Showing 240001 words to 243000 words out of 391264 words

Chapter 81 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2653

littafi idan Mun Wora.
"Don't lie to me, Nasan ba halin ka bane"



"Why should I lie? If I don't want to tell the truth, I'll just shut my mouth." fuskarshi adaure yayi maganar.



Jinjina kai chief yayi"sunayen su fa? Ka sani"



Shiru yayi bai tanka mashi ba, hakan na nufin yasani baison fada mashi.



Bai matsa mashi ba Har cikin ran shi baiji dadi ba, daurewa yayi ya canza mashi wata tambayar.



"Ina so ka fadamin komai dangane da gidan kurkukun ?addara, da kuma abunda ake aikatawa a cikin sa"!



Wani kallo Danish Ya jefa mashi mai wuyar fassaruwa, A kalla sun shafe mintuna Danish bai amsa mashi tambayarba, kuma bai da niyar amsa mashi.



Jikinshi yayi mugun yin sanyi, bai ta6a zaton zaiyi mashi haka ba, duk irin yadda ya aje girman shi Ya kaskantar da kai agurinshi duk don ya samu ya basu hadin akai ashe shi ba ayi mashi gwanin ta.



Cikin karyayyar murya ya furta"Ka yi shiru ba ka amsa min ba ko baka ji me nace ba"? Kawar da kan shi gefe yayi alamar bazai amsa mashi ba



Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
Softy chief yace"kada kayi min haka, idan ka fadamin ba iya mu zamu amfana ba, ku ma zaku amfana, Danish baka da burin daukar fansa akansu? Meyasa zaka rufa masu asiri? Mutanan da suka raba ka da iyayenka tun kana jariri suka sace ka, bayan haka suka tauye maka hakkinka na rayuwa tun baka mallaki hankalin ka ba, idan ma kana yi masu kallon iyayen ka masu kaunar ka toh ka dauna, Yakamata ka farka Danish! Mutanan da kake gani amatsayin wani naka basu ta6a sonka ba, sun raine ka ne saboda biyan bukatar kan su, duk ranar da ka mutu zasu manta da kai ne, tsawon shekara ishirin suka kuntata rayuwarka sun cutar dakai sun kuma raba ka da iyayenka saboda tsabar zalunci, kai baka tunanin ina nasu ya'yan suke? Nasan ba lallai kayi wannan tunanin ba amma inaso ka sani wallahi suna da ya'ya suna acikin mu suna rayuwar yanci cikin kulawa da gatantawar su, kai kuma sun wulakanta ka da sauran yan uwanka" a faWace ya faWa yana duban shi.



"Rayuwata ba ta ta6a burge ka ba? Lokacin da ka shigo cikin mutane amatsayin wanda baison komai ba, shin baka yi tunanin sun yaudare ka ba? Ya tambaya rai abace yana kallon shi, Maimakon yaga rauni atare da shi saima yaga ko ajikin shi, maganganun chief basu karya mashi zuciya ba, su Taj dake kallonsu duk sun fahimci hada jahilci ke damun Danish, Elders sun kashe mashi rayuwa sun yaudareshi ta yadda bazai iya gane cutar da shi sukayi ba. Sun riga da sun yi mashi hudubar su, sun gatanta shi sun nuna mashi cewa su kadaine gatan shi a duniya.





"ba gaskiya kake faWi ba, they've never hurt me. Suna sona kuma sune iyayena, bayan su bani da wasu iyaye a duniyar nan"



bai ?are maganar ba chief owais daya gama harzuka rai a6ace ya Waki gaban table din ko gizau Danish bai yi ba.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.


