Showing 246001 words to 249000 words out of 391264 words

Chapter 83 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2564

har tambayarta nayi tace mun eh itane ko" ya faWa da shagwa6a yana hade fuska.

?ura ma juna ido sukayi batasan ya zatay da shi ba tana son ta tambaye shi meya faru amma tana jin fargaban kada akoma yar gidan jiya, zai iya birkice mata tun da ta fahimci baison maganar kwata kwata.

"Mommy kina kallona ko zaki ci wainar ne in Wan maki" ya fada yana kokarin 6allo mata da sauri ta furta"a koshe nake my baby boy, na fiso ka ci ka koshi..." farfari yayi mata da idanun shi

"Yaushe zaka koma school"?

Ma?e mata kafaWa yai"shaina ?ara samun lafiya" yar dariya tayi "junaid na ganoka gudun school kake, Allah next week zan maida ka, ay naga kaji sauki jikin ka ya murmure" yamutsa mata fuska yai tare da zumbura mata baki

"Allah in kinasho in koma ki sani makarantar su Azeezaty, sai mu runka yin wasa da ita"

ya faWa tare da 6allo wainar da ya rage ma Angel ya tura abaki yana ci, murmushi tayi tare yin kasa da muryar ta"babyna" ya amsa mata naam

Takai hannu ta shafa sumar kan shi.

"Zaka iya tuna abun da ya faru ranar da muka je gidan Hajiya adama"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda ya ware idanun shi da karfi, Jikin shi ya fara kerma kamar mazari.

da sauri ta janya plate din wainar ta daura kan table, ta saukowa daga kan gadon ta zukunna agaban kafafuwan shi kamar mai neman gafara.

"Dan Allah junaid ka fada min, kaga ni mommynka ne, duk duniya baka da tamkar ni, idan ma kana jin tsoron ka fadi ne wasu suji nayi maka alkawarin bazan bari kowa yaji ba daga ni sai kai...."

tatta6e fuskarshi yayi ruwan hawaye suka taru acikin idanun shi labbanshi suka kama kerma taji faduwar gaba da ganin yanayin shi sai dai bata jin zata iya hakura a wannan karan, saboda tayi matukar ?agara da son jin meya faru da su aranar!.


Ruko hannun shi tayi cikin sigar lallashi da wayau da dabara ta karya murya tare da marairaice mashi fuska duk don ya tausaya mata ya fada mata, magiya ta dinga yi mashi yayi shiru yana kallonta da tsantsar tashin hankali akan fuskarshi.

can dai ta Wan bugu cikin shi da wayau tace"Ni dama na sani Ana guduwa tayi junaid, sai da nace mata kada ta tafi tabarmu amma shine ta tafi, ni bansan laifin da nayi mata...."

bata ?are maganar ba, sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata daga bakin junaid

Cikin shesshekar kuka yace"mommy bafa guduwa tayi ba, Allah dodone Ya kashe ta a cikin gidan nan, ni na ganshi da idona kuma itane tace in gudu in 6oye"

kamar an dasa mata aya ta tsaya cak tana kokarin tariyo maganar shi acikin zuciyarta lokaci Waya ta saki dariya tana fadin"haba junaid, abun naka hada zolaya, karya fa babu kyau, In ba zaka fadamin gaskiya ba ay basai ka shirga min karya ba..."

girgiza mata kai yai babu alamun wasa akan fuskarshi ya furta"wallahi mommy dagaske nake faWe maki, dodone Ya cinye ana adakinta, tana ta kuka hada jini a jikin ta..."

yadda kasan kanzon kurege haka take sauraron shi sai tikar dariya takeyi irin ya raina mata wayon nan shi kuwa ya ha?i?ance yana faWa mata iya gaskiyar shi sai ma ta maida maganar tashi abun nishadi.

