Showing 324001 words to 327000 words out of 391264 words

Chapter 109 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

3635

kada ku bata lokaci, saboda shi din mutum ne mai hadarin gaske, ya sha yi min barazana akan In har na kuskura na fada ma wani abun da ya ke min wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na fadamawa shiyasa nakasa sanar daku_


Tuna wannan maganar yasa Aneelerh taji tsoro ya mamaye zuciyarta, tayi shiru tana sauraron gargadin da zuciyarta ke yi mata.


_Kada ki kuskura Anila! Ba zaki Iya ja da shi ba, in har yasan kin san sirrin shi kashe ki zaiyi, mutane irinsa basu da imani zasu iya aikata komai donsu rufawa kansu asiri, Kwara ki nemi wata mafitar...."

tayi zurfi cikin tunaninta kwatsam Ta tsinkayi muryar mutum abayanta


"ANEELERH"! Ras gabanta Ya fadi jin muryar mutumin datazo nema, tuni taji tsigar jikinta na tashi, Yan hanjin cikin ta suka hau kadawa.

"Ko ba ita bace"? Zazzare Idanu tayi, Cikin sauri Ta daidaita nutsuwarta, A hankali ta juyo ta fuskance shi, Yana atsaye Cikin riga yar shara da gajeran wando, Junaid Ya jima Yana fada mata Uncle dinta mummuna ne ba ta6a ganin muninsa ba sai yau data gano mugun halinsa.

zuba mata jajayen idanun shi yayi, Cikin rawar murya ta furta"am.. um..un uncle barka da rana, dad..dama kai nake nema, um.. inaso ne dama in tuna maka maganar...."

cike da rudani yake kallonta Jin yadda take yin magana a dabarbarce kamar mara gaskiya amma bai kawo komai aransa ba yasan Anila da kunya may be tana jin nauyin yi masa magana ne shiyasa ta ruWe.


Murmushi yayi tare da cewa"Anila kenan, to meye abun rudewa aciki? Kawai don zakiyi min magana? Waini sai yaushe zaki daina jin kunyata? Sai kace ba Uncle dinki ba"? kakaro murmushin ya?e tayi kan fuskarta batare da ta tanka masa ba.

Dafe kai yai"kash Kiyi hakuri kinji shiru tun da kika tura min credentials Win ki, har yanzu ba'a neme ki ba, kema ce baki tuna min, kinsan uncle din naki da mantuwa abubuwane sunyi yawa akaina bakasai nake tunawa ba, In sha Allah zan tuntubi Md din asibitin mutuminane ai..." washe baki tayi tace"bana so na takura maka ne, nasan uzirurrukane sukai maka yawa, shiyasa bana yi maka magana, yau ma don naji kace kana gida shine nace bari na tuna maka"

"Allah sarki, nasa maki rai kina ta faman jirana, ki kara hakuri In sha Allah yanzun nan dana shiga daki zan kira shi awaya in tuna ma shi, Ki ma fara shirye shiryen fara zuwa aiki"

ya fada tare da tafa hannayen sa.

Washe baki ta kumayi alamar taji dadi tace"nagode uncle, Allah yasa ka da alkhairi Saina Ji daga gare ka, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa"

"Ameen Anila, ai baki da wata damuwa, ke da kike dani? Asibitin Obie ai namune ke sai ma kin zabi albashin da kike so a yankar maki Allah wallahi" fashewa tayi da dariya tana fadin"kai uncle, Ina kara gdy da kulawarka agare ni" batai gangancin da zai gano ta ba, lokacin da ta baro gurinsa wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tafin hannunta dafe da saitin Zuciyarta.


Tana shigowa falo taja tunga ta tsaya tana tunanin meya kamata tayi? dafe kai tay kamar mai fama da ciwon kai.


Aranta ta ayyana Ko dai ta sanarma Mami? Can kuma ta girgiza kai ba lallai su yarda ba, ko da ta nuna masu video din tun da bayani ne Ana tayi bawai videon abun da ya ke yi mata ne ba, Bakowane zai gasgata maganarta ba kai koda zasu yarda hadari ne Ta gaya ma wani acikin gidan hankalinsu zai tashi a karshe ma garin nukunuku Ya gano su.

Gaba daya Aneelerh ta ruWe, kwakwalwata na neman rikicewa..
Juyawar da za ta yi ke da wuya tayi arba da mami dake ta kallon ta.