Muryarshi a kausashe Ya furta"kai wani irin bauWaWWan mutunne? Baka da tunanine? Ko bakasan ciwon kanka bane? Tayaya ina kokarin in fahimtar dakai kana kauce hanya? Meyasa kake yaudarar kanka? duk abunda mu ke yi munayi ne saboda mu daukar maku fansar cin zalunku da akayi mu kuma ceto rayuwar sauran yaran da ke a hannunsu sannan mu kawo karshen miyagun da suka kafa kurkukun ?addarar! Kai kadai zaka iya taimaka maka Danish! Don haka dole ka bamu hadin kai..." Ran shi yakai makura agurin 6aci baima san yayi mashi tsawa ba. idanunshi sun kaWa jawur saboda bai ta6a neman abu agurin wani ya rasa ba Danish shi ne mutun na farko da yayi rejecting din bukatarsa.



Jami'an dake kallonsu sun harzu?a Musamman big guy Yafi fusata ganin yadda Danish ke wahalar da chief duk basu ji dadi ba



Ga mamakinsu murmushin gefen fuska Danish yayi tare da furta"I'm respecting you, so please don't pressure me. If you want peace with me, stop asking about the prison of destiny and stop insulting the elders, bayan haka inaso ku sani bazan ta6a baku hadin kai ba indai akan su ne, saboda ku ba kowa bane agurina, ban hada alakar komai daku ba, duk da bani da ilmi amma nasan me na ke yi, Ina da hankali baku isa kuyi min wayau ba yan uwana kadai na sani su kadai zan bawa kariya kuma ina tare dasu babu wani wayau da za ku yi min"



Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
maganar Danish ta yi matu?ar daure masu kai, Hankulansu yayi mugun tashi, gaba Waya chief ya rasa bakin magana saboda Danish Ya sagar mashi da gwiwa, yanayin fuskarshi ya nuna tsantsar mamaki da al'ajabi gaba daya ya fara sare da lamarin shi.



"Zan iya tafiya" ya fada yana kallon fuskar chief dake kallon shi kamar gunki haka Ya kame sam ya kasa magana, idan har ya biyewa zafin zuciyarshi ba karamin faWa zasuyi da junan su ba, sai dai bazai ta6a biye ma shi ba saboda shi ba ajin yin shi ba ne, bayan haka yana yi mashi Uziri duba da irin rayuwar daya taso still akwai tsantsar tausayin Danish a cikin zuciyar shi.



bai jira Amsar da chief zai ba shi ba, Ya mi?e Ya nufi hanyar fita daga room Win, yana ru?e handle din kofar yaji ta adatse.



juyowa yayi tare da kallon chief, bawan Allah Ya dafe kan shi da tafukan hannayen shi, tsabar bacin rai da takaici ne ya addabe shi, wata irin zufar 6acin raice ta fara tsastsafo mashi, la66ansa har kerma suke shima sam bai iya fushi ba, zuciya ce da shi.



"Ka buWe min kofar zan fita" babu wasa akan fuskarshi yayi maganar



A fusace chief yace"I'm not done talking to you! Come back and sit down. If you don't answer my questions, we'll spend the whole day here."



kwatsam Yaji alamun buWe kofar, aruWe ya Wago yana kallon shi yayi mamakin yadda ya iya bude kofar bayan computer ce ke controlling din ta, dole saida izninsu kofar zata buWe.



har ya Waga kafa zai fita kenan chief ya yi hanzarin mikewa ya bi bayanshi yana isa gaba daya ya faWa kan bayanshi yayi hugging dinshi tighly kamar zasu koma mutun Waya.



Cikin rauni na murya ya furta"Danish, I'm really disappointed in you.You embarrassed me, I never thought you'd do this to me you're hurting the heart that's trying to save your life. ban ta6a zaton za ka yi min haka ba"



ya faWa yana jan numfashi haWi da ?ara cusa jikin shi ana Danish, wlh tsabar bacin rai ne yasa shi yin hakan saboda gaba Waya ya fara sarewa da lamarin shi, kafin su baro gida adakin Danish sai da ya ro?e shi akan ya ba su hadin kai yace mashi ya amince amma sai gashi yanzu ya bijire ma su, Bai ta6a zaton zai kunyata shi ba.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.


