Showing 177001 words to 180000 words out of 391264 words

Chapter 60 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2633

marker yayi zanan, kafafuwanta kamar na cokula, ga gashin kanta a haukace ko wacece wannan?



Murmushin gefen fuska chief ya saki kafin ya wurga eye balls dinsa kan bed dinsa a kwance ya hango shi, sai sharar bacci yakeyi kamar matacce, yar singlet ce a jikin shi fara kyal, tare da short ja, yayi wani fresh dashi.



Gaba Waya ya barbaza papers din da yayi amfani da su, ga notebooks dinsa daya watsar, hannun shi yana aruke da pensil da alama yana cikin yin practicing na rubutu bacci yayi awon gaba da shi.



Cikin takun sanWa chief ya ?asa daga gaban gadon ya zauna tare da sunkuyar da kanshi saitin fuskar danish ya ?ura mashi ido yana kallon shi, wani irin bugu zuciyarshi ta fara doka mashi, kamannin shi sun 6aci da yaron hatta dogon hancin su, da launun hair dinsu, da shape din bakinsu iri Waya sak, uwa uba reddish eyes dinsu masu kyan gaske da jan hankali, yadda yake yin baccin cikin kwanciyar hankali ba karamin kayatar da chief yayi ba, har baisan sa'dda ya manna masa peck a forehead dinsa, ya daura zira ziran yatsunsa saman tattausar farar fatar fuskar Danish mai kama data jinjiri saboda hasken ta da laushinta ya shafa ta a hankali..



In a low voice ya furta"I hope you will be my cousin, I will be proud of you. I will give you all my care. If it is confirmed that you are my blood cousin, I myself cannot describe the joy I will feel. I will hug you tightly, I will shed my tears on you, kuma nayi maka alkawarin zan ?watar maka duk wani hakkinka na rayuwa da aka tauye maka! WaWanda sukayi silar sadaukar dakai zansa suyi danasani mara amfani....." cak ya tsaya da magana ganin ya fara motsi, da sauri chief ya dago da kanshi batare daya dauke ido daga kallon shi ba, gyara kwanciyar shi yayi.



Ajiyar zuciya ya dan sauke ganin bai farka ba, hakanan yai sha'awar karanta rubutun da yayi a jikin papers din daya watsar kan mattress, paper din farko jagwalgwalone yayi bai iya gane komai ba, paper na biyune yaga ya rubuta I miss you, my Angel. Come back home..."



yayi mamakin handwritting dinshi cos yayi kokari ba kadan ba, har kokwanto yayi anya shi ya rubuta? Wayar paper din ya dauko ya duba rubutun dake akai.



"I'm waiting for you, chief. Come back home..." murmushi chief yayi har dimple dinsa ya lotsa...

Next paper daya duba sunan Daddy hateem ne ya rubuta duk da akwai kuskure amma yayi kokari..." bayan ya kammala reading dinsu, ya ajiye mashi abun shi gefe daya, har zai mike yaji ya dam?i hannun shi, ya Wan furgita saboda bai tsammaci zai farka ba..a hankali ya buWe idanunsa sunyi ja dakyar yake ware su akan fuskar chief, da wata irin kasala ya furta"You're back." jinjina mashi kai yai alamar eh..



Mi?ewa zaune yayi tare da yin mi?a chief ya bi shi da kallo, ya jinjinama girman jikin shi, ba karamin kato bane ko'ina na jikin shi a murWe yake irin na majiya karfi masu jini ajika.



"Fadamin kayi missing dina"? Daga mashi gira yai"nayi missing dinka sosai, tun dazu nake jiranka don muyi karatu baka dawo ba..." cheif yace"ai naga ka fara" ya fada yana nuna zanen dake akan white board din.



sunkuyar dakai danish yayi hadi da yin murmushi.



Da zolaya yace"abunda na koya maka kenen"! Girgiza kai yay "a'a!

"Wacece ka zana? Na kasa gane fuskar, Jemaima ce ko Azeeza"? Dagangan ya kira sunan su don ya bugi cikin shi...

Kasa ?asa da murya ya furta"Angel" dariya ce ta kubce ma chief, danish ya kura mashi ido yana kallon shi.



