Showing 288001 words to 291000 words out of 391264 words

Chapter 97 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2597

shirya"?


"Eh, duk sun shirya" ajiyar zuciya ya sauke.

Bayan sun shiga Gidan, atsaitsaye Ya gaisa da su Commender kafin Ya nufi bedroom dinsa, don Ya shirya...

(Tayaya akai Chief Ya ku6uta daga tarkon da Mahaifinsa Ya Wana masa"?)

Bayan da ya kira Mommynsa awaya, ba'a fi minti biyar ba, sai ga hamshakiyar motarsu ta shigo a parking space security din dake driving dinsu yayi parking, A hanzarce Gimbiya Malikat ta fito daga mazaunin baya na motar, Jikinta sanye da tsadaddiyar Lafaya lace, hadadden shade din data sanyawa idanunta ba karamin kawatasu yayi ba, takalman kafarta kadai abun kallo ne, tana tafiya p.a Winta na take mata baya, wata katuwar mace karkarfa, Jikinta sanye da Suit, tasha kitson zane akanta.

Cikin takun qasaita take tafiya, yanayin fuskarta sam babu walwala, saboda Hankalin ta ya tashi da jin abunda Owais Ya fada mata.

Kaitsaye suka Nufi master suite din Mai girma sharafudden.

Abakin kofar Room Win suka dakata da yin tafiya, Gently ta Waura Thumb Winta akan Biometric scanner Win dake jikin handle din kofar, nan take kofar tayi Unclocking Win kanta...

Juyawa tayi tare da kallon P.a Winta, abunka ga masu Izza a jini, da ido tayi mata alamar ta tsaya anan, with respect ta amsa mata da okay ma'am..

shigarta keda wuya kofar tayi locking kanta..

?akin tabi da kallo, kwatsam idanunta suka hango mata shi kwance kan floor kamar matacce kwata kwata baya motsi.

Numfashin shi ne kadai ke fita.. Hankalinta yayi mugun tashi, a sukwane ta zare shade din dake akan fuskarta..cikin sauri ta nufe shi ta zukunna agabanshi ta sanya hannayenta biyu ta dago da kanshi ta kwantar saman laps Winta.

shasshafa fuskarshi tayi muryarta na rawa ta furta"My son! Lafiya ka kwanta kan floor kamar wani mara gata? Meke damunka ne? Owais kana Ji na kuwa?

tariyo maganar da sukayi awaya tayi lokaci Waya zuciyarta, ta raya mata ba baccin lafiya yakeyi ba, saboda yanayinsa yafi kama da na wanda yasha kwayar maye.

a hankali ta kwantar da kan nashi kan floor, ta mike tare da kai idonta kan coffee table din dake a seating area.

Cups ta gani biyu akai, matsawa tayi gaban table din, ta dudduba cups Win, ita dai bata ga komai ba har ta juya zata koma wurinshi kwatsam idonta ya hango mata packet na pills daga gefen table din kiris ya rage ya shige karkashin sa.


Yatsun hannunta na kerma ta dauki packet din ta soma karanta rubutun dake a jikin shi zaro ido tayi saboda ta gane sleeping pills ne.


Hankalinta ya tashi ba kadan ba! tamkar zata fashe da kuka ta furta"why Owais! Why! Me ya hadaka da maganin bacci mai hadarin gaske.." juyawa tayi tare da kallon shi bawan Allah baimasan inda kanshi yake ba..

fitowa tayi daga dakin hannunta ruke da fakitin, P.a na ganinta tay saurin russina mata..

"Duba min maganin nan" ta fada tare da mika mata roban

"Inaso akawo min antidote dinsa Yanzun nan.."

Jinjina mata kai p.a tay, tare da juyowa ta bar gurin, tana atsaye tana jiran ta, badajimawa ba saigata ta dawo hannunta ruke da Injection ta mi?a mata.

Tasa hannu ta kar6a, tare da juyowa ta koma Wakin, kasancewar tana da ilmin abun bata sha wahala ba, bayan ta kamma yi mashi allurar.

Zama tayi gefen shi, tana kallon shi, zuciyarta cike fal da tunin meya faru tsakanin shi da mahaifin shi..

Tsawon mintuna ashirin, Ya fara zubda gumi a jikin shi, kamar an yayyafa mashi ruwa, yatsun hannunsa dana kafafunsa suka fara kerma kamar wanda sanyi ya kama, ajiyar zuciya ta fara saki ganin ya fara dawowa hayyacin shi...a hankali ya bude idanunshi wadanda suka kaWa jawur ya kurawa ceilling din dakin ido kamar ya manta da abunda ya faru.