"Mommy ki daina dariya, ba abun dariya bane wlh dagaske nake maki" wani kallon rainin wayau ta wurga mashi kafin tace"junaid bana hanaka yin rantsuwa akan karya ba..."

kuka ne Ya ci karfin shi wannan karan ta Wan ji faduwar gaba duk da bata yarda da maganar ba ta dauki abun shiririta arude ta ke lallashin shi cikin shesshekar kuka yace"mom.. my ba karya bane, ki daina min dariya, ni banaso dodon daya kashe ana ya kashe mu mommy, dan Allah mu gudu mubar gidan nan ni wlh tsoro nake ji..."

bata san sa'adda ta rungume shi a kirjinta ba, hankalinta yayi mugun tashi saboda kukan da junaid yake yi mata tasan halin kayanta ba karamin abune zaisa junaid yin kuka ba irin haka, tabbas wani mummunan abu ya faru da ya yi silar zaucewarshi sai dai zuciyarta taki yarda da maganar shi, gani take bame yiyuwa bane.

_______________________________
'?

A ?alla ta fi karfin mintuna a tsaye tana kallon Unaisah dake a kwance kan darduma ta nannaWe kafafunta cikin hijab, idanunta suna a rufe gam sai yan siraran hawayen da ke sintiri kan fuskarta tayi kukan tayi addu'ar amma har yanzu zuciyarta taki sarara mata daga radadin da take mata, gani take kamar ta rasa Danish.

aranta tana ji in har kurkukun ya koma tabbas zata bishi ne ko da hakan zaiyi silar rasa ranta don ji take bazata iya rayuwa batare da shi ba.

"Unaisah!" ummi ce ta kira sunan ta, tayi shiru tamkar bata ji ta ba

"Nasan kina ji na, ni bansan ya zanyi dake ba, duk irin kokarin da nayi gurin kwantar maki da hankali kinki daina kukan nan, ga abincin ki dana sa akawo maki shima kinki ci, to wai kukan da kike shi zaisa ya dawo ne? Tun da kinyi addu'ar sai kibar ma Allah komai In sha Allah zai dawo...." cikin sigar lallashi ta faWa tare da zukunnawa gaban prayer mat din

"Dan Allah ki tashi ki ci abincin ki..." da wata irin karyayyar murya ta furta"aunty Ummi, ba zaki gane ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, zuciyata bata min dadi ji nake kamar zan rasa raina ne, yaya Omar ya 6ata min rai, shine silar komai, wallahi Aunty ummi naji zafin kalaman daya gaya ma Danish, duk da baida ilmi ko jahili akayi ma gori sai yaji ba dadi"

jikin Ummi ba karamin sanyi yayi ba, ga wani irin tsantsar tausayin Unaisah daya kamata, tasan bai wuci hada soyayyarshi ke azabtar da ita ba.

"Kiyi hakuri Unaisah, In sha Allah Danish zai dawo, Allah shi zai tsare sa aduk inda yake, mu taya shi da addu'a ni inaji araina ko dan saboda kaunar da yake yi maki zai dawo"

dakyar ta buWe idanunta wadanda suka kada jajawur ta dubi ummi duk da halin da take a ciki tayi mamakin kalmar kaunar data furta.

fahimtar hakan yasa ummi tay saurin furta"naga kamar yafi kaunarki a cikin yan uwanki, kema haka shiyasa nace haka, kada ki Wauka ko ina sanya maku ido ne"

shiru tayi bata tanka mata ba.

"ni abun da nake tunani watakil ya ke6e kanshine awani guri don ya gusar da bacin ranshi in ba haka ba Danish ay ba za ace ya 6ace ba, mutumin da ba shi kadai bane tsaf zai iya kawo kan shi gidan nan..."

bata kare maganar ba ta dakata tana kallon Unaisah ganin yadda ta zabura ta mi?e tsaya kamar zata fadi saboda rashin kwarin jikin ta

"Ina zuwa"?

"Yanzu zan dawo aunty ummi, wani abu zan duba" tana fadan hakan tasa kai ta fuce daga dakin cike da sa ran hasashen ta zai zama gaskiya, maganar da ummi tayi ta tuna mata da wani abu daya ta6a faruwa.

________________=؋?Chief Owais=ت?

Kwance yake akan gadon shi, yar singlet da short ne ajikin shi, damuwa ta hana shi ta6uka komai, ya dade bai shiga tashin hankalin daya shiga a yau ba, wayarsa dake akan bedside drawers sai ringing ta ke yi daga kiran ya katse wani ke shigowa sautin ya cika kunnuwan shi, amma baya jin zai iya picking din su yasan bai wuci Na hannun damansa bane suke kira don suji ko an ga Danish.

