Showing 3001 words to 6000 words out of 391264 words

Chapter 2 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2543

walwala ya furta"da ace nasan da zancen nan da tuntuni na cireta araina, dama ni ba Iyawa zanyi da ita ba, owais din shi yafi dacewa da ita, suje can su ?arata," Ya faWa tare da jingine kanshi jikin Sofa.



Shiru suka yi na Wan wani lokaci, babu wanda Ya furta magana sai daga bisani Justice nadeem Ya furta"Zaki Ina budurwarka ta Canada Kyakkyawar balarabiyar nan"



Da zolaya ya faWa yana duban shi.

Kallo ya jefa mashi mai kama da harara kafin Ya furta"ta koma gidan su"

Zaro ido justice Nadeem yayi"me? Kana nufin tabar gidanka"

?aga mashi gira yai alamar eh,

"But why"?

Bai cika son tada maganarta ba, saboda hakan Yana fama mashi raunin dake a zuciyarshi.

Cikin sanyin murya ya furta"bansan meyasa ba, rana Waya ta haukace min ta soma kokarin juya min ba, badan naso ba nabarta ta dawo Nigeria"

Justice Yace"banji dadi ba, me zai hana ka nemi gidansu inyaso saika gabatar da kanka wurin Iyayenta"?

Murmushin takaicin Zaki yayi"tana da aure har da ?arta, ban ta6a fada maka bane"

Jin wannan maganar Yasa Captain ware manyan idanunshi, hatta Ziyad dake sauraransu saida Ya zaro ido da alamun mamakin kalaman Zaki

A ruWe justice Nadeem ya maimaita maganarshi"tana da aure har da ?a? Amma ta zauna a gidanka tsawon shekaru tamkar ma'aurata? Kafin Ya ?are maganar Captain Yace"tayaya hakan zai yiwu? Nima fa nasan Matar duk lokacin da zanje canada a gidan ka nake taras da ita, nayi tsammanin ?ar aikin ka ce, shiyasa ban ta6a kawo ma raina wani abu ba,"



Girgiza kai Zaki yayi"ba ?ar aikina bace, Taimakon ta nayi, na ru?e ta agidana saboda ta nuna min bata da kowa bayan mun fara sha?uwa take bani labarinta, Hankalina Ya tashi jin cewa tana da aure, amma agidana mijinta ya tura mata da sakon saki, ganin hakan yasa muka cigaba da yin rayuwarmu, naso ta amince min in aure ta saboda bani da burin daya wuce na mallake ta, nasan tana sona sai dai tafi ?aunar takomama mijinta saboda ?arta da tabar mashi"



Gaba Waya sun lura da canzawarshi, hakan Ya ?ara tabbatar masu da irin kaunar da yake yi mata.



Mi?ewa yayi da sauri Ya nufi bedroom dinshi, Da sauri justice Yabi bayanshi, Yana Shiga Ya zura hannayenshi cikin aljihun short dinshi, Yayin da zuciyarshi ke cigaba da tafarfasa



"Bana so hakan Ya dame ka, Yarinyar nan ko tana so ko bata so, Kai ne mijinta, Saboda kafi cutuwa, Tsawon shekara goma sha shidda kuna rayuwa agida Waya tamkar ma'aurata? Ka raineta ka kashe mata ma?udan kudi, Idan har ta butulce maka Allah ma bazai barta ba"



Justice ne yayi maganar, yana daga tsaye abayanshi

"Duk abunda nayi mata nayi ne don Allah..." kafin Ya ?are maganar justice yace"nasan don Allah kayi mata amma wallahi bazan bari ta karya maka zuciya ba, tun da nake da kai baka ta6a nuna kana son wata ?a mace ba, sai akanta, don haka dole ta aure ka, shi kuma mijinta Ya ha?ura ya nemi wata, nasan ma yayi auranshi tun da jimawa"

Juyawo Zaki yayi idanunsa akan justice Yace"nagode da kulawarka agare ni, amma mubar maganar, saboda hakan bamai yiwuwa bane, Ni bazan tursasa mata akan ta so ni ba, ta Wauke ni tamkar yayanta tana girmamani, tun da nake da ita ban ta6a nuna mata inasonta da aure ba itama haka "

"Ita ai ba makauniya bace, in ba kaiba wani namijine zai dauki dawainiyar baligar mace kamarta almost 16years, idan bazan manta ba, lokacin da naje gidanka a canada, ina lura da duk wani motsinku, Idan ka shiga daki da dare zaka kwanta tana binka bata fitowa har saita tabbatar da kayi bacci take fitowa, kaima kuma haka, sannan baka Iya cin abinci idan ba atare da ita ba, itama haka, kana nufin wani abu bai ta6a shiga tsakaninku ba"? ya faWa yana bin sa da kallon tuhuma.