"Owais,"

jin muryar Mommynasa yasa shi saurin kai idonshi gare ta..wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya tattara karfin jikinshi Ya samu ya mike tare da matsawa kusa da ita, cikin sauri ta rungumoshi kan kirjinta, hannunta daya acikin sumar kan shi..

"My son, are you Okay? ta fada cikin kulawa.


Jinjina mata kai yai alamar eh, bata kara tanka mashi ba, yayi shiru yana faman jan numfashi har saida Ya ?arasa wartsakewa Ya dawo hayyacin shi kafin ta tambayeshi dangane da kwayar maganin baccin daya sha!

"Kai nake sauraro Owais, ka daga min hankalina, kuma meya hadaka da daddynka, dayaja harya kulle ka adakin sa"?

ta fada tana kallon fuskarshi, still bai dago daga jikinta ba.

Cikin disasshiyar murya ya furta"mommy, zanyi maki bayani, amma ba yanzu ba, pls ki kwantar da hankalinki, ba abunda ya faru tsakanina da shi..."

fuskarta ayamutse tace"meyasa bazaka fadamin yanzu ba"?


A gajiye ya girgiza kanshi"mommy, tafiya zanyi, abokan aikina suna jira na, I don't want to lose the opportunity I have, In har banje ba, all our plan will be ruined"

gefen fuskarshi ta shafa da hannunta"shikenan, Na fahimce ka, bazan matsa maka ba, nasan yanayin aikinku, amma pls, ka kula mun da kanka Owais..." lumshe idanunshi yayi tare da jinjina mata kai, ya ruko hannayenta biyu acikin nashi"mommy, Ina barar addu'arki, nasan kinayi min, amma kwanakin nan ina bukatar ?ari akan wadda kike yi min, bama ni kadai ba, hada abokan aikina .." cikin sanyin murya tace"in sha Allah Owais, zanyi maka addu'a, ay bana mantawa dakai, amma kayi ma daddynka magana akan yayi maka addu'a ?

girgiza kai yayi"a'a mommy, nafi bukatar taki, in har kikayi min kamar yayi minne, and pls, bana so daddy yasan kin bude min dakin nan, kiyi min hanyar da zan fita daga gidan nan batare da wani ya ganni ba..."

ta Wan rude da jin abunda Yace amma sai bata kawo komai aranta ba, saboda ta yarda da Wan nata da kanta tayi mashi hanyar barin gidan batare da security officers din da mahaifinsa yasa tsaron gidan sun tuhume su ba.

Kunji yadda akai Chief Ya ku6uta daga tarkon daddynsa
'?


Fitowar Chief daga Part dinsa tayi daidai da fitowar Danish Da Salsabeel.

Gaba Waya Hankulan U.s Army din Ya dawo kan shi, yayi matu?ar jan hankalinsu yadda kasan Diamond a sararin samaniya saboda kyan da yayi Cikin shigar Isod Combat Uniform, Ya rufe fuskar shi da Mask, hadaddiyar sumar kan shi ya daure ta da head ties jelar gashin ta sauka agadon bayansa.

?afafuwansa suna asanye da wasu hadaddun Combat boots ko a kakin yakin bakomai ya sanya ba babu protective gear saboda baya bukatar su.

har ya sauko down basu daina bin shi da kallo ba, tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin Matashin sarauyin da kakin Yaki su kayi ma kyau irin Danish ba ya fita daban acikin su, ya fito a suffar jarumtakarsa, sadaukin namiji mai ji da karfin sa..

Kallo Waya big guy yai masa ya kau da kai gefe, taj kuwa sai da yadan sha jinin jikin shi aranshi ya ayyana ba mace ba ko namiji ya kallesa sai ya burge shi, ina ma amfanin kyau irin nashi ba ilmi wannan ay masifa ne bakaramar 6arna zaiyi ba, a ganinsa kyawun shi ne ke ruWar Unaisah da kuma tausayinsa shiyasa ta ke nema ta zauce akan son shi.

A hankalin Salsabeel Ya ruko hannun Danish acikin nashi.

Bayan sun karasa saukowa down U.s Armies suka fara zuzuta kyawun da kakin su ka yi mashi hatta chief sai da ya yaba, gaba daya suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan.

abun daya 6ata ma big guy rai Yana niyar ya shiga Motar da chief zai hau Chief ya ja hannun Danish suka shiga motar, Yaji zafin hakan sai dai Ya hakura Ya shiga Motarsu Taj.

bayan us armies din sun shisshiga motocinsu, da gudun gaske suka fuce daga Estate din saboda Lokaci.