Shaf ya manta da bakin da za su yi, saida tunanin Ya faWo mashi aran shi kafin ya mike ya janyo wayar shi tare da duba screen din My dad shine sunan daya gani saida ya fara daidaita nutsuwarsa kafin yai picking call din

"My Son, Ya kake Ya aiki, ka manta da daddyn ka ko"?

Duk da halin da yake aciki sai da yaji nutsuwa ta shige shi jin muryar daddynsa

lumshe idanun shi yayi cikin sanyin murya ya furta"lafiyalou daddyna, ni na isa in manta da bugun zuciyata? Mutumin da nake kwana in wuni da tunanin shi araina saboda kaunar da nake masa"

Sautin dariyar mai girma sharafuddeen ce ta ratsa kunnan shi cike da nishadi yace"My Son kasan duk wata hanya da zaka kare kanka agurina, ka faranta raina, but meke damunka ne? Naji muryarka kamar baka jin dadi..."

Shiru yayi jim dama yasan zai yi wuya in daddyn nasa bai gane wani abu ba, dayawan lokutta ta muryar shi kadai yake gane halin da yake a ciki.

"Babu komai, yanzu na tashi daga bacci ne, shiyasa kaji voice dina wani iri"

"Hmm owais kenan, har ni zaka boye ma damuwarka"?

"Daddy, ka yi hakuri zan iya kiranka anjima mu yi magana"?

"Okay, in ba baka kira ba, Ni zan kiraka, ko inzo gidan naka da kaina kasan bana wasa da lafiyarka" yar dariya chief yayi saboda yaji dadin maganar shi ba wani jimawa sukayi ba sukai sallama

layin Omar ya danna ma kira kusan sau uku tana ringin bai Waga ba sai a kira na hudu yayi picking.

Kara wayar yayi a kunnan shi"Omar, kana Ina"?

On the other hand big guy yace"na tafi neman bugun zuciyarka saboda bana so in rasa ka" shiru yayi jimm yana maimaita maganar big guy harya fahimci ranshi ya 6aci saboda yayi mashi karya, location dinshi ya nuna yana agidan kamar ko ya sani yana akwance kan gadon bai jima da tashi daga bacci ba.

"Omar zamuyi magana, nasan meke damunka, pls don't forget to get the soldiers ready and go to the airport, jirgin su commender yakusa yin landing nan da minti talatin "

"Consider it done, sir, amma ya yakamata kaima ka shirya mu tafi airport din atare, zasu fi jin dadin tarbar da zamuyi ma su"


"Just do what I say" ya umarta, bai bari big guy ya kara magana ba yayi rejecting call din don baya jin zai iya fita daga gidan a halin da yake a ciki.

*Unaisah Angel*

Bayan fitowarta daga dakinsu bata nufi ko'ina ba sai upstairs tana tafiya jiki duk ba kwari ta tura kofar Wakin ta shiga daga ciki bata ga kowa ba.


Gadon shi tabi da kallo sai ta dinga ganin kamar zata gan shi kwance yana bacci, kau da idanunta tayi ta juya ta nufi toilet dinsa.

A hankali ta daura tafukan hannayen ta, ta tura ?ofar ta buWe ta, dira ?afarta ke da wuya taci karo da abunda yayi silar razanar da ita ta daddage ta fasa kara tana ambaton sunan Allah ta dafe kanta da tafukan hannayenta, hadi da runtse idanunta jikinta ya fara kakarwa, wani irin faduwar gaba taji tamkar ana dakan sakwara a kirjin ta.

dukkan ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tayi matu?ar firgita da abunda idanunta suka gane mata, tayi matukar razana, yatsun hannunta na kerma ta bude kofar Wakin garin saurin ta fita cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da ?asan hijab dinta dake ja da kasa gaba Waya ta wuntsila ta yi kundunbale ta kife ?asa hankalinta yayi mugin tashi jikinta yadau zafi rau wata irin zufar tashin hankali ce ta fara tsastsafo mata.

