Showing 258001 words to 261000 words out of 391264 words

Chapter 87 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2642

bazan lamunta ba, ba zaki sa nayi karamar magana ba, baki isa ki kunyata ni ba, kina hauka ne unaisah? Meye abunso atare da shi? Yaron da baida adinini arne ne, ga jahilci cike da kai, sannan bashi da wani galihu, bayan haka ina yake da halin da zai iya ruke min ke!?

wani irin jiri jirin tashin hankali ta gani acikin idanunta kalaman daddynta sunyi matu?ar Waga hankalin ta, tayi mamakin furucin da yayi akan danish kamar dai ya manta cewa komai ya faru arayuwar shi bayin kan shi ba ne...

"Unaisah Ina burin da kike shi na son auran attajirin me kuWi? Mai ilmin addini dana zamani mai cikakken asali wanda zai gatantaki Ya tarairayeki ya baki kyakkyawar kulawa?

"Daddy, na jima da soke wannan burin, ba dole sai na auri miji mai kudi zan samu farin ciki ba, sau dayawa wasu masu ilmin basu aiki da shi daddy, ni kawai miji na gari nake nema kuma na samu daddy, duk abunda ka lissafa Danish zai iya bani fin su, saboda yanayi min soyayyar da bazai iya cutar dani ba, yana yi min son da zai iya hana kanshi farin ciki saboda farin ciki"

Ta Wan numfasa kafin taci gaba da cewa" ka kira shi jahili daddy banji dadi ba, bayan kasan ba shi yaja ma kanshi hakan ba, idan ka amince min, zanyi amfani da son da yakeyi min in musuluntar da shi..."

bata ?are maganar ba, Ya dakatar da ita ta hanyar Waga mata hannu! wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makogwaronsa, Ya ma rasa me zaiyi ya huce haushin sa, Yayi mamaki wai har Unaisah ta iya gaya mashi da bakinta bata ji kunyar shi ba lallai ba karamin so take ma shi ba, zata iya komai akan shi..

Kafadunta Ya dafa da tafukansa Ya jijjigata har saida Sumar kanta ta yarfo ta gaban fuskarta fashewa tayi da kuka don ta gane bai fahimce ta ba..

Da kakkausar murya ya furta"Bazan ta6a amince ma soyayyarku ba, ba son shi kike ba, tausayin shi kike ji, tun wuri ki cire zancen zaki aure shi, saboda na riga da nayi maki miji sadakinki ne kadai bai biya ba, kuma yana sonki, shine za6ina unaisah in har ba bijiremin zakiyi ba, bana so ki bani kunya kada kisa na karya alkawarin da nayi masa, ki cika min burina Unaisah, danish ba dole saida ke zai iya rayuwa ba, ga sauran yan uwanki nan sai ya zabi daya acikin su, Unaisah burin kowace uwa ta sama ma ya'yanta uba nagari ba jihili ba.


abun da Taj bai sani ba tuni tajima da sumewa, idanunta daya gani a kakkafe shi yasa shi gane hakan..cikin jin faduwar gaba ya hadiye sauran maganarshi da bai amayar ba, saboda tashin hankali, Ashe nashi wasane bai ta6a ganin true love ba sai yau, ay yayi zaton daga layla da majnoon andaina samun irin soyayyar nan, sungumarta yayi kan fadar shi ya kwantar da ita kan gadon su, Ya fito daga dakin jiki na kerma Ya tafi dauko ruwa kafin dawowar shi, Batool ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi ta zauna gefen gadon tana kallon wani sabon salon kwanciya agurin Unaisah, tayi zaton dadin baccine yasa ta dauki tsawon lokaci bata leko waje ba.


"Sister Ya kamata ki tashi, Aunty Ummi ta hanamu baccin marece.."

ta fada tare dakai hannu ta Wan bubbuga ?afar Unaish shiru bata farka ba,

"Unaisah wani irin bacci ne wannan kamar mai fama da cutar bacci" ta fada tana kara bubbuga legs din ta.

Adaidai lokacin Taj ya fado dakin hannun shi ruke da robar ruwa me sanyi, Yana ganin Batool yaci burki gaban shi na faduwa yasan muddin tasan Unaisah suma tayi sai ta yi kukan da zai jawo hankalin sauran yan uwanta.


