Showing 198001 words to 201000 words out of 391264 words

Chapter 67 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2652

aunty ummi ki kira mana ita mu gaisa, ko hankalinmu ya kwanta" tayi maganar tana kallon Ummi, gaba Waya hankalinta yana akan wayar hannunta da alama chatting takeyi batasan ma me suke cewa ba..



"Dama kun daina wahalar da kanku gurin yi mata magana, saboda hankalinta ba akanku yake ba.." acewar Parvin.



Waga murya batool tayi"Aunty Ummi..." aWan firgice ta Wago da ido tana kallon ta"batool! Lafiya kike kwala min kira kamar baki san ina akusa ba"? Dariya su naufal sukayi

Batool ta marairaice mata fuska"aunty ummi muna ta yi maki magana kin yi shiru baki amsa mana ba.." maida hankali tayi akansu



"Okey, Ina sauraronku lafiya"?



Kafin wani ya furta magana acikinsu ba zato ba tsammani, sallamar Unaisah Ta katse masu hanzarin su, kusan atare suka mi?e da gudun gaske suka nufeta hada masu tuntu6e garin sauri, Batool ce ta fara karasawa gareta ta faWa jikinta suka rungume juna kamar zasu koma mutun Waya sai faman tikar dariyar murna sukeyi, gaba Waya sukayi mata rumfa kamar zasu lasheta yadda kasan sunyi shekara basu ganta ba,

Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su Waya bayan daya tayi hugging din yan mata, sajeed Ya buWe hannu zai rungumota tayi saurin ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi saboda gudun kada ta samu ciki.





*_______________________________Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*







Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su Waya baya daya tayi hugging din yan mata, sajeed ya buWe hannu zai rungumota tayi saurin ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi, gani take kamar ciki zai shiga, har naufal ya kai hannu zai yi hugging dinta again ta ?ara ja da baya hadi da girgiza kan ta, mamaki ne ya kama su Naufal ganin yadda ta hana su ta6a ta kamar taga wani mugun abu.



"Meyasa mu bazaki rungume mu ba, ko bakiyi kewarmu ba"? murmushi ta sakar masu"kuyi hakuri ba haka bane, nayi missing dinku gaba Wayanku.." girgiza kai sajeed yayi ni ban yarda ba Allah, naufal yace"kinfi son su batool shiyasa kika rungumesu ko"? Javed ma yace"ni banji dadi ba, wariya kike nunawa atsakanin mu.." gwalo parvin tayi masu, Sarah tace"nan fa ba prison bane, mun riga da mun gane jinsin mu, ku maza mu mata don haka kuyi hakuri no more hugs atsakanin mu ehe" dariya suka sanya.



Batool tace"bayan haka aunty ummi ta fada mana babu kyau mace ta rungume namijin da ba muharramin ta ba, koda ruke hannunsa ne" wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Unaisah dake sauraronsu taji dadin yadda suka fara gane abunda ake koya masu.



Gaba daya kalamansu akan kunnan chief dake abakin kofar shigowa falon maganar Batool ta faranta ranshi dama yajima yana son a fahimtar dasu game da mannewa juna da sukeyi amma yanzu alhamdulililah sun fara hankali



Mubeen yace"amma ay a prison mu na yi kuma baku ta6a hana mu ba"

Harara Parvin ta watsa mashi"ay lokacin muna a jahiliya period ne, yanzu kan mage ya waye..."



maganarta ta basu dariya, fashewa ummi tayi da dariya ashe tana tsaye abayansu.



Unaisah na ganinta tayi sauri nufarta suka rungume juna

"Oyoyo my babe Unaisah, welcome back home munyi kewarki abar kaunarmu"



"Nima nayi kewarku aunty ummi fatan na same ku lafiya..." ta fada tare da dago da kanta



"Lafiyalou Unaisah, ya jikin patient din? Ko har an sallame ta"!



"Yau za'a sallame shiyasa na taho gida, taji sau?i sosai, tama ce in gaishe mata da ku" murmushi ummi tayi"Allah sarki muna amsawa, wlh naji dadin samun lafiyarta..."





