Showing 330001 words to 333000 words out of 391264 words

Chapter 111 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2617

yata, yaya shureim bana jin dadin komai, hankalina ba akwance yake ba, Ina so nagan su..." dakyar ta karashe maganar..


Gaba daya a kunnan su Mami da basu dade da shugowa dakin ba, Gaba dayansu sunyi tsaitsaye cirko cirko suna sauraron maganar Benazir, tausayinta ne ya kamasu mami tuni idanunta sun ciko tab da kwalla, batasan ya zatay ba, ita kanta zataso Benazir ta hadu da bayin Allahn nan ko ta samu nutsuwar hankali..

Zeenatu dake kuka kalaman benazir sun karya mata zuciya, wani kukan takuma fashewa da shi.

"Benazir, Kiyi hakuri, Ki kara jurewa dan Allah, Na roke ki, sanya damu arai bazai haifar maki da komai ba, saima ta fama maki raunin dake a cikin zuciyarki, bana so a koma yar gidan jiya, dan Allah Benazir kiyi hakuri zamu tayaki da addu'a kema ki dage in sha Allah zasu bayyana"

Hajiya sarah ce ta yimaganar cikin sanyin murya.

Girgiza kai Alhaji ubaid yai shi kanshi abun na damun shi.

"Kinga kukan Ya isa haka, Kiyi shiru, in sha Allah Idan Uncle dinku ya dawo zanyi magana da shi ya taimaka yasa a yi cigiyar su agidan jaridu watakil adace..."


gaba daya tunaninsu har yanzu babu labarinsu ita kadai tasan Da zaman su..


A hankali ta dago daga kan kafadar dr shureim Idanunta sun kada jawur ta dube su ji take kamar ta fada masu Taj da Unaisah suna nan kuma tasan inda suke, ko dan ta samu su tayata neman yafiyarsa.


Girgiza kai tayi"nagode da kulawarku agareni, Amma basai an yi cigiyarsu a gidan jaridu ba, Aneelerh ta fada min sunyi iyakar bakin kokarinsu gurin yada hotunansu a social media da Gidan jaridu amma har yau babu labarinsu...." ta dan dakata kafin ta daura da cewa"dan Allah kada ku damu da halin da nake a ciki, bawai don banyi imani da kaddara ba, wlh nayi kokarin In manta da su a cikin zuciyata amma abun Ya faskara..."

ta faWa tana matse kwalla.
Kallonsu Dr shureim yayi"pls Ku barni da ita, ku je ku ci abincinku, Zan yi mata nasiha" Alhaji ubaid yace"yawwa shureim pls kayi kokarin shawo kanta, bana so ciwonta ya tashi" amsa mashi yai da toh, fita su ka yi ya rage saura su uku

Kallon zeenatu yayi, Tana atsaye bakin kofar sai shesshekar kuka take.

"Calm down your mind, Ki kawo min lunch din ta a daki" ta amsa da toh ta juya ta fuce..

Ruko hannunta yai suka zauna kan gadon ta.

Nasiha ya farayi mata cikin kwantar da murya har saida taji zuciyarta ta dan lafa da radadin da takeyi mata.


Sai da yaga ta samu nutsuwa sosai kafin yace"akwai inda ke maki ciwo" girgiza ma shi kai tay"a'a ya shureim, lafiyana lou"

"Okay, " ya fada tare da sauke ajiyar zuciya.

Shigowa zeenatu ta yi cikin dakin, hannayenta ru?e da tray mai dauke da lunch ta mika ma dr shureim Yasa hannu ya kar6a yadago ya dube ta"thanks, yanzu sai hankalin ki ya kwanta, tunda auntyn naki ta daina kuka" murmushi tadan saki.


"Ki je ki ci abincin ki"

Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh.


Bayan fitar Zeenatu daga dakin Ya maida hankalinsa akan Benazir, A baki ya soma bata abincin tana ci, sai kallon shi takeyi har saida Ya tsargu da kallon Yace"Akwai wani abu ne"?
"Yaya shureim dan Allah ka taimaka ka kaini gidansu Anila Inason ganinta."