Jin motsin adakin yasa Batool ta juyo ganin daddyn Unaisah yasa ta mi?e da fara'a tace"ina wuni daddy, i'm sorry watakil ka yi sallama banji shigowarka ba..." yawu ya haWiya dakyar ya tattara nutsuwarsa yana kokarin danne damuwar shi yace"lafiya lou daughter.." da alamun rudu kan fuskarta tace"daddy naga water bottle a hannunka.." washe baki yayi"eh ni zan sha ne, kishi nake ji" murmushi tayi"ko kazo ganin Unaisah ne" a kagare ya daga mata gira"bacci take, yanzu nake kokarin tadata" da sauri yace"kinga bari ni in tashe ta, kije gurin ummi naji kamar tana nemanki..." kamar taso ta Wago shi, ta lura kamar wani abu badaidai ba, amma sai batayi mashi gaddama ba, ta fuce daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya datse ?ofar dakin, ya zauna gefen gadon da sauri ya cire murfin robar ya yayyayafa mata ruwan kan fuskarta.

dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya..


"Unaisah, Pls ki yi hakuri ki tashi, kinji! I won't hurt you anymore..."

dakyar ta iya buWe idanunta wadanda suka kada jawur ta dube shi

Wani irin ciwon kaine Ya far mata...
Cikin disasshiyar murya tace"daddy, kada ka raba ni da Danish, zan iya rasa raina.."


Kwata kawata baya son tana fadin zata rasa ranta akan Danish, Ranshi baci yake kamar ya hadiyi zuciya, kuma yana akan bakanshi bazai janye ba.


"I'll think about it, Yanzu bana son duk wani abu da zai Waga hankalinki, kwanciyar hankalinki nakeso..." hankalin ta ya Wan kwanta, gani take kamar daddynta zai duba mata ne.

"Amma daddy, baka son Danish ko"? Girgiza mata kai yai"Ina son shi Unaisah, Kuma ina jin tausayin rayuwar shi, maganganun da kikaji nayi Wazu rainane Ya 6aci bawai don ina nufin hakan ba, ni kawai banaso kina sakar mashi jikin ki ne"

cikin kwantar da murya ya faWa.

Ruko hannun shi tayi a cikin nata"daddy pls ka min alkawarin ba zaka raba ni da shi ba"!

Dafe kai yai da tafin hannun shi, ji yake kamar ya kifa mata mari saboda haushin da yake ji in ta ambaci sunan Danish

"Kina so In amince ma Soyayyarku?In kuma ba shi damar Auren ki"? jin wannan maganar daga bakin daddyn nata yasa ta mi?e zaune cike da zumudi tace"Eh daddy..."

Numfasawa yayi kafin yace"Zan baki Umarni, If you do what I say, I promise to fulfill your dream of marrying your choice".

gabanta ne ya Wan faWi duk da batasan umarni da zai bata ba, taji fargaba sosai..

"Daddy, wani irin Umarni ne? Ka faWa min in sha Allah zan yi maka biyayya" ta faWa cike da jin fargaban amsar da zai bata..

Ido cikin ido su ke kallon jun.

"ki bashi Umarnin, ya yi mana jagora zuwa Gidan Kurkukun ?addara..."

wata irin razananniyar faduwar gaba taji, kamar zata zauce ta daddafe kanta da tafukanta dama saida ranta ya ayyana mata abun da zai umarce ta da tay...

"Inaso in tabbatar da kaunar da ya ke yi maki, ta hakanne zan gane shin jarumtakarsa takai in mallaka mashi lu'u lu'u na?

ya faWa yana kallon idanunta da suka rune zuwa Jajawur kamar Jan gauta.

Cikin shesshekar kuka tace"daddy, pls ka bani wani umarnin daban, wannan is too hard for me! I can't force him I don't wanna put his life in danger"


Kwata kwata babu annuri akan fuskarshi, ya haWe rai sosai saboda yana son ta Wauki maganar shi serious

"Unaisah, karna kuskura na ?ara ji kin furta kalmar kada ki jefa rayuwarsa cikin hadari! Ke ba musulma bace? Ba kiyi imani da Allah ba? Ko baki yarda da ?addara ba? Ko kuwa ?arancin tawakkali ne ke damunki"? Runtse idanunta tayi tana jin wani iri yanayi a zuciyarta mara dadi

"Ba haka nasanki ba Unaisah! Kin canza min! Ina zuciyar imaninki take? na fahimci so ne ke nema ya rufe maki ido, Unaisah kin manta mummunar ?addarar data rabamu? Kin ta6a tunanin zaki ku6uta daga kurkukun ?addara? Kin ta6a tunanin zamu sake haWuwa? Ikon wanene yin hakan"?