Kallon su Naufal tayi sun haWe fuska babu annuri duk don saboda ta?i hugging dinsu, jemimah ta tuntsire da dariya tana fadin wai ma haushi suke ji don kinki rungumarsu jibar su ma kattai da su.."bata ?are maganar ba, Sajeed Ya tallabi keyarta nan take ta fara ta6e baki zatayi kuka,

Naufal Ya Waga hannu zai buge bakin da sauri ummi ta ru?o hannun shi tana dariya tace"ya isa haka pls, wasa takeyi maku"



"Pls Angel, To mu gaisa da hannu" Sajeed Ya fada tare da mika mata hannu shi, shiru tayi jimm har ta mi?a hannu zata ruko nashi ba zato ba tsammani chief ya shigo falon yayi hanzarin daura hannunshi akan na Sajeeed, gaba daya suka shiga nutsuwarsu sam basu san da zaman shi ba.



cikin girmamawa suka fara gaishe da shi, ummi ma ta gaida shi ya amsa mata, Sajeed baki ya ki rufuwa saboda sunyi musabaha da chief, ya?i sakar mashi hannu.





"Pls chief can you hug me"? ?aga mashi gira chief yayi tare da yin huggin dinshi, wani irin dadi ya lullu6e shi.



"Nima pls" acewar Naufa, mi?a mashi hannu yai da sauri naufal ya rungume chief harwani bude hanci yakeyi yana shakar kamshin turaren shi



Kunya ta hana Haris yin magana, lura da hakan yasa chief mika mashi hannu da sauri ya matsa kusa da shi suka rungume juna, bayan ya saki haris Ya rungume javeed da mubeen wayyo dadi, tsabar murna kamar anyi masu albishir da gidan Aljanna, Ummi sai satar kallonshi takeyi saboda kyan da yayi mata, kai ko amafarki bata ta6a tsammanin zata haWu da chief face to face ba sai gashi cikin ikon Allah ?addara ta haWa ta zama da shi agida Waya, ta yaba da hankalinshi, nutsuwarshi, wayewarshi, saukin kanshi da ilminsa komai Allah Ya bashi uwa uba ga tarin Dukiya.





Gaba Waya yan matan sun Waure fuska, ganin su naufal sun fara yi masu gwalo saboda chief ya rungumesu..." bubbuga ?afa Jemimah tayi muryarta da shagwa6a tace"wayyo Allah, mu ma dan Allah yaya chief ka rungumemu..." dariya sajeed yayi tare da cewa"no bazai rungumeku ba, jinsin ku daban namu daban, kowa ya rungumi jinsinsa koba haka ba guys"? Ya fada cike da shakiyanci yana kallon su Javed,

Naufal yace"haba kamar dai a jahiliya period? ay haramunne na mijin ya rungume mace, nan fa ba prison bane kan mage ya waye.. " gaba Waya suka tuntsire da dariya, Unaisah hada dafe ciki, chief dake atsaye ya goya hannayenshi kan kirjin shi, idanunshi na akan fuskarta wani irin kallo yake binta da tashi ta saki baki tana ta dariya f??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????araren hakoranta tass da su bata ta6a jan hankalinshi irin na yau ba.. Babu wanda Ya lura da irin kallon da chief yakeyi mata gaba daya ya shagala

A hankali ya kau da idon shi Ya juya Ya nufi part din shi.



"Wallahi inason ku yan uwana, kuna faranta min raina, Allah yabarni daku, wallahi mai rabani daku sai Allah, shiyasa naketa zumudin in dawo gida saboda nasan anan ne kadai zan samu farin ciki da kwanciyar hankali...." cikin jin dadi tayi maganar,

Ummi ta ruko hannun"mu shiga daga ciki, mun barki atsaye.." gaba Waya suka nufi Sofas din falon, kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, shi dai sajeed kalmar muharram ta tsaya mashi arai, so yake yaji wanene muharramin nan da shi kadai zai iya rungumar mace, abun da bai sani ba ita kanta Batool din batasan wanene muharram ba, tabbas ummi ta ta6a faWa mata amma karatun bai zauna akanta ba.