"Nadeem, Ba abunda kake tunani bane, nasan nayi kuskure na ajiye macen da ba muharramata ba a gidana, amma wallahi ban ta6a shigarta ba..... " muryarshi na rawa ya ?are maganar, wani irin yanayi yake jin kanshi tunawa da rayuwarshi da ita.



Numfashi yaja kafin yaci gaba dacewa"Ta saba min da kanta, komai ita take yi min, bansan menene so ba sai akanta, ban fara muradin yin aure ba sai akanta, ashe ita din ba rabona bane...."



"Da ace kuWi zasu Iya siyamin ita, wallahi har dukiyata zan iya salwantarwa saboda ita, bana tunanin zan samu macen da zata Iya maye min gurbinta, Ni ita kadai nakeso Nadeem" kwallar dake taruwa a cikin idanunsa har sun fara kokarin gangarowa saman kuncin sa.



Hankalin Justice Ba ?aramin tashi yayi ba, ko a mafarki bai ta6a tunanin mace zata Iya tan?wara zuciyar Zaki ba.



Dafa kafadunsa yayi da hannayenshi

"Inaso ka faWamin shi mijinta tsawon shekara nawa su ka yi atare"?

In a low voice zaki Ya furta"?asa da 2 years, ta faWa min aranar data haifa mashi baby tabar gidan badan bata son shi ba, kawai taji ya futar mata arantane"

"Kasan mijin nata"?

"Taya za'ai nasan shi? ni ko sunan shi ban ru?e ba, saboda kishinta da nake ji"

Murmushi justice yayi tare da ruko hannun Zaki, suka zaune gefen gadon shi.



"Iyayenta masu hali ne"? ya jefa mashi tambayar.



"Yeah, mahaifinta ya ta6a ruke mukamin Governor a jihar joss, amma bai jima a mulkin ba ya sauka sakamakon ciwon kafar dake damun shi, bayan haka ?anin Mahaifinta Former president ne Na nigeria, Alhaji Musa wadata, Yayan Matar Uncle sharafudeen Hajiya Laurat, nima a wurin ta naji labarin ta" jinjina kai justice yayi"?ar masu Hali ce, Alhaji musan nan Yana Waya daga cikin wadanda suka fi kowa kuWi a africa bayan family dinmu, amma nayi mamakin da har ta gudu tabar nigeria basu nemo ta ba, meyasa tabar mijinta da ?arta? Shine abun tambayar"

"Naikaina Labarinta Yajima Yana Waure min kaina, Sonta ne Ya makantar dani shiyasa ban mayar da ita ga Iyayenta ba, saima na taimaka mata wurin 6oye kanta agidana, naci gaba da bata kulawa"



Justice ya ce Labarinta Akwai ruWani Acikinsa, Ta fito daga babban family, ga ta kyakkyawa da ita amma ahaka har ta gudu daga gidan mijinta? Akan wani dalili? Me ta nema tarasa?"

Ya faWa yana kallon Zaki,

"Nayi kokarin nemanta don inji ya ta koma gidansu? Iyayenta sun kar6eta ko kuwa? Shine fargabana sai dai bani da hanyar da zan Iya kiranta, tabar min wayarta a hannuna, bansan kowa nata ba, in ba hajiya Laurat ba"

Numfasawa Justice yayi kafin yace"kada ka damu Wan uwana, zan iya yin komai akanka, gobe Idan Allah yakaimu a family dinner zanyi magana da hajiyar laurat din dangane da ita Yarinyar," har cikin ranshi yaji dadin maganar justice, ya kwantar mashi da hankalin shi sosai harya fara tunanin yadda haduwarsu zata kasance da ita, sun jima adakin suna tattaunawa daga bisani suka dawo falo wurin su Captain.



