Showing 42001 words to 45000 words out of 391264 words

Chapter 15 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2583

da hukunci kuma dole ayi biyayya......



Komai dake faruwa akan idanun zahra, tsoro duk ya cika ta ganin rikicin dake shirin 6allewa, tun Wazu ta 6oye kan ta a bayan su hindu dake a tsaitsaye, jikin ta sai kerma ya ke yi saboda batason tashin hankali arayuwarta...



Pravin Allah Allah ya ke baba obie yaki amincewa da zaman su a hall din ji yake tamkar ya shiga zuciyarshi don ya samu damar tunzura shi akan kada ya bar su, jikin shi sai tsuma ya ke yi.





Chief owais dake kallon shi amsar shi kawai yake jira, cike da fargaban kada Ya kunyata shi a bainar jama'a duk da yasan abune mai wuya baba obie yayi mashi hakan saboda baya son 6acin ransa.



Gyaran murya yayi hankali gaba Waya ya dawo kan shi, kafin ya soma magana yana duban kowan nan su



"Bana son abun da zai cutar da ahlina, sannan bana son duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a zuri'a na...." tunkafin ya kare maganar, munafuki pravin ya soma sakin shu'umin murmushin farin ciki don yasan karshen zancen zai ce ne a kore su.



"Bawai don bana son yaran bane, Wa na kowa ne, sai don ina son mu ?are dinner din nan lafiya, zaman su acikin mu, ba lallai ya zama alkhairi ba, tun da wasu sun nuna basu bu?atar ganin su,......" da tsantsar mamaki chief owais ya ke kallon fuskar baba obie, hajiya saratu da su laura har sun fara sakin fuskokin su sai kace akan su za su zauna....



Chief bai tsaya jin karashen zancen ba, saboda zuciyarshi ta karaya, a raunace Ya sakin hannun baba obie, ya juya ya kalli prime minister wanda tuni ruwan hawaye sun kwanta luff a idanunsa...



Cikin sanyin murya ya furta"am sorry uncle, banyi tsammanin abun zai kai haka ba, dana san ba za a kar6e su ba da banyi gigin zuwa da su dinner din nan ba, dama nayine saboda farin cikin ka" ya faWa yayin da yake mayar da idanunsa kan baba obie



"zan tafi tare da su....'



yana ?arasa maganar cikin takun sauri Ya nufi su unaisah, wani irin murmushi ne ya bayyana akan fuskar pravin da su hajiya saratu.



"Owais"!! Har Ya kusa kaiwa bakin kofar muryar Baba obie ta katse shi, Cak ya tsaya da tafiya, dama da biyu yayi hakan don yasan baba obie bazai iya jurar 6acin ranshi ba.



"Meyasa ba zaka tsaya kaji karashen maganata ba"? A hankali Ya juyo yana duban fuskarshi, Nan take murnar pravin ta koma ciki.



Matsawo yayi kusa da shi, fuskarshi dauke da murmushi yace"kamar yarda kayi saboda farin cikin Uncle dinka, Ni kuma saboda farin cikin ka, na amince su shigo ayi shagalin dinner din nan tare dasu, sannan bana so na sake jin wani ya fadi abun da zai 6ata ransu, Umarni ne wannan!!



Yana ?arasa maganar shi, Chief owais ya nufeshi, gaba Waya yayi huggin dinshi.



rai a6ace hajiya saratu ta nufi hanyar fita daga hall din.



"Karki kuskura ki fita! Dawo ki zauna" muryar Sir mubarak Ce ta katse ta, tana faman haWe rai ta dawo ta tsaya hannunta dafe da ?ugu.



Dam?o hannun hajjaty pravin yayi, yana faman fitar da huci Yace mata ta biyo shi subar hall din, sam ya manta da hajiya saratu dake kallon shi, ga alama ya fita hayyacinsa, jikinshi duk yayi zufa sai kace babu a.c a hall din



Muryar hajjaty da tsantsar tashin hankali ta furta"pravin meke damun ka ne? Agaban mutane kake ru?e hannu na? ina zaka kaini ne? bayan ba agama dinner din ba, dan Allah ka kyale ni" ta fada tana kokarin cire hannunta daga mugun ru?on da yayi mata.