A cikin Mota Chief Ya kira Sheikha Mujeeda, Aransa yana Allah Allah ta Waga Yasan ba ta daga kira in ba an fara tura mata sakon neman izni ba amma cikin ikon Allah tayi picking yadan yi mamaki amma da ya tuna maganar da sukai akan Danish sai ya gane dalilin dayasa ta daga kiransa bayan sun gaisa yace mata Wanta na barar addu'arta zasu yi wani aiki mai hadarin gaske.

yanayin muryarta da damuwa tace In sha Allah zanyi mashi addu'a, In yana kusa ka bashi wayar"

mika ma danish wayar yayi baisan wanene ba Ya kar6a ya kara a kunne yayi shiru baice komai ba har saida gimbiya Mujeedat ta furta"My Son kana lafiya"? arude Ya kalli Chief tare da tambayar who is She? Murmushi Chief yai tare da cewa"matar daddy minister" nan take ya tariyo lokacin farko daya fara ganinta, bazai ta6a manta yadda ta cire mask din fuskarshi ba ta zuba mashi kyawawan idanunta.

Cikin sanyin murya ya gaishe da ita with respect, ta amsa mashi kafin tace"chief ya fada min zakuyi wani aiki mai hadarin gaske, In sha Allah zan tayaku addu'a..." yace mata ya gode, har tana zolayar shi da cewa tasan da daddy minister ne suke waya sai yafi sakin jiki saboda sun saba amma ita kamar baison yi mata magana..

Ko gama wayar basuyi ba ya mika ma Chief saboda wani yanayi dayake ji atare da shi, Zuciyarshi Ta kasa samun sukuni tun kafin su bar garin Ya fara jin matsananciyar kewar Unaisah.


Tafiya yankin azaba sun Wauki tsawon awanni akan hanya, da misalin sha biyun dare, suka qaraso cikin Dajin da suka haWa katafaren sansaninsu, dajin yana a kusa da evil forest, katafaren Military base ne mai girman gaske ga wasu Irin Dakarun Sojaji masu ?ira irin ta zakuna kowan nan su yana asanye da army combat uniform dinsa, Cikin takun majiya karfi suke sintiri a cikin sansanin tamkar da rana saboda hasken electricity din dake a ko'ina na sansanin.

Bayan sun fito daga cikin motocin su, duk inda suka gifta cikin girmamawa sojojin ke sara masu tare da yi masu maraba da zuwa, a haka har suka shiga inda masaukinsu yake domin su dan hutu na wucen gadi.


THE DAY=?y?=?z?


Asubahin fari suka farka daga bacci, musulman dake acikin sukayi sallah awani ke6a66en wuri dake a cikin sansanin, bayan sun yi kalacin su, gaba Waya sojojin suka hallara a filin dambe, suka fara motsa jikin su har dambe sai da su ka yi a tsakaninsu wanda ya kasance kamar gasa ce su ke yi, Danish ya zama zakaran gwajin dafi a wurin an kasa samun wanda zai kayar dashi dayawa sun kara samun kwarin gwuiwa da ganin irin kwazon shi, bayan sun gama damben suka Wan huta har wuraren ?arfe shida na marece kafin daga bisani suka fara shirin shiga evil forest.

A helipad din dake a wani sashe na cikin Sansanin Wasu dankara dankaran Jiragen ya?i ne a jere masu saukar ungulu da aka tanadar masu, ko da ido ka kalle su sai gabanka ya fadi, already fighter Pilots Win da zasu Yi jigilar daukarsu tuni sun shige cikin helicopters din.

Bayan komai ya daidaita, har dakarun sojojin sun gama shiga cikin jiragen, Kafin wani Lokaci jiragen suka lula sama, yayin da trucks Win makamai dake tafiya akasa suke bin su.

*FATAN NASARA*

____________________________________
'?


*=?%?GIDAN KURKUKUN ?ADDARA=?%? &?*


Farkawarta kenan daga bacci, A hankali ta buWe idanunta tare da kallon rufin gadon, Har na tsawon mintuna, har rama ta qara saboda azabar rashin lafiyar da tayi.

ta wutsiyarta idanunta ta hangi mutun kwance gefenta, da sauri ta wurga idanunta akanta, ajiyar zuciya ta sauke ganin tsohuwa khala, da alama tayi nisa acikin baccin ta, ta Wan yi mamaki don tunda ta tsinci kanta a dakin khala bata ta6a kwana kan gadon ba, a saman kujera take yin baccin ta a zaune kamar dogari.


