Showing 84001 words to 87000 words out of 391264 words

Chapter 29 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

3564

fito rudu rudu kamar zasu fasa fatarta, tayi kuka tamkar ranta zai bar gangar jikin ta, komai na duniyar nan ya sire mata, taji takaici da tsanar rayuwar da ta daukarwa kanta saboda takasa hakuri ta rungumi ?addarar ta, Sai gashi yau taji abunda Ya jefata adanasani, Yan kananun Yara da basu ji ba basu gani ba, wadannan ma tun suna jarirai suke fuskantar jarabawar rayuwa, Ita kuwa da ilminta da hankalin ta da tunaninta ta faWa harkar karuwanci saboda ta kasa cinye jarabawarta lamarin yayi matukar gigita tunaninta...



Faucet ta kunna ruwa ya soma shararowa ta tarfa hannu tana watsa shi akan fuskarta, kamar an zare mata karsashin jikinta, da wata irin kasala ta fito jiki babu ?wari ta faWa kan gadonta tare da kifa kanta jikin pillow, bakomai take tariyowa ba face rayuwarta ta baya...

Sam ba taji motsin shigowar mutun ba, saboda ta lulu duniyar tunani

A hankali batool take tafiya tana tunkarar gadonta, hayewa tayi kan gadon ta zauna kusa da ummi tana le?en fuskarta



"Aunty Ummi," kamar daga sama taji muryar batool, a hankali ta buWe idanunta da suka kumbura ta daura su kan fuska batool.



"Dan Allah ki daina kuka aunty ummi, bana son ganin hawayen ki, bana jin dadi" ta fada muryarta na rawa alamar zata fashe da kuka.



Janyota ummi tayi tare da kwantar da ita kan kirjinta, sosai ta rungumeta ta daura hannunta akan bayanta batare data furta magana ba.



Aranta tana mai mamakin tawakkalli irin Na Yaran, abunne da daure kai, da ace wani mai karancin imanin ne hakan ta faru da shi da tuni yajima da hadiyar zuciya ya mutu amma su a haka suka jure da dadi da ba dadi sukai ta rayuwar ?unci a kulle tun kafin su mallaki hankalin su.



Numfashi taja, wani irin kaunar yarance taji ta ?ara kama zuciyarta, har ta fara tunanin tawace hanya zata taimaka masu don ganin sun inganta rayuwarsu tun da basu san komai ba .

Bakomai ne ya fado mata aranta ba face zagin da ta ta6a yima batool har ta kirata da sunan jahila wadda bata san komai ba sai ci da bacci... Runtse idanunta tayi sosai tana mai jin takaicin kalaman da ta furta mata, gashi yanzu yarinyar tafi kowa kaunarta

Shafa sumar kan batool taci gaba dayi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba dasu arungume da juna kamar zasu dawwama ahaka.......=ؔ?



___________________________________
'?



*d'Unaisah Angel=؋?=؝?*



Fitowa tayi daga part dinsa bayan ta gama gyara masa shi, A hankali take saukowa down daga kan stairs zuciyarta cike fal da tunanin abubuwa da dama wadanda suka faranta mata rai a yau kamar wata zautacciya sai faman sakin murmushi take yi.



"Daughter i'm back" miryar taj ce ta katse mata zancen zucin nata, kallon shi tayi fuskarta da fara'a, da sauri ta karasa sauko down, mayafin kanta har yana kwancewa daga kanta ya zame ya faWo kan kafadarta, sumar kanta ta rufa mata bayanta.



Tana ?arasawa ta fada kan kirjinshi kamar wadanda suka dade basu ga juna ba.



Murmushi yasaki yana fadin"sannu da kokari ina fata kin yi abun da Ya dace"



Wagowa tayi da kanta ta daura idanunta akan nashi"har gyara masa part din sa nayi, kafin ma na kammala har ya fita ban same shi ba"



"May be ya tafi gidan kakansa ne" acewar chief,



"Kinsan me naje yi agida" girgiza mashi kai tayi alamar a'a.