"Haba my bro, Unaisah ce wannan Aljanar? Abu kamar agidan mahaukata, Ai ni dana ganta ?arama nayi zaton jamaimah ne ." sunnar dakai kasa yayi batare dayace uffan ba...

nan take chief ya fahimci halin damuwar da yake aciki harya Wan rame ta wurin kwarin idanun shi sunyi ja.



"Fadamin meke damunka.."?

Shiru yayi jim kamar mai tunanin wani abu

"Ina so Unaisah ta dawo gida, I miss her, I want to see her. She forgets me, Bata nema na..." kasa ?arasa maganar yayi da sauri ya cusa kanshi cikin pillow.



wani irin tausayin shine ya kama owais cikin sanyin murya ya furta"am sorry danish, unaisah zata dawo gobe in sha Allah, kuma ka daina tunanin ta manta dakai, kana aranta...." muryarshi da rauni ya furta"har yanzu fushi take dani, bata sona"



har yau chief baisan soyayya ce atsakaninsu ba, yafi tunanin shakuwace mai karfi shiyasa ko kusa abun bai damun shi.



"Ina wayarka"?



"Tana akan mirror," ya faWa batare daya dago da kan shi ba

Mi?ewa chief yai ya nufi mirror din ya dauko wayar, ya danna power ta kawo haske

Wayarsa ya curo yayi copying contact din Unaisah ya saka awayar Danish...



Kiran sunan shi yayi, dakyar ya amsa mashi na'am

Na sanya maka contact din angel a phone inka, zaka iya kiranta ku gaisa, ko ka tura mata text message kamar yadda na koya maka..." dago da kanshi yayi wani irin dadine ya lullu6e shi, mika mashi wayar chief yayi yatsun hannun shi na kerma tsabar zumudi ya karba saida ya shiga wurin rubuta sakon ya kasa tabuka komai.



Mi?a ma chief wayar yayi"ka rubuta min..." girgiza kai chief yayi"kai ya kamata ka rubuta...yamutsa fuska yayi kafin ya fara kokarin rubuta mata sakon saida ya kammala chief ya duba abunda ya rubuta dakyar ya gane meya ke nufi a sakon ya hade kalmomin babu space babu ?a'idojin rubutu irin dai na yan koyo,

"Kayi kokari" ya faWa tare da mika mashi phone"ka danna send" ya amsa mashi da toh...

"Zan shiga gym ko zaka bini? Daga mashi kai yai akamar eh, da sauri ya mike chief ya ruko hannun shi kamar wa da kani suka fita a tare.=؞?



_________________________________
'?



Meya faru bayan komar dr shureim gida?



Tsaye yake gaban sofa ya goya hannayen shi kan kirjinshi, fuskar shi babu annuri idanunshi sun kaWa jawur tsabar 6acin rai da fusata, abun da ya faru bayan fitar shureim da zeenatu kwatsam Motar su Alhaji musa ta kunno kai cikin gidan tunkafin bodyguard din dake driving dinsu yayi parking saiga kira daga likitan shi dr Mark, bayan yayi picking ko sallama baiyi ba muryar mark ta katse shi"yalla6ai! Da sanin ka dr shureim Ya fita da zeenatu...." lokaci Waya yanayin fuskar shi ya canza zuwa tsantsar bacin rai



Saida ya mula yasha iska kafin ya furta"bada sani na ba"!



Dr mark yace"yalla6ai, dole fa sai kayi takatsantsan idan ba haka ba zamu iya samun gagarumar matsala, saboda mutane sun Wauki hotunan dr shureim tare da zeenatu rungume da juna, a bainar jama'a sai yaWa shi sukeyi a social media..." a kiWime Alhaji musa ya furta"what! Are you sure"?



"?warai kuwa yalla6ai, ka duba whatsapp dinka, zan tura maka hotunan ka gani da idon ka..." katse kiran yayi, wani irin gumine Ya wanke fuskarshi saboda bacin rai! Har shi zai sanya doka agidan shi a karya"?



Alhaji ubaid dake zaune gefen shi Ya lura da yanayin shi

"Musa lafiya? Meya faru ne"? Ko kallo Alhaji ubaid bai ishe shi ba, Ya buWe murfin motar Ya fito tamkar mayunwacin zaki Ya nufi gate security officers, suna ganinshi suka mi?e suna jiran tsammani

Wata irin tsawa ya daka masu da ta gigita dodon kunnuwansu, yana huci ya furta"da iznin ubanwa kuka bari dr shureim Ya fita da zeenatu huh!? Kafin in fita basaida na gargadeku akan kada ku kuskura ku bari ko kofar falo ta le?o ko ba....." ya Wage sai masifa yake zazzaga masu ta inda yake shiga batanan yake fita ba.