Kasa kauda ido tayi daga kallonta, wani irin kaunar dattijuwar take ji acikin zuciyarta, batasan sa'adda ta matsa kusa da ita ba takai hannu ta shafa gefen fuskarta mai tarin tamoji tamoji, ta manna mata sumbata kan goshin ta ta danyi murmushi har chin dimple dinta Ya motsa.

"Bayan Wan uwana gabriella, bani da abu mafi soyuwa daya wuce ke, Inasonki Khalana.." kamar daga sama ta tsinkayi muryar Khala acikin kunnanta"Nima Ina sonki Jikata" zare brown eyes dinta tayi fuskarta dauke da annurin farin ciki ta furta"Khala, Idonki biyu"? Ta fada akagare da son jin amsarta..

A hankali Khala ta buWe idanunta akan fuskar Gabriellah.

"Ya jikin naki Jikata"? still da murmushi kan fuskarta tace"Naji sauki, yanzu babu inda keyi mani ciwo"

Tattausan murmushi khala ta sakar mata"haka nake sonji, Na lura kamar Kina farin ciki Yau, saboda tunda nake dake banta6a ganin murmushin ki ba..." yar dariya Gabriel tayi

"khala, kece silar farin cikina, da na yanke kauna da rayuwar duniyar nan, amma silar haduwana dake da kuma alkawarin da kika daukarmin na haWani da Wan uwana Yasa naji Ina son na rayu, Ina son na zama jajirtacciya jaruma kamar ke, kuma ina son na Wauki fansar abunda akayi mana" tunda tafara magana khala ke binta da kallo, arayuwarta tana Son ya'ya musamman idan tagan su cikin nishadi da walwala shiyasa aduk lokacin data ga ana azabtar da rayuwar su take jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu saboda ba?in cikin da takaici.

"Amma khalana, Idan muka yi nasarar ku6uta daga kurkukun nan, atare zamu rayu ko"? Murmushi khala tayi"Idan na fita bansan inda zanje ba, bani da kowa, ko kina da inda zaki ajiye ni"?

Shiru gabriella tayi tare da ta6e bakinta kamar zatay shagwa6a tace"nima bani da kowa, amma dani da Wan uwana Gabriel, zamuyi aiki tukuru, donmu gina gidan da zamu zauna, nayi maki alkawarin zamu baki kyakkyawar kulawai..."

cike da nishadi khala ke sauraronta..

Kwatsam suna tsaka da yin fira, ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka jiyo masu wani irin sautin Bugun ganguna dumdum kamar dodon kunnan su zai fashe, tsabar sautin bugun gangar Ginin Har girgiza yakeyi, hatta gadon da suke kwance akai ya kama girgiza.

gaba daya Gabriella tabi ta ruWe, baiwar Allah dama ba lafiyar kwalwa gare ta ba, da sauri ta toshe kunnuwanta da tafukan hannayenta.


Tsohuwa Khala kuwa tashin Hankali da farga Ya hana ta motsa sai faman zare idanunta takeyi.

Lokaci Waya suka daina Jin bugun gangar, sai kuma suka fara jiyo WaddaWar Busar sarewa tana tashi

lokaci Waya yanayin fuskar Khala Ya sauya, aruWe ta furta"ELDERS"


Cikin ruWu Gabriellah ta kalle ta cike da rashin fahimtar me take nufi..


Dam?o hannunta tayi acikin nata"akwai abunda na manta ban fada maki ba, daren yau dare ne mai hadarin gaske, bugun gangar da kika ji alama ce dake nuna ?arasowar ELDERS.

"abunda nakeso dake ki 6oye karkashin gadon nan, kada ki kuskura ko tari kiyi idan ba haka ba zaki jefa rayuwar ki cikin haWari ne.."

Hankalin Gabriella ba karamin tayi yayi ba, muryarta na rawa ta furta"Dan uwana fa? kada su kashe min shi..."

katse ta khala tayi"babu abunda zai same shi, kiyi abunda nace maki kawai"

saukowa sukayi daga kan gadon da sauri Gabriella ta shige karkashin gadon, ba laifi Yana da faWi da tsawo, kamar ?aramin Waki, tayi mamakin ganin buhun huna kusan Biyar a karkashin gadon ga wasu akwatinan ?arfe, jikinta na kerma amma saboda karanbani saida ta yi kokarin kwance buhun don ta ga menena aciki, Sai dai takasa saboda mugun Waurine akayi masu, tatta6a jikin buhun tayi sai taji kamar Makamai ne a cikin su...