Tana ta kokarin mikewa donta gudu taji motsin buWe ?ofar tuni tasha jinin jikin ta, ta ?ame a durkushe ta kasa Wagowa yayin da ?wa?walwarta ke tariyo mata Halittar da tagani a cikin toilet dinsa kamar Wolf (kerkeci) jibgegen gaske.

?amshin turaren Chief ne Ya ziyar ci kofofin hancin ta, Kafin DaddaWar muryarsa ta katse zancen zucin ta

"Unaisah? Are you Okay"? Ay tana jin muryarshi ta yi wani irin yunkuri da iya karfinta na karshe ta zabura ta mi?e, gaba Waya ta faWa kan broad chest dinsa ta ?an?ame shi, cikin shesshekar murya take faWa mashi abunda ta gani a cikin toilet din tare da yi mashi nuni da yatsan ta.

Sam ya kasa fahimtar me take nufi, sai kallonta yake yadda ta kankame jikinshi ta hanashi motsawa daga gani ta tsorata ba kadan ba.

"Unaisah, what's wrong? Who's in the toilet?"

Batare data Wago ba ta furta"dodo ne a toilet din sa,"

"Okay, zanje na duba, ki jira anan" ya fada tare da ruko hannayenta a hankali ya banbare su daga kan waist dinsa.

yayi mamakin uwar zufar daya gani akan fuskarta kamar an yayyafa mata ruwa ga zafin da jikinta ya Wauka yaji shi har jikin shi da ta rungume shi sai faman jan numfashi take tafin hannunta Waya dafe da saitin zuciyarta.


"Ki kwantar da hankalin ki, Ina atare dake, ba abun zai faru..."

yawu ta haWiya tana faman zare idanunta acikin nashi ta amsa mashi da toh.

har ya Waga ?afa zai nufi toilet din Yaji ta dam?o upper arm dinsa, slowly yakai duban shi gare ta.

Girgiza mashi kai tay a tsorace tace"Don't go alone, I don't want anything to harm you"

murmushin gefen fuska ya sakar mata har cikin ranshi yaji dadin nuna damuwa da ta yi akan shi hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba.

"Kada ki damu, ba abun da zai faru dani in sha Allah" ya fada yana kallon Heart shaped lips dinta da suka ji?u da ruwan hawayen ta.

Ta?i sakin rigar shi saboda ta tsorata da abunda tagani tana jin fargaban wani abu ya same shi, shi da bai saba da wahala ba.

Ma?e mashi kafada tay kamar ?aramar yarinya cikin sanyi murya tace"hankalina bai kwanta daka shiga ba, pls kada kaje, ka kira salsabeel awaya yazo ya gani ko ka kira sheikh imam malik"

A hankali ya cire hannun ta daga kan arm dinsa

Kamar ta sanya mashi kuka, bai jira ya kara jin me zatace ba, Ya nufi toilet din sai da ya fara karanta addu'ar shiga kafin ya sa tafin hannunsa ya ture ?ofar A hankali ta buWe.


Without feeling nervous ya fada cikin toilet din, Yana shiga idanunshi sukayi mashi kyakkyawan gani yayi matu?ar mamakin ganin shi kwance cikin kwamin wanka Ya cika shi da ruwa, ko kayan jikin sa bai cire ba ahaka ya kwanta a ruwan Kamar ma bacci yake yi.


_Tsantsar mamaki da al'ajabi ne suka bayyana karara akan fuskar shi, Ikon Allah mutumin da suke ta wahalar nema kamar zasu tada garin abuja, ba irin neman da jami'an su basuyi mashi ba sako da lungu na garin saida suka bincika basu gan shi ba ashe yana acikin toilet dinsa kamar al'jani, ko taya akai ya shigo gidan? Bayan har gate officers Win gidan sai da ya tambaye su koya dawo gidan suka ce mashi bai dawo ba, gani yake kamar amafarki yake kallon shi saboda zuciyarsa taki aminta da abun da idanunsa ke nuna mashi_

Da tsantsar ruWani ya furta"Danish! Is that you?"


*DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE
'?*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: __________________________________
'?