"Kinyi breakfast acan asibitin" cikin kulawa ummi tayi mata maganar,

"Eh, nayi" labari ta fara basu na Benazir duk suka kasa kunne suna sauraranta

"Matar tana sona nima ina sonta aunty ummi, mun shaku da juna, har grandma dinta muna mutunci da ita dayake adaki daya muke kwana kuma kinsan wani abu aunty ummi.." girgiza mata kai tay alamar a'a



"bata gane cewa ni ba yarta bace, bansan wani hali zata shiga ba idan ta farka daga bacci taga bani akusa da ita..." cikin sanyin murya tayi maganar.



Ummi tace"baiwar Allah, wallahi ta bani tausayi, ubangiji Allah Ya bata lafiya, inayi mata fatan Allah ya bata wata yar" suka amsa mata da ameen



"Wani abu daya bani mamaki aunty ummi, matar tana kama da Batool yadda kikasan ita ta haifeta Allah..." murmushi ummi tayi, batool ta washe baki jin an ambaci me kama da ita"wallahi har naji ina son ganinta" murmushi unaisah tayi"hmmm ai ba ita kadai ke kama dake ba, ranar dana fara ganin yayanta dr shureim saida na Wan razana, yadda kikasan yayi kakinki, ke gaba dayansu kamar family dinki ne..." wani irin faduwar gabane Ya darsu a zuciyar Ummi, sunan dr shureim da Unaisah ta faWa ya tsaya mata aranta.



"Dan Allah daske kike? Acewar batool,

"Wallahi dagaske nake, Allah ya zuba masu ruwan kyau, grand ma dinta balarabiyace..."



dafe kai ummi tayi da hannu Waya, gabanta na cigaba da faduwa.. Gaba daya sun lura da yanayinta,

"Aunty ummi lafiya" da sauri ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace ba komai unaisah, can kuma tace.



"Unaisah, kikace sunan yayanta dr shureim! Ita kuma Ya sunan ne"?







Murmushi Unaisah tayi kafin tace"Aunty Benazir" ummi tayi jimm kamar mai nazarin wani abu.





"Namanta ban fada maku, wani abun farin ciki daya faru ba.." har suna hada baki wurin furta"menene" dariya ta danyi kafin tace"kun tuna auntyna da nake yawan baku labarinta a prison" kallon juna sukayi batare da sun iya gano wacece ba.



"Duk wanda ya tuna sunanta zan bashi kyauta ta musamman" ta fada cike da nishadi



Nan fa suka fara canki canka,

Hawwa tace"na tunata, sunanta Aunty adama" girza kai unaisah tayi"a'a ita wannan mommy adama take"



"Kamar aunty bahijja ne" acewar hibba, dariya unaisah tayi"no ba haka sunan yake ba"



Sajeed yace"Sunanta aunty laila" dariya unaisah tayi"no ba haka bane Allah indai baku fada ba, bazan baku tsarabar da nayi maku ba.." ta fada tana karkaWa kafarta gaba Waya kamar ta manta da zancen Danish kamar an goge mata tunanin shi a brain dinta.



"Sunanta Aunty Aneelerh, indai ba haka sunan yake ba to kuyi min dundu abayana" dariya Unaisah tayi tare da kallon batool"kin canka dai dai, aranar kafin in bar gida kunsan meya faru...."? Girgiza mata kai tayi, nan fa tafara basu labarin zuwan aunty Anila ko gajiya batayi, sai surutu takeyi kamar parrot, gaba daya hankalin ummi baya atare da su, kamar bata acikin nutsuwarta har saida kunnuwanta suka jiyo mata muryar Unaisah tana fadin"ashe ita aunty aneelerhn kawar aunty Benazir dince, atare mukaje asibitin abun da ya farantamin rai Aunty Aneelah ta haifa min dan kani sunan shi baby junaid, tama yi min alkawarin zata kawo min shi har gida..." wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Su Batool.