Washe baki tayi adabarbarce ta furta"ma.. mi dama yanzu nake niyar shigowa kitchen din don in tayaku aiki"! Wani kallo mami ta yi mata.


"Aneelerh lafiyarki kuwa? Tun dazu Ina tsaye abayanki baki lura dani ba har kiran sunanki nayi kusan sau uku baki amsa min ba, meke damunki ne!" yawu ta haWiya ?ut jikinta na tsuma tace"mami ki yarda dani babu komai, ba abunda ke damuna"


"Anya Anila? Ko dai baki da lafiya? Ta fada tana karewa fuskarta.

girgiza kai tay"lafiyana lou mami"
Ba don ta yarda da maganarta ba tace"toh," har zata juya ta dan dakata"Kunyi waya da mahboob ne"?

"A'a,"

"Kinsan ba kai gare shi ba, kada yabar mana yaro da yunwa, Ki kira shi ya dawo da junaid gida" amsa wa tay da toh.

"Naji kince zaki ta ya mu girki, mun kammala ay, ga gidan nan ki kara gyara shi" ta amsa mata da toh.

Mami na barin gurin ta sauke ajiyar zuciya.

________________________________________
'?

*PRAVIN*

Cike da zumudin son ganin ta, ya shigo dakin tashin farko yai arba da awarwaron ta akan floor inda ta watsar da su, Hankalinsa ba ?aramin ta shi yai ba, a yadda yasan Hajjaty da tsafta ba karamin abu zaisa tabar dakinta a yamutse ba gyara ba, hakan yasa shi fahimtar babu lafiya.

Sam bai lura da ita ba, har saida ya karasa tsakiyar dakin, Idanunsa suka sauka akanta tana a kwance kan gadonta bayan data gama koke koken bacci ne yai awon gaba da ita, from head to toe yabi ta da kallo kamar mahaukaciya, naWin sarin jikinta duk ya warware, har inners din ta sun fito, ga gashin kanta a hargitse kamar bata gyara shi ba, aransa ya ayyana meya faru da ita? Meke damunta"?

damuwace karara akan fuskarta, hawa yai kan gadon ya matsa kusa da ita, da ya dubi fuskarta sai da yaji gabansa ya fadi, Gaba daya kwalliyar da tayi ma fuskarta ta baci da jan bakin data shafa ma lips dinta.

Lumshe idanun shi yayi tare da sake buWe su kan fuskarta
A hankali ya Shafa fuskar da yatsun sa har izuwa kan wuyanta ya dire su kan kirjin ta.

Numfashi ta Wan ja tare da sauke shi da hucin zafi.

Baya so ya katse mata baccin ta, amma yana son yaji meke damun ta.

Can kasan makoshi ya furta"My lovely wife, am back, nayi kewarki sosai"

ya faWa tare da manna mata sumbata kan lips dinta.

ya saba duk in ya dawo daga aiki ko ya dawo daga tafiya ya shigo dakinta zai taras da ita tayi gayu ta gyara ko'ina na dakin don ta faranta masa kuma zata watso da gudu ta rungume shi sannan ta yi kissing din shi amma yau sai yaga akasin hakan taya ba zai damu ba?

Hannunshi ya zura ta bayanta yana kokarin kwance igiyoyin rigarta bai aune ba yaji ta dam?i hannunsa, da sauri ya kalle ta, A hankali ta buWe idanunta wadanda suka kada jawur ta sauke su a cikin nashi, gaban sa ne ya ?ara faWuwa ganin yadda idanunta suka yi ja kamar an watsa barkono acikin su.


Arude ya furta"kin tada min hankalina, meke damunki ne? Gaba daya dakin a hargitse babu gyara, ke kanki ba acikin nutsuwarki kike ba, wai meke faruwa ne"?

Maganganun marwa ne suka soma dawo mata a cikin zuciyarta, Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, hakan ba karamin daga hankalinsa yai ba, duk yabi ya rude cikin rawar murya yake yi mata magiya akan ta fada masa damuwarta..

Lumshe idanunta ta danyi kafin ta kuma bude su akan fuskarta.

Zuciyarta naci gaba da tariyo mata abun da marwa ta faWa mata akansa.

Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar Pravin ta katse ta ransa adan bace ya furta"wai ba zaki fada min abun da ke damunki ba ne? Kina ji ina magana kin share ni"!