In a weak voice tace"Allah"

"Toh inaso ki sanya ma ranki, duk wani abu da zai faru da shi mu?addari ne daga Allah, tun zuwan shi kurkukun kaddara bazai hana Allah ya jarabce shi da wata ?addarar ba, har kwarama yaje can yayi jahadi gurin ceton rayuka...."

nasiha ya cigaba dayi mata tun bata fahimtar shi har ta fara yin amanna da maganar shi...

"Daddy, ni damuwana he's not a muslim, banson ya mutu batare daya kar6i kalmatusshada ba"

ta faWa hawaye na bin fuskarta...

Ruko hannayenta yayi acikin nashi ya ru?e su gam kafin yace"In sha Allah zai musulunta Unaisah, idan sheikh imam yazo zamu nemi taimakon sa"

"Amma daddy, nima ina neman alfarma agurinka"!

"Wace alfarma"?

"Ku tafi dani, Nima ina son in bada gudummuwata..." waro idanu waje yayi aranshi ya ayyana bazai yiwu ba, amma a fili sai yace"Zan yi magana da chief, kinsan dokar aikinsu babu mace, amma in har ya amince zamu tafi dake" ajiyar zuciya ta Wan sauke, fatanta Allah yasa Chief ya amince mata, dalilin dayasa ta za6i tabisu saboda abu biyu, na farko don ta kashe Jan wuya, duk da batasan wanene shi ba, kuma batasan ko yana Waya daga cikin members na kurkukun ?addara ba, sai dai taji aranta dakyar in ba ya cikin Elders, abu na biyu donta ba Danish kariya, koda Ajali zai riske shi, toh su mutu atare zaifi mata kwanciyar hankali.

Kiraye kirayen Sallar isha'i da aka fara yi ne, yasa Taj mi?ewa ya dube ta"zan tafi, kiyi kokarin aiwatar da umarnina, in sha Allah silar biyayyar da zakiyi min, ba zaki ta6a danasani ba, saima ya zama silar farin cikin ki na har abada" cikin sanyin murya tace "in sha Allah daddy, zanyi masa magana, duk yadda mukai zan sanar dakai"

"Gobe da safe, in tashi da labari mai dadi" jinjina mashi kai tay

Mi?a mata hannu yayi da sauri ta sauko daga kan gadon ya rungumota, yana ?ara lallashinta da bata baki har saida ya tabbatar taji hudubarshi kafin su ka yi sallama da juna kamar karsu rabu..

_________________________________
'?

Idan muka koma bangaren Benazir sam ta kasa walwala, maganganun Zaki sun tsaya mata arai, sun hana ta sukuni gani take kamar batayi masa adalci ba, tayi kuka sosai har zazza6i saida ya lullu6eta, Wlh Yabata tausayi bata ta6a ganin rauninsa ba sai awannan lokacin, yayi mata taimakon da har abada bazata ta6a mantawa da shi ba, ya bata lokacin shi! Ya bata kulawarshi! Ya bata ci da sha Da suturu harma da aikin yi, ya kuma ruketa agidan sa na tsawon shekara goma sha bakwai bai ta6a goranta mata ba, sun shaku da juna, ya zama tamkar uba agare ta!

babu wanda yasan wani abu dangane da zuwan Zaki, daga Ita sai Alhaji musa suka san da maganar, fatanta Allah yasa kada Uncle musa yayi ma Daddynta maganar don batason duk wani abu da zai da?ile maganar komawarta dakin Mijin ta, taso taji daga bakin uncle me Zaki ya fada masu sai dai takasa ma tunkarar shi saboda bata son taji abunda zai hana runtsawa.

Har kiran Layin Zaki tayi don ta kara bashi hakuri amma kwata kwata kiran baya shiga..

Tunani ta somayi me zatayi don ta saka mashi?