Alhaji ubaid Har ya fara kokarin lallashin shi aikuwa Ya daka mashi tsawa kamar Wan cikin shi Ya nuna shi da yatsa yace"karka kuskura kasa baki, magana nake akan ?ata, ka wuce ka shiga ciki" jikin Alhaji ubaid na 6ari kamar mazari Ya juya ya nufi cikin gidan abisa umarnin Alhaji musa wato ?anin shi >?#?





Hankulan gate officers din ba karamin tashi yayi ba, tsantsar tashin hankali da firgici ne akan fuskokinsu.



Dakyar wani daga cikin su ya samu kwarin gwiwar fadin"yalla6ai har tambayar shi mukayi da iznin wa zai fita da ita yace mana da izninka, munyi kokarin tuntu6ar layinka amma baka Waga ba...." bai ?are maganar ba sakamakon zazzafan marin da Alhaji musa ya wanka mashi wlh daga tsaye duk girman jikin mutumin saida Ya dur?ushe kan gwiwowinsa.



Kallon sauran gate officers din yayi waWanda tuni sun sha jinin jikin su, babban tashin hankalinsu taya zasu fahimtar da shi cewa su ba laifin su bane? Alhaji musa bala'e ne, wani irin bauWaWWan mutunne, bahago mai wuyar sha'ani.



Wani mai rabon shan duka daga cikin su ne Yayi shahada wurin furta"yalla6ai, har kiran hajiya sarah mukayi awaya muka tambayeta da izininta zasu fita tace mana eh, ta kuma ce kaima da sanin ka...." bai kare maganar ba, Alhaji musa ya daddage Ya kwashe shi da mari da tafukan hannayenshi biyu nan take bakin officer din ya fashe jini ya fara bulbulowa.

kallon sauran yayi yana jiran jin bayani daga gare su, sai tsuma suke yi suna ja da baya da alama sun razana....

"Ban ta6a sanin ku dakikai bane sai yau! Wallahi ku kuka da kanku! ....." zubewa sukayi akan gwiwowinsu suka dinga rokonshi sunayi mashi magiya don ya yafe masu, ko ta kansu bai bi ba, Ya nufi cikin gidan cikin takun nan nashi na izza,



bawan Allah Alhaji ubaid Ashe yana la6e ta window yana leken abunda Alhaji musa yakeyi ma masu gadin gidan, Yaji haushi ranshi Ya 6aci sai.......=ؔ?



Adaidai lokacin da motar dr shureim Ta kunno kai sai ga motar hajiya sarah yau ta dawo da wuri, atare suka nufi parking space bayan sunyi parking, kusan atare shureim da zeenatu suka fito, kafin hajiya sarah ta fito da sauri zeenatu taje ta rungume ta



"Sannu da dawowa mommy, ya aiki"?

Shafa kanta hajiya sarah tayi"lafiyalou my baby,..." ta fada tare da kallon shureim murmushi suka sakar ma junansu,

"Sannu da dawo Aunty, ya aiki?

"Lafiyalou shureim ya mai jikin"?

"Mai jiki Alhamdulillah, taji sau?i sosai, gobe muke sa ran za'a sallame ta...

da fara'a tace"Alhamdulillah, amma naji dadi, gobe in sha Allah tare dani zaku tafi..." atare suka jera suka nufi falon gidan, basu san bomb yana nan zaune yana jiran su ba.



Lokacin da suka shiga falon kusan atare suka ci burki suna kallon shi, akace labarin zuciya atambayi fuska, tundaga kan yanayin shi suka sha jinin jikinsu, Yana zaune kan sofa ya haWe fuska kai kace bai ta6a dariya ba, ya murtuke fuska ga wani gumi da ya jike gaban rigar shaddar jikin shi, tsabar fusata zufa ta ko'ina take tsastsafo shi."



Kallon kallon suka fara jefa wa junansu, tsakanin dr shureim da hajiya sarah, kamar an dasa masu aya sun gaza ?arasa shiga ciki....