"Auntynki na faWa mawa ta hada maki wani abu mai dadin gaske zuwa anjima zatay ba?uwa, amma fa ban gaya mata wacece zata zo ba"



"Naji dadi daddy, kana ji dani"



Mayafin ta dake akan kafadarta ya ruko yana fadin"bari na gyara maki shi" A hankali Ya soma naWa mata shi, bayan ya kammala ya manna mata sumbata kan kuncin ta kafin ya Wago da kansa



kwatsam! Ba zato ba tsammani Yaji saukar dundu akan bayanshi tamkar za'a rusa shi, tsabar zafin da yaji ne yasa shi saurin dafe bayan da hannu, tuni ya fara ganin jiri a cikin idanunsa.



Hankalin ta amatu?ar tashi ta wurga idanunta don ganin wane yayi wannan aika aikar saboda itama taji sautin dundun da akayi mashi.



Har saida gabanta Ya faWi lokacin da tayi arba da shi atsaye yana huci tamkar mayunwacin zaki, tsabar fusata jikin shi har gumi yake fitarwa, magana yakeso yayi amma saboda zafin da zuciyarshi keyi mashi ya kasa sai la66ansa dake kerma.



Harara ta watsa mashi saboda ya bata haushi, zuciyarta ajagule ta ru?o hannun taj Tana fadin"Inna lillahi! daddy dan Allah kayi hakuri..."_ bata ?are maganar ba, danish Ya fusgo ta tare da janyota jikin shi, yasa hannu biyu ya rungumeta kamar zai maida ta cikinsa



Lamarin yayi matu?ar Waurewa taj kai, idanunsa jawur yake kallon danish Yama rasa me zaiyi, amma tabbas dundun da yayi masa ya kusa yi mashi illa saboda zogin da bayansa keyi mashi kamar an WoWana masa wuta yadda kasan ba hannun mutun bane yayi dundun, yaji zafinsa sosai.



Kiciniyar kwace kanta tafara yi hawaye tuni sun wanke fuskarta ganin baida alamun sakinta ne yasa ta daddage ta gartsa mashi cizo kan kirjinsa, ko gizau baiyi ba, saima ya kara hadeta da jikin shi, zuciyarta har tafarfasa take yi mata saboda 6acin rai.



Kallon kallon suke jefawa junansu tsakanin shi da tajuddeen, kwata kwata bai yi yun?urin Janye angel daga jikin danish ba, saboda ya fahinci Yaron ba shi kadai bane tun daga kan dundun da yayi mashi ya shaida hakan.



Shigowo Falon big guy da Wan saurinsa Yana ganinsu Ya nufe su da mamaki Yake kallon Danish daya rungume unaisah

"Lafiya? Meke farune"?

Taj ne yai karfin halin fada masa abun da danish yayi masa



Zuciyarshi ta sosu Harara Ya watsa masa kafin Yace"Sakar ta, tun kafin na 6ata maka rai, kaida bawani koshin lafiya ba har ka fara neman rigima? Ko kunya baka ji ba ka rungume Yarinya gaban ubanta! Idan ma baka sani ba to bari na fada maka wannan da kake gani mahaifinta ne wanda Yai silar zuwanta duniya...." ko ajikinsa bai ma fahimci me Big guy yake nufi ba, sai ma haushin shi da yake ji, Jira yake big guy yakai hannu zai raba shi da ita anan ne zaiga ainihin true colour dinsa...



Atsawace big guy yace"baka ji me nace ba, ka sake mana"!



"Ka daina yi mashi tsawa, Ka kyale shi kawai, nayi mashi uziri saboda baisan komai ba, kuma Yaro ne sai muna lalla6a shi"



Big guy bai tsaya sauraron Taj ba Ya kai hannu zai ja rigar unaisah, wata irin kururuwar tsawa danish Ya daka mashi tamkar saukar aradu, Gaba Waya saida suka firgita saboda Yadda sautinta Ya cika masu kunnuwan su, Unaisah dake manne ajikinshi tsabar kiWima kiris Ya rage ta saki fitsari a wando, saboda firgitar da tayi.



idanunsa sun kaWa jawur Yana huci Ya furta"kada ka kuskura ka ta6aba, Ranka zai 6aci, zanyi maka abun da baka ta6a tsammani ba, Idan har kayi gigin shiga tsakanina da ita...." ya faWa yana faman cije red lips dinsa, yadda kasan ba daga bakinsa kalaman suka fito ba saboda girman su.





da gudun gaske Naufal da Sajeed suka fito daga dakunansu, kamar wadanda aka koro tun wannan tsawar da danish ya kwatsa kowan nan su Ya firgita har wadanda ke adaki, kai hatta Ummi da batool sai da suka farka daga bacci jiki na 6ari suka sauko down stairs, Waya bayan Waya suke fitowa ?wansu da kwarkwatarsu, hankalinsu gaba daya yana akan Daninsh dake a rungume da unaisah, jikinta sai kerma yakeyi duk tabi ta ruWe, numfashinta kanshi dakyar take fidda shi.