Zuciyarta ta bata amsa da cewa me zai hana ta hada shi da Aneelerh! aranta kuma ta ayyana zaiyi wuya su sasanta cos zaki bazai kara gangancin fadawa tarkon son macen da kaddara ta rabata da mijinta, kamar dai ita =ؔ?

_________________________________
'?

Har wuraren ?arfe shaWaya na dare bata runtsa ba, saboda matsananciyar damuwar data addabi zuciyarta, sai faman juyi takeyi kan matress kamar me fama da ciwon ciki, maganganun daddynta dana Salsabeel ne suka dinga dawo mata cikin kwalwar kanta, bata san ya zatayi ba, bata da wata mafita daya wuce ta amsa bukatarsu sai dai tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar man dinta a cikin haWari amma idan ta tuna burin da take da shi na kashe jan wuya, da kuma nasihar daddynta sai taji kamar ana kara mata kwarin gwiwarta.

*CHIEF OWAIS*

Bacci ya ?auracewa Idanun shi, Ina zai sa ran shi yaji dadi? chief irin mutanan nan ne waWanda idan suka kwallafa rai ga abu suka saka buri da naci da komai in har ba su ga sun Cimma nasara ba to fa hankalin su bazai ta6a kwanciya ba..

Ya ?untata kanshi Ya hana zuciyar shi sukuni, baisan taya zai 6ullowa lamarin ba, Danish Yana nema Ya zamar ma shi ciwon kai...

Yayin da yake wannan tunanin safa da marwa yake a tsakar bedroom Winsa, boxer short ne kaWai a jikin shi, fuskarshi a yamitse ba annuri..

Jefi jefi in damuwar ta addabe shi tafin hannunsa yake cusa cikin sumar kanshi ya yamutse ta kamar Wan mahaukaci wani lokaci da karfi ya ke bugun iska da hannayen shi.

Phone ringing dinsa ne ya katse hanzarin shi, kamar bazai duba mai kira ba, zuciyarshi ta takura mashi akan ya duba, juyawa yayi a sukwane cikin rashin kuzari ya dauko wayar dake aje kan mirror chair, yayi mamakin ganin almost 16 missed calls, picking call din yayi tare da kare wayar a kunnan shi yai shiru yana jiran jin me zaice


"Owais, ya ake ciki game da kai farmakin?..."

"Only a few days remain"


"Ko zaka Iya faWamin menene shirin ku a yanzu ni kuma zan ?arfafa maku gwiwa"

Har yanzu bai yarda da mutumin ba, shi mugu bashi da kama, zai iya bayyana ta suffar mutanan kirki don ya shiga jikin mutun...

"I'm sorry to say, bazan iya faWa maka ba, in har dagaske kana son taimakona ba dole sai kaji me muke shiryawa ba"

"Hakane, Ka faWi gaskiya, Owais, shawarar da zan baku shi ne, Ku sanya malaman addini su tayaku addu'a, sannan ku ma iyayenku magana su tayaku da addu'a, ku kuma yawaita sadaka ga marayu da mabu?ata suma su tayaku da addu'a, ku nemi kariya daga wurin Allah, in sha Allah badai mutun da Aljan ba sai Allah...." bai ta6a jin 6oyayyan mutumin ya burge shi irin na yau ba yaji dadin shawarwarinsa

Har ya buWe baki zai yi mashi godiya yaji Wuff yai rejecting call din..


Hakanan Yaji Yana ra'ayin ganin Unaisah, wall clock Ya kalla ?arfe 11 na dare, yasan i war haka tayi bacci


Jaraba kiran layinta yayi, tana fara ringing ta yi picking yayi mamaki bai zata zata Waga ba ..

Kara wayar yayi a kunnan shi yama rasa me zai ce mata.

Sanyayyar muryartace ta ratsa kunnanta

"Barka da dare chief, ka wuni lafiya"?

"Why are you still not sleeping"

"I woke up for the night prayer" yaji dadin jin hakan

"Okay, if you dont mind I want you to bring me the girl's backpack"

"Toh" rejecting call Win yayi, sai da yayi unclocking Win kofarsa don ta samu damar shigowa, kafin ya shiga bathroom don yayi wanka.

Saukowa tayi daga kan gadon ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta ta cikin madubin.

Silk Pyjama ne a jikinta, riga da wando launin blue sky, rigar tana da dogon hannu sun yi matu?ar yi mata kyau.