"Daddy, yaushe ka dawo..."? Zeenatu ce ta ambaci sunan shi, da sauri ta nufe shi har takusa isa, Hajiya sarah tayi saurin cafko hannunta, shigowa ciki dr shureim yayi kamar jira yake su shigo ciki Ya mi?e agadarance ya nufi shureim Yana huci Ya furta"shureim da iznin ubanwa ka fita da zeenatu"?

Har saida gaban shureim ya fadi saboda kalmar ubanwa da alhaji Musa ya furta.





dakyar ya iya buWe baki Yace"bada iznin kowa ba, ni na fita da ita saboda ta fada min tagaji da zama ita kadai agidan...." bai kare maganar ba Alhaji Musa ya dam?i gaban rigar shi ya jijjiga shi idanun shi jawur Ya kalli cikin idanun shureim.



Hankalin su hajiya Sarah ba karamin tashi yayi ba, Allah kadai yasan mai yayi niyar yi mashi amma sai ya fasa ya saki kwalar rigar ya cije la66ansa a zafafe ya ce"shureim ni kayiwa karya? Ka ce da iznina ka fita da ita? Dama malamai suna karya? Kai ko kunya baka ji ba? Ina tsoron Allahn da addinin naka huh? Runtse ido dr shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin furucin Alhaji Musa ba, kuma bai ta6a tsammanin zai iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi hakan ba.





"Ka bani mamaki shureim? A bainar jama'a ka rungume zeenatu a kirjinka, ?ato dakai baligi salon kaja min zagi a idon jama'a, so kake ka zubda min mutuncina da kimata..."? Fasa ?ara zeenatu tayi ta fashe da kuka tana fadin"Daddy ka daina yi mashi faWa! banaso, Ka kyale shi! ba laifin Shi bane nice na rungume shi.."



bata ?are maganar ba, Ya dankara mata ashariya kamar bamaguje



watsawa tayi da gudu ta nufi upstairs tana kuka tamkar ranta zai fita, tsautsayine Yaja Hajiya sarah ta buWe baki furta"Yakamata kasan irin kalaman da zaka gaya mashi, wannan ba dacewa bane, shureim baiyi abun kunya ba kaine kayi abun kunya! Akan wani dalili zaka rufe shi da fada saboda kawai ya dauki yar uwarshi ya fita da ita! Shi ne laifi?...." kafin ta kare maganar Alhaji musa ya yai kukan kura ya Waga hannu zai Webe ta da mari da sauri Dr shureim ya shiga tsakaninsu, kai tsaye marin sauka akan fuskar shi, ji kake tasss! Waro ido waje hajiya Saratu tayi, zuciyarta ta hasala, Idanunta sun kaWa jawur batasan sa'adda hawaye suka wanke fuskarta.



Dr shureim dake atsaye hannunsa dafe da kuncinsa, tsabar radadin marin da yaji har wasu taurari masu wutsiya ya gani suna gilmawa a cikin idanun shi, zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshin shi, cikin karyayyar murya ya dubi Alhaji musa Ya furta"ni kadai yakamata ka hukunta saboda ni nayi maka laifi, saboda na Wauki zeeenatu na fita da ita, kuma ni ne nayi karyar cewa da saninka, saboda ni a tunanina zeenatu yar uwatace ina da right din da zanyi iko da ita.." ya fada yana kallon cikin idon Uncle din nasa.



"Duk akan Zeenatu kake tada jijiyoyin wuya? Meyasa? Kawai saboda na fita da ita munje asibiti duba yar uwarta! Wai duk kullan nan na menene? Ya jefa mashi tambayar, gaba Waya ya daure Alhaji musa da mamakin shi



"Uncle yakamata ka sani, mu fa ba makafi bane, duk wani motsinka akan yadda kake tafiyar da rayuwar Zeenatu muna lura, Wallahi abinda ka aikata yau ya sa na fara kokwanto! sannan inaso ka sani don munayi maka biyayya ba hakan yana nufin muna jin tsoronka ba, ni bana tsoron kowa sai mahallici na......"



waro idanu waje Alhaji Musa yayi jin furucin shureim, yayi mamakin yadda ya iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi magana batare da jin shakkar shi ba, Hajiya Sarah taji dadin martanin da Shureim ya mayar masa.



gaba Waya kalaman dr Shureim a kunnan Alhaji Ubaid dake a la6e yana sauraron su, yaga komai daya faru akan idonshi, har hawaye saida ya zubar saboda yaji zafin kalaman da alhaji musa ya jefi shureim da su, sannan baiji dadin marin da yayi mashi ba, yaji takaici kamar ya binne kan shi. Yasan bazai iya yin komai ba shiyasa ya hana kan shi zuwa wurin su.