Numfashi taja tare da sauke shi da karfi.

Ta yi saurin daidaita nutsuwarta cikin disasshiyar murya tace"s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????annu da dawowa.

"Ba wannan na tambayeki ba, ki fada min meke damunki"

"Kada ka damu, babu komai"

"Karya kike yi, Dole akwai abunda ke damunki"

"Hakane, bana so na tada maka hankali ne, wlh Cikina ke ciwo, kasan halin da nake shiga idan na fara ciwon ciki" girgiza kai yai"ban yarda ba, kawai ki fada min abunda ke damunki"? Ya fada fuskarsa a daure.

Tunani ta soma yi ya zatay da shi? Don bata jin zata iya fada masa abunda marawa tace akan shi, tasan bazaiji dadi ba in yaji anyi masa kazafi kwara ta bar abun acikin zuciyar ta.

Kurama juna idanu sukayi har na tsawon mintuna goma, sai da ransa ya gama baci jin tayi shiru taki tanka masa, yana huci yace"yau ni kike boye ma abunda ke damunki? kina da wanda yafi ni ne? Okay, kada Allah yasa ki fada"

Saukowa yai daga kan gadon Har ya kusa fucewa daga dakin tayi saurin mikewa ta duro daga kan gadon ta nufe shi da gudu ta faWa bayanshi tare da zagayo hannayenta kan kirjin shi

Dakatawa yai da yin tafiyar da kakkausar murya ya furta"kin shirya fadamin"?

"eh" batare daya juyaba yai shiru yana sauraronta.

"Hajiya saratu ce ta bata min rai, taci mutuncina pravin, ni bansan wata irin tsana tayi min ba..."

karya ta shiga shirga mashi abun da ba halin ta ba, duk don ta samu ta kawar masa da tunanin abunda ke damun ta.

Ransa ya baci da jin abunda hajiya saratu tayi mata.

Cikin shesshekar kuka ta kara da cewa"ita ce ma ta cabemin kwalliyar da nayi maka"

ta fada tare da ruko sareen dai dai Inda hajiya saratu ta goge mata kwalliyar da shi ta nuna mashi da yar shagawaba tace"ka gani ko"?

Runtse idanun yai ji yake kamar yaje ya shake wuyan hajiya saratu.


Yana huci yace "bazan ?yale ta ba, dole In rama maki cin zalun da takeyi maki, mara mutunci kawai.." still da shagwa6a ta tallabo fuskarsa da tafukanta"babe, Ni ban fada maka don ka rama min ba, wlh na yafe mata, kawai banji dadi bane, amma komai ya wuce, mu kyale ta kawai"

Jinjina mata kai yai tace"ina fata kun dawo lafiya? Ya baba Obie? Ya kuka baro aminin nasa"?
"Mun baro shi lafiya, Baba Obie Yana a part dinsa, da anjima ki shiga kiyi ma shi barka da dawowa"


"Okay, fada min me kake son in kawo maka"?


"Bana jin yunwa, Naci abinci agurin hajiya saratu, A yanzu nafi bukartar ki"

ya fada tare da daukarta kamar Yar baby, Dariya ta saki tana kallon shi..
Jujjuyata yai kafin ya nufi gadon su da ita, ya jefa ta a hankali, tana daga kwance tana kallon shi yayin da yake a tsaye yana Unbuttoning din rigarsa.

"Ba zan raga maki ba, almost one month, dakyar nake Iya bacci saboda rashin ki"

Tace"nima haka, ba raga maka zanyi ba, ka tafi ka barni da kewarka"

_________________________________
'?

Shigowa dakin ta yi, tana kokarin Yaye veil din da tay rolling, taga wayam babu pravin data bari yana cin abinci adakin.


"Ina ya shiga ne? Ko ya shiga toilet"! Ta fada aranta, tare da nufar toilet door ta danyi knocking shiru ba'a amsa mata ba, sai dai taji sautin safkar ruwa alamar ana amfani da shi.


Watsa hannayenta tayi, ta koma ta zauna daga gefen gadon, Ta curo waya daga cikin yar purse dinta ta danna na Hajiya laura Kira.

"Mara mutunci, Sai yau kika tuna dani?

"Banson iya shege matar Yaya, don kar in tuhume ki shine kika rigani magana ko"?