______________________
'?





A hankali Motar Dr Jazz Ta ?araso bakin Entry Hall na shiga gidan baba Obie, Bayan yai parking Winta ya fito ya nufi cikin gidan, A katafaren Main Falo din gidan Ya taras da Twins zaune saman sofa tare da wani matashin saurayi kyakkyawan gaske kallo Waya zaka yima fuskarshi ka shaida Wan uwan Justice ne, gaba Wayan su wankan suit ne a jikin su, Cike da jin fargabansu Ya nufe su, Cikin sanyin murya yace"barkanku da hutawa"

Ko kallo bai ishe su ba, Kamar Yayi magana da bango, kuma sun ganshi.

Kusan sau uku Yana maimaita maganar da yayi masu amma babu wanda Ya amsa mashi, hakan Yasa shi yanke shawarar Tafiya yabar wurinsu Har Ya Waga ?afa zai tafi muryar Zayn takatse shi.



"Kai zo nan"! da kakkausar Murya Ya faWa tare da yafuto shi da hannu, Irin kiran da akeyima kananin Yara, Jazz baiji komai aranshi ba Ya nufi Zayn.

Yamutsa fuska zayn yai yayin da yake binshi da kaskantaccen kallo Yace

"Kai makaho ne? Baka gan mu bane zaka wuce batare daka gaishe da mu ba"? Fuska adaure yayi mashi maganar.

Cikin sanyin murya Jazz yace"Nayi maku magana kusan sau uku babu wanda Ya kula ni"

Harara Zayn ya watsa mashi, Dr. nawaz dake a kishingide yana duban su Yace"zayn dama har yanzu wannan kwandon sharar Yana agidan nan? Nayi tsammanin Uncle Mubarak Ya saki babarsa sun koma kasarsu"

Ta6e baki Zayn yayi"gayanan dai kana kallon shi, baida banbanci da masu gida, Har yafi mu jin daWi, Uncle Mubarak ya Waure mashi wurin zama"

Yamutsa fuska Dr.Nawaz Yai"Kaci sa'a ba'a ?asar nake zaune ba, da tuni nasa anyi watsi dakai, donni bana son bare ya ra6i Ahlinmu," Jazz dake atsaye yana sauraron Rashin mutuncin da suke yi mashi, tuni idanunsa sun cicciko tab da kwalla.

"Ya isa haka!" Zaid ne Ya faWa tare da kallon Jazz, Da hannu Yayi mashi alamar Ya tafi, bawan Allah Jiki asanyaye ya nufi Hanyar kitchen din gidan, tunkafin Ya karasa Able ta fito daga ciki hannunta ru?e da tray na kayan marmari, ganin jazz yasa ta dakata da tafiya fuskarta da fara'a tace"Jazz Ya jikin naka"?

Fuskar shi babu walwala Yace"da sauki"

"Allah Ya kara lafiya" ya amsa mata da ameen, ganin Yana ?an kalle kalle Ne yasa ta fahinci akwai wani abu da yake nema don haka tace"ko akwai wani abu da kake bukata ne"?

?aga mata kai Yai haWi da cewa"Eh, Ina neman Faryat ne,"

"Muje na raka ka, Nima wurin su zanje kai masu Kayan marmari," amsa mata yayi da toh, ta yi gaba yabi bayanta, aranta ta ayyana ko me zai kai shi wurin faryat? Tantiriyar Yarinyar nan da babu Allah aranta"

Upstairs suka hau, bayan sun sauka third floor, suka nufi Balcony dake acan sama,Tsayawa fasalta kyawun wurin 6ata baki ne sai wanda Ya gani, tunkafin su karasa Jazz Ya hango Su zazzaune saman wasu hadaddun Kujeru Bugun Dubai, Matasan ?an mata ne masu ji da kansu, A kalla sun kai su uku Kowaccensu Ta dauki wanka na kece raini, Kamshin turarensu tuni Ya soma Cika mashi hancinshi.