"Da yaushe"?
"Ko yanzu kace sai in shirya mu tafi"
"Kin fada mata ne"?
Shiru tayi jim don rabon da suyi waya da Aneelerh kusan two weeks babu wanda ya tuntubi wani amma saboda tana son Taje din yasa tay mashi karyar sunyi waya harma ta fada mata zasu zo

Yace toh idan sun kammala Cin abincin zai kai ta.

Dadine Ya lullubeta bayan sun gama cin abincin, Ya fita don yaje ya shirya.


Jikinta na rawa ta dauki waya ta danna ma Anila kira, don ta sanar da ita batun zuwansu, almost 3 times tana doka mata kira ba'a picking a karshe ta hakura da kiran nata ta fada toilet don tayi wanka.



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*



*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite


Health College
Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun ?addara Takun ?arshe page 61 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 29, 2024
Sponsored Link
Takun ?arshe
Zaune yake a mazaunin driver na motarsa, ita kaWai ya ke jira su tafi, har ya fara gajiya da jiran ta, wayarsa ya zaro daga front pocket din rigarsa ya danna mata Call.

"Idan kika ?ara minti Waya baki fito ba zan koma ciki ne." Yana fada yayi rejecting call Win, jingina kanshi jikin headrest ya yi tare da lumshe idanun shi.

Sam bai ji tahowarta ba, sai dai ya ji motsin buWe cardoor din, buWe idanunsa yai tare da kallon ta baki a buWe ganin yadda ta ca6a ado kamar wadda zata je gidan surukanta, Wani hadadden Code lace ta saka orange riga da skirt sun Wan kama jikinta, mayafin kayan a kafaWa ta daura shi, ga wani hadadden daurin dan kwali da ta yi, ba?ar sumar kanta ta sauko har mid back dinta, fuskarta ta sha make up....,sunkuyar da kai ?asa ta yi ganin kallon da Dr Shureim Win ke yi mata.

"Benazir, wa ki kai ma kwalliyar nan? sai ka ce wadda zata je bikon mijinta?" Tuntsirewa ta yi da dariya, ta yi mamakin jin ya canki abunda ta shirya, don wannan kwalliyar da ta yi saboda Taj ta yi ta, yau ta Waura Wamarar janyo hankalin shi gare ta.







"Zai iya yiwuwa."



ta faWa tana sakin murmushi, ta6e baki ya yi tare da Wan girgiza kan shi ba tare da ya kawo komai a ransa ba, Kafin ya yi wa motar key a hankali ya yi reverse, a tsanake Ya ke yin driving Win su...



"Zeenatu ta ganki da zaki fito daga gidan?"



Ya tambaya yayin da yake juya sitiyari.



"Eh, amma bata nuna zata bini ba, naji tace zata bi Aunty Sarah Office, may be shiyasa bata damu da ta biyo mu ba."



Tafiyar mintuna ?alilan Suka ?araso layin su Aneelerh, Bayan Baba mai Gadi Ya buWe masu gate Dr Shureim ya shigar da motar ciki, a parking space ya dakata.



"Mu shiga ciki" Girgiza kai ya yi, "ki fara shiga za???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n shigo daga baya" amsa mashi tayi da toh,



Fitowa ta yi ta nufi cikin gidan, bakinta Wauke da sallama ta shiga...



"Muryar wa nake ji kamar Benazir?" Murmushi ta saki tare da sauke idanunta akan Mami da Ummi dake zaune a falo suna kallo a tv, gaba Waya suka Wago suna kallonta bayan sun amsa sallamar da ta yi...



"Wlh ni ce Mami, na yi maku zuwan bazata ban kira na faWa ba" ta fada tare da karasawa ta dan du?a gaban sofa Win da suke a zaune ta gaishe da su.



"Ina wuninku, fatan na same ku lafiya"



A tare suka haWa baki "lafiya lou, ya mutanan gidan naku?"



"Suna nan lafiya, Sun ce agaishe masu da ku."



"Ina Zeenatu da Shureim namu"? A cewar Mami,



"Yaya Shureim shi ya kawo ni, yana a waje, shi ya ce in fara shugowa zai biyo ni, mun baro Zeenatu a gida za su je office tare da Mommynta."



Mami tace"Allah Sarki, na ji kin ce kin yi zuwan bazata baki kira kin fada ba, nan ay kamar gidan ku ne Benazir, naji dadin zuwanki..." Still fuskarta dauke da murmushi..