Fashewa hajiya laura tayi da dariya"Sorry aminiyar arziki, bana fada maki zanje dubai ba? Sai jiya na dawo agajiye wlh" hajiya saratu tace"kai haba, Ashe kun dawo, Ya gajiyar tafiya"

"Alhamdulillah, gajiya tabi jiki, akwai fa kaya, munyi sabuwar Wauka, Na tura maki videos ta whatsapp yakamata ki hanzarta zabar wanda kikeso tunkafin akwashe kizo kina cizon yatsa"

Hajiya saratu tace"Amma naji dadi wlh, dama ga hidima muna da ita, dazu Owais ya nemi alfarmar ayi family meeting a birthday dinsa, kuma kinsan In Owais zaiyi birthday, ko biki albarka saboda yarda baba Obie ke ji da shi ina mai tabbatar maki za'ai harka ta arziki" dariya suka sanya gaba dayansu

Laura tace"amma da mamaki Owais daya saba yin birthday a canada inda aka haife sa kice wannan karan A Nigeria za'ae, Amma fa naji dadi wlh, Allah ya nuna mana lokacin lafiya"

Sun dan jima sunayin waya da hajiya laura kafin su ka yi sallama.


Gallery ta shiga ta buWe hotunan da tayi ma Parveen aranar dinner din Hateem batare da sanin ta ba.

Kamar ibada kullum saita kalli hotunanta, ta6e baki ta Wanyi.

_____________UNAISAH ANGEL


Tana a kwance kan gadonsu, Ta lumshe idanunta yayin da brain dinta ke tariyo mata memories dinsu da Danish, wani sa'in ta yi murmushi wani sa'in ta zubda kwalla, Amma yau tunanin nata ya kasu gida biyu, saboda kalaman da Chief ya furta mata adaren Jiya da su ta wuni aranta, bata ta6a zaton mutun me matsayi irinsa zai iya aje girmansa da komai donya ja ta a jiki ba.

"Unaisah" muryar Ummi ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula

Su biyu suka shigo dakin, Hannun Batool ruke da wooden tray mai dauke da dinner dinta akan table ta daura mata shi.

"Su daddy sun dawo"

Ummi tace"a'a may be sun tsaya yin sallar isha'i ne naji an fara kira, yanzu dai ki daure ki tashi kije ki yi wanka"

Ma?e kafaWa tayi"Pls aunty Ummi, dan Allah kibarni, Bana son maganar wankan nan nafi jin dadin jikina a haka, Ni wlh tsoron ma taba ruwan nake"? Baki asake ummi ke kallon ta.

Batool tace"pls Ki daure kiyi wankan zaki ji dadin jikin ki, baki ga yarda kika koma ma ba? Kamar yar mahaukaciya"


Ummi tace"fada mata dai, Gashin kanki ko kyan gani babu, Pls ki tashi kiyi amfani da ruwan zafi zaki fi jin dadin jikinki" girgiza kai tay

Ummi ta dubi Batool"in muka bita ta lalama bayi zatay ba, Abun da za'ay ki kama hannunta ni in kama kafafuwan mu shiga da ita ciki muyi mata wanka" kafin ummi ta karashe maganar suka ga ta zabura ta mike tsaye tana girgiza

dariya suka kwashe da ita.

"Dan Allah ku kyaleni, tun da nace bana son wankan, Ba jikina bane wai"

Basu tsaya sauraronta ba, Ummi ta haye ta cafko ta tare da daukarta saman kafadarta, tana ta zabga mata masifa akan ta kyaleta hada ambaton sunan daddy.

Shigewa Ummi tayi da ita cikin toilet.

Jim kadan ummi ta fito bayan ta wanke mata gashin kanta, ta barota a cikin toilet din, kafin ta fito Batool ta dauko mata kayan da zata sanya.

Bayan ta shafe mintuna, sai gata ta fito tana ta faman daure fuska, Jikinta a sanye da bathrobe..

Kallo daya tay masu ta wuce ta nufi gaban dressing mirror ta zauna, ummi ta fara gyara mata gashin kanta cikin kankanin lokaci ya fara she?i.

"Zaki iya shafa lotion din ko in shafa maki" yamitsa fuska tay"zan iya" murmushi suka saki, kamar babu laka a jikin ta kwata kwata bata da kuzari, dakyar ta shafe jikinta da body lotion bayan ta kammala tace su fita zata saka kaya ummi tace"wani dare ne je mage bai gani ba Unaisah? Time da baki a hayyacin ki kin san sau nawa inayi maki wanka"?