Rungumar da chief yayi mashi ba karamin kashe mashi karfin jikin yayi ba, Zuciyar shi taso ta karaya sai dai baya jin zai iya amincewa da su, kalaman chief sun tsaya mashi aranshi sun kuma sanya mashi kokwanto a tunanin shi, ga wani irin yanayi da yake ji mara misaltuwa atare da shi yana ji kamar suna da connection da chief, sam ya kasa ta6u ka komai yanayin fitar numfashin shi sam babu kwanciyar hankali.



Lumsassun idanunshi ya Waura akan hannayen chief daya dafe flat tommy din sa, Har cikin ran shi baiji dadin bijire ma shin da yayi ba, baisan ya akai yake jin mutumin aran shi ba, Yana matu?ar ?aunar Chief baya son bacin ran shi.



Komai dake faruwa akan idonsu big guy, sun yi shiru suna jira suka ga martanin da zai mayar wa chief.



A hankali Danish ya daura tafukan hannayen shi akan na chief ya dam?e su sosai yana mai jin wani irin yanayi mara misaltuwa, In a weak voice Ya furta"Ka yi hakuri, bazan iya ba ku hadin kai ba, pls kada ku tursasa min akan abun da banyi niya ba.." yana faWan hakan ya 6an6are hannun chief daga ru?on da yayi mashi ya fuce daga dakin, wani irin jiri ne ya kusa Wibar shi da sauri ya dafe ?ofar da tafin hannun shi.



Da ?arfi Big guy ya ture kofar Observation room Ya futo Yana huci Ya nufi Danish dake kokarin komawa gurin su Sajeed, da sauri sauran Jami'an dake a tare da shi suka biyo bayan shi ganin yadda ya fusata, sun san halin shi yana da bad temper.



Taj dake abiye da su hankali atashe Ya ke danna wayar sa layin Salsabeel ya kira cikin sa'a ya Waga ko sallama baiyi ma shi ba ya faWa mashi abunda ke faruwa, salsabeel ya zabga salati dama sai da yai fargaban faruwar hakan, saboda shi yasan wanene Danish, mutum ne mai kafiyar tsiya ga girman kai da rashin yarda.



"Yanzu haka ina acikin head quarter din, wallahi nasan za'a rina shiyasa na yanke shawarar zuwa saboda shi" acewar salsabeel bayan sunyi sallama taj ya mayar da dubanshi ga big guy wanda tuni Ya cimma Danish wani irin kukan kura yayi tare da kai hannu Ya dam?i kwalar rigar shi, Jami'an dake a kewaye da su suka rurru?e hannun big guy suna kokarin su raba tsakanin su.



Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana, Kusan atare su Unaisah suka mi?e idanunsu azazzare suke kallon su cike da faduwar gaba.



Da wata irin kakkausar murya ya furta"Who the hell are you? Wan uban wanene kai a kasar nan? Me kake ta?ama da shi ne huh? Kana da wani gata ne daya wuce Allah da shi chief din ne? Saboda tsabar rainin wayau yana magana kana amsa mashi da gira tsaran wasan ka ne shi"? Ya faWa yana bin shi da wani ?as?antaccen kallo, big guy irin bauWadWun mutanan nan ne masu saurin fushi, wani lokaci sai daga baya su yi dana sani, shiru Danish ya yi batare daya tanka ma shi ba.



Big guy yaci gaba da fadin"Da kasan wanene chief da ba ka yi mashi haka ba, in ba dan aikin shi ba kai ka kai matsayin da zai kula ka ne? Ka rasa wa zaka yi disrespecting sai mutun mai kima da daraja a idon mutane, mutumin da ya ke hana idon shi bacci don ya taimaki rayuwar al'umma, mutun mai tausayin da jin ?an na ?asa da shi..." ya faWa A harzuke Yana kallon cikin idanun Danish wanda yayi kasa?e yana kallon shi, karfin halin mutumin ya bashi mamaki yadda ya dam?i kwalar rigarshi batare da jin shakkar yin hakan ba.