Ummi ta ce"Ga mutuniyar taki can, ta Waura aure da zaman Waki, dan Allah Benazir in kin shiga ki yi kokarin kwantar mata da hankali, kwanakin nan mun rasa gane kanta,"



"Bata da lafiyane?"



Mami ta ce, "Hmmm, ta sanya damuwa a ranta ne, wai kwanakin nan tana yawan yin mafarkin su Uzair shine fa duk tabi ta hana kanta sukuni..."



"Subhanallah!" Fuskarta da damuwa ta faWa tare da mi?ewa ta nufi dakin Aneelerh..



A bakin kofar dakin ta tsaya, kusan sau uku tana doka mata sallama shiru ba'a amsa mata ba, har saida ta fara gajiya da tsayuwa, a ?arshe ta yanke shawarar shiga ciki.



Tana Shiga idanunta suka sauka akan Aneelerh dake a kwance kan gado, ta ?urawa Ceiling idanunta ko kyaftawa bata yi, lamarin ya daurewa Benazir kai, a ranta ta ayyana wannan wata irin damuwace da zata sa aita maka sallama baka ji?



Ta karashe zancen zucin tare da kai hannu saman kafar Anila ta 6aka mata bugu, wata irin zabura ta yi, a firgice ta mi?e zaune tana zare idanunta muryarta na rawa ta furta,"Na shiga ukuna!" hannunta Waya dafe da saitin zuciyarta.



Hankalin Benazir ba karamin tashi ya yi ba, ganin yadda Aneelerh ta rame kwata kwata bata a cikin nutsuwarta.



"Ni ce fa..." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta sauke Idanunta akan Benazir don sam bata lura da ita ba.



Numfashi ta dan ja tare da sauke ajiyar Zuciya ta ?a?aro murmushi kan fuskarta..



"Benazir ke ce? Meyasa baki fada min zaki zo ba?" Bata tanka mata ba har saida ta samu guri ta zauna daga gefen gadon kafin ta maida hankalinta kan Aneelerh.



Duk tabi ta dabarbarce ganin irin kallon da Benazir ke yi mata, washe baki ta shiga yi tana kokarin danne damuwarta ta ce, "Sannu da zuwa Benazir, ya ki ke? Ya su Mami? Ina ya Shureim da zeenatu?"



Cike da damuwa Benazir ta furta, "Don Allah meke damunki haka Aneelerh? sau uku ina doka sallama baki amsa ba, nama yi zaton kin shiga toilet ne ko bacci kike yi, ashe idonki biyu kina a kwance kin takura kan ki, why pls dubi yadda kika rame? Fuskarki duk ta yamutse kamar wata tsohuwa" Ta fada tana ?are mata kallo..



A rude Anila ta girgiza kai muryarta da in-ina ta ce,"Lafiyana lou ba abun da ke damuna..."



Kaitsaye Benazir ta ce, "?arya ne wallahi, Dole akwai abunda ke damunki sai dai idan baki son fadamin ne."



Murmushi ta dan yi,"Bafa wani abu bane, kawai ina yawon yin mafarki akan Uzair...." tunkan ta kare maganar Benazir ta tari hanzarinta, "Mami ta faWa min hakan, amma ban yarda ba Anila, Look, nifa nasan wacece ke, mafarkin Uzair bazaisa ki shiga damuwa har haka ba, bayan kinsan mafarki ba gaskiya bane, in ma hakanne a yadda nasanki da tawakkali Addu'a zaki dage kina cigaba da yi masa bawai ki tsananta damuwa ba, kawai ni yanzu ki fadamin meke damunki kinsan tsakanina dake babu 6oye-6oye, Kinsan sirrina nasan naki, kuma dai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, pls In har kin yarda da ni...."



Shiru Anila ta yi jim tana tunanin kodai ta fadawa Benazir watakil ta taimaka mata su nemi mafita, ru?o hannayen Benazir ta yi acikin nata, suka ?urawa juna ido..



A hankali hawaye suka fara zarya kan kuncin Anila, hakan ba ?aramin Waga hankalin Benazir ya yi ba.