"Wayyo Allah Angel maimakon ta shigo mu gaisa da ita, meyasa baki fada mata irin kaunar da muke yi mata ba.." parvin ce tay maganar, batool tace"Yaushe zata kawo mana Wan kaninmu junaid mu gan shi, wlh munji dadin haduwar ki da aunty Aneelerh, saura muma mu hadu da ita amma dai zatazo nan ko"? Daga masu kai tayi"don ma namanta ban kar6i number dinta ba, amma zan ma daddyna magana nasan bazai rasa layinta ba"



"Unaisah! da sauri Ta kalli ummi na'am



"Wai ni kam dama can anan abuja kuke zaune keda daddynki"? Girgiza kai tayi"a'a a joss muke" gaban ummi ne ya ?ara faduwa, karfin hali tayi wurin furta"okey, amma ita auntyn naki Aneelerh, ya kike da ita ne? Ta fada cike da son jin karin bayani



"Matar uncle dina ne Uzair"



Shiru ummi tayi bata kara yin magana ba



Motsin shigowar mutun a falon ne Yaja hankulansu ga kallon kofar, Senior agent din da ya kai su Unaisah mall ne ya shigo hannun shi ru?e da shopping bags, ya goyo backpack dinta abayan shi, mi?ewa tsaye sukayi suna jiran ya karaso

A tsakiyar falon Ya ajiye mata shopping bags din kafin Ya sauke backpack din bayanshi ya ajiye ta"i'm sorry na tsaya amsa kira ne"_ murmushi tayi tare da cewa nagode sosai"

Yace"Never mind" ya fada tare da juyawa ya fuce daga falon

Gaba Waya suka zagaye bags din suna kallon su ummi tace"tsarabar mu ce wannan"? Unaisah tace"eh nakune, nima akwai nawa ciki"



Zukunnawa ummi tayi agaban shopping bags din A hankali ta fara curo kayan tana ajiyesu kan rug, su Azeeza sai tsalle suke suna murna ganin cookies da chocolates kala kala dama mayinsu ne, kamar shazu mamu suke wurin shan zaki.



Tun kan aje ko'ina suka fara kokarin kai hannu zasu Wauka, ummi tace su tsaya ta raba su.



"Unaisah wadannan uwayen kaya haka? Wanene ya siya maki su? da mamaki ta fada tana kallon fa.."



"Atare da chief mukaje shopping mall, bakiga wurin ba ya hadu, ni fa bani na zabi kayan ba, shi yace mutumin daya kawo kayan komai yaga idanuna sun kalla ya daukar min shi ko da mara amfani ne" jinjina kai ummi tayi cike da mamakin maganar ta maida dubanta ga kayan, gasunan tili guda.



ta fara Waga kayan tana ambaton sunayen su a fili, Fragrance set, hair accessories, gel nail kit, skincare set, jewelry box, lace robes, slippers, diary with a lock and key, throw blankets, shaving kit, smartwatches, earbuds, sports jersey, bluetooth speaker, da sauran su ga Writting material kala kala, can idon ta ya hango mata bras har kala uku da yan panties biyu, dagowa tayi tare da kallon unaisah baki asake tace"waWannan fa"? Dariya Unaisah tayi tare da sunnar da kanta ?asa wata irin kunyace ta kamata"wlh Aunty Ummi bansan hada bras acikin kayanba, sune suka daukarmun" dariya ummi tayi"ah toh ni dama nasan bada saninki ba, wannan ay sai dai Batool duk da bansan size dinta ba amma nasan zasuyi mata, ke kuma saiki bari in naki sun kara cukowa" gaba Waya su Naufal suka tsuntsire da dariya, daure fuska tayi rai a6ace take aika masu da harara, ummi tace"ku kuma meye nayi mata dariya kawai daga anyi abu cikin raha" kumshe dariyar sukayi



"Sorry my babe, kada ranki ya 6aci, ni da wasa nayi maganar" ta6e baki tayi tana faman wurga masu naufal harara.



Ummi tace"abun dai da yawa wlh, ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi.." ta fada tare dakai hannu tana kara dudduba kayan"suma dai waWanda suka daukar maki kayan sun iya taya 6era barna.."ta fada tana yar dariya.



"Hada phone, bayan kina da waya? Da sauri unaisah ta kalli phone box din"



Da sauri batool tace"dan Allah sister ki bani dama bani da waya..." saejeed yace nima inaso dan Allah, haris yace wlh na riga ku dan Allah ni za'a ba, rigima suka sanya da sauri unaisah ta Wauke phone box din, ta ru?e a hannunta, ummi tace"kin raba gardama, ki ajiyeta agurin ki" ta amsa mata da toh,



Kwashe kayan Unaisah da Ummi sukayi atare su ka maida su cikin bags din, ummi ta dibar masu chocolates da cookies ta rarrabamasu kowa ya buWe nashi yana ci, sauran tace"za'a ajiye su adakin unaisah, duk rana zamu dibi kaWan mu sha idan ba haka ba nasan ba zaku raga masu ba, duka zaku shanye su" amsa mata sukai da toh.