"Sir, ka yi hakuri ka daina yi mashi faWa, me zai hana mu lallashe shi ni inaga idan muka bi shi ta lallama zai bamu hadin kai kodan abunda muka ji wurin yan uwanshi dole muyi mashi uzuri" CI ne yai maganar cikin kwantar da murya



Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
Agent zahra Yace"sir Please, ka kyale shi, He's still young, it's not your place to argue with him, He doesn't know anything, We need to persuade him gently." cikin tausasa murya ya faWa yana kallon fuskar Big guy tamkar baisan suna magana ba Ya haWe rai ba annuri ko kaWan akan fuskar shi.



Dafa kafaWar shi COO yai"Allah Ya huci zuciyar ka Yalla6ai, mu kan mu bamu ji dadin abun da yayi ba amma yakamata muyi mashi Uziri saboda baisan komai ba..."



bai kare maganar ba Unaisah ta fashe da matsanancin kuka, kamar jira su Batool su ke ta fara kuka suma suka fashe da kukan gaba daya sautin shesshekar kukan su Ya karade kunnuwan jami'an dake agurin, tsabar tashin hankaline Yasa suka fashe da kuka dama tun da suka fito daga dakin tambayar zuciyarsu araunace take saboda raunin da aka fama masu



ga kuma wani tashin hankalin da suke kallo duk da basu san meya faru ba amma sun fahimci Danish ne yayi wani abu badai dai ba.



"OMAR, pls ya isa haka! Ka sake shi, nayi magana da Salsabeel awaya ya faWa min yana acikin head quarter din yanzu zai shigo"



idanun shi jawur Ya dubi Taj a fusace Yace"Taj I won't let him go. He must return and answer the chief's questions, ya 6ata min rai ya rasa wazai disga sai chief din mu? Tsaran wasan shi ne? duk kokarin da ya ke yi akan su shi baya gani ne? Ni bana son mutun mara Wa'a irin shi ..."



Ya fada tare da cije le6en shi ya maida dubanshi ga Danish wanda tuni Jikin shi Ya fara kakarwa wata irin zufar 6acin rai ce ta fara tsatstsafo mashi, Numfashin shi ya fara hauhawa yana fita cikin sauri, lokaci daya temperature din jikin shi ya Wau wani irin zafi, idanun shi suka rune zuwa Ja.



"Yaya Omar dan Allah Ka sake shi, nayi maka alkawarin zan shawo kan shi" cikin shesshekar kuka Unaisah tayi maganar



Haris yace"dan Allah Ya Omar ka ?yale Danish, Idan laifi yayi maku ku yi hakuri zamu fahimtar da shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya yi hakuri Ya saki Danish



Adaidai Lokacin da Salsabeel Ya faWo arean da suke yana faman wurga idanu don ya gano inda suke kwatsam idanun shi suka sauka akan gungun jami'an da su ka kewaye su.



Gaban shi ne yayi wani irin faduwa aguje ya nufe shi har yana bangaje jami'an dake sintiri kamar mahaukaci haka suke kallon shi



Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
Yana ?arasawa ya sanya karfi ya raba tsakanin big guy da Danish Yana faman haki ya dubi Danish wani irin faduwar gaba yaji ganin sa6ar majici akan wuyan shi babu wanda Ya lura da sabar sai shi da Allah ?addara zai ganta, wahalallan Yawu ya haWiya la66anshi na rawa ya furta"Danish, please...don't. Please, Danish, try to control your anger.."



gaba Waya jami'an sun ruWe da ganin yadda Salsabeel ke lallashin shi, Musamman Big guy ranshi ya ?ara 6aci a faWa ce yace"meya sa ka ke bashi hakuri"?