"Zan fada maki saboda na yarda dake, amma dan Allah ki rufa mini asiri Benazir, bana so kowa ya sani mu barshi a matsayin sirri tsakanina da ke.." A ?agare Benazir ta jinjina mata kai.



Nan take Anila ta fayyace mata komai, tun daga ranar da suka je gidansu Hajiya Adama da abunda ya faru bayan dawowarsu game da 6atan Ana, da inda suka ga Baby Junaid a sume cikin drawer shelve da yadda Junaid ya burkice masu suka rasa gane kanshi, komai saida ta sanar da ita, har wayar Ana ta curo daga cikin pillow case ta kunna mata videon ta mika mata don ta gani da idanunta.



tunkan ta ?arasa kallo yatsun hannunta keta kerma kamar wayar zata kife kasa, idanunta azazzare cike da tashin hankali ga wani irin faduwar gaba da take ji, labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha..., bata ?are sallallamin ba Anila ta yi saurin toshe mata bakinta da tafin hannunta gudun kada wani ya ji yo su.



Tuni hawaye sun wanke fuskar Benazir, Sai faman girgiza kai ta ke yi.



Cikin muryar rada Anila ta ce,"Allah abun tsoro dan adam abun tsoro, muna nan sake da baki ashe muna a tare da mugun iri acikin mu! Benazir ki fada min taya hankalina zai kwanta? Wai Uncle dina shi ne yake aikata wannan fasikancin a cikin gidan nan? Babban tashin hankalina Ina Ana? Yau kusan wata uku babu ita Benazir, ina jin tsoron ace ya kashe ta...." Ta fada tana kuka ?asa kasa.



A hankali Benazir ta zame hannun Anila data toshe mata baki da shi.

Hawaye wasu na bin wasu akan kuncinta ta ce, "Anila dama Ana ta 6ace shine baki fadamin ba tun lokacin da abun ya faru?"



"Na yi zaton da son ranta ta gudu shiyasa ban fadamaki ba saboda na saka ran zata dawo."



Jinjina kai Benazir ta shiga yi.



"Mugu bashi da kama Anila, munafuki kamar na Allah, wlh bazamu kyale shi ba, dole mu ?watarwa Ana hakkinta sannan mu maka dan iska gurin hukuma...."



bata kare maganar ba Anila ta yi saurin katse ta, "Pls ki daina Waga murna bana so wani ya ji, yanzu me yakamata mu yi? Kin dai ji ta ce mutunne mai hadarin gaske in har muka yi kuskuren da maganar ta koma masa zai iya salwantar da rayuwarmu tunda ba imanine da shi ba, Allah kaWai ma yasan munanan ayyukan da yake aikawata bayan wannan da Ana ta fada."



Jinjina kai Benazir ta yi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abubuwan dake faruwa da ita a gidan Uncle Musa, yun?urin kashetan da ake yi ga kuma kurciya da aka yi mata, tun rana ta farko da aka fara yi mata take zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta.



Anila da ta zuba mata ido ganin ta yi shiru bata da niyar yin magana yasa ta dafa kafadarta, "Benazir kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Numfasawa Benazir ta yi kafin ta ce, "Aneelerh, akwai damuwa, nima fa akwai wanda ke bibiyar rayuwata a gidan Uncle Musa, kusan sau hudu ana yunkurin kashe ni....."



Waro idanu waje Anila ta yi, cike da ruWani take kallon Benazir ya yin da gabanta ke faduwa rass rass!!!



Nan Benazir ta labarta mata komai da ya faru da ita tun farkon zuwanta gidan..



"Aneelerh wallahi ba don Allah yana kawo min Wauki ba, da tuni an jima da kashe ni, don ma yanzu babu tabon yatsun hannun mutumin a wuyana ya goge dana nuna maki kin gani"



Hankalin Anila fa ya tashi sosai, duk tabi ta rude, "Benazir! anya ba iska bane? In ba haka ba wanane zai yi maki hakan agidan Uncle Musa? Gidan dake a tsare da Security Officers taya wani bare zai iya shigowa har dakin ki ya yi yun?urin kashe ki??" ta fada tana zare idanunta...