Komawa tsohuwa khala tayi kan gadon ta kwanta tare da lumshe idanunta, zuciyarta cike fal da fargaban abun da zai biyo baya don tasan muddin Elder ya ?araso adakinta zai huce gajiyar shi.

bakomai yafi damunta ba face zuwan Garkuwa, Allah Allah take su karaso saboda batason Elders suyi nasarar Salwantar da rayuka a wannan daren, In har daren yau ya wuce Bata cimma burinta ba, bata jin zata Iya jure rayuwa adoron duniyar nan, saboda in har ta kuskura asirin ta Ya tonu na abunda take kullawa Allah kadai Yasan Mummunan hukuncin da zasuyi mata, donma saukinta daya Elder Yana Ji da ita.

Bata kare zancen zucinta ba, Kamar daga sama Taji dirar wani abu adakinta,

Sautin shu'umar dariyar shi ce ta karaWe kunnuwanta, Tuni tasha jinin jikin ta.

"Da wata irin Murya irin ta tantiran ?an'duniya Ya furta"Idan ma bacci kike, toh ki farka..." yunkurawa tayi ta mi?e zaune, tare da kai dubanta gare shi, Yana atsaye cikin wata rantsattsiyar alkebba launin Ja mai adon duwatsu irinta sarakuna..ya lullu6e kanshi da hular alkyabbar, rabin fuskarshi arufe yake da takuntumi, kafafunshi suna asanye da wasu hadaddun takalma na alfarma, yayin da hannunsa ke aruke da sanda ta zallar Zinari.

ba'a Iya ganin fatar jikin shi saboda ya lullu6e ko'ina hatta yatsun hannunsa safa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya sanya masu.

Gabriella dake labe ta kasa kunne tana sauraronsu, da ga inda take tana Iya hangen kafafuwan Elder..

"Taya zan Iya bacci batare dana sanyaka acikin idanuna ba, tun bayan daka tafi kabarni da kewarka, idanuna sunyi maraicin ganin ka, sanyin idaniyata, mijina uban ya'yana, sarki Waya tak da ke mulkar zuciyata..." cike da qasaita yake sakin dariya yayin da yake tinkarar gadonta cike da dattako yake taka matakalar gadon.

"Meyasa soyayyar mu bata tsufa ne? Aduk lokacin dana ganki sai inji kamar ana rura wutar sonki a cikin zuciyana, bazan Iya misalta kewarki da nayi ba.

yayin da yakeyin maganar, wani irin kallo khala take binsa da shi mai wuyar fassaruwar, ta tsane shi fiye da yadda ta tsani mutuwarta, shine silar komai =ؔ?

gaba daya tayi zurfi a tunaninta sam ta manta da shi akusa daita, batai aune ba taji ya janyota jikin shi, wani Waci taji aranta, sai taji kamar ta hada jikinta da wuta saboda tsanar da tayi mashi..

Sumbatar kuncinta yayi, cikin wani irin salo ya fara sarrafa ta.

Gabriella dake la6e a karkashin gadon, gabanta sai faduwa yakeyi ganin yadda gadon ke girgiza kamar zai rubzo mata, gani take kamar mutumin dayazo ne ke cutar da Khala.

kasa jurewa tayi duk tabi ta rude jikinta sai kakarwa yakeyi bata san sa'adda ta saki ?ara ba, da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta.

Lokaci Waya Elder Ya raba jikin shi daga na Khala, ido cikin ido suke kallon juna..tun daga yanayinta ya fahimci akwai wani abu da take boye masa.

Kamar daga sama taji Ya furta"kamshin mutum nake ji adakin nan..." arazane ta ware idanunta akan fuskar shi, jinjina mata kai yayi

"Ke da wanene Kuke rayuwa adakin nan? Kuma Yana ina"? Ji tayi kamar ta fasa ihu saboda tashin hankali, batasan ya akai ya gane akwai mutun ba..
.
"Kinyi shiru baki bani amsa ba, Ko kin bani za6i In gano da kaina"?

Yawu mai daci ta hadiya muryarta na rawa tace"bakowa, Ni kadai ce, nayi mamaki da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login