ?are maganar dr shureim Ya furta"Ya Salam! Mami tasan bata da lafiya"? Girgiza kai Tani tay"dana je faWa mata na iske tana bacci shiyasa ban tadata ba"





Hankalin shi atashe Yayi saurin nufar upstairs, azafafe Yake taka stairs din harya haura second floor, Yana isa gaban ?ofar Wakin yajiyo wata Murya irin ta giggan tantira daga cikin Wakin



"Don't waste My time, idan baki bani haWin kai ba, zan kira daddyn naki awaya in fada mashi,"



?shesshekar kukan zeenatu yajiyo tana fadin"ni wlh banso, ka kyaleni, ka kyaleni nace banaso" zuciya da sake sake ta raya mashi wani mugun abunne ke shirin faruwa, gabanshi na faduwa Ya ture ?ofar Wakin da hannu kai tsaye idanun shi suka sauka akan jibgegen katon nan Ya haye kan gadonta yayi mata rumfa da gabjejen kirjin shi ta ma?ure kanta jikin headboard, jikinta sai kakarwa yake yatsun hannunta dana kafafuwanta sai kerma suke, ta rufe kirjinta da tafukanta, Yar rigar wanka ce a jikinta da bata wuci gwiwar kafarta ba, sumar kanta duk ta rufe fukarta....wani irin kishi ne Ya rufe dr shureim baisan sa'adda yai kukan kura daga inda yake yai wani ?wa??waran taku Ya dam?i kafar dr mark A firgice Zeenatu ta ware idanunta akan fuskarshi la66anta sai kerma suke.



Dr mark ko ajikin shi, Fuskarshi a murtuke ba annuri Ya dubi Dr shureim da ya ruke kafar shi.



A gadarance yace"malam Lafiya ka ru?e min ?afa" ya faWa yana bin shi da wani kaskantaccen kallo



Rai a6ace dr shureim yace"uban me kake yi akan gadon ta"? ta6e baki dr mark yai tare da nuna mashi Syringe Win hannun shi"Ubanta ne Ya kira ni don in duba lafiyar yar sa, ko kana da Ja ne" ya faWa tare da Wage mashi gira, ?arfin halin mutum ya Waure mashi kai ko kunya bai ji ba Ya kure karamar yarinya kan gadon ta.



"Amma dai baka da hankali, Don ubanta Ya kiraka ka duba kafiyarta sai yace maka ka shigo har dakinta saman gadon ta? meyasa ba zaka tura me aiki ta kira maka ita ka dubata a falo ba? Hakan da kai ka kyauta??




Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko??Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
Ganin dr shureim zai raina mashi wayau yasa shi saukowa daga kan gadon Yana wani buWe kafadunshi Ya tsaya agaban shi"meye naka aciki huh? Yakamata kasan irin kalaman da zaka furta min, Ni ba sa'an yin ka bane, kada kace zaka shiga hurumin aikina, ba yau na fara ba!? kuma umarnin mahaifinta nake bi"





A harzuke dr Shureim yace"oh shi uban natane Yace ka shigo dakinta har kan gadon ta don kayi mata allura kuma haka ake allura abi a danne mutum"? Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallon tuhuma.



"Malam ka tsaya a iya matsayinka, nima in tsaya a nawa, tun wuri ka fuce daga dakin nan tun kafin na 6ata maka rai"! A kausashe Ya faWa Yana Huci saboda baya Waukar raini, daga gani yana ji da karfi, juyawa yai da niyar ya koma kan gado saboda kunya bata ishe shi ba, a zafafe dr shureim Ya dam?i Strong Arm dinsa, a sukwane dr mark yai mashi wani kallo mai nuni da kashedi





"Sakar min hannuna! Karka kuskura ka bari na maimaita abunda nace"! Girgiza kai dr shureim yai duk da ya Wan sha jinin jikin shi amma baya jin zai iya bari dr mark Ya koma kan gadon zeenatu da sunan zai mata Allura, ko ba dan kishinta da yake ba hakan bai dace ba kwata kwata



Hankalin Zeenatu ba karamin tashi yayi ba jikinta sai kerma ya ke yi kamar wadda sanyi ya kama cikin shesshekar kuka tace"yaya shureim ka ?yale shi dan Allah, wlh idan daddy ya ji ka hana ya dubani ranshi zai 6aci, ni allurar ce bana so tun da akwai magani ya kyale ni in sha" idanunta sun kaWa jawur





Wata irin zufar 6acin rai ce ta wanke fuskar dr shureim?