Da karfi hajiya saratu ta furta sunansa"pravin!!" ko kallo bata ishe shi ba, ?o?ari kawai ya ke yi yaja hajjaty don su bar hall din, ita kuma ta dage akan bazata bi shi ba, gaba daya hankulan mutane ya dawo kan su.



"Nashiga uku pravin, dan Allah ka kyaleni, nace maka bazan bika ba....." gigitacciyar tsawa hajiya saratu ta daka mashi da kakkausar murya mai haWe da zafin kishi ta furta"ka fara haukane? Agabana kake ru?e hannun ta? Anya kuwa kana acikin hayyacin ka"



?agowa ya yi da idanunsa waWanda suka kaWa jawur ya dubi hajiya saratu da masifa ya furta"Bai shafe ki ba!" har sai da taji gabanta ya fadi, Su hajiya laura sun saki baki da hanci suna kallon ikon Allah, hatta su Hajiya malikat da su sir mubatak mamakinne ya kamasu yadda ya rufe ido yana jan hajjaty da tsiya yake son fitar da ita daga hall din.



Alhazawan canada suna ta kallon ikon Allah abu kamar a drama, anbarsu a duhu sun kasa gane meke faruwa...



Tsawar da Sir mubarak Ya daka mashi ne yasa shi saurin shiga taitayinsa, A fadace yace"wannan wani irin shashanci ne? Baka da hankali ne? Ina ruwanka da ita? Tun da ta nuna batason tafiya ka ?yale ta mana!"



Kallon hajjaty pravin yayi idanunshi jawur yana huci ya furta"idan har baki bini mun koma gida ba ranki zaiyi mugun 6aci, wlh kada ki bari na riga ki fita daga hall din nan" yana fadar hakan Ya juya tamkar mayunwacin zaki Ya nufi kofar fita hall din cike da sa ran hajjaty zata bi bayan shi, sai dai har ya fuce babu alamun zata bishi, kamar an ru?e ?afafuwanta, hakanan taji ba ta son tabi shi, taji kunyar abun da yayi mata, agaban jama'a, tasan dole adasa masu ayar tambaya, ita kanta a ruWe take batasan dalilin dayasa pravin ya rikice mata ba, Hajiya saratu yau taga abunda yafi karfinta, tamkar a mafarki take ganin komai, akan idonta pravin ya ru?e hannun hajjaty bainar jama'a batare da ya ji tsoronta ba, lallai zai fuskanci horo mai tsanani daga gare ta, har ta ita kanta hajjatyn yaja mata bala'e domin kuwa bazata ?yale ta ba, ransu twins su yayi mugun 6aci musamman zayn shi da yafi zuciya......



Bayan hatsaniyar ta lafa, senate lateef ya dubi su unaisah "tun da mahaifinmu ya yanke hukunci akan ku zauna, ba mu da ja, ya zamar mana wajibi mu tarbe ku, amma kafin nan ku sauke facemask dake akan fuskokin ku" ya fada yana nuna faces din su.



Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyin su.



"Kamar ka shiga zuciyata, nima abun da nakeso nace kenan, gaskiya ba zamu bari ku shiga da wannan face mask din ba, yakamata mu ga fuskokin ku," tun da aka fara rikicin nan sai yanzu his excellency abdul razak ya sanya baki,



His excellency deen yace"to nima dai abuWe min inga fuskokin nan, ko hankalina ya kwanta" ya fada da Wan murmushin kan fuskarsa.



A hankali Batool ta Waura yatsun hannunta da ke kerma ta ru?o face mask din ta yaye shi daga kan fuskarta, Har saida gabansu ya fadi da ganin kyawun fuskarta, wato wani guntun murmushi da tayi ta sunnar da kanta kasa ba karamin tafiya yayi da imanin su ba, wasu tuni sun fara danasanin sanya su kuka da su ka yi.



Bayan batool ta cire nata, Sajeed Ya zame face mask din fuskarshi, tsabar kiWima da ganin fuskarshi yasa hajiya laura Wan zaro idanunta ga dukkan alamu akwai wani abu da ya ruWe ta da shi, kyawun sajeed ba ?aramin tafiya yai da imanin su ba.