Salsabeel bai tanka mashi ba saboda tashin hankalin da yake tunkaro su batare da su sun sani ba, In har evil heart dinshi ta motsa zai rikiWa ne ya canza halitta, ya tarwatsa head quarter din gaba Wayanta ba ?amar 6arna zai yi ma su ba.



Da hannu ya dafe saitin zuciyar Danish, Ya marairaice mashi fuska tare da girgiza mashi kai alamar A'a...



gaba daya jami'an sun kasa fahimtar me Salsabeel Ya ke nufi!





Wani irin dogon numfashi Danish Yaja cikin zafin nama Ya bangaje hannun Salsabeel daga kan kirjin shi yana faman fitar da huci mai zafi ya mi?i hanya, aguje su Unaisah suka bi bayan shi suna kwala mashi kira ko kallo ba su ishe shi ba, bai sha wahalar gano kofar da suka shigo Soc din ba Ya fu ce daga ciki Ya nufi main enterance gate na head quarter din.



Kafin karasawar shi big guy ya kira layin Waya daga cikin jami'an dake tsaron gate din Ya basu Umarni karsu kuskura su bar shi Ya fita.



Lokacin daya karaso Yana tafiya kamar baya acikin hayyacin shi, hankulan jami'an dake sintiri gaba daya ya dawo kan shi, fisatattun jami'an dake tsaron gate din suna ganin shi suka gane shi ne matashin da aka basu umarni karsu bari ya fita, aikuwa azafafe suka yi mashi ?awanya kamar zasu rufe shi da bugu.



Yan uwanshi sai kuka suke suna ambaton sunan shi hadi da yi mashi magiya akan ka da ya tafi ya bar su, babban abunda suke ma fargaba in ya fita ina zai dosa?



Dakyar chief ya iya lallashin zuciyarshi cike da rashin ?warin jiki ya fito daga Wakin Ya nufi su big guy dake atsaitsaye curko curko sun kasa kunne suna sauraron Bayanin da Salsabeel ya ke yi masu dangane da Danish





"Ga chief nan" taj ne Ya fada kusan atare suka kai duban su gare shi, damuwa ce karara akan fuskar shi.



Bawan Allah da buWar bakinsa sai cewa"Ina Danish? Ina sauran yaran"? Kafin wani daga cikin su Ya bashi amsa sautin ringing wayar big guy ya katse hanzarin su

Da sauri Ya kara wayar a kunnan shi.



Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
"Sir, Yaron nan fa Ya fita! Mun yi kokarin mu dakatar da shi amma mun kasa, gaba Waya ya watsar da jami'an da sukai kokarin hana shi fita..." a kidime Big guy ya furta"what? Ya fita! Garin yaya hakan ta fadu"?



Wani irin faduwar gabane Ya Warsu a zuciyoyin su, sunyi matukar mamakin jin hakan shin tayaya akaima har ya iya fin karfin jami'ansu Ya fuce daga head quarter din?



"Yaran suna nan, amma Waya daga cikin ?an matan mai launin ido ruwan toka ta kubce mana, yanzu haka wasu daga cikin jami'an mu sun bi bayan su"



Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, Salsabeel bai tsaya yaji karashen zancen ba, Ya watsa aguje Ya fuce, Agaggauce Senior agents din suka rufa mashi baya, ya rage saura big guy da chief atsaye suna fuskantar juna



"Meya faru Omar? Meyasa Ya tafi? Wani ya 6ata masa rai ne ko abunda ya faru tsakanin mu ne"?



Dakyar big guy yai karfin halin zayyana mashi abunda ya faru bayan fitowar Danish



Girgiza kai yayi cikin sanyin murya yace"meyasa Omar? Meyasa zaka yi mashi haka? Kamanta wanene shi? Yaron da bai san komai ba yanzu daka bata mi shi rai ina kake tunanin zai dosa? Wa ya sani agarin nan"?
Saurari Littafin >>>>Kurkukun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login