Kaitsaye idanunsa suka sauka akan Faryat, wadda ke asanye da mini skirt ya matse jikinta, da?yar skirt din Ya wuce Ass dinta, Rigar jikinta kuwa Ko cibinta bata rufe ba, ta bayyana shape din kirjinta hatta nipples dinta kana iya ganin tsininsu, babu mayafi akanta Kitson kalabar da akayi mata ne mai kyan gaske ansanya mata sparkling stones masu jan hankali saman gashin kanta, yatsun hannunta yana asanye da gold knuckle rings, Haka zalika Hancinta na amanne da nose ring, wata ziririyar sarka ce a kafarta, Yarinyar karshe ce wurin Iya barikanci, Hatsabibiyar gaske bata jin magana ko miskala zarratin, sai dai fa akwai kyan sura, komai nata irin na hajiya saratu ne banbancinsu girman jiki da shekaru.



Matashiyar dake a gefenta, Yusra ce ?anwar Yaseer, Kallo Waya zakai mata saika sake kallonta, Tsabar haWuwarta, itama fara ce sol, kamanninta sak dana mahaifiyarta Her excellency Muhibbat, gata doguwa tubarkalla, bayan ita sai Zulaihat kanwar Ziyad Wankan tarwaWa ce alaunin fata tana da saukin kai ko a fuska ka kalle ta, babu wanda Ya lura da Jazz A cikinsu Hankalinsu na akan firar da suke Yi.



able ce tayi masu sallama, Tare da ajiye masu tray din kayan marmarin saman round table din dake a tsakiyar kujerun su, juyawa tayi da sauri ta fuce tabar wurin.

Wani irin shakkar Yi masu magana Yake ji, Sai faman bin Faryat Yake Yi da kallon ?urulla.



"Na jaraba kiran layin Sister Hindu bata yi picking ba, may be ko bata a kusa ne da wayar, ita dai Yazrin nayi mata uziri, saboda tafiyar da suka sha nasan haryanzu gajiyar tafiya bata sakesu ba" Zalaihat ce tayi maganar tare dakai hannu ta dauki tufa tana ci

"Ina ga mezai hana mu shiga gidan yi masu bangajiyar tafiya, Su mommy ma suna acan"

"Ni dai ba inda zanje, sai zuwa gobe idan mun haWu wurin Dinner din daddy Hateem" Acewar Faryat Tana faWa tana farfari da idanunta.

"Gobe akwai shagali, zamu yi sharholiyarmu son ran mu, Har nakagara goben nan tayi," Yusra ce ta fada tana karkaWa kafarta.

Har Faryat Ta buWe baki daniyar tayi magana, Sautin ringing din wayar Jazz Ya dakatar da ita, Kusan atare suka wurga idanunsu kan fuskarshi, nan take yaji gabanshi ya faWi rass saboda kwarjinin da suka yi mashi.



Yamutsa fuska Yusra tayi tare da kau da idonta

Zulaihat kuwa Murmushi tasakar mashi

"Dan uwa, Tun yaushe kazo wurin nan ne?

Yana faman Kame kansa Yace"tare da abla muka zo"

"Amma meyasa bakayi mana magana ba jazz," cikin kulawa ta fada tana dubanshi Ta fuskanci Hankalin shi ba kwance yake ba

"Wa kake nema ne"?

Kallon Faryat da yayi ne yasa ta gane ita yake son gani"

Murmushi zulaihat tayi,

Faryat dake kallon shi, wani irin shu'umin murmushine akan fuskarta, yun?urawa tayi ta mi?ewa ta dubi su Yusra"ni zan shiga ciki, bazan jima ba yanzu zan dawo" Yusra dake harararsa tace"faryat kin bani kunya, Ki rasa wa zaki kula sai wannan halittar" ta fada tana nuna shi da yatsa

Zulaihat tace"Please Yusra, babu ruwanki da shiga sabgarsu" Ta6ebaki Yusra tayi

Ba tare daya ankare ba, Faryat ta ru?o hannunsa tare da jan shi suka soma tafiya atare, wani sanyine yaji ya ratsa zuciyarsa, duk da yasan ba lallai Faryat ta sassauta mashi ba, Ya riga daya san halin ta.

Kaitsaye suka nufi bedroom dinta dake a gidan, adai dai bakin kofar shiga Dr.Jazz Ya dakata da tafiya, da sauri ta kalle shi hadi da kashe mashi ido Waya tace "my babe meyasa ka dakata da yin tafiya? Let's go inside," ta fada tana matse hannunsa dake acikin nata, har cikin zuciyarshi yake jin matsar da take yi mashi. Muryarshi ?asa ?asa Ya ce"basai na shiga ciki ba, mu koma falo mu yi magana"

?aure mashi fuska tay "Jazz, you will lose your chance to talk to me if you don't go in," she warned. "If you don't go in, don't expect to see me again"!