Ras gabanta ya fadi waro idanu waje tay har zata fasa zazzaga masifa Batool tace"zolayarki takeyi"

cije le6e ta yi, dakyar ta mike ta nufi kayan da Batool ta aje mata kan bedmattress ta dauka ta nufi wurin closet dinsu can cikin dakin ta shige don kada su ganta.


Jim kadan suka jiyo takun tafiyarta a tare suka dube ta, oversized shirt ce tare da wando plazzo Green colour, ta daura veil din kayan a saman shoulder dinta.

Ummi tace"ku dai Allah yayi maku ruwan kyau, dama kika rame sai kika kara kyau, musamman Collarbone dinki ya kara kawata kyawun kirjin ki" yamutsa fuska tayi cikin sanyayyar voice dinta tace"Anya aunty Ummi ba sharri kike min ba? Kashin wuya ne abun kyau"?

Batool tace"wlh dagaske yayi maki kyau" tabe baki tayi

"Kizo ki zauna ki ci abincin ki" ta fada tana nuna mata tray din.


Jiki asanyaye ta nufi gafen gadon ta zauna, Batool tayi serving dinta, sam takasa Cin abinci, ko kamshin shi bata son Ji.

"Pls ki daure ki ci ko kin samu karfi a jikin ki" girgiza kai tay"bana jin dadin shi, Ko naci amayar da shi"

Duk yadda sukaso taci abinci takiya, Suna tsaka da rarrashinta su ka ji yo dirar motoci a cikin gidan.

Jikinta na kerma ta mike tsaye ummi na tambayarta ina zataje tace"Su daddy sun dawo zataje gurin su"

"Batool taimaka mata ku tafi, kwarama da suka dawo watakil idan shi ya yi maki magana asamu ki ci abincin"


Fitowar su daga dakin yayi daidai da shugowar su falon.


Taj ne Agaba kan wheelChair dinsa Sai faman gungurata yakeyi, Chief da sheikh Imam suna abiye da bayansa A masallaci suka hadu da shi bayan sun kammala sallah Anan harya yai mamakin ganinsu yace ashe sun dawo sau uku yana zuwa gidan neman sa saidai ace mashi baya nan ya kuma tambayi meya faru da su? Ganin rauni a kafar Taj, Chief yace in ba damuwa yazo su tafi gida sai su karasa magana acan.


Takun tafiyarsu ne Yaja hankulan su Chief ga kallon direction din da suke, kaitsaye idanunsa suka sauka a cikin nata, kayan jikin ta sunyi mashi kyau.

Karasowa sukayi Cikin girmamawa suka gaishe da sheikh Imam


Kasa amsawa yayi saboda hankalinsa daya tashi ganin goshinta a nade da bandage, ta rame ba kamar yadda yasanta ba ita.

"Subhanallah, Unaisah meke damunki"? Murmushi tay,

"Bani da lafiya, amma naji sauki"

Chief yace"mu karasa ciki" gaba daya suka nufi falon kowa ya samu guri ya zauna, Ummi tana a labe bakin kofar dakin su..

"Chief, Hankalina ba akwance yake ba, Inaso nasan meya faru daku? Farmakin da kuka je kaiwa anyi nasara ko kuwa? Naga Taj da rauni a kafa, ga Unaisah ma ba lafiya, kaima haka naga ciwo a goshinka, Sannan Ina sauran yaran suke ne"?

aruWe ya tambaya yana dubansu.

Gyaran murya Chief yai kafin ya soma magana calmly.

"Ba zamuce bamuyi nasara ba, Alhamdulillah munci rabin yakin munga tasirin addu'a, abubuwa da dama sun faru masu dadi da marasa dadi..."dan dakatawa yai yana kallon Unaisah dake a zaune gefen daddynta ta daura kanta saman kafadarsa lumshe idanun ta tayi don batason jin karashen zancen na shi.

"We lost Danish, Salsabeel ya samu karaya a hannunsa, Umar has a brain injury, gaba daya an kwantar da su a asibiti, su Commender ma Sunyi rashin daya daga cikin sojijin su, sauran yaran suna a part din Taj..."


Muryarsa na rawa ya furta"danish Ya mutu ne"?

"Bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, saboda bamu ga gawarsa ba" tashin hankalin da damuwane tsantsa akan fuskar Sheikh


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login