"Saura ku, Ku cure naku mu gani" Zaki ne ya fada yana nuna sauran



Sajeed ne ya taimaka wurin Cire ma Azeeza nata, Duk tabi ta ?an?ame shi, fuskarta tayi sharkaf da hawaye har wani zazza6i ya lullu6e ta, ganin fuskar Azeeza ya yi matu?ar razana Sir mubarak har sai da ya kalli fuskar Mom turai, ba shi ba, hatta Dr jazz da su Ibad kusan a lokaci Waya suka jefa wa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar mamaki da al'ajabi.



Jamimah dake a ma?ale jikin angel, babu alamun zata motsa, ru?o hannunta Angel tayi tare da cire mata mask dinta, fuskar ta 6aci da hawaye hada majina hakan yasa basu samu damar ganinta da kyau ba.



Kusan atare Javed da Haris suka tu6e nasu face mask din, Kallon kallon aka komayi atsakanin Iyalan obinna kowa da abun da ya Waure ma shi kan shi.



"Parveen ku cure naku" cikin sanyin murya Unaisah tayi masu magana



Batare da 6ata lokaci ba, Parveen ta cire nata mask din, wani irin bugu zuciyar hajiya saratu tayi, ha?i?a ta razana da ganin kamannin ta dana yarinyar, har sun 6aci kamar tayi kakin ta, banbancin su launin fata, ba ita ba harta sauran matasan family din da iyayan mamakine tsantsa akan fuskokin su...



Lokacin da Naufal ya cire mask din fuskar shi, wata irin firgita hajjaty tayi, har sai da ta dafe saitin zuciyarta da ke yi mata wani irin mahaukacin bugu, tagaza yarda da abun da idanuwanta suke gane mata, gani take tamkar mafarki ne ba gaske ba, domin kuwa ita dai tasan wanda ya mutu baya dawowa, harta su Hajiya Muhibbat sai da suka saci kallon fuskar hajjaty da ta naufal saboda wani abu daya ja hankalin su....



Gaba Waya sun rikice Sun ruWe, sun gaza gasgata abunda idanunsu ke nuna masu



Tamkar an kulle masu baku nan su, Sun kasa magana, Lamarin ne yafi karfin tunanin mai tunani, mamakin su tayaya akai yaran suke bala'en kama da ?an family din su?



_Ba zata juri bugun da zuciyarta ke yi mata ba, da azalzalarta akan son ganin fuskar yaron da hateem ya kwallafa rai akanshi, tabbas tana son ganin shi, kowa na gurin burin shi Danish ya cire mask din fuskar shi, sunyi matu?ar ?agara da son ganin sa, walking gently gimbiya mujeedat ta tako ta tsaya gab da inda danish yake atsaya kamar mai wani nazari abu akanshi, idanunshi na kallon kasa sam bayason hada ido da kowa_



Sanya hannu tayi ta cire mask din dake akan fuskar shi............



Kiris ya raga zuciyar gimbiya mujeeda ta daina bugawa saboda razanar da tayi, gaba Waya hankulan su ya dawo kan shi, Wani irin mugun bugu zukatan su suka soma yi, yadda kasan ana dakan sakwara, Gaba Waya suka zazzare idanunsu gami da buWe bakunansu saboda tsabar kiWima kamar sun ga wani mugun abu, wato Sun gigita sun razana da ganin wanan abin al'ajabi da yai matu?ar ?aga hankulan su, Afirgice Chief Of Staff Na canada Ya dubi fuskar Security Advisor da wani irin ruWani akan fuskokin su, at same time su ka yi saurin kallon Prime minister Hateem, Baba obie kuwa kusan suman tsaye yayi da ganin wannan Kama ta ban al'jabi, Senate lafeef da su His excellency sai faman jinjina kan su suke yi sam sun gaza magana kamar kurame, sai yanzu suka gane dalilin dayasa hateem ya firgice ma su da kaunar yaron ashe shi yasan abun da ya gani, Kai kowama dake a wurin ya rasa lissafin kwalwarsa saboda ganin fuskar Danish, Wai shin Ina Nazli? Ay tun da tayi tozali da danish tsabar firgici da ruWani yasa har batasan sa'adda ta saki wayar hannunta ba, gaba Waya ta kife kan flloor, Jikinta ya kama kerma kerma tana faman zazzare eyes din ta akan fuskar shi yadda kasan twin brother din ta.