"Danish is that you"! Ya faWa yana bin fuskar shi da kallo, babu alamun yaji maganar shi, babu inda ke motsi a jikin shi in ka cire numfashin shi dake fita cikin nutsuwa.

Walking slowly chief ya isa bakin bathtub Win ya zu?unna kan kafafunsa ba tare daya kau da ido daga kallon fuskar Danish ba.

Allah kadai yasan farin cikin da ya mammaye zuciyar sa wanda misalta shi ma bazai yiwu ba, Yau da ya rasa Wan tahalikin nan Allah kadai yasan halin da zai shiga.

Abun da ya faranta ranshi da baije ko'ina na, ko da suka bata mashi rai bai yi fushi ba, bawan Allah sai ya dawo gida yayi kwanciyar shi cikin ruwa hakan na nufin bazai iya rayuwa ba tare da yan uwansa ba, duk runtsi duk wuya yana atare da su.

Cikin sanyin murya ya sake ambaton sunan shi"Danish" Shiru bai motsa ba, cike da fargaban kada ace wani abun ne ya faru da shi chief ya daura tafin hannunsa na dama saman forahead dinsa ya shafa shi har zuwa kan karan hancin sa.


Ba zato ba tsammani yaji Danish Ya dam?i wuyan Hannun sa, eye lids dinsa na kerma dakyar ya buWe idanun shi da su kai mashi nauyi ya dubi chief.

Da wata irin kakkausar murya yace"saboda yan uwana na dawo nan"


Wani irin faduwar gaba Unaisah taji, yayin da take kokarin shigowa toilet din cike da fargaban me zata taras jin shiru chief bai fito ba shiyasa ta yanke shawarar bin bayan shi.


Lokaci Waya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata muryarshi, tayi matu?ar yin mamaki saboda ita lokacin data shiga toilet din jibgegen wolf tagani zaune cikin bathtub Win shiyasa ta raza, yanzu ta gane shi ne ya rikiWa ya dawo mutun.

wani irin tsantsar farin ciki ne mara misaltuwa ya wanke zuciyarta, dama saida ranta ya bata zai dawo, hasashen da tayi ya tabbata maganar da ummi tayi ce ta tuna mata da ranar daya rikiWa kafin ya zama maciji da jikin shi ya dauki zafi rau cikin kwami ya shiga ya tsuma kanshi da ruwan sanyi.

yanzu ta gane idan ranshi ya 6aci yana son yayi cooling temper dinsa ruwan sanyi yake shiga, taji tausayin shi, shi dai rayuwarshi wani sa'i kamar bata mutane ba.

"Danish, ka tada min hankalina, daga ni har yan uwanka da abokan aikina, babu irin neman da ba ayi maka ba a garin nan, saboda kai ko abinci na gaza ci, ban ta6a tsammanin damuwar da nayi dakai takai har haka ba..." ya faWa yana kallon cikin idonshi.

"Da na san ranka zai 6aci da ban matsa maka mun tafi head quarter ba, banji dadin abunda big guy yayi maka ba, na tsawatar mashi kuma ya gane kuskuren shi, bazai ?ara gigin bata maka rai ba"

yanayin yadda chief ke yi mashi magana da sigar lallashi ba karamin kwantar mashi da hankali yayi ba, zuciyarshi taso ta karaya da jin irin kaunar da yake yi mashi, tun daga kan facial expression dinsa yaji ya yarda da duk wani abu daya faWa masa.

"Kayi hakuri idan na bata maka rai, sannan inaso Ka faWa min duk wasu sharrudda da zamu bi don mu zauna dakai lafiya batare da mun 6ata maka rai ba saboda naji jiki ba kaWan ba lokacin da aka sanar dani ka fita nayi zaton bazan ?ada ganinka arayuwata ba" softy ya fada tare da tsamo hannun Danish daga cikin ruwan ya haWe yatsun hannun su cikin na juna, yayi shiru yana sauraron shi.

"Sannan Alfarmar da zan roko a gurinka, nasan baka yarda da ni ba, amma dan Allah ko dan saboda yan uwanka kada wata rana kayi fushi ka koma inda ka fito.." ya Wan dakata yana kallon yanayin fuskar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login