Ido cikin ido suke kallon kallo tsakanin su, Taurin kan dr shureim da kafiyarsa sunyi matu?ar daure mashi kay,? mutane da dama suna jin shakkar shi sai gashi yau Allah Ya hada shi da shureim?



"Yaya shureim na ro?e ka, ka sake shi, bana son tashin hankali"?



"Wallahi ba zaka dubata ba! Muddin ina numfashi, wannan wani irin yahudanci ne? Daga kai sai yarinya adaki saboda rashin ta ido har kan gadonta"?



?Dr mark ya gama hasala Har yayi wani yunkuri Zai kai mashi naushi Zeenatu tay saurin saukowa daga kan gadonta, ta faWa tsakanin ta riqe dr shureim tana kuka.??



Da ace Zeenatu bata yi gaggawar raba tsakanin su ba, da Allah kadai yasan me dr mark zai yi mashi saboda ya fusata shi.





Sassauta fushin fuskarshi yayi, tare da kallon zeenatu da ta kankame shi, hankalin shi ya Wan tashi da jin zafin jikin ta



Ganin mayen kallon da mark ke binta da shine yasa shi juyawa da zeenatu suka bashi baya.



Shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da zaro wayar shi ya danna ma Alhaji musa Kira bugu uku Ya Waga.



"Sir, Wannan balaraben na gidan ka ya hana in duba lafiyarta saboda kawai Ya iske ni akan gadon ta ina kokarin yi mata allura shine ya rufe ni da faWa yana gaya min magana mara daWi" ya faWa yana kallon bayan dr shureim, sarai yasan sunan shi amma saboda girman kai Ya kira shi da sunan balarabe



on the other hand Alhaji musa yace"Dr shureim Ya dawo gidan ne"?



"Yeah, shi nake magana akai, Yanzu haka muna adakinta"



"Okay, mark ka tafi kawai, i will call you later" ba don yaso ba ya amsa mashi da Okay"



duk suna sauraron shi abun da ya ?ara bata ma dr shureim rai jin ya fada ma alhaji musa yadda ya iske shi adakin batare da jin nauyin hakan ba, hakan na nufin dama ya saba zuwa dakin zeenatun ya hau gadon kuma da sanin Alhaji Musan.



Harara dr Mark Ya watsa ma bayan shi, tare da jan Tsoki ya fuce daga Wakin.



Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, tallabo fuskarta yai da tafukan hannayen shi, idanunta amarairai ce ta kalle shi wani irin tausayinta ne ya kama shi, kumatunta sunyi ja, pink lips dinta sun kumbura daga gani ta jigata taji jiki ba kaWan ba



"Me ke damunki"?



Muryarta da shagwa6a tace"ciwon ciki, daga fitowana daga wanka, na fara jin ciwon ciki yaya shureim nasha wahala kamar zan mutu har fadowa nayi daga kan gado, sai da Tani ta shigo ta iske ni kwance kasa ina murza cikina.. Shine ta kira daddyna awaya ta fada mashi shi kuma ya kira mark don ya dubani ni, ni kuma bana son allura"




Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko??Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
Calmy yace"amma zeenatu why baki ce ya jira ki fito falo ba? Hakan ya dace ya shigo har dakin ki kan gado zai duba ki"? La66anta na kerma tace"yaya shureim ni banma san lokacin daya shigoba, ina kwance kawai na gan shi akaina, dama haka yake yi min in dai zaizo dubani baya tsayawa falo Waki yake shugowa, kuma daddy da mommy sun sani..."



?Girgiza kai yai sha'anin rayuwar gidan uncle nasa sai du'a i, yafi jin haushin Tani da ta kira Alhaji musa, sai kace mami bata agidan ay da ta sani ta tada ta daga baccin da duk hakan bata faru ba.



Ganin kamar damuwa akan fuskarshi yasa tace"ya shureim ranka ya 6aci ko"? Dakyar take magana saboda cikinta dake mata radadi, Girgixa mata kai yai"bakomai, ina maganin naki" da hannu ta nuna mashi kan mirror

Juyawa yai ya nufi closet dinta ya dauko mata abaya ya mi?a mata, hannunta na kerma ta kar6a tasaka a jikin ta.



"Kin ci abinci"?



"Bana jin yunwa Wazu da safe na cika kina"?



"Okey, ki zauna ki jira ni"



make mashi kafada tay"dan Allah kada ka tafi kabarni ni kadai"



"Ba tafiya zanyi ba, ruwa zan dauko" amsa mashi tay da toh ta zauna gefen gadon tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannun shi ruke da Cup din ruwa ya zauna ya taimaka mata tasha maganin ganin yadda hannunta ke kerma bayan ta kammala sha, yasa Yace ta kwanta ta huta, marairaice mashi fuska tay da shawaga6a tace"so kake inyi bacci donka tafi kabarni ko"?