"Idan ka cigaba da yanke hukunci cikin fushi, wallahi zakayi danasani"! Kamar sakarai haka Alhaji musa Yabi shureim da ido wato ta ko'ina ya daure shi da mamaki, Ya kasa furta kalma, ga wani gumi dake tsastsafo mashi...



"Shureim ka yi hakuri dan Allah!.." hajiya sarah ta faWa idanunta cike tab da kwalla,"kada ki damu Aunty", A fusace Ya haura kafa ya nufi room din shi, girgiza kai hajiya sarah tayi rai a6ace ta nufi dakin ta.



Lokaci Waya Alhaji musa yaji jiri na niyar Wibar shi, da sauri ya zauna kan sofa, ya dafe kanshi dake sarah mashi da hannu biyu"



_________________________________=؋?
'?



Lokacin da motocin su Baba Obie suka ?araso asibitin, a gaggauce nurses suka fito da Stretcher, Hajjaty da Abla suka Wauko marwa da taimakon nurses suka kwantar da ita kan Stretcher, kaitsaye suka nufi cikin asibitin da ita, da sauri su Hajjaty suka mara masu baya tare da su Baba Obie, mutane sai miko gaisuwa suke yi cike da girmamawa musamman da ya shiga ciki Nurses da Docs kamar zasu dur?usa ?asa tsabar yadda suke gaishe da shi cikin girmamawa, tuni labarin zuwan shi asibitin ya isa kunnan Md Dr. Jidenna dama mutumin shine, yare Waya ?abila Waya sai gashi ya fito da sassarfa ya nufi Baba Obie tare da wasu daga cikin docs na asibitin, barka da zuwa suka yi mashi da?yar yake amsa masu duk sun fahimci baya acikin kwanciyar hankalin....., a Waiting Area su Hajjaty suka zauna kamar masu zaman makoki, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya suke yi na sakamakon ciwon marwa, babu wani mai kwanciyar hankali acikinsu, fuskokinsu sunyi jawur ruwan hawaye ya ji?e su.Pravin kuwa Yana ru?e da qugu ya haWa uban gumi duk da sanyin A.c Win dake a wurin, ya kasa zaune ya kasa tsaye kamar mai fama da Wan kanoma...



Su kan su likitocin da sukayi arba da Marwa saida suka ruWe saboda basu ta6a ganin patient mai irin lalurar ta ba, ba wai kuturtar ba toshewar bakin nata kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba!! Wasu ?wararrun Medical team ne suka fara bincikarta, kafin su fara aikinsu sai da suka fara tambayar me ya jawo mata ciwon!! nan fa su Hajjaty da su Abla suka kora masu bayani dalla dalla dangane da yadda marwa ta tashi dare Waya da lalurar suka ce su kansu basu san menene makasudin ciwon nata ba...bayaninsu ya ?ara rikita Docs din, wannan wani irin ciwo ne farat Waya?



A ?alla Medical team din sun Wauki tsawon awanni wurin duba lafiyar marwa, abun ya fara basu tsoro, saboda sunyi gwaje gwaje da aune aune but every result came back inconclusive. No trace of infection, no signs of trauma, lamarin Ya rikirkita su, sunyi iyakar bakin kokarinsu amma still babu wani sakamako daya nuna cewa Marwa tana da wani ciwo ko wata lalura, saima wani abun Waure kai lafiyarta qalou....'! Babu irin kokarin da likitocin basu yi ba akanta sun baje fasaharsu da kwarewarsu amma ba wani cigaba sakamakon dai Waya ne....W'



tun safe har wuraren karfe biyar na yamma babu wani abu da likitoci suka gano,



Lokacin da likitocin suka fito, sun hada uban gumi akan fuskokinsu kai kace ba A.c a dakin, su kan su sun jigata basu ta6a cin karo da patient din da ya basu Wan banzan wahala irin marwa ba, duk irin kwarewarsu da kwazon su basu iya gano komai ba....



Su Hajjaty suna a zaune bayin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login