saboda ruWu tunani su ka yi ko dai Nazli ce ta koma inda danish yake atsaye hakanne yasa sukayi Saurin kai idonsu inda take atsaye don suga idan tana nan, Ganinta yasa suka ?ara rikicewa.



Security adivisor ya kasa samun nutsuwa saboda al'ajabin da ya kama shi, Muryar shi na rawa rawa yana tangyadi cikin harshen turan ci yace" dama prime minister yana da wani Wane da ba mu san da shi ba, ko kuwa ?aninsa ne? Ko dai giyar dana sha ce takai mun karo? Pls ku yi min bayani yadda zan fahimta.



Senate lateef ne ya bashi amsa da cewa"ba su haWa ala?ar komai ba, kama ce kawai" babu alamun za su gasgata maganar shi.



"Abun da Waure kai, amma ya ya akai su ke bala'in kama har haka? Kamar an yi photo copy din fuskar Hateem, ko ma ince Nazli" his exellency Deen ne yayi maganar, Yazrin sam takasa samun nutsuwa Sai kallon shi take yi ko ?yaftawa babu, wato danish ya girgiza su da kyawun shi, Hankulan su Faryat ya tashi haikam tsabar yadda su ke kallon shi kamar za su haWiye shi, yadda kasan irin kura taga naman nan.



Ha?i?a sun rudu da prisoners, babu wanda bai yi mamakin sanyin kyan su ba, da al'ajabin kamanceceniyar su da ?an uwan su yadda kasan ya'yan cikin wasu daga cikin su tsabar yadda kamannin su ya bayyana da juna...



Ganin kallon nasu ba mai ?arewa ba ne gashi sunbar yara atsaitsaye, da sauri Ziyad ya ce



"Lokaci yana tafiya, yakamata acigaba da shagali"



kafin Ya ?are maganar sautin wa?a mai ratsa zuciya ya karaWe cikin hall din, ?aya bayan Waya Suka juya suna nufar wurin zaman su kowa da abun da yake sa?awa a cikin zuciyar shi.



Hateem kamar jira yake yi a samu maslaha, jiki na rawa ya nufi danish ya ru?o hannun shi acikin nashi, burin shi su haWa ido don su kalli juna dakyau amma ya?i bashi damar hakan, murmushi ne dauke akan fuskar sharafudeen sai faman kallon su ya ke yi, yaji dadin ganin hateem a irin wannan yanayin.



Da zolaya yace irin wannan kallo haka? Ka da fa ka lashe mana yaro" ?ar dariya hateem yayi,



Chief owais da ke kallon su ba karamin kwanciyar hankali ya samu ba ganin ya faranta ran uncle din sa



"Uncle ka tafi da shi, zaman shi anan bazai yiwu ba, saboda baya son hayaniya, kuma baya son ana kallon sa, From now until nightfall, I entrust him to your care" wani irin farin ciki ne ya ?ara lullu6e prime minister, kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna, cikin sanyin murya yake fadin"nagode owais, wlh ka gama min komai, bazan ta6a manta alkhairin ka a gare ni ba, Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta min" addu'o'i ya dinga zuba mashi, bai manta da sheikh imam ba wanda ke atsaye tun dazu murmushine akan fuskar shi.



"shukran jazeelan Ya sheikh, Allah ne kadai zai iya biyan ka, saboda babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani da su wurin yi maka godiya" ya faWa yana ru?o hannun sheikh imam gaba Waya wani irin annurin farin ciki ne akan fuskokin su.



Unaisah da ke ta sauraron su aranta Allah Allah take Danish ya amince da bu?atar chief yabi prime minister don tasan halin shi da kafiya ba kowa ke iya tankwara shi ba.