*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*

*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga D
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 8
by
Novels Elite Admin
May 23, 2024
Sponsored Link

_ *~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?
'~*_







3,F 'DB/1=؋?
'=?%?





~Takun ?arshe=?%?~







B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??





An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?







Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'







__________________________
'?











Tana ?arasa fadar hakan ta sanya hannu ta ture ?ofar ta shiga ciki, A ?alla Yafi karfin mintuna biyar a bakin kofar yana yanke shawara da zuciyarsa, ha?i?a Yana matu?ar jin tsoron Allah, bayason zama daki Waya da macen da ba muharramarsa ba, hakanan ba tare da wata lalura ba, balle kuma faryat da ta kasance tantiriya, sai dai baya jin zai iya rasa wannan damar, Allah ya jarabce shi da tsananin ?aunarta, Itace mace ta farko da ya fara jin tsantsar sonta tun lokacin daya mallaki hankalinsa, ya mutu akan kaunar faryat yana son yarinyar duk da kasancewarta mara jin magana.



Numfas??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????awa yayi kafin ahankali ya tura kofar dakin nata ya shiga daga ciki, katafaren dakin kwana ne, kamar na ?ar sarki, tsabar haduwar furniture din dakin, Komai na cikinsa Launin black pink ne.



Bayan shigarsa dakin, Sanyayyan sanyin A.c ne mai haWe da daddaWan kamshin turaren faryat ya ratsa hancinsa da fatar jikinsa, Lumshe idanunsa yayi slowly ya buWe su akan faryat dake a tsaye gaban dressing mirror, ta juya baya kitson kalabar kanta ya sauko har mid back dinta, ta cikin madubin ta ke jifar shi da shu'umin kallo.



Ganin ya?i ?arasowa gare ta, yasa ta juyo ta nufe shi, dab dashi ta Waya suka soma jefa wa junansu kallo.



Ba zai iya jurar sha?ar ?amshin turarenta ba da kallon surar jikinta hakan ba ?aramin jefa shi yanayi ya ke yi ba, Muryarshi na rawa ya furta"Am.. umm.. tun da naganki zan tafi"



ba zato ba tsammani yaji ta Waura hannayenta saman kirjinshi, muryarta da shagwa6a ta furta"Ni ban gaji da kallon ka ba, My honey, tsawon lokaci bansanya ka a idanuwana ba, nayi kewar komai naka jazz.. " kafin ta ?are maganar, jazz ya tari numfashinta da cewa"Faryat tayaya zan yarda da kalamanki? Bayan ke da kanki kika faWi cewa bazaki ta6a sona ba, kuma ba zaki iya aure na ba"



Juya mashi baya tayi haWi da goya hannayenta saman kirjinta kafin ta soma magana.



"Jazz, I won't hide it from you. Nothing has changed. I love you, but I can't marry someone who has no origin", (Jazz bazan 6oye maka ba, Har yanzu babu abun da ya canza, Inasonka amma bazan Iya auran wanda bashi da asali ba,)" ta faWa tana girgiza kanta, kafin ta Waura da cewa.



"kaima ka sani jazz mommyna da daddyna ba zasu ta6a yarda mukasance atare ba, jazz I come from a wealthy family. How can I love someone like you who has no origin? What is your family status?" ta jefa mashi tambaya ba tare da ta jira amsar shi ba taci gaba da magana



"Ta ya ya zan auri Wan tsohuwar mai aikin gidan mu" tun da ta fara magana sai yanzu ta juyo ta fuskance shi, Jikin shi yayi sanyi lakwas, hawaye tuni sun soma taruwa a cikin fararen idanuwansa, kalamanta sun kashe mashi kwarin gwiwarshi, sai yajima gaba Waya ya tsani kan shi, ta fahimci halin da ya shiga sai dai ko kaWan bata ji tausayin shi ba.



"Jazz Hamsha?an masu kuWi suna rububi akaina, waWanda duniya tasan da zamansu, How can I choose a meaningless future for myself when I could have so much more?" a tsiwace ta faWa tana zare mashi kyawawan idanuwanta masu dauke da zira ziran eye lashes.



Hawayen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login