Kusan atare suka hada baki suna tambayar meya faru? danish dan Allah kayi mana bayani meyasa ka ruke Unaisah ka sake mana ka matseta.. Sajeed ne yai maganar,

Big guy daya gama harzu?a Har Ya yunkura zai ?ara kamo rigarta Taj yai saurin dam?ar damtsen hannun shi, suka hada ido da juna girgiza mashi kai yai alamar a'a saboda shi yasan mai yaji dakyar in ba sai yayi jinyar bayansa ba.



"Haka zamu zuba mashi ido muna kallon shi? Baka ga yadda Ya matse ta bane? Ko magana takasayi"!



Cikin muryar lallashi Taj Ya dubi Danish dake ta faman zare idanunsa tsabar masifa har ?an?ance su yakeyi



"Dan Allah kayi hakuri ka sake ta, indai saboda ni ne bazan ?ara taba maka ita ba" Mamaki da al'ajabine Ya kama su Ummi dake kallon Ikon Allah



"Meyasa zaka bashi hakuri? Kaida ?arka? Tsoron shi kake ji ne"? A harzuke Big guy yai maganar



Taj yace'ba tsoron shi nake ba, fitina ke bana so, idan mukace zamu bi ta karfi da yaji donmu kar6e ta wlh ba zamu iya ba sai dai muja yai mata wata illar kwara mu lalla6a shi' guntun tsoki Big guy yaja, gaba daya haushin danish Ya cika shi, duk da yana tausayin prisoners sai dai ayanzu lamarin danish Ya fara sanya shi kokwanto akansa, gani yake kamar yaron yana da wata muguwar manufa.



Haduwa su Naufal sukayi suna ta yi mashi magiya don Ya sake ta, Amma Ya ?i sakinta



Suna acikin wannan Halin, a lokacin da basu yi tsammani ba, Sallamar Salsabeel Ta katse su, gaba Waya suka dago suna Kallon shi



Ganin shi yasa danish sakin Unaisah tai taga taga zata faWi da sauri batool ta ru?ota, sai faman haki takeyi tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu....



Sunyi tunanin shi kadaine Yazo, kusan atare muryoyinsu khadeeja Ya daki kunnuwansu, tunkafin su karasa shigowa suka fara kokarin tunano su wanene? Saboda sun haddace muryarsu ko tari sukayi za su iya sheda su.



?aya bayan Waya suka fara Shigowa bakunansu dauke da sallama, Lokaci Waya suka Ci burki suna Kallon su Unaisah dake kallon su, kusan atare zuciyoyinsu ke harbawa da matsanancin karfi, Tsabar rudani da al'ajabi Ya hana su gasgata abunda idanuwansu suke nuna masu, har abada ba zasu ta6a mantawa da muryoyin yan uwansu ba, balle kuma kamannin su da basu ta6a gogewa a idanunsu ba, Kokwanto sukeyi anya kuwa yan uwan sune da suka baro prison ba rai? Ko dai mafarki sukeyi ne? Ko kuwa idanunsu ne suke nuna masu badai dai ba? Tayaya ma haka zata yiwu?



Murza idanunsu suka farayi don su kara tabbatarwa da kansu abun da suke gani dagaske ne ko akasin hakan!



Kamar yadda suke al'jabin ganin su haka suma su Rubina suke kallon su da matu?ar ruWani akan fuskokin su, babu mai magana acikinsu falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, har na tsawon mintuna kafin salsabeel Ya fara magana



"Abun da kuke tunani dagaske ne, Ku daina kokwanto, wadannan da ku ke gani ?an uwanku ne, da kuka baro agidan kurkukun ?addara, ni kuma sunana salsabeel Wan tsohuwa tamira, nasan ba lallai ku shaida kamanni na ba, amma ita Unaisah ta gane ni...." fuskar shi dauke da murmushi ya yi maganar, har lokacin babu wanda ya motsa daga cikin su kamar gumaka, tsantsar tsabar rudani da mamaki ne Ya daure su har suka kasa magana, Hatta khadeeja da take da tabin hankali tayi kasa?e tana bin su da kallo kamar tana so ta tuna su wanene su ...... .