Lallausar Curly hair dinta tabi da kallo, duk Ya har gitse saboda rashin kwanciyar hankali ta manta when last tayi fixing dinsa.

Fragrance set ta Wauko ta feshe ko'ina na jikinta da shi, cikin kankanin lokaci daddadan kamshin turarenta ya buWe Wakin

ta Wauko veil ta yafa ma kanta kafin ta saka flat shoe a kafarta.

Back pack din ta dauko, ta daurata kan mattress, ta curo wasiyar da Unaizah ta bata guda biyu ta boye su cikin diary Winta, don bata jin zata iya rabuwa da su tunda kamar amana ta bata, tafison ta dam?a ma iyayenta da hannunta.

Goya jakar tayi abayanta, ta fito daga Wakin, gidan shiru babu kowa a falon alamar duk sunyi bacci adakunansu..

Bata nufi ko'ina ba sai Wakin Chief, tana ?arasa bakin kofar takai hannu zatayi knocking sai taji ?ofar ta fara kokarin buWe kanta ta Wanyi mamaki

Almost 3 times tana yin sallama ba'a amsa mata ba, ta kutsa kai ta shiga ciki, bata ga kowa ba, sai dai taji sautin safkar ruwa daga toilet dinsa, wurga ido tayi tare da kallon glass wall din toilet nasa yayi duhu sama ka dai take iya gani..

Gajiya tayi da tsayuwa, ga wata kasala da take ji, wasa wasa ta fara gyangyaWin bacci, har ta saki backpack din hannunta ta fadi kan floor ba tare data lura ba..


Lokacin daya fito waist dinshi Waure da towel fari kyal, fatar shi tayi freshi danshin ruwa ya ji?ata...yana kokarin Waga kafa ya nufi dressing mirror ba zato ba tsammani ya hango mutun kwance kan rug kamar an jefar da ita a gurin ta baje sai sharar bacci take yi, ga backpack Winta yashe gefe Waya...

Yayi mamaki cos bai tsammaci zai iske ta adakin ba, ya daisan ya cire security din kofar, abun da ya fi daure mashi kai ta yadda bacci yayi awon gaba da ita akan rug dinsa, kamar wadda tasha kwaya..

Walking slowly ya nufi rug din Ya zu?unna daga gabanta, ya nutsu yana kallonta, yanayin yadda take fitar da numfashi cikin nutsu kirjinta na sama da kasa ba karamin tafiya tayi da imaninsa ba, kamar jinjira la66anta sai kerma suke.

Sai yanzu yayi tunani me ya hanata bacci da wuri? tabbas akwai damuwa aranta wanda silar hakan ta kuntata kanta ta hana idanunta bacci shiyasa da tazo dakinshi baccin yaci karfinta har yai awon gaba da ita batare da sanin ta ba..

Baya jin zai iya tada ta daga baccin, bai shirya katse mata jin dadin ta ba, baccin da takeyi sauki ne agare ta.

Yanke shawarar canza mata gurin kwanciya yayi, A hankali ya sanya hannayen shi biyu ya tallabota ya dago da ita tare da mi?ewa Ya nufi katafaren gadon shi da ita, kusan itace mace ta farko da zata kwanta akan shi,

A tsakiyar mattress din Ya shimfidar da ita, duk da baccin da takeyi hakan bai hanata jin dadin sauyin gurin kwanciyar da akayi mata ba, numfashinta har canzawa yayi, lallausan duvet Winsa ya janyo ya lullu6e ta shi har zuwa kan kirjinta, kasa janye idanun shi yayi daga kallon ta gaba Waya ya shagala da kallon kyakkyawar sexy face dinta wani irin yanayi ya fara ji a jikin shi hakan yasa shi saurin mi?ewa Yabar gaban gadon, badan bai yarda da tsoron Allahn shi ba sai don gujewa sharrin shaidan...

Can cikin bacci kunnuwanta suka soma jiyo mata daddaWar kira'ar karatul qur'anin shi, kamar amafarki take sauraron karatun a lokaci yana zaune kan darduma jikinshi sanye da farar jallabiya, raba dare yayi yana kai kukansa gurin Allah, bayan ya kammala ya buWe kur'ani yacigaba da karantawa.

Yana tsaka da karatun, tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci ta dinga mirgino kiris Ya rage


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login