"Unaisah ke da Batool, Ku kwashe kayan ku kai dakin ku, ku ajiye su dakyau" atare suka amsa mata da toh, kafin suka fara kwashe jakukku nan suka kai su dakin su.



*UNAISAH ANGEL*



Around karfe biyu na rana, tana a kwance kan bed dinsu ta Waura kanta bisa pillow, ta Wan lumshe idanunta bakomai take tunani ba face Aunty Benazir, tun bayan data dawo gida hankalinta ya?i kwanciya ta damu da son sanin awani hali take a ciki? Meya faru bayan ta farka daga bacci?





"Ya Allah kasa kada aunty Benazir tayi kukan rashina, bana son tayi maraicina rashina akusa da ita! Zuciyarta ce ta raya mata me zai hana taje wurin chief ta tambaye shi awani hali Benazir din take a ciki tun da yar uwar shi.



da sauri ta sauko daga kan gadon, ta dauko mayafi ta yafa akanta, taje gaban Shopping bags din da suka ajiye ta Wauki Waya ta zazzage kayan cikinta a gidan drawer, ta Webi turare biyu ta hada da chocolates da cookies kala shida ta sanya a ciki tasan ma ba lallai ya kar6a ba, kawai tayi tunanin takai mashi ne.



Mi?ewa tayi hannunta ru?e da ledar da sauri ta fuce daga dakin atsanake take tafiya..



Adaidai lokacin Danish Ya fito daga bedroom din shi yana daga tsaye a second floor, ya sanya singlet da boxer shorts a jikin shi, ya dafe handrail da hannayen shi, yana bin down stairs da kallo kwatsam idanun shi suka hango mashi ita, kamar a mafarki Yake kallonta, kwata kwata baisan ta dawo gidan ba, saboda bai fito waje ba, yana adakin shi yana karatu bacci ya Wauke shi bayan ya farka ya shiga bathroom yai wanka hakanan yaji yana sha'awar fitowa waje yasha iska cikin ikon Allah yaci karo da ita...



Yaji dadin ganinta sosai, har saida yaWanyi murmushi dimples dinsa suka lotsa, ji yayi kamar yaje gurinta yayi hugging din ta ya faWa mata irin kewarta da yai, sai dai yasan ba abune mai yiwuwa ba, saboda sharuddan data gindaya mashi, kuma yayi alkawarin bazai ta6a karyawa ba, in har ba ita da kanta ta janye kudurinta ba.



Yanayin fuskarshi ne Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, zuciyar shi ta karaya ganin ta nufi upstairs kuma yasan bai wuci part din chief zataje ba, duk yadda ya kwallafa rai akan son ganinta amma ita bata damu da shi ba kamar ma ta manta da shi, da ace lokacin bayane kafin su samu sabani yasan shine mutun na farko da zata fara nema idan ta dawo daga wani guri.



Kifa kan shi yai jikin handrail din yana jin wani irin Waci aran shi....



Lokacin da ta je part din chief bata iske shi ba, sau uku tana yin knocking bai buWe ba, ranta ne ya bata ya fita hakan yasa ta juyo ta nufi stairs a hankali take taka matakalar, ranta ne ya bata kamar ana kallon ta, da sauri ta wurga eye balls dinta tana bin downstairs da kallon ganin ba kowa yasa ta maida dubanta ga second floor ganin zata ganshi yasa shi sauri juyawa ya buWe room door dinsa zai shiga tsayawa tayi cak da yin tafiya tana kallon bayan shi har saida ya shige..



"Danish" acikin zuciyarta ta ambaci sunansa, sam takasa karasa cigaba da tafiya sam ta manta da shi sai taji wani irin a zuciyarta kamar bata kyauta ma shi ba.



ganin shi da tayi yasa taji kewar shi ta mamaye ta sai dai bata jin zata iya zuwa gurin shi, ta san dalilin dayasa shima baizo gurin ta ba, saboda alkawarin da ya daukar mata, tun a prison tasan halin shi da ru?e alkawari in har ba ita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login