"Tayaya ma haka zata yiwu? Ni fa nagaza gasgata abun da idanuna suke nuna min, Kaina Ya ?ulle dan Allah ku fahimtar dani, ni dai a iya sanina kafin mu baro gidan kurkukun ?addarar amace muka barsu yanzu kuma sai mu gan su da ransu da lafiyar su? dama wanda Ya mutu Yana dawowa ne"? Sajeed ne Ya faWa fuskarshi da alamun ruWani

Salsabeel Ya fahimci halin da kowan nan su Ya shiga, In har ba faWa masu ainihin abunda ya faru yayi ba, toh zaiyi wuya su yarda da bunda suke gani, cikin sanyin murya ya fara ba su labarin abun da ya faru bayan barin su gidan kurkukun ?addara......



Waiwaye adon tafiya



Tayaya akai Salsabeel tare da su khadeeja suka ku6uta daga gidan kurkukun ?addara!? Bayan a iya sanin mu su deeja sun mutu sakamakon zuciyarsu da ta bugaS'S'S'



Bari mu koma baya don jin meya faru?



Suna shiga Cikin Toilet Win, Danish Ya datse ?ofar da sihirin shi, ya Janye tukunyar fulawar daga kan ?ofar, nan ta ke ta bayyana duk irin wahalar da suka sha ta ?i buWewa shi Bugu Waya yayi mata gaba Waya ta 6alle murfin ?arfen ya dare biyu, Sun yi mamaki da al ajabi yace da su Ba zai bi su ba, zai tafi da Akwatin kayan su tare da back pack Win su, za su tarar dashi a bakin ?ofar da zasu 6ula idan sun ?arasa hankalin su bai kwanta da maganar shi ba, gani su ke yi kamar wani mummunan abun zai faru da su idan baya atare da su, ganin sun toge sun?i tafiya yasa shi Kwantar masu da hankali, da?yar ya samu su ka Zu?unna ?asa tare da kutsa kai Waya bayan Waya su ke shiga cikin ?ofar da rarrafe, Bayin Allah ga yunwa ga ?ishin ruwa, ga raWaWin da zuciyarsu ke yi masu, Ita kanta hanyar da suka biyo Wata uwar ?ura ga yanar girgizo da ?wari sai hawan masu jiki su ke yi, Amma saboda rashin kwanciyar hankali yasa basu damu da su ba. Babu mai magana acikinsu saboda ?unar da ran su ke yi masu, Angel ce tai ?o?arin tunasar dasu akan suci gaba da ambaton addu o in data koya masu ko sun samu sassaucin a wurin Allah, sun Wau ki shawararta ahaka suka Dinga tafiya da rarrafe babu ?a??autawa, idan suka gaji su kan Wan zauna su huta kafin su dasa da wata tafiyar, A ?alla sun shafe tsawon awanni Takwas suna rarrafawa ba tare da sun kawo ?arshen ?ofar ba, a takure su ke Bayin Allah sun ga rayuwa gwiwowin ?affuwan su duk sun gurje sun sage, ma?oshinsu ya bushe ?amas, tun suna ambaton ?ishir ruwa suke ji har sun gaji sun yi shiru......... =?-?



A tsugunne yake gaban gawar tsohuwa tamira, yayin da hawaye ke sintiri kan fuskarsa, idanunsa sun kaWa jawur da su, zuciyarshi ta gama karaya, tamkar baya a cikin hayyacin shi, gaba Waya rayuwar duniyar ta sire mashi, duk sai yaji ya tsani kanshi, bai da wani buri daya wuce shima Ya mutu, sai dai baya son ya mutu batare daya gyara rayuwarsa ba, yana da burin wata rana yayi rayuwar yanci, kamar ko wani Wan adam, yana son yayi sallah ya gana da ubangijinsa, Tun kafin Ya mallakin hankalinsa Rayuwarsa take a cikin gidan kurkukun ?addara cikin kunci da takaici, idanunsa sun jima suna gane masa bakin zaluncin da ake aikawata agidan kurkukun ?addara, babban takaicinsa mutuwar mahaifinsa tamira batare da ta cimma burinta ba na ganin ta kawo karshen zaluncin shuwagaban nin gidan kurkukun ?addara, bai ta6a tsammanin zata riga shi mutuwa ba, yaso ace yacika mata burinta sai dai kash ?addara ta riga fata......