Kafin ta ?are zancen zucin nata ba, da mamaki taga danish yabi prime minister hannun su ru?e cikin na juna suka nufi hanyar fita daga hall din ko irin ya waigo ya kalle su baiyi ba, ajiyar zuciya ta sauke, sarai ta fahimci masu satar kallon ta.



gimbiya mujeedat sai bin su da kallo take yi, tarasa ma wani irin tunani zatayi game da bawon Allan nan mai tsantsar kama da Nazli, kasa jurewa tayi da sauri ta bi bayan su, ita ma Yazrin ta bi su, Nazli ce kaWai ba tayi yunkurin bin su ba, kwata kwata babu annuri akan fuskarta, Ita bakomai ne damuwarta ba face abu biyu, na farko yaron da ke kama da ita! arayuwarta ta tsani ace wani yana kama da ita, saboda izzarta, tafi so mai nata ya kasance ita kadai ke da shi, bayan wannan sai Unaisah! Hankalin ta bai kwanta da ita ba, saboda wani kallo da taga sun jefa wa juna a tsakanin ta da chief owais nan take taji bata son ganin yarinyar, Nazli tana da zafin kishi, izzarta ce ke hanata bayyanawa.



Fuskarta babu annuri ta kai hannu ta dauki wayarta dake kan floor, da wani irin takun qasaita ta juya tabar wurin su.



Mom turai da ke ta kallon su tun Wazu take son tunkararsu ganin babu dama ne yasa ta yi shiru tana kallon bada?alar da ake yi, yanzu kuwa da ta samu dama, Da sauri ta nufi wurin Azeeza saboda sun bata tausayi da suna kuka, hanky ta zaro daga purse dinta, ta zu?unna agaban ta tare da sanya shi kan fuskarta ta shiga share mata hawaye



Cikin kulawa tace "Stop crying kin ji ko? everything is over now, we are welcoming you to our family" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyinsu har sun fara Wan sakin jikin su.



A hankali Sir mubarak Ya nufi Jemimah dake a ma?ale da Angel ta cukuikuiye mata rigarta zukunna yayi agabanta, ya ru?o hannayenta a cikin nashi yana rarrashinta ganin har yanzu tana shesshekar kuka.



"Sorry baby girl, share hawayen ki...."



muryarta na rawa ta furta"wlh baku son mu, shiyasa ku ke korar mu, ni dai gida zan koma Allah" a fadace ta faWa tana faman zabga masu harara, ?an kumatunta sunyi jawur da su.



Ba zato ba tsammani Taji Sir mubarak Ya dauketa dungurum Ya daurata kan kirjin shi, wu?i wu?i tayi da idanunta.



"Sai mu ga da wasu kafafun zaki koma gida, ay tun da ki ka shigo wurin nan sai mun ci abinci dake, idan kuma mutun yace zaiyi min rigima zan sanya bindiga ne in har be mashi tsakiyar kan shi"



Ya fada Yana daura yatsan shi akanta, Murmushi kowan nan su ya dan saki.



"Bismillah ku shiga daga ciki mu zauna, ko baku gaji da tsayuwa bane"



Zaki ne yayi maganar Yana nuna masu cikin hall din, su kansu so suke su zauna kafafuwansu har sun fara ru?ewa kawai suna fargaban shiga ne.



Ganin hakan yasa zaki matsawa ya ru?o hannun Sajeed Dana Naufal Ya shiga da su cikin hall din, Da sauri Dr Jazz Ya matsa Cikin su ya ru?o hannun javed dana haris yayi ciki da su.



Bayan mom turai ta gama sharewa azeeza hawayenta, ru?o hannun ta tayi suka nufi table din su.



babu wanda yayi tsammanin Hajiya malikat zata tanka, don tunda aka fara rikicin bata sanya baki ba, sai yanzu data matso kusa da su ta Wan saki fuskarta tana fadin"naga kowa dan uwansa yake dauka nima bari na dauki nawa" ta fada tare da ru?o hannun Unaisah, ta haWa dana batool dake a gefenta"mu shiga ciki ?an mata," wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da sauri suka bi bayan ta, chief owais dake atsaye ya goya hannayensa kan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login