Yanayin yadda takeyi mashi magana ba karamin kashe mashi jiki ya ke yi ba, ba zai juri kallon ta ba.



"Ba tafiya zanyi ba, zan koma falo," mi?ewa tay"nima zanje falon"

"Pls ki kwanta ki huta, babu lafiya a jikinki"



Kuka ta saka mashi"haba ya shureim nagaji da zama ni kadai, ya kake so nayi da raina? nasan tafiya zakai kabarni..." lallashinta ya farayi"ya isa haka ki daina zubda hawayenki bana so, Idan saboda ni ne muje falon tare saiki kwanta kan sofa, in har hakan zai kwantar maki da hankali" ajiyar zuciya ta sauke ya zaro hanky daga aljihu ya share mata tears din fuskarta, ya ru?o hannunta suka fito daga dakin



________________________________
'?



?A bangren su Aneeleerh har wuraren biyu na rana suna agidan, Sun Mori lokacin su tare da su Unaisah sallah kadai ta tadasu, sun sha fira da su kamar ?awayansu, sun Webe masu kewa ba kadan ba, musamman Aneelerh taji dadi tayi farin cikin ganin yadda Junaid Ya saki Jiki da Unaisah in a short time su ka shaku da junan su, wasan doki suka dinga yi mashi ita da Batool, akan bayanta ta Waura shi ta dinga rarrafe tana zagaye sitting room din batare da gajiyawa ba, Sai murna yake yana fadin doki sukuta sukuta.



Aneelerh tasha ruwan mamaki Ganin Yadda Yake ti?ar dariyar, yaushe rabon da ta ga dariyar Junaid tun ranar da Ana ta 6ace ko murmushi bayayi ga ?iwuya amma yau ya sake kamar bashi ba, har ta fara tunanin in suka koma gida zata lalla6a shi cikin lallami ta tambaye shi meya faru da ana? aranar watakil ya fada mata tun da taga bakin shi ya buWe.


Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko??Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.


har video Benazir ta Wauke su da wayarta saboda sun burgeta taji daWin walwalwar da su ke yi cikin nishaWi bayan sun gama yi mashi wasan dokin, Unaisah ta daure idanunta da mayafinta ta dinga zagaye dakin tana neman su, Batool taja hannun junaid suka dinga garata sai da suka wahalar da ita dakyar ta cafko baby junaid ya dinga ihu Yana tsalle yace mata shima ta Waure mashi ido yayi wasan, ta cire mayafin ta Waure mashi idanunshi yadda bazai ji zafi ba, kamar makaho haka ya rin?a mi?a hannu ya na laluban su da gangan Unaisah ta je gaban shi ta tsaya don kada su wahalar da shi, cafko rigarta yai da hannayen shi ya ?ankameta yana fadin ya kama ya kama.



Duba agoga Aneelerh tayi kafin ta kalli Benazir"yakamata mu tafi, kada mami taji na dade" sai lokacin Benazir tace"yanzu abun hawa zamu hau mu koma? nasan ko na kira dr shureim ba lallai yazo ba saboda rashin lafiyar zeenatu..." ta fada tare da ta6e baki



Murmushi Aneelerh tay saboda ta gano me take mawa



"Pls ki kira mijina ya maida mu gidajen mu" cike da zolaya tace"ki dai iya bakinki, Kada babyn naki taji kina kiran sunan ubanta da sunan mijinki, Yanzu ki tada mana 6alli" murmushi Benazir tay tare da kallon su Unaisah dake a zaune kan rug sun gaji da wasan hutawa suke.



Waya ta curo ta danna ma Taj kira tana fara ringing yai picking,?

Tunkafin tay magana Yace"Aneelerh ykk ya su Unaisah, Ina fata kunji dadin kasancewa da su"?

"Alhamdulillah, gasu nan zaune sun gama shan wasa da baby junaid, shima yau yaji dadin ganin yar uwarsa"?

ta fada tana kallon su?



"Masha Allah, Naji dadin jin hakan, Yanzu nake kokarin, kiranki,yakamata su koma yan uwansu sun fara neman su"



"Allah sarki, Nima abun da yasa na kiraka kenan, mun s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hirya tafiya kuma dr shureim bayanan Ya tafi Wasu aka kira shi daga gida har yanzu bai dawo ba, mun kira layin shi baya shiga" ta faWa tana kallon Benazir data tsare ta da ido fatanta Allah yasa ya amince yazo ya dauke su.