Babban burinshi Su Unaisah su tsira da ransu ko dan su kai labarin gidan kurkukun ?addara saboda al'umma su san da zaman shi, ko an samu wadanda zasu yi shahada su kawo karahen zaluncin da ake aikatawa.....



Hawayen dake sauka kan kuncinsa a hankali suke WiWWiga saman gawar tsohuwa tamira....



Gaba Waya ya manta da lokacin shi da ke tafiya, sam ya shafa'a ya manta da zancen binne gawarsu da yace zaiyi saboda hankalinsa ya gushe.



Kwatsam yayi zurfi acikin tunaninsa, ba zato ba tsammani kamar daga sama Yajiyo sautin dirar wani abu mai matu?ar razanarwa, harta ginin dakin sai da ya girgiza, lokaci Waya ya zabura ya mi?e zuciyarshi na harbawa da karfi da karfi, tunkafin ma yaga menene ranshi ya bashi cewar Giants ne na gidan kurkukun ?addara, mutanan da babu Wigon imani aransu, zuciyarsu tamkar dutse take, kurame ne kuma makafi ne basa ji basa gani umarnin Elders din su kadai suke bi.



Wani irin wahalallan Yawu salsabeel Ya hadiya mai Wacin gaske, tuni zufa ta soma wanko mashi, gaba daya yabi ya zauce saboda bai da karfin da zai Iya ja da su, sunfi karfin shi nesa ba kusa ba.



Tsabar kidimar da yayi ce ta shi yin zarya a dakin tsohuwa a kokarinsa naya nemo hanyar da zai kubutar da gawawwakinsu gudun kada su wulakantasu ..



Kafin yayi wani yunkuri Ya soma jiyo takun tafiyarsu, A matu?ar firgice Yake kallon fadadan kafafuwansu.



Kusan su uku ne, Wasu irin gabza gabzan samudawa masu kirar Zakuna, kamar fatalwu haka suka fado dakin, from head to toe sun rufe jikinsu da bakaken kaya baka Iya ganin komai nasu.



_Yawu salsabeel Ya haWiya, ta ko'ina zufa ce ke tsastsafo mashi ta cikin hudojin gashin fatarsa, muryarsa da tsantsar tashin hankali Ya furta"zanyi maku bayani...." bai ?arasa maganar ba, Muryar wani basamude daga cikin su mai amon gaske Ya furta"Salsabeel ka yi kuskuren ?etare iyakarka, ka riga da kasan hukuncin wanda Yaci amanar Elders! Sakamakon ka mutuwa ce, zakayi mummunar mutuwa salsabeel zamu kashe ka sannan mu watsa ma karnukan mu naman ka su cinye shi, bayan haka waWannan ?as?antattun gawarwakin da ke a kwance zamu kwanta da su, idan muka gama biyan bu?atarmu da su, zamu cire sassan jikinsu muyi farfesu da su, Kasusuwan jikin su kuma zamu rataye su ne......_ =?3?=?3?=?3?





*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*





*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*



3196407426



First bank



Bature Hafsat Muhammad,



*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

YOU MAY LIKE THESE POSTS
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
SUBSCRIBE US[14/10, 6:05 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 20 Complete
by
Novels Elite Admin
June 20, 2024
Sponsored Link

Novels Elite English
_*~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?*~_







3,F 'DB/=؋?=?%?=؞?





~Takun ?arshe=?%?~







Dedicated to Aunty Kubra=؋?=؞?







B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??





An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?







Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'





_AUNTY XEE Thank you for being there for me. Your support has been a lifeline.=؋?=؞?_





__________________________E20
'?







Tashin hankalin da ba'a saka masa rana!, Idanunshi azazzare Yake duban su, jikinshi ya soma kakarwa, tsabar kiWima zuciyarshi tamkar zata fasa ?irjinshi saboda bugun da takeyi masa, bakomai ne yafi Waga masa hankali ya zautar dashi ba face kalmar zasu kwanta da gawawwakinsu, Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un wannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login