Girgiza kai Benazir tayi, "Wlh Anila ba iska bane, mutunne! Abunda yasa na kara karfafa zargina saboda abu biyu, na farko kurciyar da aka yi mini! Aka rabani da dangina, Na biyu labarin da Ana ta bada, Shine ma ya farfaWo da tunanina, koma wanene mutunne kuma yana amfani da sihiri kamar yadda Ana tace Uncle Wan-iya yana amfani da sihiri gurin sarrafa ta"



Da ?warin gwiwa ta yi maganar tana duban Anila wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari.



"Ina zargin mutumin da yayi min kurciya shine yake son kashe ni.."



Cikin shesshekar kuka Anila tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'iun! Banazir mun shiga Uku! Wanene wannan? Laifin me ki ka yi masa da ya ja har ya ke son raba ki da rayuwarki? Wai dan Allah meyasa hakan ke faruwa da rayuwarmu? Daga wannan sai wannan?"



Maganar Anila ta sake tuna mata abunda ta faWa mata game da Taj, cikin saurin ta ce, "Anila! Kinsan tunanin da nake kuwa??" Girgiza kai tayi da sauri, "A'a."



Gyara zama Benazir ta yi,



A labarin da kika bani na abunda ya faru da su Uzair, kin tuna Alhazawan da suka yi ma le?en asiri? Har suka rikiWa suka handame uba da ?a'yansa saboda yayi masu le?en asiri...?" Cikin sauri Anila ta jinjina kai,"Kwarai kuwa haka ne!"



"To baki tunanin ko halin da nike ciki nada ala?a da hakan, sai nike ganin kamar idan muka fada ma Taj komai zai taimaka masu gurin yin binciken da su ke yi akan Alhazawan nan da kuma 6atan Uzair? Kuma kinga Taj yanzu jami'e ne shi, sannan yana a gidan Director General In har muka je masu da maganar wallahi ina mai tabbatar maki zasu dauki mataki akan Uncle dan-iyan, tunda su jami'ai ne sun fi mu sanin ta yadda zasu bullowa lamarin, ko ya kika gani?" wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anila ta sauke, Wlh sham ta shafa'a ta manta da cewa Taj jami'in bincike ne ai da tuni ta sanar da shi komai.



"Ban ta6a sanin ni shashasha bace sai yau da kika ankarar dani, Mu da muke da jami'i a hannu, Wlh gaba Waya kaina ya kwance tsawon kwanakin nan inata neman mafita, kwata kwata tunanina bai bani in tuntubi taj ba, nama manta da cewa shi jami'i ne sai yanzu da kika tuna min."



Murmushi suka sakar ma Juna.



"Yanzu ya za a yi? Babu bu?atar 6ata lokaci, da zafi zafi ake bugun ?arfe, ?wara muyi amfani da damar da muke da ita tunkafin lokaci ya kure mana" A cewar Anila.





Benazir ta ce, "Ay daga nan sai gidan DG, Nifa dama da shirina nazo wlh, na ma manta ban fada maki abunda ya kawoni ba saboda halin dana riskeki..."



"Anila kusan One month bana samun Unaisah a waya! Shima Taj kona kira baya picking? Baki ga na rame ba nima? Damuwa ce wllh, Gashi kwanakin nan sai munanan mafarke-mafarke na ke yi akanta da ni kaina, Ina ji araina kamar wani abu na faruwa da su..."



Fuskarta a marairaice ta faWa, Anila ta ce, "Ai bake kadai ba, Ni kaina Idan na kira bana samun su a waya, wlh hankalina ba a kwance yake ba, don ma tashin hankalin videon nan da na gani ya dauke mun hankalina almost 2 weeks ban neme su ba."



"Ba surutu yakamata mu tsaya muna yi ba, na baro Dr Shureim a waje yana jirana, ki tashi ki shirya mu tafi."



_________________________________
'?



"Shiru Har yanzu basu fito ba," A cewar Ummi, Mami ta ce, "Kinsan ?awaye In aka haWu ba'a gajiya da fira,"





Ummi ta kuma cewa,"Kuma na ji ta ce ita da yayanta ne, shi ba zai shigo bane? An bar shi a waje yanata jira."



"Nima abunda na gani kenan, bari na je na yi masu magana su je suce ya shigo." tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login