Shiru yayi jimm na Wan wani lokacin kafin yace"Okay, Naso na maida ku gida amma bana a kusa, zansa jami'en mu ya kai ku" haWe fuska Benazir tay tuni idanunta suka ciko tab da kwalla, gani take kamar ya Wago su ne shiyasa yace zai turo jami'en su ya kaisu amaimakon shi



"Shikenan, Mun gode ssai," tay mashi sallama,?



Kallon juna su ka yi ita da Benazir



"Nasan saboda ni ne yace bazai maida mu ba" ruko hannun ta Aneelerh tay"pls ki yi hakuri kamar yadda na fada maki, bana so yaran nan su fahimci wani abu kwara mu rabu lafiya, ki daure idan muka shiga mota zamuyi magana, nayi maki alkawarin zan taimaka maki mu shawo kan shi"



?A hankali Benazir ta share hawayen ta, har ga Allah bata son tafiya tabar gidan ji take kamar su kwana anan sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba.



Suna azaune jami'en da taj ya turo yayi masu sallama Yace su fito Yana jiran su.



Hankalin Unaisah ba karamin tashi yayi ba ganin za'a rabata da baby junaid, bawan Allah sai ?ara kankameta ya ke yi duk don kada su raba shi da ita,? bayan sun fito abakin motar suka tsaya, Aneeleeh ta kar6i junaid yana kukan rabuwa da Angel tace mashi yai hakuri za ta zo har gida ta same shi, dakyar tayi mashi wayau ya hakura.



"Toh Mu zamu wuce, zamu tafi mu bar ku da kewar mu" Anila ta fada tana kallon su, duk sun Waure fuska saboda basu son su tafi




Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko??Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.


"Dan Allah yaushe zaku dawo"? Cikin sanyin murya batool ta yi maganar, Benazir tace"in dai mune kusha kuruminku, har sai kun gaji da ganinmu" dadine ya lullu6e su, mi?a masu hannu tay da sauri suka matsa kusa da ita ta haWa su duka ta rungume su, Cikin kunne ta yi ma Unaisah raWa"zan kar6i contact dinki a gurin Aneelerh, Ki kula min da kanki, Ina kaunarki sosai" murmushi unaisah tasaki"nima zanyi kewarki mommyna"



Bayan sun raba jikin su daga na juna ta dubi Batool ta shafa gefen fuskarta da tafin hannun ta



"zanyi kewarki, Yau na fara ganinki amma kin kwanta min araina, kamar yadda Babyna ta sace zuciyata, Ina kaunarki, Ki kula min da kanki" dariyar farin ciki batool tayi"in sha Allah, nagode sosai aunty Benazir, nima ina sonki, " taso ta tambaye su dr shureim amma saita kasa saboda kunyarta da take ji.



Mi?a masu hannu Aneelerh tay, itama tay hugging dinsu baby junaid ya haWe rai Idanunshi sun ciko tab da kwalla.



Sumbatar kumatun shi Unaisah tay, cikin sigar lallashi tace"I'm sorry my little bro,? Zanzo har gidan ku, Aunty aneelerh pls ki kwantar masa da hankali bana so yayi kukan rashi na" ta fada tana kallon fuskar junaid



"Kada ki damu bazan bari yai kuka ba, ku gaida mana mutanan gidan" atare suka amsa masu da toh



Akan idonsu Motar su ta fuce daga gidan, fitar su keda wuya Ummi ta fito daga kofar falon har bayan motar saida ta gani yayin da take karasa fucewa daga gate din

Sun yi tsaye cike da jimamin tafiyar su, baby junaid Ya tsaya masu aransu.



Kwata kwata basu lura da ummi ba har saida ta ambaci sunayen su da sauri suka dube ta?



"Daga ina kuke? Motar waye naga ta fita yanzu? Kallon ta su ka yi ba tare da sun furta kalma ba



"Ba ku ji Ina magana bane"?



Ajiyar zuciya suka sauke atare Unaisah tace"bamu san motar wanane ba,? muma yanzu muka fito"



"Daga ina"? Kallon juna su ka yi

"Kamar baku da gaskiya, ku fada min mana daga ina kuke" ta fada tana jifansu da kallon tuhuma.



"Mun je part din daddyna ne, daga can muke" ba dan ta yarda da su ba tace"shine ko ku fadamin ay dana shirya mun je tare, gaskiya baku kyauta min ba" ta fada tana jifar su da harara dariya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login